← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 94

Sashe 10

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saida Alhaji ya tabbatar bacci yay awon gaba dashi sanan yazare hannayenshi daga cikin gashin kanshi dan sosamai kai yakeyi saisa yayi bacci, tun yana yaro yakeson ana sosamai kai tareda dan massage nan da nan zakaga yay bacci, kwalin taba yaga ya leko daga aljihun riganshi, ahankali Alhaji yasa hannu yadauki kwalin yana karantawa sanan gentle yabude kwalin, karan tabane aciki guda 6 da lighter mai kyau, wani irin ijiyan zuciya Alhaji yasauke ahankali sanan yace “why Son?” Har cikin ranshi baiso Zayn yafara shan taba ba amman kuma bazai iya hanashi ba shifa komenene inhar zaisa Zayn farin ciki zai iyamai, kawai maidamai kwalin yayi a aljihu yace “dasauki taba kakesha ba giya ba ko wiwi, shima kuma taban nan gaba zaka daina duk kuruciyane ke damunka” sanan yatashi ahankali yay folding hannunshi akirji yana kallonshi kaman zai hadiyeshi, aduniyan nan kap baida abinda yakeso kaman yaron nan, shi kanshi baisan iya adadin son dayakemai ba, baiso daidai da sauro yacije shi balle kuma uwa uba mutum yabatama dan shi rai ai sai inda karfinshi yakare kodako mahaifiyar shi ce, indai kanaso kaci riba dashi kasamu kome kakeso daga wajenshi to kabiyo ta hannun Zayn, takalmin kafanshi yabi da kallo hakan yasa yazo bakin royal bed din ya ciremai takalmin yana kallon yatsun kafanshi komi na Zayn irin nashi ne wato da Allah yatashi mai kyautan Zayn yamai kyautan ne nagata dan yaro yabashi da komi sak nashi ya dauko jibidai farin fatan mahaifiyarshi mamarshi kaman baturiya dan Fulani ce ita amman bai dauko haskenta ba bakin fatar Babban shi ya dauko sak babu wani banbanci, murmushi Alhaji yakara yi sanan yaja bargo ya rufamai kafin yakara dukowa yatofamai addu’a sanan yabude wani sliding glass door yafito daga bedroom din, wasu bodyguards guda 4 ne gaban bedroom din ganinshi duk suka zube alamun gaisuwa, bama takansu yabiba yace “Zayn is asleep, dazaran yatashi akwai almond milk dinshi da honey nahadamai a glass cup kusada shi kubashi yasha sanan kumai setting ruwan wanka yayi daganan saiku barshi” dasauri sukace “yes sir” sanan yawuce yafita.

Wuraren 6 na yamma yatashi, shifa yanada son bacci, kuma yawanci yana baccin ne sabida baya na dare, dare yana club, bin dakin dayake yayi da kallo hakan yasa yaja dan gajeren tsaki tunawa dayayi yana Nigeria he’s not just happy, ahankali yatashi zaune yana bin dakin da kallo, ganin milk nashi akan side drawer yasan aikin Baban shine yasa ahankali yamika hannu yadauka yakai baki yanasha ahankali harsaida ya shanye sanan yatashi tsaye da kyar yana kara yatsine fuska wani haushi na kamashi ya danna wani botur a bango” da gudu all the bodyguards suka shigo dakin, tsaki yayi awulakance yace “I need just one person out!” Yay maganan kaman yanama kashi magana, duk wucewa sukayi suka fita daya ya tsaya wanda yake babban su, akufule Zayn yace “bakasan abinda yakamata kayi ba” wucewa dasauri yayi yashiga bayin ganin yariga ya shanye madaran, hadamai bubble bath yayi da ruwa mai dumi sosai sanan yafito, wani mugun kallo yakaramai yace “get out” wucewa yayi yafita shikuma yashiga cire kayanshi ahankali anan kasan dakin yabarsu yawuce yashiga bayin, idan kaga bayin zaka iya ranstewa ba bayi bane dan harda wani durmemen tv ne aciki, ga flowers ta ko’ina, shiga ruwan yayi yayi resting head nashi sanan yadauki remote ya chanza tashi zuwa na kwallo kafin ya ijiye remote din yanadan yatsine fuska wankan ma bashi wahala yake kaman amai, danna wani botur yayi dasauri bodyguard din yazo gaban bayin dan baima rufe kofa ba yace “yes Sir” “my cigarettes in my cloth” yay maganan agajiye kaman baiso yayi, kayan daya cire bodyguard din yashiga duddubawa ganin kwalin taba da lighter aciki yasa yashigo bayin yakawomai hannu yasa ya karba sanan yawuce yatafi, kunna tabar yayi yakai bakinshi ya zuko, wani kalan dadi yaji yadan lumshe idanu sanan ya fuzar da hayakin yana tunani saida yasha kusan kara 5 abayin sanan yay wankan da kyar yay wankan tsarki yafito yana daure dawani tsinannen towel dan karami a waist ya zauna kan kujera dake dakin yakara danna botur din dake wajen wani bodyguard ya shigo kafinma agayamai yasan mezaiyi bayi ya shiga ya wanko hannayenshi tass sanan yaje closet nashi yadauko wasu lafiyayyun cream kaman na mata yazo yana shafamai ko ajikinshi danna wayama yake saida aka gama sanan yafitomai da kayan dazai saka kallon kayan yayi native ne hakan yasa yace “get me english wears, i wants shorts, sneakers, neck chair, a t-shirts with my perfumes” komawa closet din yayi wani Kenzo belted straight short dark blue yadaukomai da dolce gabana white logo print t-shirt, sai Rick owens clip fastening neck chain silver, sai wani Bell & Ross 40MM diamond writs watch dawani Nike Air Force high top sneakers, saikuma wani farin singlet na CK da boxer ma na CK, da all turarukan shi yakawo mai, ganin kayan sunmai yasa da yatsa yamai alamun ya ijiye ya fice, ajiyewa yayi yawuce yafita shikuma yatashi ya shirya cikin kayan dasuka amsheshi sosai kaganshi kokai waye saika kara juyowa ka kalleshi sabida kalan kyan dayayi kana ganinshi kaga rich Bobo, wayanshi yadauka a hannu da kwalin tabanshi sanan yafito daga bedroom din saiga Baban shi dan tsayawa yayi ganinshi hakan yasa Alhaji yakaraso dasauri cikin falon yana kallonshi yace “wanan kyau haka da Son dina yayi sai ina”? Hannu yamikamai ahankali yace “car keys Papa” dan kallonshi Alhaji yayi sanan cikeda lallashi yace “Zayn nadauka yau hutawa zakayi ina kuma zaka daga zuwanka” hade fuska yayi yace “ka dawo dani against my will are you trying to ground me ne kuma yanzu” dasauri Alhaji yace “no no nooo, Zayn kasan duk inda zaka anan Nigeria u cannot go alone, nasan bazakaso hakan ba amman kayakuri nan ba Indiana bane please my Son, kaji yaron Albarka, nasan nama laifi but banace maka sorry ba” Alhaji yakara matsowa kusadashi sanan yadaura hannunshi yakama kafadarshi anatse yace “your Dad have so many enemies Zayn, inada yan adawa dani kaina bansan iya yawansu ba, kuma wanan da next meeting namu da board na directors dudda ban fadama kowaba but I am planning to announce you as the new CMD, inaso nabarmaka komi nawa nahuta na tsufa Zayn baka gani ba, so please Zayn dina you should be careful, ko’ina zaka go with bodyguards naka, go with them do that for your Papa please my son” yanda yaga Baban shi na lallabashi tunda ya iso garin nan yasa yaji yadan bashi tausayi, shi bawai ta CMD shi ko menene yakeba all he wants is kawai yafita yaji dadi, murmushi ya kakalo sanan ya gyadama Alhaji kai ahankali alamun ya yarda dasauri Alhaji yace “ka yarda bodyguards sudinga binka”? In a very very lazy voice yace “yes Paapa” wani irin dadi Alhaji yaji yaciro key mota daga aljihun shi yarike a hannu sanan yace muje waje kaga motan ka, waje sukayi bodyguards su hudun na binsu abaya wajen wata wild car Alhaji ya taaya sabuwa fil ko bare ledan kujerun ba’ayiba sanan yabama babban bodyguard din key motan yace “drive safe, kubiyu zaku dinga binshi” sanan yakalli Zayn din yace “ankira magrib muyi salla kafin kafita ko”yatsine fuska yayi ahankali yace “zanyi ahanya Papa” “tom adawo lpy, ku kulan mini da d’ana” atare sukace “yes sir” sanan daya yabudema Zayn din bayan mota, ahankali yatako yashiga bayan ya zauna sanan yamaida kofan yarufe yakoma gama ya zauna bodyguard dake tukin yaja motan Alhaji na daga musu hannu suka fice.

Wani kalan ijiyan zuciya Zayn yasaki murya chan kasa yace “I hate this house” murya chan kasa yace “take me to Area 3 Old lady’s house”…..
Chapter 10 · 0% Book details