← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 94

Sashe 17

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren 6 nasafiya wani kalan sanyi dakuma zugi na innanaha da hannunshi keyi yafarkan dashi daga wahalallen baccin dayakeyi bude idanunshi tass yayi yanabin dajin dasuke da kallo gasu Lamido duk suna kwance akan bargon dasuka shimfida akasa suna shakan bacci abinsu shikuma kwance a kan ciyayi, wani kalan fuzar da iska yayi abakinshi yana kokarin yunkurawa yatashi zaune amman yakasa sabida hannunshi dayake akarye kaman ya kurma ihu yakeji hannun ya kumbura, ahankali yabi buredi da pure water da aka bashi jiya daya zubar yakeyi akasa da kallo, yunwa yakeji bana wasa ba rabonshi da abinci tun na safen jiya da Mami tabashi baida wani cin abinci dama sabida su taba da sauransun dayake sha suna cikamai ciki amman inhar bai shaba sanan baici abinci ba yunwan dayake zuwa yaji yana zama extreme, dudda kalan yunwan dayakeji baikai kalan kishin ruwan dayakeji ba, lips dinshi sun bushe, bakinshi ya kape sabida tsan tsan kishi dayakeji ga azaban ciwo, tunda yake shi baima taba ganin pure water ba sai jiyan dasuka bashi, ganin abin yayi kaman fitsari amman yanda yakejin kishin nan yanzu he’s willing yasha maybe yamasha zaiji sassauci a zugin da hannunshi kemai, yunkurawa yayi da hannunshi dakeda lafiya amman ina abin yagagara sabida hannun a daure suke tare koyaya yay motsi damai lafiyan saiyaji amara lafiyan, wani kalan kara na azaba yasaki yahakura da tashin yana kallon sama yana tunani cikin tsananin tsoro da azaba da fargaba dakomi ma yace “am I going to die”? Yay maganan ahankali muryanshi a tsinke shi baitaba sanin akwai kalan wahala da azaba haka aduniyan nan ba saiyau, hawaye ne suka zubo daga gefen idanunshi na tsananin wahala ahankali yace “Dad, Mami I am scared” yay dan shiru sanan kaman karamin yaro yace “I am afraid of this place, I am afraid of this people, Papaaa” har cikin ranshi yakejin tsoron komi na wurin, shi baitaba fada ba, he just lived a wired life, baidama friends at all, rayuwanshi kawai yayi shaye shaye, yaci abinda yakeso, yasha abinda yakeso and have sex, ko matayen dayake sex dasu bawai yana magana dasu bane no, kawai yayi abinda yakeso yabasu kudi su wuce, ko kina sonshi kin sama kanki wahala ne dan baimasan yaya ake soyayya ba, baisan anything kan life ba, his entire life revolve around, shaye shaye, cin mata, kallon ball, ga zuwa club, babu any aboki namiji ko Aboki ya mace in his life, he is Zayn, and he is alone kaman yanda Baban shi ya haifeshi alone haka ma life bashing yake alone. Baisan inane wajen nan ba, baitaba zuwa wani gari a Nigeria ba banda Abuja wanda nan iyayenshi suke sai lagos, lagos ma airport kadai baitaba fita daga airport ba, baisan inane nan ba, baisan wani daji ne nan ba, baisan tayaya aka kawoshi nan ba, tayaya su Papa zasu rescuing nashi, ahankali yace “am I gonna die today”? Yakara tambayan sararin samaniya dayake kallo wanda rana ke shirin fitowa, hawaye ne suka zubomai ahankali cikin wata kalan raunanniyan murya irin muryan wanda yay loosing hope completely dinan yay giving up yace “Ya Allah save me please” (niko M shakur nace yau kasan da Allah Zayn).
Tafiyan abu dayaji akan hannunshi yasa dasauri yajanye idanunshi daga sararin samaniya yakalli hannu, wani bakin babban gizogizo yagani irin na dajin nan wani kalan zabura yayi yatashi yakwala ihu. “Ahhhhhhhhhh Spider, Spiderrrrrrrrrrr somebody help meeee” yanda yake ihu with all his power saika tausayamai kaman zai zare, farkawa kidnappers din sukayi jin kalan ihun da Zayn keyi duk atsorace suka zazzauna, ganin yanda yake ihu yana juye juye yakasa kabar da gizogizon shima gizogizon ya rude dan ihun Zayn ya rudashi yana neman hanyan guduwa, wani kalan tsaki Oga yaja. “Mtssswwwww what kind of a spoilt boy is this” sanan yakalli Lamido yace “please tashi kaciremai abinchan daga jiki koyabar kunnuwanmu suhuta dan dodon kunnena na gab da mutuwa” azuciye Lamido yatashi zuciyarshi tai bakin kirin sabida yanda Zayn yatadasu daga bacci yana zuwa gabanshi hannu daya yasa yacire gizo gizo yaa jefar sanan akufule ya dumama Zayn wani annamimin naushi akan idonshi yace “dan shegiyan yaro kawai malalaci gizogizo yakema ihu haka saikace mace” tashi Oga yayi dasauri ganin nushin dayama idanun Zayn dayasa Zayn yakife fuskanshi kan kafafunshi dasauri yace “haba Lamido kakosan iyayen yaron nan zasu tambayi proof of life zaka tsiyayemai idanune” cikin fushi Lamido yajuyo yadawo Ya kwanta yace “shiyaja ai uban wayace yatadamu kashe shi girgizon zaiyi, saisa na tsani yaran masu kudin nan wlh, bana ragamusu idan mukai kidnapping nasu, Allah ya soshi namiji ne da wlh ya cinyemai gutsu” kallon Lamidon yayi dahar yamaida idanunshi Ya Lumshe sanan yakalli Zayn da fuskanshi ke kife kan kafafunshi yay shiru kaman anyi ruwan sama an dauke sanan yakoma shima ya kwanta ranshi abace da abinda Lamidon yayi.
Zayn ji yayi idanunshi na dama da Lamido ya nusa yama daina aiki, jiyayi kaman irin an fasa kwai abu kawai tsiyayowa yake daga cikin idanun hakan yasa yay shiru yama kasa kuka yakasa ihu yakasa komai sai dan karen azaban dayakeji gashi bazai iyakai hannunshi yataba idanunba saisa kawai yadaura fuskanshi akan kafafunshi yay shiru yariga ya sadakar mutuwa zaiyi.
****

Saida ta chanza kaya agurguje kafin ta kwaso tumakon su fito tana addu’a Allah yasa kada Rakiya ta rutsata agidan, kayan fulanin ta tasaka dan rigan fulanin da suka koma kaman brown tsabagen sakawa koda yaushe yay mata chachas ajiki sai zanin dabai gama kaimata har kasa ba ta daurashi tsaf sai fararen kafafun dake sanye da silipas dinta da duk yagama sudewa shima Shafa tabata, kanta ta daureshi tsaf da adiko (dan kwali) na wani kodaddiyar atampa, goshinta sanye da wani oldi (sarka) ja na beads dayan fulani kesawa a goshi, kunnenta na sanye da dankunni na beads suma ja, sanan tadaura babban hulan hat 👒 na zuwa kiwo dinan akanta tadaure igiyan a gemunta sabida rana, hannunta rikeda sandar kiwo, tai wani irin bala’in kyau dudda babu wani something meaningful kokuma mai kyau ajikinta amman ka kalleta baraka iya cire idanunka akanta ba saika gama karemata kallo tsaf sabida she looks simply beautiful abinda yake karasa Modibbo ke bala’in sonta kenan.

Ahankali take tafiya sabida yunwan datakeji tun safe ko ruwa ba’a bata tasha ba, amman bata wani damuba dan yawanci dama idan tafita kiwo saitayi nisada karkaran su zata tsaya ta tatsi nonon shanu tasha abinta tai nak sanan tasakesu tashige cikin wani kogo Awani dutse daya zaman mata kaman gidanta tai bacci ta abinta.

Sosai tai nisa dan sunbar karkaransu gabaki dayama suna dajin Allah awakan sai cin ganyayyaki suke suna jin dadinsu, gawani babban dutse (rock) awurin tsakiyan dajin hawa dutsen tayi sanan tashiga cikin wani lungu daga waje bazakace lungun nada fadi aciki, daga waje barama kagane lungu baneba dan yay kama da dan fashewan dutse, sai kashiga daga ciki, fadi ne dashi dayay girman daki gawani kalan sanyi ni’ima aciki, wani kofi ne mai kyau awanke awajen, tsugunnawa tayi tadauka tana murmushi sanan ta ijiye sandarta tajuya tafice, cikin tumakan ta shiga sanan ta tsugunna gaban wata saniya ta tara kofin tana tatsan nono tana murmushi, saida tagama tatsan iya nonon datakeso sannan ta mike tsaye rikeda cup din a hannu yana kallon fresh nonon dake cikin kofin, wani kalan murmushi tasaki daya bala’in karama fuskanta kyau sanan tawuce wajen dutsen tahau batare daya shiga kogon ba tazauna awaje, ijiye kofin tayi agefenta sanan taja hulan kanta ta saukarda shi abayan wuyanta sanan tasa hannu tadauki kofin takai bakinta tafara shan nonon, tanasha tana kallon yanda shanaye da tumakan ke shanawa abinsu sunacin abincin su suma, kaman daga sama taji wani kalan ihu daya bala’in firgitata saida cup din hannunta ya kibude yafadi tundaga nan sama inda take har zuwa chan kasa nonon ciki yabare akasa kofin ya fashe, bin ko’ina tashigayi da kallo bataga kowaba, duka rugarsu ita kadaine kezuwa kiwo wajen nan dan nan bangaren dajin babu kowa anrigada anfita daga karkaransu daman gudunma su Modibbo kada yasan inda take zuwa kiwo yasa batayi a rugarsu saita kawo tumakan sun fita daga gari, cikin ikon Allah kuma Allah yabata har daki awajen Wanan dan kogon nata idan tazo dazaran tagama shan nono shiga take ta narki bacci abinta bayan ta tashi takara debo nono tasha sanan da yamma sutafi gida. Babu wani kwana ko lungu da sako dabata sani ba cikin wanan dajin gabaki dayanshi, bata sabajin mutane adajin ba hakan ta firgita sosai to waye adajin nan dahar yake ihu? Kodai koma waye ke ihun maciji ne ya sareshi kokuma wani abune yafaru? Taje taduba ne? Wani kalan ajiyan zuciya tasauke tasan ba Modibbo bane dan baisan wajen nan ba, hannunta tasaka ahankali tabaya tajawo hulanta tamaida kanta tasake kulle igiyan da kyau yakama fuskanta chas, sanan ta tashi tashiga kogon sandarta tadauko tafito wanan karan bata tsaya sauka normal sauka ba wani kalan tsalle tayi tadiro tundaga kan dutsen har kasa chak, murmushi tadanyi dan ta tuna Shafa ne, Shafa tahanata tsalle tsalle da dirke dirke tacemata babu kyau mace nayi.

Ahankali tafara tafiya zuwa direction din dataji ihun wanda taji yataho daga yankin gabas din dajin, gently take tafiya babu ko alamun tsoro akan fuskanta sosai tai tafiya mai nisa bataga wanda yay ihun ba hakan yasa tace to Kodai kunneta ne kokuma kukan tsuntsune, dan tabe baki tayi ganin tayi nisa sosai da inda take tajuya tafara tafiya kaman daga sama taji magana. “Nifa nagaji Lamba tun jiya banci abinci mai kyau ba, munje rugar fulanin chan ko shaguna basu dashi, gashi Oga yahanamu mu shiga cikin city mu kashe yaron nan muhuta” jin sahun tafiya yasa dawani irin sauri Farrah takalli bishiyan dake kusada ita na mangwaro dayakeda ganye acike, hawa bishiyan tayi da bala’in sauri kada aganta abunku da yar karama bacewa tayi asaman bishiyan tai lamo tana rungume da sandarta kirjinta na bugawa dum! Dum! Dum!
Chapter 17 · 0% Book details