← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 94

Sashe 22

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 1️⃣3️⃣
Direct wani babban asibitin da Mami ke aiki suka wuce dasukakai Abuja, jikin manya manyan likitoci har rawa yake aka wuce wani observation room da Zayn, dakin daza’ayi mai general check up kafin eye Doctors suganshi, Mami kuma scrubbing in tayi dan itace in charge surgeon ma Farrah she just feel this is the least she can do for the small brave girl after saving her son’s life, shikuma Alhaji zama yayi acikin wani executive lounge da only VVIP guest dinsu ake bamawa, Malam dai yadawo dan kallo yana tareda su amman bai zauna akan kujeran da Alhaji da Uncle ke kai ba dan sunmai wani kalan mugun kwarjini yana kujeran dake bayansu, kaganshi zaka dauka wani almajiri ne, ringing da wayan Alhaji yayi yasa ya farka daga zurfin tunanin dayakeyi dasauri yadauki wayan ganin Gwamnar Adamawa ne ke kiranshi, amsa wayan yayi sanan yay murmushi yace “Alhamdulillah, thank you excellency, to to to shikenan” zare wayan yayi daga kunnenshi ya katse sanan ya kalli Uncle dake kallonshi yace “ankama daya daga cikin kidnappers din” dasauri Uncle yace “Alhamdulillahi naji dadi sosai Yaya” shiru Alhaji yayi yanadan karkada kafa yana tunani sanan yace “zan iya yafema mutum duk wani laifi dazai iyamin aduniyan nan dakake tunani amman banda laifi daya shine cutar mini da Zayn” yasakeyin shiru saikuma ya bude malummalum dinshi yadauko wani clean handkerchief yakai kan idanunshi yana share hawayen dasuke fitowa yace “inda sun kashemin Zayn da yaya zanyi da rayuwata eh” kama kafanshi Uncle yayi yace “Yaya dan Allah kadaina kuka nace kuma kadaina maganganu haka bagashi yanzu an ganshi ba” cikeda damuwa da rauni yace “inda yarinyar chan bata taimakeshi ba, da yanzu shine yake kwance a operation room rai a hannun Allah, you know something I am going to reward that girl handsomely wallahi kuwa” sanan yajuyo yakalli Malam dake dunkule waje daya sanyin AC ya isheshi yace “Malam kome kakeso kafadamini zan maka shi dan diyarku ta chanchanci sama da haka awajena mekake so kanason gida a birni”? Wani kalan washe baki malam yayi yana murmushi azuciyan shi yace “inama tamutu su biyani diyya nafi kowa kudi a kauyen mu” anatse yace “a’a Alhaji Baran iya rayuwan binni ba, kawai dai kudi nafiso na gyara gonata da sauran ayyuka” murmushi Alhaji yayi yace “tom shikenan zan saya maka gona dai dai gonaki dari a kauyen ku” wani kalan zaro idanu Malam yayi yakasa gasgasata maganan dayaji gonaki dari yajiance sanan Alhaji yace “zan kara maka da naira miliyan goma kaje kaja jari” wani kalan fadowa yayi daga kujera yay rarrafe yazo gaban su Alhaji, kwanciya yayi flat akasa yana kuka yana musu addu’a, murmushi Alhaji yayi yace “tashi kaje ka zauna” sanan yakalli Uncle yace “jeka kawo cash na 10M kabashi” dasauri Uncle yace “nadauka sai an sallami yarsu za’a bashi”, girgixamai kai Alhaji yayi yace “kawomai miliyan gomanshi a leda kabashi yazauna yana kallo shima yanajin farin cikin da sanadin diyarshi nima inajin kalan farin cikin nan yanzu ahaka. “Kaico! Wayyoo Alhaji, aradun Allah zuciyata zata buga, yau ni Malam nine mai da miliyan goma, Wayyoo Allah na” dan dariya Alhaji yayi sanan yatashi yawuce dakin da Zayn yake ciki shikuma Uncle yatashi fuuu yafice ko kallon Malam baiyiba Malam kuma sai sumbatun kudaden daya samu yake.

Yana zaune awajen Mami tafito tana sanye da kayan operation, tashi Malam yayi dasauri ganinta yace “ta mutu ne”? Turus Mami tayi tana kallonshi tambayan yamata bambaran akunne amman takakalo murmushi tace “bata mutu ba, kuma Alhamdulilah mun samu mucire kwayar bindigan nan da yan awanni zata farka zomuje kaganta” gyadama Mami kai yayi sanan tai gaba yana biye da ita abaya zuwa dakin da Farrah keciki, tana kwance kan gado da kayan operation ajikinta, kanta sanye da hulan operation, an rufamata bargo zuwa cikinta, daga wuyanta kana iya hango katon plasta da aka manna a kirjinta inda akai aikin, ga oxygen a hancinta tana fitar da numfashi tana saukewa, wani kalan bakin ciki Malam yaji daya ganta shi da yanzu zata mutu dayaji dadi daya huta daman ta zamemai nauyi aka, yanzu tamutu zai sami kudin diyyanta sanan yahuta da fitinan Inna, dan kallonshi Mami tayi itadai batasan ko kawai she’s seeing it out of paranoia bane but the man doesn’t look happy to see yarinyar tai surviving surgery, to anya ma uncle dinta ne as he claim kuwa, anatse Mami tace “kace ba kaine mahaifinta ba”? Janye idanunshi yayi daga kan Farrah cikeda kauyanci yace “eh hasalima haryau ba’asan mahaifinta ba duka kauyen mu” ahankali Mami tace “Maman ta fa kace tarasu”? Gyadama Mami kai yayi yanadan tabe baki yace “mahaifiyarta dani kadai iyayen mu suka haifa, tunda tafara fita binni tana saida nono ta lalace, hartazo tagudu muka nemeta muka rasa, rana daya kawai tazomana da durmeme ciki kauye, wai ita tai aure amman mijin ya gudu yabarta todai a kauye ta haifesu yan biyu, yan kauyen mu suka tasata agaba tai cikin shege tazo tana karya cikin sunna ne da aurenta akanta, shine ta tattara ta gudu da yaran tasake barin kauyen, bata kara dawo da yaran ba saida sukai shekaru shadaya aduniya ta dawo dasu gida tana ciwo sosai da kauye yadauka ciwon kanjamau ta kwaso ayawon Duniya shine tadawo, babu kalan kunyan duniya da uwarta bata sakani ba, Toh dai ahaka ta mutu ciwon shine ajalinta, yaran suka dawo hannuna, bata wani dade da mutuwa ba yayan wanan ma ta mutu” yanuna Farrah, ahankali Mami tace “Allah ya jikan su da rahama” hakanan taji Farrah tabata tausayi taga tabon duka daban daban ajikinta yafi akirga wanda kana gani kasan clearly is the case of child abuse amman dai tai shiru, ahankali tace “bari nadan je chan wajen su Zayn naduba shi zaka iya zama da ita, dazaran ta farka bayan kwana biyu idan taji sauki za’a maidaku” “to Hajiya angode Allah saka da Alkhairi, Allah yakara girma” fita Mami tayi security dake gaban dakin tama whispering. “I don’t trust him, keep an eye on him please” yes Ma ya amsa mata sanan tawuce.

Kujera Malam yaja ya zauna yana kallon Farrah, kaman yadauki filon nan yadanne mata fuska tamutu yahuta yakeji, yana zaune ahaka ya saka ya warware shi kadai aka bude kofan dakin, Uncle ne rikeda Leda baka wani irin tashi Malam yayi yace “wayyo Allah kudade na sunzo” kafin ma Uncle yabashi kudin ya karba yana leka ledan saikuma ya rungume kudin yana hawaye wani kallon wulakanci da raini Uncle yamai sanan yawuce yafita daga dakin yawuce dakin Zayn.

Kallon kudin Malam yayi sanan yakalli Farrah yace “tunda yanzu ga miliyan goma na a hannuna chass ni nama yafe gonaki darin na gudu abina ko, Allah yabani miliyan goma daga sama babu abinda nayi tasha kawai zani nakoma kauyen mu, Wanan kuma idan sunga dama su yardata kosu dawo da ita kauyen mu su suka sani koba hakaba” yana gama tunanin yawani mike tsaye ledan ya ijiye kan kujera yadauko bandir daya na kudi yakirga dubu goma yasa a aljihu sanan ya daure bakin ledan ya makaleta a hammata gam gam sanan yabude kofa yafice, fita yayi daga asibitin batare daya hadu dasu AlhaJji ba yana fita motan daya gani yatare yace akaishi tasha.

Imagine yourself kina kwance a comfort na bed dinki kina duba pictures and videos na hadaddun atampopi kina gamawa kawai ki zaba, place an order, make payment akawo miki har gida batare dakin fita kinje kasuwa ba.

Imagine yourself in the middle of stress da kata kata na biki but you don’t have to worry akan atampopin anko dan akwai wacce zata miki supplying nasu har gida?

Imagine yourself kina tunanin that perfect and best gift dazaki bama kawarki be it birthday gift, wedding gift, suna gift or just casual gift, and M Shakur told you Atampa ne!

Just picture it lokacin da za’a kawo miki atampan acikin wata lafiyayyen fine jaka za’a saka miki atampan akawo miki ba abakin Leda ba kaman yanda aka sabayi a kasuwa?? Sweet right?
What if M Shakur tagaya muku yau all imaginations, dreams dinan naku can become through by introducing ATAMPA REALM to you guys💃
ATAMPA REALM is an online store dake saida atampopi variety of them, daki bari, masu kyau, masu ado, wayanda ake yayi, akan kudi kuma kalilan don’t you want that??
Atampa Realm are life savers, biki, akwati, birthdays or anything they come through and represent!! Ina gayamuku atampopin su makes statement🌹

All you have to do is give them a call 📞 +2348097573597

Ga wayanda basason kira you can chat them up a WhatsApp by clicking on this link:;
wa.me/+2348097573597

You can also follow them on Instagram by clicking on this link;
https://www.instagram.com/p/CiQcu1loZ7c/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

You can join their WhatsApp group by clicking on this link;
https://chat.whatsapp.com/CUmRWXy4evqLtOoYp3XmNt
Chapter 22 · 0% Book details