← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 94

Sashe 51

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn taji ana mata amman she don’t care kawai kukanta take a inda take tsugunne gefen hanya. “Farrah!” Kaman daga sama taji wata tausassiya murya yakira sunanta dayasa ahankali tadago kanta da rinannun idanunta, ido da ido tayi da Ya Habeeb dake sanye cikin suit da white glasses kan idanunshi ko ba’a fadamaka ba kana ganinshi kasan aiki zashi, ganin itane yasa cikeda mamaki yakalli agogon hannunshi this is 8:40 na safe, karfe 9 zasu shiga exam, cikeda damuwa yace “what are you doing anan crying? Where is your driver? Why are you alone?” Tunda yake mata tambayoyin kallonshi kawai take batasan mesaba samin kanta tayi da fashewa da kuka sama dana dazu ma, ganin yanda take kuka ga duk wanda zai wuce sai ankallesu yasa gently ya tsugunna agabanta, ahankali yasa hannunshi cikin aljihunshi yaciro wani soft tissue kan fuskanta yakai yana kallon jajayen idanunta dasuka cikada hawaye yashiga sharemata, murya chan kasa yace “stop crying” sanan yakai hannunshi yakama kafadarta yace “let’s go” tashi tayi ahankali jakan bayanta yacire ya amsa sanan yakai hannunshi yakama nata, wani kalan taushi taji dakuma dumi a hannunshi, yana rikeda ita yashige gaba tana biyedashi abaya gaban motan yabude sanan yajuyo yakalleta yace “get in” ahankali takaraso tashiga ta zauna sanan yamaida kofan yarufe yabude baya ya ijiye jakanta sanan yadawo ta bangaren driver ya zauna, wani bottle water ya dauka dake cikin motan shi na ruwan zamzam goran yabude ahankali sanan yamika mata ruwan yace “drink up” dan kallonshi tayi sanan takalli ruwan, ahankali tasa hannunta ta amsa takai bakinta ta kurba tasha sanan gently tadan juyo ta kalleshi hada idanu sukayi murya chan kasa yace “ya isheki?” Gyadamaikai tayi ahankali, hannunshi yamika mata tasamai goran ruwan aciki ya maida marfin ya rufe sanan ya ijiye kusadaahi tareda tada motan yaja yana madaidaicin gudu, idanunshi nakan hanya yace “what happen to you”? Murya chan kasa tace “Ya Zayn ne” da juyoda fuskanshi yayi ya kalleta har wasu sababbin hawayen sun kawo sun cika mata idanu, dauke idanunshi yayi da sauri yamaida kan hanya yace “meya miki?” Dan dago kanta tayi ta kalleshi kaman yanda shima yajuyo suka hada ido batasan mesa ba kaman idanunshi compelled her into talking, daga A zuwa Z tafadamai abinda yafaru, murya chan kasa yana kallon hanya yace “where are your real parents”? Dan shiru tayi tana kallon kan titi kuma ahankali tace “ni bansan Babana ba, amman Mamana tarasu tabarmu nida Yar uwata itama tarasu saini kadai, su Dad and Mami da Ya Zayn sune suka ceceni daga hannunsu Baffa na akauye” hannayenta biyu tadaura akan fuskanta kawai ta fashe da kuka sosai bana wasaba ita tunda take bata tabajin gorin wanda yacimata rai kaman na Ya Zayn ba, yanaji tana kuka baice mata komi ba harsukakai school bama tasani ba dan tarufe fuskanta, parking yayi yakalli agogon hannun 9:00 yasan za’adan kara time before exam hakan yasa yay folding hannunshi a kirji yana kallon yanda take kuka………

Gabaki daya anger rashin kunyan datamai jiya hartana kiranshi stupid irresponsible boy, da anger shairin datamai this early morning taja Dad namai fada da fushin dasu Mami keyidashi duka yahada yajuye mata akai, he thought he will feel better dayaga yabata mata rai amman ga mamakinshi he’s feeling so awful, zuciyanshi yakasa natsuwa sabida yanda yasauketa kan hanya dudda yakusan kaiwa office dan duka duka haifi 6 blocks yakai ba dan mugun gudu yake but hakanan samin kanshi yayi dasake juya kan motan dan yaje ya dauketa daga inda ya ijiye ta yakaita school danta gayamai tabar kudinta agida dame zatahau motan dazai kaita school gashi batada waya, dan tsaki yayi yadaki sitarin mota ahankali yace “what’s wrong with me, why am I feeling bad?” Yatambayi kanshi, dan tsaki yaja ahankali yace “mema nake biyemata danta batamin rai nima saina bata mata we are not mate why am I even paying attention to that small girl”? Yaja tsaki abin na batamai rai, kaiwa wajen daya sauketa yayi ganin babu ita yasa yakashe motan yafito yana waige waige ganin masu sakama taya iska awajen yasa yay wajensu da sauri baima tsaya musu sallama ba yace “dan Allah malam kunga wata yarinya Yar makaranta haka tasaka uniform pink and green da black ajakan makaranta anan” da sauri daya daga cikin yaran yace “wata Yar faran yarinya haka kaman baturiya bata da tsawo sosai ita”? Dasauri Zayn yace “yes, tana ina?” Yaron yace “aini na dauka ma tanada iska ne dan ta tsugunna sai kuka take amman naga tashiga mota ta tafi yanzun nan motan bai jima da tafiya ba” gyadamai kai Zayn yayi da sauri yace “thank you” sanan yajuya yashiga motanshi ya bala’in damu wani mota tashiga, takai school wani kudi zata bama mai motan, jan motan yayi zuwa school dinsu da gudu.

Duk yana kallonta tana kuka yana duba tai saida yabarta tai kuka na good 5min, daidai time yay clicking 9:05 yakira sunanta ahankali. “Farrah” janye hannayenta tayi daga jikin fuskanta sanan tajuyo takalleshi ahankali yabude motan yafito daidai motan Zayn na dannawo filin parking din, bude bangarenta Habeeb yayi sanan ahankali ya tsugunna gaban motan kaman wanda zai bata hakuri, dan murmushi yayi yakalli hannunta da handkerchief dinshi keciki yakai hannunshi yazare sanan yakai handky din kan fuskanta yace “yau nasan dalilin dayasa keda Miemie are best of friends, ashe kema haka kika iya kukan banza” batasan mesa ba but maganan yabata dariya dudda kuka take but saida taidan murmushi, shima murmushi yayi daidai yagama sharemata fuskan sanan yamike tsaye ahankali tareda mika mata hannunshi, Zayn da tun bude kofan da Habeeb yayi ya hango Farrah jiyayi kirjinshi nawani kalan bugawa dari dari dududum dum dum kaman ana buga banga yakasa koda kwakkwaran motsi acikin motan yana kallonsu.

Fuskanshi Farrah ta kalla ahankali lumshe mata idanu yayi sanan yabudesu ahankali wani kalan natsuwa taji ahankali takai hannunta tasaka acikin nashi fitoda ita yayi daga cikin motan sanan yamaida kofan yarufe hakan yasa ta jingina da kofa motan, baya yabude yadauko mata jaka sanan yazo dinta take dan murmushi yayi yace “turn around” dan juyawa tayi tabashi hannunta yasaka mata jakan sanan tajuyo takalleshi kaman yanda yake kallonta, cikin wata kalan tattausan murya yace “no more crying, go inside and write your exam nasan kawanki na chan tadamu bata ganki ba” gyadamai kai tayi ahankali sanan tawuce yabida da kallo, tsayawa tayi kaman ance ta tsaya saikuma ahankali tajuyo takalleshi hada idanu dasukayi yasa ta sunnar da kanta kasa da sauri tashiga wasa da yatsunta ahankali tace “Thanks Ya Habeeb” wani cool smile yasakin mata yace “take care Farrah” dan dago idanunta tayi ta kalleshi batasan murmushi tasakin mai akunyace sanan tajuya da sauri tawuce tashiga cikin school.

4️⃣3️⃣

Wani kalan zafi da Zayn yaji kirjinshi namai baisan lokacin dayakai hannunshi kan kirjin yana wani kalan shafawa ba yana bubbugawa yana nishi da sauri da sauri idanunshi sunyi jajir, jin numfashi shi na neman daukewa ganin yanda Farrah tasakin ma Habeeb wani kalan murmushi tawuce tashiga school yasa baisan lokacin daya bude case din motanshi ba yaciro kwalin tabanshi dake wajen yabude da sauri hannunshi har rawa yake yazaro kara daya yakai baki yadauki lighter yakunna tabar sanan ya cillar da lighter anan cikin motanshi ya zuki taban yawani fuzoshi waje yana kallon yanda Habeeb ya tsaya yana kallonta harta shige cikin school wani kalan bude motanshi yayi yafito ko maida motan baiyi yarufe ba tsabagen wutan bala’i dake cinshi yataho yana tafiyan nan kaman sarki ya dumfaro inda Habeeb yake daidai Habeeb najuyo wa daidai shima yana tsayawa chak agabanshi Saura kadan suci karo Habeeb yakoma baya da sauri yana kallonshi, fuskanshi yadanso yabace mai saikuma yaganeshi Zayn ne yana sanye cikin shiga na suit kaman shi bakinshi da taba yanasha yanama Habeeb din wani kalan kallo ya fuzo hayakin taban fuskanshi, dan lumshe idanu Habeeb yayi sanan yabudesu ahankali tareda sakin dan murmushi yamikamai hannu yace “Hello Zayn” wani banzan kallo Zayn yamai tundaga kai har zuwa hannun dayake bashi sanan yazaro karan taban daya gamasha yawani jefar akasa nan gabanshi sanan yakalleshi strictly yace “this should be the first and last time zan ganka tareda kanwata cus I don’t appreciate when strangers are talking to her” yawani juya tareda bashi baya, ahankali yace “take this as a warning” yawuce fuuuuu yashiga motanshi yaja dawani mahaukacin gudu da saida security makarantan suka fito da gudu dan sun dauka hatsari akayi, Habeeb yadade tsaye awajen yanabin sahun tayan motan Zayn da kallo sanan yabude motanshi ahankali yashiga yatada motan yawuce.

Har yakai office Zayn yakasa dawowa daidai, ana gaidashi amman ko mutum daya bai amsaba dan zai iya firing mutum lift yashiga direct yawuce office din Babanshi dayaga Layla zaune wajen secretary suna hira dan dole sai Zayn ko Uncle sunzo ne zaa iya bude office din, ganin Zayn yataho fuskanshi ba rahama yasa ta tashi ahankali zata biyoshi yawani slamming door din tareda saka key yace “I am on DND secretary” dasauri tace “yes sir” wani abu Layla taji ya tsayamata awuya Wanan wulakanci har ina.

Fadawa kan dogon couch din office din yayi ya kwanta tashi zaune yayi dasauri har lokacin bayajin dadi, mikewa yayi yawuce water dispensing machine yadeba ruwa mai sanyi yasha still yakasajin sanyi aranshi. “Why why why I am feeling bad?” Ya tambayi kanshi dasauri, yarasa maisa yakasa manta yanda yaga Farrah nama Habeeb murmushi, kishi kishi ne, haushi haushi ne, duka jiyake, he just feel her smile belongs to him, shi kadai ya chanchanta datama kuka, sanan tama dariya all, tana gama exam dinnan ma zaima cireta daga school din yamaidata wani sabida yarabata da wachan yarinyar friend din nata da Yayanta shi yama manta sunansu, in the entire history na life dinshi yaune rana na farko da abu ya batamai rai yana cikin damuwa yaji ya tsani komi sex din baimaso ma yayi, normal shi yanda ranshi yake abacen nan dako secretary Dad dinnan ne da yanzu ya danneta harsai damuwanshi taragu, wani kalan mugun tsaki yayi ya kwanta flat akasa akan centre carpet na office din yana kallon agogon bangon dakin, ai 12 zasu gama exam, before 12 yana school din zaiga ubanwa zatama murmushi.
Chapter 51 · 0% Book details