← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 94

Sashe 54

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mai gari dawasu manyan mutanen gari ne suka tarbesu sanan aka hadu aka wuce falon mai gari, duk aka zauna kafin kace me mutanen kauye sun taru agaban gidan mai gari ana yada cewa gwamna yazo, saida sukadan natsu sannan Dad yafadi wanda suke nema tukunna da sauri Mai gari ya aika aje akira Malam yazo fada yanzun nan kada yabata lokaci.

Malam na zaune kan tabarma yanacin dafadukan shinkafa da wake dan yanzu rayuwa tai kyau tun kudin da Alhaji yabashi yanzu agarin sune yangayu bayan gidan mai gari, dagashi sai Rakiya ne agidan Inna as usual tanachan gidan nai gari sallama dayaji anata bugawa a kofar gidansu yasa yahakura da abincin yamike yana zura silipas yace “waye, ganinan zuwa” butanshi yadauka yakafa abaki yasha ruwan sanan ya ijiye yay zaure yabude kofa, ganin yaran mai gari Madibbo da babban aminin mai gari yasa yace “ah’ah Tanimu da Modibbo ne, Meya kawoku nan” Tanimu dake kallonshi yace “munyi manya manyan baki a rugar nan, mai gari na neman ka yanzun nan” dan zaro idanu Malam yayi yace “incedai Lafiya” dasauri sukace “lafiya lau muje ance kada mubata lokaci” gyara riganshi Malam yayi yace “to shikenan muje” yana biyedasu abaya har zuwa gidan maigari dayaga kusan duka mutanen karkaransu agaban gidan ga yan sanda nataresu kada su shiga, suna zuwa yaga anbarsu sun wuce faduwa gabanshi yayi yana tunanin mesukayi, suna shiga falon yaga Alhaji (Dad) da wanan kannin nashi (Uncle) dayama ganinsu yaganesu wani bakin yawu yahadiye yana addu’a Allah yasa badai sun gaji da Farrah sun dawomai da ita bane tunda tabar gidan nan gidan yanzu kaman anjanna more kudinsu suke sunaxin dadi hankalinsu kwance yana zaman lafiya da Inna abinshi idan sun dawomai da Farrah ai yashiga uku, waje yasamu ahankali yazauna duk jikinshi yau wani kalan sanyi yace “barkanku da war haka Alhaji dafatan kun iso lafiya, ince bawani abu Farrah tayi kuka dawo da ita ba”? Yay maganan yana karabin falon da kallo yana neman Farrah, murmushi kowa na falon yayi Maigari yace “ba abinda yakawosu ba kennan, abinda yakawosu yafi karfin wannan” wani kalan yankewa gaban malam yayi yafadi yakara kwalalo idanu yace “tooooh” gyaran murya Dad yayi yace “to Alhamdulillah da Allah yasadamu anan wajen gabaki daya” yadanyi shiru yanadan girgiza kai kafin anatse yadubi gwamna yace “gwamna wato kaga Allah yanada yanda yakeyin abubuwan shine sai yanzu nakara gasgata hakan rabo ne yakawo Zayn wanan gari” murmushi gwamna yayi yace “rabone kam yaron dako hanyan dazaibi yazo adamawa bai saniba balle kauyen kudiri” dan murmushi Dad yayi sanan yakalli Malam yace “Malam kasan nai adopting diyarka abisa ka’ida na shari’a dudda hakan bai dauke cewa amusulunce kaine mahaifinta mai asalin iko akanta ba tunda kaine yayan mahaifiyarta uwa daya uba daya saisa yau natako nazo garin nan domin ka” gyadamai kai Malam yayi yana kallonshi shi kawai kalman dayace yake bala’in tsoronji shine suce sun dawo da Farrah kokuma sun gaji da ita zasu maidota, Allah ka dawwamar da ita achan Malam yay addu’an azuciyanshi.

Anatse Dad yace “Malam namo nemawa yarona daka sani Zayn, wanda diyarka Farrah ta taimakamawa awanan gari, nazo nemama d’ana Auren yarka Farrah idan ka yarda” “waiiii!” Malam yafadi yana goge gumin dake ketomai yashiga murmushi yace “Alhamdulillah Alhamdulillah, yooo Alhaji idan ban baku Auren yarnan ba wayema zan bamawa” yasake washe baki yace “kuda kuka mata sutura sannan ni kawunta ma kukamin suruta ai nafadiwa mai gari shatara na arziki dakukamin dan haka Alhaji amatsayina na jinin Farrah, amatsayina na Kawu kuma Uba awajenta nabaku Farrah, ni so samune ma adaura Auren yanzu kubani sadakinta tunda ga mutane daman makil awaje ko mai gari” Malam yay maganan yana washe baki, mai gari ya gyadamusu kai yana murmushi yakalli Modibbo dake gefenshi yace “jekira Alaramma” dasauri Modibbo yatashi, Gwamna yabada ordwr anshigo da goro biscuit da alawa da abubuwa da yawa wanda yasa aka siyo aka loda a booth din mota tun da safe yau dama, nan aka shiga shigo da abubuwa Dad sai washe baki yake yakalli Uncle dake zaune dunkum kaman dusa yace “ciro wayanka kai video komi” gyadamai kai Uncle yayi yaciro wayanshi, Gwamna yace “abar mutane su shigo” kafin kacema fadan yacika makil wasu awaje wasu ta window, liman yatashi atake aka daura aure tsakanin ZAYN GANUWA && FARRAH MUHAMMAD akan sadaki miliyan goma!.

4️⃣7️⃣

Zaune yake a office din Dad yana sanye cikin wani black suit dayamai kyau bana wasaba idan kaganshi da farko baraka yarda Zayn bane dan he’s so concentrating, tunda Dad yabashi aikin nan sai yaune ranan dayasan yazauna ma aikin dan murmushi yayi yadago kanshi dan yagama cikin just how many minutes, hakanan kawai wani kalan faduwa gabanshi yayi dayasa ahankali yakai hannunshi kan kirjinshi yashafa daidai atishawa yazomai dan mikewa yayi tsaye yanabin duka office din da kallo kafin yakalli ogogon bangon office din yaga 1:30 na rana, dan ijiyan zuciya ya sauke sanan yafara tafiya yay hanyar kofa gently yasa hannu yabude kofan sanan yafita, Layla yagani zaune kusada secretary dinsu kallo daya yamata yadauke kai shi baison mace tafiya naci da maita offing nashi abin yake, maida kofan yayi yawuce dasauri Layla tabiyoshi daidai ya shiga lift kafin kofan yarufe ta shige tana kallonshi tace “wai mekake nufi ne batare akace muyi aikin nan ba kullum Saika dinga koroni kana hanani shiga office din” wani matsiyacin kallo yamata sanan ya yatsine fuska kaman badashi takeba wani kalan kulewa tayi hakan yasa tace “wai maisa kacika rainama mutane wayau Zayn eh inamaka magana kamaidani mahaukaciya” wani kalan juyoda idanunshi yayi ya kalleta sannan yadauke idanun abin bakaramin zafi yamata ba hakan yasa tace “wai sabida kazamiyan yarinyar nan Farrah kakemin haka?” Kaman ta tabo wani abu ajikinshi dasauri ya kalleta fuskanshi babu alamun wasa ganin haka yasa tace “yes Zayn, tell me meke faruwa dan bangane maka ba, kai mutum ne dabaka damu da kowa aduniyan nan ba sai kalla, why are you so caring towards that girl, kana fifitani akanta meta fini dashi? Nafita wayewa nafita ilimi nafita kyau nafita karatu, look at me kalli jikina babu abinda zaka nema da bazan iya baka ba, kana marina kanta tell me sonta kakeyi ne are you in love with Farrah Zayn!” Wani kalan bugawa kirjinshi yayi jin kalman so datafadi daidai lokacin sukakai ground floor hakan yasa yabi ta gefenta zai fita hannunshi takama dasauri tafashe da kukan datake rikewa sosai ahankali tace “Zayn please wlh kome kakeso zan baka, I want to be your girlfriend mudinga komi tare har shaye shaye please Zayn” wani kalan juyowa yayi yakalleta sannan yakai hannunshi kan hannunta data daura kan nashi yacire tareda murde hannun idanunshi suna kadawa yace “listen and listen attentively! Karki sake bari wannan bakin naki ya ambato sunan Farrah, and as for this place you can find anybody to work with but forget working with me and lastly” yay maganan yana huci yana matso da fuskanshi dab da nata yana kallon kwayan idanunta yace “I don’t f*ck beggars masu rokon maza su cisu naaaa! Zayn yafi karfinki” yakarashe maganan yana jefarda hannunta sanan yajuya fuuuu yawuce mosque abinshi.

Tsugunnawa awurin Layla tayi tana kuka, inhar bazata sami abinda takeso ba to wlh kome Momy keson mishi zata tayata, tanason Zayn yana bala’in burgeta saisa daman taso suyi soyayya suci juna dan Allah ya kera yaron da kyau wlh bata tabayin saurayi kwatankwacin Zayn ba balle nai kama da Zayn.

Salla yayi dan anriga anyi jam’i tun dazu yana idar da sallan ya jingina da bango yay shiru maganan Layla namai yawo azuciya are you in love with Farrah, son Farrah yake? Ya tambayi kanshi he’s trying to compare the thing yanzun nan Layla take kuka wiwi sosai agabanshi babu abinda yaji azuciyanshi saima dada murdamata hannu dayayi yamata warning kan karta sake kiran sunan Farrah, da Farrah ne ke kuka haka daba karamin damuwa zaiyiba, he can’t stand seeing her angry, nor sad, wani zubin idan yaganta he just want to tease her dan kawai tamai tsiwa tana zaromai manyan white eyes dinnan nata kaman idan ance ta dakeshi zata iya, he loves seeing her happy and smiling tunda yake baitabajin hakan game da any mace ba koda yay sex dake yaji dadi ba sai Farrah da babu abinda ya tabayi da ita beside ma she’s too small, is that what love is? Is he falling in love with Farrah yaya ake gane soyayya? Wayanshi yaciro dasauri yashiga browsing how to know you are in love with someone yadage yana karatun sosai.
Chapter 54 · 0% Book details