← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 94

Sashe 72

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowa yayi ganinshi da roses yasa Mami tace “waya aikoka”? Cikeda girmamawa yace “Small Alhaji” sanin Zayn suke cema small Alhaji yasa tanunamai centre table din tace “zoka ijiye anan” karasowa ciki yayi ya ijiye sannan yamata sallama yawuce yatafi, girgiza kai Mami tayi tamike danta wuce sama abinta bakin riganta yaja card din yafadi akasa yay kara juyowa tayi ganin card din akasa yasa agajiye tadan duka tareda daukan katin idanunta suka sauka akan Thank you for breastfeeding me Angel, Hubs Zayn, dawani kalan sauri har hannunta na rawa ta maida katin cikin flowers din sannan tajuyo tana kallon dakin ganin bakowa yasa tasauke ijiyan zuciya tawuce sama da sauri, Innalillahi wannan wani kalan shaidani yaro gareta ne? Dasauri tagyara maganan ta wani kalan shiryayyen yaro ne da ita haka, ranan da aka raba kunya ta tabbata kafin Zayn ya amsa nashi yakare cus Zayn baida a single kunya, wato dazu shida ubanshi plan sukayi tana fita ya ritsa yarinyar adaki yamata yanda yaga dama ko, har cikin ranta tun yanzu Farrah tafara bata tausayi cus tasan waye danta, Zayn da mace inaaaa! Yan iskan mata ma dasuka saba Zayn yakusan kashesu balle Farrah dababu abinda tasani she just hope she will be okay and Zayn will be sensible enough yabita ahankali, and dagayau zatasa hannu wajen gyara Zayn din dan Mama tariga yasa tai alkawari she will never stand against Marraige din, duk lokacin da Zayn yabukaci matarshi baruwanta tabashi kayanshi, ahankali tace “Allah sa shiriyanshi tazo kenan” tai maganan tana tsayawa gaban kofan Farrah knocking tayi tareda kiran sunanta Farrah, hijabi Farrah dake kwance kan gado tadauka ta zunbula dasauri tace “Na’am Mami” dan gani take idan Mami taganta zata gane abinda yafaru, ganin Mami bata shigo dakinba yasa tai wajen kofa tareda bude kofan tadan kalli Mami ahankali, murmushi Mami tasakin mata tace “kina kan dadduma ne” Gyadamata kai Farrah tayi dan batasan mezata ceba, murmushi Mani tayi tace “kinada sako kan table a falo bari na kwanta nagaji, good night dear” ahankali tace “night Mami” Mami tawuce dakinta itakuma tafito ahankali daga dakin zuwa kasa tundaga kan bene taje hango wasu jajayen flowers a basket masu bala’in kyau Wanan ne sakon, su kadaine akan table, karasawa tayi tadauka ahankali tanajin kamshin dasukeyi dayasa tai murmushi tajuya tana tafiya tace “Mami ne tasayomin flowers nasa adakina su dinga kamshin” tai maganan tana bude dakinta tana shiga ta maida kofan tarufe sai yanzu taga card an tura cikin flowers din hannunta tasa taciro card din daidai tana zama abakin gado.
“thank you for breastfeeding me Angel” wani kalan yirrrrr taji batasan lokacin data jefar da both flowers da card din akasa ba tai maza tahau gadon tareda jan bargo tarufa har saman kanta ranta nabaci yasha mata nono duk ranta na baci sabida bashin datayi shine kuma harda turomata da flowers sabida yagayawa duka duniya yasha inda Mami tagani fa.

Ajiyan zuciya tasauke ahankali tana tuna fuskanshi dazu data kalleshi dayana bacci, he looks super cute and innocent, she just wish he was that innocent, maganan su Shafa ne yafado mata arai cewa tana sonshi, dasauri tace “Allah ya tsaren” tai maganan zata kife taji zafi dasauri takwanta ta side murya chan kasa tace “kuma Allah ya isa daka shamin nono bazan kara bari katabani ba dagayau”, tai maganan tana kwafa tace “kaje kataba wayanda kasaba tabawa ninafi karfinka” ahaka bacci ya kwasheta da maganan Zayn aranshi.

Tareda Dad suka shigo cikin gidan yanda Dad yaga yana nishadi yasa dadi ya lullubeshi yace “duk randa kaga dama zaka dauki matarka yau bakaga yanda Grandma dinka tama Mami fada ba, nariga nai magana cikin week dinnan daza’a shiga za’a gama saka komi na gidanku saiku tare ko” gyadamai kai Zayn yayi yana murmushi, Dad yace “wai wannan murmushin na menene Zayn”? Cikeda farinciki yace “Dad I am just so happy, Dad thank you dakamin aure kuma ka auramin Farrah, Papa I love that girl so much wlh” Dad dake murmushi yace “ai nagani, yanzu inaso ka rikita mata brain da soyayyan ka show her u are my son, ta gigice da soyayyanka da ita kanta Mami saitai mamaki yanda yarinyar zata soka” wani kalan murmushi Zayn yayi yace “yes Dad” Dad yace “saimun bawa yan bakin ciki kunya wlh” gyadamai kai Zayn yayi zai wuce side nashi Dad yace “bazakaje kadubata ba” kallon side din Mami yayi yay murmushi yace “Dad tagaji yanzu tai bacci sai gobe, gud night Papa” yay side dinshi, Dad yabishi da kallo bakinshi har kunne danshi yay aiki wato ta gaji, Allah kama Zayn dina albarka yay addu’an yana wucewa side din Hajiya Fatima.

6️⃣6️⃣

Wacece tadade takeson tafara business din ORIFLAME takasa yi sabida tsadan Registration dinsu??????📢📢📢
Please this might not mean anything to you amman tell your sister, Yar uwanki, wata from your Family, makotan ku suzo koku dari nawa ne za’ayi muku FREE REGISTRATION na shiga ORIFLAME.
Akwai riba acikin ORIFLAME sosai, yanzu kika samu aka miki free registration ahankali ahankali zaki dinga siyan abu daya biyu uku kina saidawa kina kara saya.

Sanan idan kikai registration kika zama member akwai huge discount daza’ayi miki wajen siyan kayansu.
All you have to do idan kinason FREE REGISTRATION IS CLICK ON THIS LINK kima HASSANA magana.

wa.me/+2348052302040

Ahankali take bude idanunta daga dadaddan mafarkin datayi kan Zayn yanata mata iskanci yana murmushi dan gajeren tsaki taja tana kallon yanda gari yah haske sosai batai salla ba dasauri ta tashi jitayi gabaki dayanta ajiki dasauri takalli gadon inda tatashi meke jikata haka what’s wrong with her, sake cire zanin gadon tayi tawuce bayi dashi tasa a laundry sannan tayo wanka tafito ta shirya cikin wani simple straightforward gown na material baby pink tasaka hijabi tai salla saida ta idar sannan tai azkar tamike tazo gaban madubi mai ta shafa sannan tadau turaruka ta feffesa, knocking dakinta akayi tareda shigowa matan dake bata magani ne kafin ma tai magana takarba ta shanye tana yatsine fuska tace “wai maganin nan basa karewa Anty” dariya matan tayi batare data bata amsabatafice dankwalin kayan tadaura aka sannan tafito hanyar dakin Mami tayi, Mami nakan gado tana waya daga asibiti ne tana gwada musu yanda zatai operation ganin Farrah yasa kafinma tai magana tace “Daughter na jeki karasamin breakfsat din danake hadawa a kitchen da clinic nake waya” gyadamata kai Farrah tayi tajuya tafito tasauka kasa zuwa kitchen din.

Chips kawai yarage da kwai, amman tafiga tayi coffeee wanda yasan Zayn akemawa tayi kunu sannan tayi shayi, fitodasu taji ta ajiye a dinning sannan takoma kitchen din tana soya Irish din.

Ahankali aka bude kofar kitchen din batare daya juyoba tace “Mami ki koma nariga nagama this is the last one nake soyaw………” kasa karasa maganan tayi sabida kamshin turaren Zayn daya ratsa ko’ina na kitchen din, batasan mesa ba hakanan jitayi gabanta yafadi rasss! Dakewa tayi tacigaba da abinda yake batare daya juyoba. Maida kofan kitchen din yayi yarufe yana rike da mug na coffee dahar ya tsaya a dinning ya tsiyaya, yana sanye da kayan sport na Nike black, rigan mai kalan singleti ta kamashi kirjinshi da abs dinshi sun fito fasss taciki dakuma gajeren wando hannunshi da safan hannu saiwani cute white towel a shoulder nashi sai uban kanshi yake kaman bashine yagama workout ba, ahankali yake tafiya yana dumfaro inda take tsaye gaban gas daidai bayanta ya tsaya ya manna gabanshi da bayanta batare dayay magana ba adan firgice tadan yunkura zatai motsi hannunshi dakenan bakomi yakai tagabanta yadaura kan cikinta dayan hannun kuma yakai yana kurban coffeee yana kallon tsakiyan kanta, wani kalan kabarda hannunshi tayi dagakan cikinta tajuyo da kalleshi da manya manyan idanunta farare tas tace “mehaka?” Dagamata gira daya yayi tareda zare mug din daga bakinshi ya ijiye akan slap na kitchen din yana kallonta shima tace “haka ake gaida miji”? Hararanshi tayi tajuya tana daukan spoon din datake juya Irish din dashi tace “baza’a gaidaba din” dan murmushi yayi yabi gashinta daya zubo har waist da kallo taredabin dankwalinta da kallo dayaga lema Lema akai hannunshi kawai taji saman kanta yaja dan kwalin dasauri tawani kalan juyota kalleshi tace “mehaka kake ciremin dan kwali” dan kwalin yakalla tareda kallon gashinta yace “kinyi mafarkinane maisa gasshinki ajike”? Wani kalan kunya taji yarufeta dayasa tabude baki zatai magana ganin yanda yake kallonta yasa cikeda borin kunya tace “who are you dazan dinga bama explanation, think whatever you wanna think” tai maganan tanasa spoon zata fara kwashe Irish din tazuba a flask, cikeda soyayya yadaura hannunshi kan nata yace “kawo natayaki kwashewa” yanda yarike hannun nata shock din dataji yasa dasauri tasakinmai spoon din takoma gefe, murmushi yayi yajuye a flask sannan yafara kokarin kwaso sauran kana gani kasan bai iyaba hakan yasa tai murmushi aranta tace “inama ya kone” kaman yankan wuka subucewa cokalin yayi a hannunshi yafada frying pan din hakan yasa man yay tsalle ya kadan ya tsulla akan hannunshi wani kalan ihu Zayn yayi na azaba dawani kalan sauri Farrah tabude idanunta tai kanshi da sauri ganin kalan ihun dayayi yarike wajen arude tace “mugani mugani sake mugani” cikeda bala’in shagawaba Zayn yaki cire hannunshi dagakan wajen yace “its hurt, Paaapa na kone” kaman Farrah zatai kuka tajashi dasauri zuwa gaban tab takama hannun zuwa kasan tap din tabude tana wankemai ya tsaya yana kallon cute face nashi, ahankali yace “are you sure baki sona”? Chak ta tsaya da wankemai hannun datakeyi ahankali ta kalleshi, kallon dataga yana mata yasa tajuya da sauri tai wajen gas din rago wan Irish din sun kone hakan yasa takashe gas din, murmushi yayi yawuce yafita daga kitchen din batare dayace mata komiba, saida taji karan rufewan kofa sannan tajuyo takalli kofan ita tai addu’a ya kone but maisa dataga nan ya dillan mai she became so worried har tana tausayinshi? Banda haka all through dayake cikin din hakanan she was happy a mind nata yanzu daya fita kaman tace yadawo.

6️⃣7️⃣
Chapter 72 · 0% Book details