← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 94

Sashe 21

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 1️⃣2️⃣
Saida suka fita ta tsaya chak hakan yasa Shafa dasuke tafiyan tare tajuya takalleta, cikin fushi tanuna mata kogon tace “wai kinsan shi daga wani waje ne Farrah? Shi namiji ne Farrah ba kamar Yar uwanki datake mace ba, zai iya kare kanshi idan zasumai wani abu, banda ma haka ba yanzun nan agaban mu yay waya za’azo a daukeshi ba eh”? cikin kurmanci Farrah tanuna mata to su tsaya afara zuwa daukanshi kafin sutafi, zuciyanta yaki bata sutafi su barshi tausayinshi takeji sosai, sosai ran Shafa yabaci shiru tadanyi tanabin wajen da kallo sanan takalli Farrah tace “kinsan iya yawan abubuwan dakika fito dasu kiwo? Jibi chan saniya dayace kadai anan, Farrah so kike kisa kanki a matsala ko, meya kamata kiyi yanzu inace ba tumakan nan yakamata kije ki nemo ki tattarosu ki kada gida ba, kinsan wayanan dabbobin sune tattalin arzikin Inna na duniya da lahira ko, wlh ko kasheki tayi wanan karan bazan damu ba babu abinda yashafeni, karma kizo wajena kina kuka ni kinga tafiyata” tawuce zata tafi kaman ance Farrah takalli gabas su Oga ne dukansu hudun suka bullo dawani kalan bala’in sauri tasa hannunta ta fizgo hannun Shafa bama tajira mezata ceba tajata suka shiga kogon jikinta na tsuma, itama Shafan faduwa gabanta yahauyi sosai dan lokacin da Farrah ta fizgota ta hango mazan da bindigogi a hannunsu, kallonsu Zayn yayi ganin yanda suka shigo da gudu suna shaking hakan yasa yadafa bango da kyar ya mike tsaye ya kalli Farrah itama kallonshi tayi sanan ta gyadamai kai alamun eh sune, cikeda bala’in tsoro Shafa tace “sune Farrah?” Gyadamata kai Farrah tayi hakan yasa Shafa tace “kozo muyi sauri mu fice mu gudu karkaran mu muboye achan ni wlh banso na mutu yau” tai maganan tana hanyar kofa tafice dasaurin ta kallon Zayn Farrah tayi sanan tamai alamun yazo sutafi ahankali yabiyota abaya, ganin sun fito yasa su Oga suka hau gudu suma gudu sukahau yi Shafa agaba Farrah abayanta, Zayn abayan Farrah suna saukowa dagakan dutsen da gudun su, harbi sukahau yi amman cikin ikon Allah ko dayansu bai sama ba har suka karasa saukowa, ganin Zayn baya iya gudu sabida hannunshi yasa dasauri Farrah takama hannunshi ahankali ya kalleta daura hannun tayi a shoulder ta sanan tafara gudu shima Zayn na gudu Shafa na gabansu tana famfala gudu, su Oga na binsu abaya sun kusan cimmusu, juyawa Farrah tayi ta kalli bayanta, ganin Oga na saita bindiga saitin Zayn dake wani kalan haki yana gudu yasa dawani kalan sauri tasaki hannun Zayn tawani irin hankadeshi yafadi ta tare bullet din sai gefen kirjinta wani irin kara tayi ! bullet na nan ne kaman garwashi dake tattare dawuka mai kaifi, the pain is so sharp da saikaji kaman kabar duniya chak Shafa ta tsaya jin ihun Farrah daidai Farrah tawani irin faduwa akasa jini nawani kalan bulbulowa ta inda aka harbetan, juyowa Shafa tayi ganin Farrah azube akasa yasa tawani kalan Kurma ihu. “Kurmaaaaaaaa!” Sanan tawani taho kanta dagudu ta tsugunna shima Zayn dake kasa tashi yayi da sauri yana kallon Farrah da bala’in mamaki na she just saved him yama kasa tabuka komi sai rawan da hannunshi keyi kawai, murmushi Oga yayi yana tahowa cikin tafiya na kasaita yace “perfect haka ake harbi nakoya muku saiti nakoya muku amman abanza yau kun wasting bullets abanza a hofi” wani kalan rudewa Shafa tayi yanda taga jini na bulbulowa Farrah na tari yasa tasa hannu ta dumbuzo kasa ta maka akan ramin bullet din tana kuka takalli su Oga tace “Allah saiya kashe ku kuma azzalum……” bata karashe maganan ba sabida wasu kalan jiniyan motocin yan sanda dasukaji na tashi ata ko’ina sanan ga mutanen gari sun fara bullowa sabida karan harbin dasuka dingayi dazu ko’ina ya amsa, gakuma karan helicopters kusan uku dayasa su Oga suka kalkalli sama jikinsu nawani irin rawa, cikin ihu ganin mutane yasa Shafa tace “ku kamasu su yan sanda sukazo kamawa masu kidmashin ne” mazan gari suka yunkuro hakan yasa suka kwasa da gudu daidai lokacin motocin yan sanda na shigowa dajin, dan sunada device dake tracking bullet kaman magnet ne zai kaika wajen da akwai bullet, ga jirage nayawo asama, wani kalan ajiyan zuciya yasauke yana kallon yanda Shafa ke jijjiga Farrah dake tari har lokacin idanunta sunyi jajir suna fitarda hawaye, wasu manyan sojoji suka taho da microphone suna kiran sunan Zayn. “Zayn Ganuwa are you here”? Shiru Zayn yayi dan at this point iyayenshi kawai zai gani ya mike tsaye, helicopter su yasauka daga nesa sosai a filin, Mami dakuma Baban shi yaga sun sauko daga ciki, da Uncle, dawasu manyan Doctors ganin su yasa yamike tsaye ahankali yafara tafiya.

Daga nesa Alhaji yace “Innalillahi Zayn dina ne haka, Zayn” wani kalan fadawa jikinshi Zayn yayi ya kankameshi sai kuka ahankali, tsayawa Mami tayi a gefe tasa bakin gyalenta tana share hawaye ganin yaronta is fine, da kyar Alhaji yasakeshi sanan yay cupping fuskanshi yace “kowaye yamaka Wanan abun I will not rest sai justice yay taking place” gyadama Baban shi kai yayi sanan yasaki Dad yajuyo yakalli Mamin shi budemai hannu tayi hakan yasa yarungumeta ahankali ita tama kasa magana jin jikinshi zafi yasa tadagoshi kafinma tai magana Alhaji yakamashi yakalli Drs din yace “mu tafi sai su dubaka a jirgi” shida Baban shi suka wuce Doctors din suka bisu abaya, ajiyan zuciya Mami ta sauke sanan ahankali tadaga kafanta zata wuce kaman ance ta kalli wajensu Shafa dake jijjiga Farrah da idanunta ke kullewa idanunta suka sauka kan wasu yara biyu da dukansu ke sanye da kayan fulani daya na kwance akasa ga jini duk yabata riganta daya na rikeda ita tana kuka sosai dawani irin sauri Mami tace “Alhaji!” Tsayawa Dad yayi sanan yajuyo dasauri Mami tai wajensu Farrah ta tsugunna kansu takai yatsunta biyu ta taba gefen wuyan Farrah sanan tace “we have a gun short injury, bring first aid kit for me” Mami tai maganan cikin sauri tana ihu sanan takalli Shafa dake kuka sosai tace “kanwarki ce Ya akayi aka harbeta”? cikin kuka sosai Shafa tace “garin taimakon danku ne!” Chak Mami ta tsayar da abinda takeyi takalli Shafan, Gyadamata kai tayi cikin kuka sosai tace “tafito kiwo taga……..” nan takorama Mami labarin tassss wani iri jikin Mami yayi daidai one of the Doctors yakawo first aid kid, Ahankali tadago kanta takalli Zayn dake kallonsu yana tsaye tareda Baban shi sanan tasa hannu ta karbi first aid kit din tabude tawanke kasan da Shafa tazuba awajen tamata allura daidai Malam dashima yaji labari abinda ke faruwa awajen garinsu yataho wajen ganin Farrah ga likitoci akanta yasa da sauri yataho wajen yace “Maiya sami Farrah Shafa’atu”? Daidai lokacin Mami tagama abinda take tadago takalleshi sanan tamike tsaye ahankali tace “kaine mahaifinta Malam”? Girgizama Mami kai Malam yayi ganin babban mace yace “a’a diyar kanwata ce, marainiya ce babu uwa babu uba saini kadai” wani abu Mami taji ya tsayamata arai, anatse tace “an harbe diyarka garin kokarinta na taimakon d’ana, inaso idan ka yarda mu tafi da ita asibiti dole amata aiki acire bullet din, zaka iya biyomu idan yaso idan taji sauki sai adawo daku” kallonta Malam yayi sanan yabi yan sanda da sojoji da jiragen dake yawo asama, da wanda yake akasa, da yaron dayaga an lullube da bargo nai kyau yana tsaye kusada mahaifinshi dasuke kama wanda kana gani kasan shine yan kidmashin din suka kama daga ganinsu kaga yan birni masu kudi, ba yan yankan kai bane tunda ga yan sanda, lokacin yin kudinshi yayi yasan idan aka gama aikin zaa dawo dasu dole abasu kudi dayawa hakan yasa yace “to muje” wani gado aka kawo aka dauketa akai jirgin da ita suka shiga Mami na kusada ita tana monitoring heartbeat nata shikuma Zayn na zaune kusada Baban shi yay lakur ajikinshi sauran Drs na dubashi, shikuma Malam na zaune kusada yan sanda ya kankame jikinshi yanaji kaman Zai shide jinshi asama, tass Dr yaduba hannun Zayn sanan yakalli Alhaji yace “waya maka daurin hannun nan koma waye really saved his life daurin yayi kyau sama da wanda mu zama mumai a asibiti, idanunshi ne kawai needs work” ahankali Alhaji yace “waya maka daurin hannun?” Farrah yanuna murmushi Alhaji yayi yace “I will makesure I reward her awesomely for helping my son, for giving her life for you, me kakeso abata” murya chan kasa yace “anything” wani mugun kallo Mami tamai ita kanta tarasa gane kan wani kalan yaro ta haifa yanzu inda bataga Yarinyar nan ba da haka Zayn zai barta tamutu yarinyar data taimakeshi ta karbi bullet that was meant for him, ace Zayn yakasa fadi an harbeta adubata shi takanshi yakEe, ajiyan zuciya tayi ta zubama fuskan Farrah idanu.

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR
Chapter 21 · 0% Book details