Sashe 65
Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gidansu suka shigo driver yay parking wajen parking, ahankali tabude kofa tafito tana kallon gidan ganin ansaka canopies ana decorating gidan kaman za’ayi biki ko walima mamaki abin yabata tace “toko Ya Zayn na birthday ne yau”? Tai maganan tana tafiya tana kallon yanda ma’aikata keta aiki, ahankali tabude kofan dakinsu tashiga ciki, Mami tagani zaune kan kujera taci lace mai kyau tana mata murmushi itama murmushi tayi tace “oyoyo Mami” tafada jikin Mami, murmushi Mami tace “barka angama jarabawa yau hutun sati nawa suka baku” murmushi tayi tace “3weeks Mami” Gyadamata kai Mami tayi tace “Masha Allah, Oya je dakin ki ki chanza kaya kizo kici abinci” gyadama Mami kai tayi tana tashi daga kan kujeran tai sama, ahankali tabude kofar dakinta dayar karaman sallama. “Assalamu Alaykum” “wa’alaikumus salam” wata murya dahar abada bazata taba mantawa dashiba ya ratsa mata dodon kunne dayasa dawani kalan sauri tadaga idanunta takalli cikin dakin, Shafa tagani, Shafa Shafa ta kauyensu tana sanye da kayan fulani tsaf dawanan normal kwalliyan yan kauye dasukeyi tana kallon Farrah tana murmushi idanunta sun cicciko da hawaye, hannu Farrah takai kan idanunta dasauri ta goge tanason takara gasgata cewa ba gizo idanunta kemata ba ganin still Shafa na tsaye cikin dakin tana kallonta yasa Farrah tawani kalan juyawa da gudu tana kwalama Mami kira. “Mami! Mami! Mami” Mami dake zaune kan kujera inda tabarta tace “Na’am diyar Mami” bene Farrah tanuna mata hawaye na cika idanunta tsabagen mamaki da murna tama kasa magana, murmushi Mami tamata tace “go Shafan kine, your friend ta rugarku” wani kalan juyawa Farrah tayi ganin Shafa tayi tsaye gaban stairs asama, wani kalan fashewa Farrah tayi da kuka sosai tafara hawa stairs din da gudu Shafama na saukowa da gudu saida sukazo gab da gab Farrah takai hannayenta kan fuskan Shafa ahankali tace “Sha….fa” cikin kuka Shafa tace “Kurma” wani kalan rungume juna sukayi suka fashe da kuka sosai bana wasaba, murmushi Mami tayi tana kallonsu ganin kukan yayi yawa tace “Malamai kutashin mini daga kan bene ku koma dakinku kujechan kuyi wanka ku shirya kufito, karfe hudu za’ayi walima” Shafa tafara hadiye kukan sannan tadaga Farrah data kasa kuka tace “muje daki” ahankali Farrah tabita zuwa dakin zama sukayi abakin gado, Shafa takai hannunta tasharema Farrah hawaye tace “daina kukan kekuma Ya isa haka” murmushi Farrah tayi tace “waya kawoki yaushe kikazo”? Murmushi Shafa tayi tace “Baban Zayn yakawo du, munada yawa, da mai gari da matanshi biyu, da Malam da Inna, da Rakiya, sai Umma na da Baba dakuma ni, ni kadai Zayn da Baban shi suka kawoni nan sauran sunachan wani bangare daban awannan durmemen gidan, mazan sun tafi masallaci munzo waliman kune” dasauri Farrah tace “Waliman mu” Gyadamata kai Shafa tayi tana kakalo murmushi tunawa datayi ance kada tafadi mata komi Farrah batasan anmata aure ba, dasauri tace “eh bakin gama jarabawa yau ba” dasauri Farrah tace “ohhh dama ni aka shiryama Walima haka” hannu Shafa takai ta taba fuskanta tace “bakaramin farinciki nayiba da Rakiya tabani labari mutanen nan sun maidaki yarsu, Farrah addu’an mu ta amsu, Allah ya sharemiki hawayenki su Inna sun sha kunya kullum cizon yatsa take tana cewa inama Rakiya ce tai irin goshin dakikayi, kinga yanda kika kara kyau kuwa Farrah kaman bakeba kin dawo kaman baturiya, kinyi kiba jibi yanda kika kara jiki da mama, tsayin nedai har yanzu babu wani tsawon kirki” akunyace Farrah tai murmushi zatai magana Mami tashigo dakin ganinsu azaune yasa tace “imaza kiyi wanka babanki na jiranki a babban falo tareda bakin damukayi” Gyadamata kai Farrah tayi ta tashi tashiga bayi dasauri.
5️⃣8️⃣
Agurguje tai wanka tana fitowa Shafa itama tashiga saida Farrah tabita tanuna mata yanda zatai amfani da komi sanan tafito, salla tayi shigowa Mami tayi dawani sababbin dinkakkun lace guda biyu, pink and black na Farrah sai red na Shafa Mami tace “ganaki nan tashi ki shirya” tashi Farrah tayi Mami ta tayata shiryawa Shafa ma tafito tun tana kunyan yanda Mami ketayata shiryawa harta daina ganin Matan nada kirki tana musu abu kaman yayan cikinta, wani babban ubansun gyale Mami takawo ta yafa akan Farrah dahar saida tace “Mami wanan katon gyale saikace wata Amarya” dan murmushi Mami tayi sannan takalli Shafa da itama tai kyau sosai kaman ba itaba tace “kaita Shafa’atu ganinan nima tafe” Gyadamata kai Shafa tayi sannan suka fice waje, babban durmemen falon Dad sukayi hakanan Farrah jitayi gabanta yafadi ganin takalman mutane dayawa agaban dakin, sallama Shafa tayi suka shiga ciki Farrah na kallon mutanen dakin da duk suka juyo suna kallonta, Inna, Rakiya, Innan Shafa, Malam, Baban Shafa, Mai Gari, Gwaggo Fari Matan Mai gari uwar gidan Mai gari da amaryan, sai ga duka matan Dad harda Layla, ga Uncle da Matan shi, sanan ga Dad, gakuma Zayn zaune kusada Babanshi yaci Shadda Fara kal datamai kyau idanunshi kyam akanta.
Waje Malam yanuna musu yace “ku shigo ciki ku zauna” karasowa ciki sukayi suka zauna, Dad dake kallonta yace “how was the paper daughter na” murmushi tayi tace “it was fine Dad” murmushi yamata yace “Allah bada sa’a” ahankali tace “Ameen” tana sauke kanta kasa ganin yanda kowa ke kallontavshes so uncomfortable, gyaran murya Malam yayi yace “Farra’u” ahankali tace “Na’am Baffa” anatse yace “kice Alhamdulillah, Alhamdulillah, sanan ki dada cewa Alhamdulillah dominko Allah yamiki gata, dubemu nan dukanmu kakap sanadiyanki aduniya mun d’ana jirgin sama, sanan Hajjin bana da yardan Allah damu za’aje Alhaji duka yabiyamana aikin Hajji dukta sanadiyan ki tsakani na dake Farrah sai Allah yabiyaki” yay murmushi yace “abinda yataramu adakin nan shine nazo na sanar dake ne, amatsayina na mahaifinki, marikinki, yayan marigayiya mahaifiyar ki cewa na aurar dake!” Wani dum durum! Farrah taji akirjinta dasauri ta kankame hannun Shafa datarike gam, tashi Malam yayi ahankali yadauki wata katuwar jaka dake gabanshi yazo har gaban Farrah ya ijiye jakan yace “sadakin kine acikin jakan nan naira daidai har zuwa naira miliyan goma cur ko kwabo bata fita aciki ba” yay maganan yana tashi yakoma wajen zamanshi, sannan ya gyara zama yace “kwana hudu dasuka wuce Baban ki dinan” yanuna Dad, yawanko kafa takanas takano yazo har kauyen mu wajena da wajen mai gari tareda gwamnan garinmu gabaki daya nemawa danshi Zayn aurenki” wani kalan rawa da bari kirjin Farrah yafara, Malam yacigaba. “Duk duniya banga wanda kikafi dacewa dashi irin danshi Zayn ba dan tun farko ina mai tabbatar miki rabon aure ne yasa yan kidmashin suka kamashi suka kawoshi rugarmu sanan kuma duk ruganmu babu wanda yagansu sai ke, saisa amatasiyana na uba wanda zai iya zaba miki miji nakuma aurar dake nabasu aurenki suka biya sadaki aka gama akace sai randa kika gama jarabawa za’asanar dake, wanan walimar da za’ayi anjima ta aurenki ne munzo mu shaida mukuma samiki albarka ne sanan mu saki agidan mijinki kafin gobe ko jibi mukoma kauyen mu dan haka ina mai rokonki dakuma mai neman gafara duka abubuwan damuka miki dagani har matata dakuma yarmu Rakiya, dama rayuwa yagaji haka, sanan ina mai miki fatan alkhairi ina addu’a Allah ya sanya albarka awanan Auren naki, Allah yabaku zaman lpy da yara nagari, kiji tsoron Allah kiwa mijinki da iyayenshi biyayya, yi nayi bari nabari haka ake rayuwan aure, Zayn yaron arziki ne bazaki taba damin miji kaman shiba dan haka Farra’u kimai biyayya, Sallu Alal Nabiyil Kareem” duka yan dakin akace “sallallahu alaihi wa sallam” akahau yima annabi salati ana addu’o’i Farrah gabaki daya tama kasa tantance metakeji kawai jikinta yadauki zafi.
Saida aka gama addu’o’i sanan Malam yakara mikewa daga inda yake gaban Farrah yaje hannunshi yasa yakama hannunta anatse yace “taso” hannun Shafa Farrah tasaki kanta akasa tamike tsaye ahankali tanajin kanta kaman iska zai kwasheta tazube awajen, tafiya Malam yafara da ita har zuwa kan kujeran da Zayn yake zaune kusada babanshi idanunshi kyam akan Farrah da kanta ke kasa gyale yarufe mata fuska, hannun Zayn Malam yakama hakan yasa Zayn shima yamike tsaye kaman yanda Malam da Farrah suke atsaye, anatse Malam ya damka hannun Farrah cikin nashi yace “Zayn ga diyata, mata kuma agareka halak malak nabaka amana” Malam ya janye hannunshi, wani kalan cute smile Zayn ya sauke yana kallon fuskan Farrah, ahankali Yakai hannayenshi biyu yasauke gyalen dake lullube da fuskanta zuwa bayan wuyanta yana wani kalan kallon fuskanta cikeda so dayaki boyuwa, hannunshi yabude ahankali yasata ajikinshi ya rungume yabata halal hug yana kallon duka yan dakin yace “Baba nakarbi amanan nagode dakabani Farrah Baba” yan kauye duk sukahau murmushi akunyace Dad na dariya kaman shine ya rungume matarshi dan dadi, Farrah dake cikin jikinshi jitayi kaman ta dayemai fatan kirji da hakoranta yanda yake wani jin dadi abin nakara bakanta mata rai, almost 5min yana rungume da ita ganin abin yaki karewa gashi sai bama yan kauye kunya yake yasa Dad yace “kai ya isa haka nan yo ba matarka bace ko ance za’a kwace maka itane” dariya kowa na falon yayi hakan yasa Zayn yasaketa yanadan sosa kai, saikuma ahankali yaja gyalenta ya maida mata yana kallon fuskanta so kawai yake suhada idanu amman ina idanunta na kasa, Malam yakalli Shafa yace “Shafa keda Rakiya kuzo kutafi da ita chan bangaren mu, bayan angama komi anjima da daddare zamu kaita dakin mijinta” wani kalan faduwa gabanta Farraj yashigayi tanaji su Shafa sukazo suka wuce da ita chan bangaren da aka basu dasuka sauka akayi da ita, suna shiga atsakar falo Farrah tazube tana taba kirjinta dataji yamata nauyi sosai Shafa data karanceta ta girgiza mata kai dan batason tai abinda zaisa Rakiya tagane komi, Rakiya dake kallonta tace “Maiya sameki Yar kanwata kirjinki naciwo ne” tai maganan tana yashe baki, ahankali Farrah tadaga jajayen idanunta takalleta Rakiya data kusan kasheta da duka da wahala tana mata kashaidi kan Moddibo kullum ne yau take kiranta Yar kanwata rayuwa kenan, girgiza matakai tayi takalli Shafa tace “Shafa kaini dakin ku” dagata Shafa tayi suka shiga ciki zuwa dakin da aka basu suna shiga suka maida kofa suka rufe itakuma Rakiya ta zauna afalo tanacin ragowan kajin dasuka bari dazu da aka kawomusu da abinci.
THIS BOOK IS NOT FREE❌
Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal.
Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461