← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 94

Sashe 36

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Saida tashiga cikin motan sanan tadan saci kallon Zayn, yana sanye da T-shirt fari kal, da 3quater maroon dasuka haska jikinshi, wani kalan hadadden kamshi natashi daga jikinshi kunnenshi daya yamakala wani diamond earring akai, waya yake danna waya kaman baisan mutum yashigo cikin motan ba, dauke kanta tayi tashiga wasa da yatsunta kaman bazata ce komiba saikuma ahankali tace “ina yini Ya Zayn!” Faduwa gabanshi yayi dum! Kiranshi da Ya Zayn data karayi janye idanunshi yayi daga wayanshi yadan kalleta gyalen kanta yadan zame baya hakan yasa yana iya ganin kitson da aka mata dayama kanta kyau sosai, dauke kanshi yayi dasauri kaman bazaice komiba murya chan kasa makoshi yace “wacece wannan yarinyar”? Wacece wannan yarinyar itama bama tagane hausan nashi ba wlh, gane kaman Maryam yake nufi yasa tadan saki cute smile tace “sunanta Maryam, Miemie, uhmmm uhmmm” tai maganan tana kokarin kiran sunan da Maryam tagaya mata saikuma da sauri tadagakai ta kalli Zayn din dake taba waya tace “B….F….F Uhmmmmmm…” tai shiru tana kokarin tunawa sanan dasauri tace “Bes…….” Dan dago kanshi Zayn yayi ya zubamata mayun idanunshi yana kallon effort din dayake putting on just to get the word, ayangance yace “Besty”? Gyadamai kai tayi ahankali tana hadiye murmushin datakeyi ganin idanunshi dataga sun wani kalan cikamata idanu, dauke kai yasakeyi ganin yanda tayi sanan ahankali yace “BFF means Best Friends Forever” sake gyadamai kai tayi sanan ahankali tace “ina sonta sosai” dan dago kanshi yayi yakalleta hada idanu sukayi atare dukansu kowa ya dauke kai tamaida kanta kan titi tana kallon hanya tana murmushi shikuma yana dan daddanna wayanshi, kaiwa gida sukayi ga aka bude musu gates din one bye one suna shiga harsuka karaso wanda zai sadasu to compound dinsu suka shige, Matayen Dad dukansu na zaune a garden sun kira wani spa home service ana musu gyaran farce, Mami ce tabude kofa tafito daga flat dinsu ganin motan Zayn yashigo, kafin ma abude mata kofan Farrah tabude kofan tafito rikeda jakan makarantan ta batare data dauki ledan uniform ba wani kalan murmushi tayi ganin Mami tafito dawani kalan sauri hade da gudu tai wajen Mami rungumeta tayi da karfi Mami ta kwashe da dariya tace “oyoyo oyoyo yarinta na tadawo daga school antafi da kuka andawo da dariya ko” boye fuskanta tayi acikin Mami tanadan dariya sanan tadago kanta tace “Mami nayi BFF sunanta Maryam, Besty na” ware idanu Mami tayi tace “Iyye jeki gaida su Hajiya saikizo muje daki kibani labarin” Mami tai magana tana nuna mata su Hajiya dake garden ana musu gyaran farce, karban jakan bayanta Mami tayi hakan yasa tawuce tana tafiya ahankali kanta akasa sabida yanda kowannen su kemata mugun kallo harda Hajiya Maryam Amaryan Alhaji dantunda taji labarin Alhaji yay adopting yarinya sanan Mami yakara bamawa taji ranta yabaci, tsugunnawa tayi agabansu ahankali sanan tace “ina yinin ku” gabaki dayansu babu wanda ya kalleta ma, Hajiya Maryam tace “Anty Mariya yaushe zamuje Dubai trip dinan” baki Farrah takara budewa ahankali zata kara gaidasu taji ance. “Farrah!” Faduwa gabanta yayi dasauri tajuyo da kanta, Zayn ne yana tsaye nisada su fuskanshi babu alamun murmushi yace “come here” tashi tayi ahankali tazo inda yake tsaye, wucewa hanyar dakin Mami yayi hakan yasa itama tabishi Hajiya Mariya tadaga murya tace “gantalalle wanda aka sameshi ta hanyar iskanci saisa yake dan iska, ubangiji Allah yasa ka kare ahaka” chak Farrah ta tsaya jin zagin da akamai juyowa tayi tabude baki zatai magana taji anfizgota afirgice tajuyo Zayn ne yajata yamata wani kalan mugun kallo binshi tayi suka shiga cikin dakin, Mami dake dinning murmushi tamusu dasauri Farrah tai wajenta tace “Mami wanchan matan nama Ya Zayn mugun addu’a” dan murmushin yake Mami tayi tace “Allah bazai amsa ba, zauna kici abinci saiki je kiyi wanka, Zayn” takira Zayn dake kokarin zama afalon tace “come and eat” tahowa yayi ahankali zuwa dinning din zubamai fried rice tayi da chicken ta tura gabanshi tace “please Zayn na sanka I don’t want more trouble kada kafadama Baban ka any of this kaji” dan kallonshi Farrah itama tayi, gGyadama Mami kai yayi sanan yasa spoon yafaracin abinci itama Mami ta zauna kusada Farrah tace “yi sauri ki cinye kibani labarin Maryam”

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

THIS BOOK IS NOT FREE❌
Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal.
Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461
DUK WANDA/WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

EPISODE 2️⃣8️⃣
Bayan 3 months
Farrah ta kile kaman ba itaba, tayi dan kiba taciko, Mami na kulada ita naban Mamaki, inba wayanda sukasan Mami ba ba’a banbance cewa Farrah ba yarta bace dan tamafi kama da ita kan Zayn dan Zayn bakin Baban shi yabiyo itakuma mani fara ce kaman Farrah.
Mami har tsoron brain din Farrah take yanda take gane karatu both Islamiya da boko, Mami na kulada ita na musamman har yanzu bata bari an bata waya ba cus tanaso ta natsu tai karatu kozata bari abata waya saitajai SS2, ta wayanta take waya da Miemie da yanzu suka bala’in shaku dudda haryau bata taba zuwa gidan su Miemie ba itama Miemie bata taba zuwa gidansu ba but babu wanda baisan kawancen su agidansu ba.
Farrah rabonta data saka Zayn a idanu harta manta tun ranan daya daukota daga school ita batasan inda yake ba kuma bata tambaya ba.
Chapter 36 · 0% Book details