← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 92

Sashe 91

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

biyawa Zahra ta shirya domin taje tayi musu sannu da zuwa Sosai tayi mamakin Ganin yanda aka gyara gidansu da na su Asmy dakyal ta iya gane gidansu Dan har bene aka Dora musu Koda ta shiga ciki ma Saida tayi mamakin irin kayana alatun da aka zuba Baba ko hada kukan farinciki yake Yana godewa Allah na mallaka Masa Zahra a matsayin y'a itadai Zahra saidai tayi murmushi inda yayi Mata addu'a ta amsa da amen MD ko yasha ruwan addua Bayan ta huta gidansu dukda tayi mamakin rashin Ganin mama rabi a Gidan ta wuce gidansu Asmy nanma Tasha godiya da sa albarka Kukan farinciki ko maman su Asmy ta Shashi Bayan sun gama gaisawa Zahra tayi musu sannu da zuwa sai sannan ta samu Daman tambayar maman su Asmy ta ce mama Wai Ina mama rabi tunda nazo banganta ba "Girgiza Kai Mamansu Asmy tayi ta Ce "Ina ko zakiga rabi Ai tuni Malam ya saketa yaran Nan biyun dukansu sukayi ciki lokacin Yana batsari baisan wainar da ake toyawa ba Saida ya dawo Shima saidaga baya Anje cirewa Salamatu Cikin Rai yayi halin sa to kinsan dai maganar garin Nan magana ba boyuwa take ba asirinta ya tonu Wanda Malam ya saketa yace bazai iya Zama da ita ba "Salati Zahra tayi ta Ce "Wayyo Allah Salamatu ta mutu kenan bantaba sani ba Allah ya jikanta to Ina habibar ita ta haihu ne"Eh ta haihu d'an Wai ya mutu waya sani ma ko kashe shege sukayi"Sosai Zahra taji wani iri a ranta ta Ce "yanzu mama Suna wani Gida"Wama ya sane Mata Kullum Tana zarya Tana kuka Tana rokon Malam akan ya yafemata tayi nadama ya mayar da ita ya kiya yo me zaiyi da rabi matar da ta wulakantaki taso taga kin tozarta sai gashi kaikayi ya koma kan mashekiya Abu ya koma kan y'ay'anta shiyasa ba ason bin mutum da mugun nufi Shi shairi kwikuiyo ne Mai Shi yake dawowa"Sosai Zahra tayi sanyi ta ce "Mama Dan Allah tunda tayi nadama kusa Baki baba ya maida ita Dan Allah tunda tayi nadama kodan saboda su khairat Dan Allah mama "wani banzan kallo mama tayi Mata ta Ce "Amma bantaba sanin Baki da hankali ba Zahra sai yau matar da ta wulakantaki itace kike maganar ta dawo taci arzikinki ke wata irin zuciya ce Dake maimaikon kiyi farinciki mahaifin ki ya rabu da muguwar Mata shine kike kokarin ki Kara lakaba Masa"Ba Haka bane mama saboda su khairat za a duba"Barmun maganar Nan Zahra a Kama wata"da dare Zahra tajewa baba da maganar Akan ya mayar da mama rabi furtumarta yayi ya dinga Mata fada Akan Bata da hankali Sosai Zahra ta kafe hada kukanta Tana bawa baba hakuri akan Dan Allah ya dubi su khairat ya maidota idan ta sake wani abun saiya saketa dakyal ta samu ta shawo kan baba ya yarda Zai maidota Amma da sharadin saidai habiba ta koma wajen dangin babanta dan bazata shafawa ya'ayanshi kashin kaji ba ajiyar zuciya Zahra ta sauke ta ce ta yarda Koda baba ya maido mama rabi Bayan yayi Mata kashe sannan ya Dora da cewa arzikin Zahra ne taci harya maidota mama rabi kukan nadama hada durkusawa kamar zatayiwa Zahra sujjada Tana Mata godiya ta ce 'Har kunyar had'a Ido nake Dake Zahra ki yafemun irin zalincin da nadinga maki Shiyasa akace duk yanda ya rike Allah shiya rike Babban bango na tsaneki na tsangwameki naso ki wulakanta ki kaskanta saigashi Allah ya d'aukakaki d'aukakawar da bakowa Zai samu irinta ba Zahra a yanzu kina daya Daga Cikin macen da za ayi alfahari da ita a duniya ki yafemun Zahra nayi nadama har kunyar had'a Ido nake Dake gashinan muna Cikin cin arzikinki Shiyasa akace kaji tsoron mutumin daka wulakanta"Murmushi kawai Zahra tayi ta Ce "Allah yafe Mana tare mama"Kwana biyu Zahra tayi Wanda Cikin kwana Biyun mama rabi kamar ta goyata abinci ma saita tambayeta irin Wanda takeso Dan tunda mama rabi tasan cewar Zahra MD take aure ta sadakas tasan Zahra tayi daukakar da babu mahalukin da ya Isa yayi kasa da ita gwarama tayi hakuri ta dangwali arziki Rayuwar su Zahra na tafiya yanda ya kamata a Haka har lokacin bikinsu Chuchu ya gabato anfara shiryen shirye ta ko Ina Bangaren Zahra da MD ma Sosai suke Shirin bikinnan a Haka har lokacin bikinsu yayi Zahra hankalinta duk ya kasu biyu ga Gidan ammy Bangaren chuchu ga chan funtua Bangaren Asmy tunda aka Fara bikin take Shan gayu da wankan gwala_gwalai Sosai suke Shan masifar kyau ita da yaranta da suka Fara tafiya gwanin sha'awa duk inda suka gitta sai anyi sha'awarsu ana gobe daurin aure ta samu damar zuwa funtuaa Wanda motoci takwas sukayi Mata rakiya tare da security yanda kasan matar shugaban kasa ita kanta Zahra ta kalli wanna daukakar da Allah yayi Mata har hawayen farinciki take Wai itace Zahra da da ba abakin komai take ba yanzu ta daukaku har Haka Koda ta Isa Unguwarsu duk manyan motocin sun cika wajen kowa sai daukin su gaisa da ita ake Saida ta gaishe da tsaffin layinsu Bayan tayi musu alkhairi kafin ta shiga gidansu Asmy dakyal ta samu ta shawo kan mutuniyar Tata Akan tayi fushi sai yanzu take zuwa dakyal ta fahimta bayaninta na cewar hidimar gidansu mijintace ta hanata sakat Yauma dakyal suka barta ta taho Nan aka cigaba da shagali da Zahra da dare gidansu taje Dan ta kwana zo kuga murna wajen mama rabi Kira ta ce "lale marhaban ga y'ar arzikin tazo Yar albarka sannu da zuwa jikokina sannunku ta fada Tana yin sama da little itadai Zahra murmushi kawai take Bayan ta Gaisheta Nan khairat ta ruga da gudu Tana murnar Ganin Yar uwartata Haka safiya da yanzu itama ta Zama budurwa Mama rabi kusan raba dare tayi tana goye da little dakyal Zahra ta samu ta saukota Tana mama zata gajiyar Dake Kira take ba komai Yar Nan barni in Goya abuna washegari aka daura Auren *Jabir & Asmy* tare da *Chuchu & Adil* na Asmy a funtua aka daura na chuchu Kuma a kd kasancewar an hade dinner ya Sanya aka Kai amarya da wuri Gidan ammy aka sauketa karfe goma na dare aka Tafi dinner Wanda Zahra da MD su suka shirya dinner Sosai wajen yayi masifar kyau da tsaruwa amarenma sunyi anko suma angwayen sunsha kyau iyayen gayya kuwa MD da Zahra ba a magana sunyi masifar kyau duk inda suke suna like da juna Excord dinsu na take musu baya tare da yaransu Dake tsalle tsallensu gwanin ban burgewa Sosai cemarori ke yawo Akan Zahra da MD yanda kasan sune amaren Zahra ko an kame girma ana zaune ita ta bada tarihin amaren MD Kuma ya nada na angwayen taro ya tashi Lafiya washegari aka wuce da kowacce gidanta chuchu Abuja Asmy Kuma Nan kd grab Dan gida daya ne tsakanin gidanta da Zahra.. *After 3 years* Fitowarsu kenan daga tafkeken shopping mall din MD Dake Abuja waiwaye ta dingayi inda zataga Akhbar Dan tunda suka fito Bata ganshi ba Sosai Naga ta Kara kyau da wayewa Tana sanye da bak'ar doguwar riga Abaya Mai shegen tsada tayi roalling gyalen Sosai tayi masifar kyau ga fuskarnan Tata kallo daya zakayi Mata kasan Tana samun hutu da Jin Dadi juyawa tayi Tana kallon MD dake rike da karamar y'arsu Wadda taci sunan Amira halimatus sadiya ana kiranta da amera itama watanta biyar da haihuwa kamarta daya da Zahra Rai da Rai ta ce "Sweetheart Wai Ina Akhbar tunfa da muka fito bangansa ba "Cike da damuwa MD ya ce "to ko yayi wani wajen Nan "Kafin ya kalli Amar dake wasa da katuwar bindigar wasa ya ce My boy Ina Dan uwanka ya shiga ba tare kuke ba "Dad Nima bangansa ba "Innalillahi MD ya fada ya ce ki duba sa farfajiyar Nan Ni Kuma Bari nayi maza na duba sa ciki ya fad'a Yana komawa hankali tashe Zahra ta rike Amar ta dinga dubawa duk yaron data gani saita dubasa gaba daya hankalinta duk ya tashi chan ta hangoshi gaban wasu Cikin sauri ta nufi wajen Tana zuwa ta Kama hannunsa ta Ce "Ina kaje Akhbar tundazu muke nemanka ka bamu wahala so kake ka b'ace a wajen Nan"Akhbar na hawaye Cikin shagwaba ya ce "Mom wadannan ne sunki bani babynsu "ya fada Yana nuna Mata wadanda ke tsaye dagowar da Zahra zatayi idonta ya sauka akan Hafiz Dake rike da karamar yarinya da bazata wuce sa'ar amera ba sai karamun yaro da bai wuce shekara biyu da rabi ba waro idanu sukayi a tare Zahra ta Ce "Hafiz"Shima Cikin muryar mamaki ya ce "Zahra Daman Rai kanga Rai"Mamaki dauke da fuskar Zahra ta Ce "wlhko ya Hafiz kwana da yawa"a sanyaye ya ce"Kinyi wuyar gani Zahra saidai muji labarinki"Murmushi kawai Zahra tayi Tana kallon matarsa ta Ce "Ko matarka ce"Eh Matata ce sunanta Aisha wadannan din Kuma Yara na ne Babban sunansa haidar wannan Kuma takwarar Kice Na Sanya Mata "Kai Masha Allah Ubangiji ya Raya Mana su Gsky Ina gdy da takwara Ta fada Tana Mika hannunshi ta amshi y'ar Akhbar na Ganin Haka yayiwa hafiz gwalo ya ce "Yeyeye ka gani mom Dina ta amso Mana babyn Kuma da ita zamu tafi gidanmu tunda Ni ka hanani"Dariya Hafiz yayi ya ce "Ohh itace mom din take kenan "Eh saura dad Dina Shima Yanzu zaizo mu tafi da babyn "Hafiz najin kishi a ransa da yanzu wadannan yaran duka nasa ne in Banda kaddara ta rabasu ya kalli Zahra ya ce "Akhbar yaronki ne kenan "Eh Ya akai kuka hadu"Murmushi hafiz yayi ya ce "Tun dazu yake binmu Wai saimun basa Zahra Yaatafi da ita gidansu Karkiga har kuka ya dinga Mana Allah sarki Ashe rabon mu hadu ne"Yar dariya Zahra tayi ta ce "Alhbar kenan ko har yayi kamu To ai shikenanma tunda ta dawo gurin Mamanta kaga gaka ga babynka ko"ta fada Tana kallonshi tsallen murna yayi ya ce "Yesssss mom "kallon matarsa Hafiz yayi ya ce "Wannan ita ce zahrar da nake ta Baki labarin"Aisha da fara'a a fuskarta ta ce "Allahsarki itace kenan Ina yini"ta fada Tana kallon Zahra "Lafiya qalau momyn takwara ygd "Saida suka Dan gaggaisa da Zahra
Chapter 91 · 0% Book details