← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 94

Sashe 34

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda tashiga motan tai shiru, komi na zaman mata kaman mafarki haryau takasa manta rayuwanta just like a week ago, tun tana Yar yarinyar ta takeshan wahala agabanta aka kashe yar uwanta, dakin datake kwana na wajen tumakan gidansu, abinci saita sata idan su Inna basa nan, Shafa ita kadai ke sonta aduka garinsu, Shafa na yawan gayamata watarana sai labari wataranan ne yazo yanzu, wanan da rana daya kawai tafita taga za’a kashe mutum ta ceceshi gashi yanzu iyayen mutumin sun zamarda ita yarsu gashi yau zataje makaranta, girgiza kai tayi tareda murmushin kuka hawaye yazubo mata sharr dasauri tasa hannu tashare hawayen, hanya ta kalla tanason gidan nan babu kaman Mami dake koyamata karatu, ta shiryata ko da maman su na raye tana sonsu amman kullum fita take saida nono dakuma idan anyi karaya akirata Mamanta kullum wahala take danta kawomusu abinci basu taba ganin Baban su ba koma waye mahaifinta bazata taba yafemai ba dan mahaifiyar ta rasu da wahala hakama yar uwarta, koba komi zata dage tai karatu tanaso tazama likita kaman Mami sabida ta taimaki mutane da mata dayawa bataso mata sudinga mutuwa sabida rashin samin likita dazai lurada su. Kankame jakan makarantan ta tayi akirji tareda lumshe idanu ita tana tunanin zuci, parking dataji anyi yasa dasauri tabude idanunta tana kallon wajen, gaban wani hadadden school sukai parking, ganin motoci tayi kala kala ana parking ana sauke student maza na sanye da dogon wando, da shirt da jacket da necktie, mata kuma na sanye da skirt daya tsayamusu a guiwa da shirt da jacket da nectie sai hula na beret, da fararen safuna akafafunsu da farin safa kowa na shiga cikin school din, kana ganin school din kaga school na yan gayu, tana zaune ahaka lost in thought tana kalle kalle bodyguard yabude mata kofan motan, adan firgice ta kalli bodyguard din sanan tafito ahankali tana kankame da jakanta a hannu kaman irin mutanen nan da aka dauko daga kauye ana shirin kwace musu jakansu, zagayowa ta inda take Zayn yayi yana tafiya ahankali yana gyara zaman farin glasses na idanunshi dan satan kallonshi tayi da sauri tadauke kai wuceta yayi hakan yasa tabishi da sauri suka shiga cikin school din student na kallon Farrah duk inda sukayi sabida yanda ta kankame jakan makarantan ta a kirji tan tafiya kaman wacce ke shirin sata, ganin yanda ake kallon Farrah some student na pointing nata ana dariya yasa Zayn ya tsaya chak batare daya juyoba yanda take kalle kalle tana biyedashi yasa bamata lura ya tsaya ba kawai karo taji taci dashi students sai dariya, juyowa Zayn yayi yakalleta itama kallonshi tayi jikinta har bari yake baki ta tabe zatai kuka idanunta sun cika da kwalla sosai girgiza mata kai yayi tareda kai hannunshi ahankali ya karbe jakan data kankame akirjinta, zagayowa yayi ta bayanta ya tsaya yakama hannunshi da kanta yasaka mata jikinta na rawa sanan yazo ta gefenta yakama hannunta sukai wajen lift ya shiga da ita sanan yasa 5th floor yarufe kofan, jin abu na sama yasa kuka data rike da kyar tasakeshi hannunshi takama da sauri takalli fuskanshi cikin muryan kuka tace “Ya Zayn dan Allah kamaidani kauyen mu ni banson makarantan nafasa” baitaba jin abu yabashi dariya ba sai yGau.

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣5️⃣
Gimtse dariyan yayi yadan daure fuska baisan ya akayi ba kawai ji yayi yace “dama kinada tsoro”? Gyadamai kai tayi kaman wata Yar little baby tace “za’a dingamin dariya idan ban iya abu ba” yatsine fuska yayi kaman baiso yay maganan sai kuma ahankali yace “I will teach you” dan kwalalo mai manyan idanunta dake jikeda hawaye tayi alamun bata ganeba ahankali yace “zan koyamiki anything dabaki iya ba, babu wanda zai miki dariya” gyadamai kai tayi tasauke kanta kasa har lokacin jikinta na bari tana wasa da yatsunta, yatsun ya kalla saikuma yadauke kai yace “kidaina jin tsoro babu abinda zai faru” gyadamai kai tayi daidai kofa yabude yafice tana biyedashi tana kalle kalle har office din headmistress din school din, suna shiga office din Babban matan dake ciki wanda kana ganinta kasan itane headmistress din tace “ohh Zayn welcome, sannunku da zuwa have a sit” zama sukayi tana kallon Farrah tace “hello pretty lady” Farrah tasan hello hakan yasa ta kakalo murmushi ahankali tace “ina kwana” murmushi matan tayi tace “lafiya kalau” sanan takalli Zayn cikin harahen turenci tace “your Mom told me everything about her, zamu mata papers na primary school, yanzu abinda zai faru I will test her inga daga wani class zata iya farawa” wani textbook na English na SS1 matan tabata tabude mata wani passage ta tura mata gabanta tace “read this Farrah” tanuna mata wajen dan kallon matan Farrah tayi dudda bataji turencin ba tagane cewa karanta duka rubutun wajen akace tayi, ahankali ta gyadama matan kai, Zayn takalla ahankali shima kallonta yake raurau tayi da idanu baisan mesaba ji yayi kaman shima yace yafasa sakata a school din yatafi da ita sabida yanda tayi dauke kanshi yayi da sauri yaciro wayanshi yafara dandannawa headmistress din tace “uhum ina jinki Farrah fara” Gyadamata kai Farrah tayi dasauri kafin ahankali tace “kam…..fri…hen…..shon(comprehension), da…..man…..sta…..tree(the monster tree)” dan murmushi headmistress din tayi ganin daga asalin farkon page na textbook din tafara bama passage din take karantawa ba, dudda haka tayi kokari, dama the main challenge da ita da Mami suke tsoro shine yazo bata iya hada baki ba amman tunda yanzu ta iya hada baki kawai ahausance take karatun turencin she will pick up fast, wani takarda da maths question ke ciki aka bata wanda mainly addition subtraction da multiplication ne aciki, sai kuma numbers raise to power 2, pen tabata tace “yimin lissafin nan nagani” karban pen din tayi tayi talla hakan yasa ta iya lissafi kuma tun a primary school datayi tasan addition subtraction multiplication sign da square and power sign nan da nan tayi taba headmistress din dubawa headmistress din tayi with so much excitement tace “good job Farrah” dudda Farrah batasan metace ba but yanda tai maganan tasan ance tai daidai ne tai kokari washe cute white teeth nata tayi ta screen na wayanshi yake kallon face dinta, murmushi yadanyi ganin this is her first smile tunda tazo school dinan, tashi headmistress tayi tace “muje nakaiki class naki SS1, Zayn wait for me here u will fill out the forms” tashi Farrah tayi ahankali tana kallon Zayn ganin yanda ta tsaya yasa headmistress tace “Zayn baraka bimu ba” dan dago kanshi yayi yakalleta tashi yayi ahankali yafice tabishi dasauri har class nasu anan sama shiga class din headmistress tayi da ita shikuma ya tsaya abakin kofa teacher na ciki duka ajin tashi akayi aka gaidata murmushi tayi tace “settle down student, this is your new class mate, everyone welcome Farrah Muhammad Ganuwa with Atama clap, ATAMA 👏 ATAMA👏 LABAKO👏 LABAKO👏 LAMARINAAAAAAAA👏👏👏👏” yanda suke tafi headmistress namusu wakan Atama saida yasa Farrah taidan murmushi tana kallon yan ajin, dan tabe baki Zayn dake kallonta yayi yace “silly girl” headmistress tace “can I hear you all say welcome Farrah” atare duka yan ajin sukai ihu “welcome Farrahhhh” washe baki Farrah tayi sanan Headmistress tabata wani sit dake gaba gaba tace “once yayanki yagama cike komi zansa akawo miki all books and textbooks naki” Gyadamata kai Farrah tayi sanan headmistress tajuya tafice Farrah na binta da kallo, leka wajen tayi ganin bataga Zayn abakin kofan class din nasu dayake da ba, kalle kalle tashigayi ta window chan saigashi yazo zai wuce yana maida waya aljihu kaman waya yayi kallo ajin yayi dasauri tadagamai hannu alamun bye dauke kai yayi kaman bai Santa ba hakan yasa ta harareshi. “Focus Farrah” malaman dake ajin tai magana da sauri Farrah takalli gaban allo gabanta nafaduwa.

Komawa office sukayi kudin komi Zayn yabiya tundaga kan takalmin makarantan su, socks, sport wears, uniform, books, textbooks, babu single abu na school din dabai biyamata ba sanan ya ciremata all the forms tass kusan 1hr yayi a school din sanan yagama komi, headmistress tayi tace “ko waye direba nata dazai dibga zuwa daukanta idan an tashi needs to go to our security office yay register sabida asan dashi, we don’t release our students to just anybody for safety purpose” kallonta Zayn yayi kaman bazaice komiba sai chan yace “for now I will be the one coming” murmushi headmistress tayi tace “indai kaine ba matsala” tashi yayi yace “lemme get going” gyadamai kai headmistress tayi tace “regards to your Mom” ficewa daga office din Zayn yayi headmistress na binshi da kallo saida yafice ta girgiza kai ahankali tace “yaran yanzu, Allah dai ya gyara mana jibi yanda ya maida gemunshi jama’a, wai Wanan ne gayu awajen su” secretary nata ta kwalama kira tana shigowa note and textbooks na Farrah da Zayn yabiya tanuna mata tace “kaima Farrah GSS1 Science” kwasa tayi tafice.

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣6️⃣
Sosai take concentrating a karatun da ake koyamusu her only problem shine rashin iya turenci, ranan gabaki daya maths da further math kadai tasan tagane shima sabida lissafi ne amman sauran abubuwan dasukayi bata ganeba sabida rashin iya turenci.
Chapter 34 · 0% Book details