← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 94

Sashe 14

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Goshi Alhaji yadafa cikeda damuwa yakai kusan minti daya ahaka sanan yadago kanshi yakalli bodyguards din yace “you guys are dismissed, kuje ku kwanta I will sleep with him yau” wucewa sukayi suka fita saida suka maida kofan suka rufe sanan Alhaji yatashi ahankali yakoma dakin da Zayn din yake a kwance, gefen gadin yazauna ahankali yana kallon fuskanshi yanda yake bacci peacefully, murya chan kasa Alhaji yace “why Zayn? Why did u choose this path eh? Ban haneka da komi ba, duk abinda kakeso nabaka maisa kazabi wanan rayuwan eh? You are still very small you are just 26, kona maka aure ne eh”? Yay maganan yana kallonshi still sanan ahankali yatashi yazo ta saitin kanshi yazauna ya jingina da bangon gado yana shafamai kai kaman wani dan yaro ahaka bacci yay awon gaba dashi.
******

Monday!
Ahankali yake bude idanunshi kanshi yamai wani kalan nauyi, da kyar ya iya tashi yazauna, Madaran dayagani a glass cup kan side drawer yasa hannu ya dauka ya kurba tass ya shanye sanan yatashi ahankali he’s not even in the mood yau yakira kowa baida karfin magana sabida kanshi, bayi ya shiga yakai kusan awa biyu yana wanka bubble bath da ruwa mai zafi sosai sanan yafito sanye da bathrobe, Papa yagani zaune akan gadonshi ya shimfidamai wani complete set na suit na Italian black hadadden gaske na Armani, akasalance yace “morning Papa” “morning Zayn dina, Zayn mai kiran Baban shi da suna kala kala yau Papa, gobe Abba, gata Dad, citta Baba” Alhaji yay maganan yana murmushi sanan yatashi yana daukan hanger na suit yakaraso gaban Zayn din yamikamai yana kallonshi yace “get dress in this, we are going to office dina yau, by 10 munada a very important meeting da board of directors kaji” dan yatsine fuska yayi yace “but I……” hannu Alhaji yasa akan lips dinshi looking very serious yace “no buts today Zayn, sabida rana irin tayau ne dalilin dayasa nasaka aka dawo dakai Nigeria, just do this for your father kaji ka shirya ina jiranka a falon Maman ka” Alhaji na maganan yajuya yafice, wani kalan gajeren tsaki yaja cikeda korafi yace “I told this old man ni duk wani harka na office dinshi banso, I am not interested ahhhh, why is he so adamant” yay maganan yana shiga closet dinshi, kodan yabatama Baban nashi rai saiya yabata kusan awa daya yana shiryawa sanan ya shirya yay wani irin kyau, for the first time Zayn looks like all this serious working class young guys masu hankalin nan, dudda farin gemun na nan but still he looks so decent sabida baya saka kaya haka sai kayan yan iska, bakin coversgoe yasaka na dolce gabana sanan yafito yana baza uban kamshi babu maganan wani sallan safe, a compound dinsu yaga Hajiya Mariya dauke kai yayi kaman bai ganta ba itama haka daman duk eye service ne sabida ubanshi, flat dinsu Ya shiga Mami ce kadai zaune a dinning tanashan fresh orange juice, zubomai idanu tayi ganin yay kyau yay kaman mutum dan murmushi kadan yayi sanan yataho dinning din dukawa yayi yarungumeta tabaya yadaura fuskanshi akan shoulder nata ashagwabe yace “good morning Mami, are u still angry with me”? Girgizamai kai tayi sanan taja kujeran kusada ita alamun yazauna hakan yasa yazauna yana kallon fuskanta, murmushi tayi tace “kayi kyau sosai haka nakeso kazama serious person” murmushi yayi yace “Mami yunwa nakeji” hararanshi tayi tana daukan plate tace “ba dole ba bakada abinci sai madara tun mana yaro ina hakan zai yu” chips tazubamai da miya sanan tasa fork tadawo tazauna tafara deba tana bashi yana karba yana danna waya she just wanna get close to him, zata rage mai direct fada, zata dinga kai fada with love and affection she believe Allah zai taimaka mata, da safen nan ta tambayi bodyguards nashi suka fadamata komi daga farko zuwa karshe, hankalinshi nakan waya yana cin abincin tace “Zayn” ahankali kaman wani dan yaro yace “uhn” anatse cikeda hikima tace “kanason mu maka aure”? Dawani irin sauri yakalli Mami haryana neman ya kware dasauri yadauki glass of water yasha sanan yanuna kanshi yace “Mami ni aure, I am too small for marriage, and besides ma aure sucks, I don’t wanna tara mata sukica gida kaman Dad” yay maganan yana yatsine fuska irin dagaske abin disgust him dinan sanan yace “Mami banso na auri mace cus babu wacce zata soni for me saidai sabida what I have, sabida the family I come from, Mami kinga I want a true love, wacce zata soni tsakani ga Allah sanan zata soni regardless of koma menakeyi, infact wacce zata soni without even knowing wanene ni kuma kinga babu irin matan nan aduniyan nan” dan murmushi Mami tayi ganin this is so far the longest maganan da Zayn yamata in years, ahankali tadauki tissue tana sharemai baki cikin hikima tace “idan kanaso kasami yarinya dazata soka ahaka kaima you have to be in the best version of you, you have to be a better person someone that respect kowa be it talaka mai kudi, someone that feels emotions, someone that understands people and understand life” ahankali yake kallon Mami tunda tafara maganan murya chan kasa yace “Mami this is the best version of me” zatai magana Alhaji yafito yana murmushi ganin yanda Mami kebashi abinci yace “yauwa Matar Aljanna dama abinda nake shiri nazo nayi kenan nabashi abinci saimu tafi” murmushi Mami tayi shikuma Zayn yakauda kai yace “nakoshi Mami” sanan yamike tsaye karasowa Alhaji yayi gabanta yamata peck agoshi yace “mun tafi” murmushi tayi tace “adawo lpy Allah yabada sa’a” “bye Mami” Zayn yafadi yana gaba, hakanan taji gabanta yafadi dasauri tamike tsaye tace “Zayn” Zayn dahar yakai tsakiyan falonsu yajuyo yace “uhn” shima Alhaji dake tareda shi juyowa yayi yace “soyayyan ta tashi bakison yafita ne yazauna dake” dan murmushi tayi takaraso tsakiyan dakin gaban Zayn din ta tsaya tana kallonshi, hannunta tasa ahankali tashiga gyara necktie dinshi ahankali tace “I am feeling somehow kaman kada kafitan nan bantaba jin hakaba kuma” wani kalan murmushi yayi yarike kafadunta yace “I love you too Mami” hararanshi tayi tace “bacemin daga gani ni” dariya Alhaji yayi yace “muntafi” har gaban flat dinta tarakasu, agabanta bodyguard yabude musu bayan jeep din Alhaji suka shiga sanan aka maida kofan aka rufe suka fice daga gidan, ijiyan Zuciya tasauke tana shafa kirjinta dan wani iri zuciyanta kemata kaman batada lafiya ahankali tace “Allah ya tsareku” sanan tawuce takoma ciki.

Babban kampanine girmanshi wane NNPC, parking motansu direban Alhaji yayi a executive parking lodge sanan bodyguard yafito yabude musu fitowa sukayi Zayn yaciro dark shades yasaka daya karaba fuskanshi wani irin bala’in kyau sanan suka shiga ciki, zubewa kawai ake ana gaidasu dama dama Alhaji na iya amsa wayanda zai iya dan nashi ko kallo baiga wanda ya isheshi ba, elevator suka shiga yakaisu 31st floor, direct zuwa wani lafiyayyen conference room, bude musu kofa bodyguards sukayi Alhaji yashiga Zayn biyedashi abaya, bodyguards don suka tsaya gaban dakin, manya manyan mutane ne a conference room din kowa ya halarta CEO kawai ake jira, duka mikewa tsaye akayi ganin Alhaji, wucewa Zayn yayi direct asalin babban kujeran na Baban shi yawuce directly yawani fada akai yazauna kowa na tsaye yana kallonshi amman ko ajikinshi saima zare glass din idanunshi dayayi yakalli Uncle dake tsaye shima akujeran farko na right hand dinshi, tabe baki yayi abinshi daidai Alhaji yakaraso wajen baimabi takan mutanen ba sai tsayawa kan Zayn dayayi cikeda tsantsan so yace “kagaji ko inbude maka bottle water dinan kasha” girgizamai kai yayi ahankali hakan yasa Alhaji yazauna kan kujeran dakenan close to Zayn din na left side sanan yace “settle down” hakan yasa kowa na dakin ya zauna yana murmushi daidai lokacin wata secretary ta shigo takawoma Alhaji wasu files sanan ta wuce tafita, kafin Alhaji yace “barkanmu da safiya duka, nasan kuna mamakin wanan urgent meeting dinan dana kira ko” yadanyi murmushi sanan yakalli Zayn, hannunshi yakai yadaura akan Zayn cikeda asalin so yana murmushi yace “this is my only son Zayn Ganuwa, yayi graduating from one of the best schools in this world wato Oxford university, yanada 2 degrees daya under business management daya kuma under mechanical engineering, yanada masters a business administration not to talk of wasu good Human Resources courses, programs dayayi, he’s 26 by the way” Alhaji yasake maganan yana murmushi still yana kallon Zayn din dayama ciro waya yana daddannawa abinshi, ahankali Alhaji yazare hannunshi daga kanshi sanan yajuya ya fuskanci mutanen yace “the reason for this meeting shine” yaydan shiru sanan yace “inaso na sauka daga matakin CEO na wanan kampanin nawa, inaso nabarma dana Zayn all my companies” shiru dakin yayi kaman kankara koshi Zayn din tsayar da danna wayan nashi yayi yana kallon mahaifin nashi, Alhaji yace “lawyer na yariga yagama aiki on all the paper works komi nawa yanzu sunan Zayn ne akai, Zayn ne mamalakin sa” tura file din yayi gaban Zayn sanan yabashi pen ahankali yace “sign here son” shiru Zayn yayi kaman bazai karbi pen dinba saikuma ya karba ahankali sanan yay signing, tafi mutanen wajen suka hauyi, hadiye wani abu uncle yayi awuyanshi sanan shima yashiga tafi yadafa kafadan Zayn yace “congratulations Zayn” maganganu sukayi na wanda kampanin zai kara bunkasa sai wajajen 1 sanan aka gama, Alhaji da Uncle da Zayn suka fito masallaci sukaje salla sukayi sanan Zayn yace “Dad mutafi gida” tashi Alhaji yayi yace “bari na maida Zayn gida zan dawo anjima” gyadamai kai Uncle yayi sanan suka fito daga masallacin sukai mota.
Chapter 14 · 0% Book details