← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 92

Sashe 73

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani bayani ya sanyata cewa "Baki fad'amun komai ba Chuchu" Shiru Chuchu tayi tanajin nauyin ta fad'awa zahra Yayanta ne yayi mata haka dak'yal ta iya tattaro jarumta ta ce "Tun ranar da yatafi dake Asmy tafadamun komai na *Auren wata taran* da kukayi wlh sis bantaba sanin yayana bane yayi miki haka sai dazu" mamaki cike da Cikin zahra ta ce "Kamarya Yayanki" Shiru Chuchu tayi kafin ta labartawa zahra komai d'aya faru har suka gane Yayanta shine ya aureta shiyasa har Ammy taje ta d'auketa sannan Chuchu ta Goge hawayen da suka zubo mata tana kama hannun zahra ta ce "Dan Allah sis kar dalilin wannan yayi sanadiyar shafar zumuncin mu nasan a halin yanzu ba Wanda Kika tsana sama da yaya na Dan Allah kiyi hakuri kar abunnan ya tab'a zumuncinmu" Sosai zahra tayi mamakin jin cewa Yayan Chuchu da take yawan musu zancenshi shine Mustaphan wannan shiru tayi mamaki duk ya gama cikata kenan d'an Ammy ne "Kinyi shiru sis bakice komai ba " Chuchu ta fad'a"Sai sannan zahra ta d'ago ta kalli Chuchu ta ce "Nayi mamaki ne sis Inajin bacci mu kwanta " Shiru Chuchu tayi duk tayi sanyi ganin yanda zahra tayi ta ce "Dan Allah sis kiyi hakuri ki daukeni tamkar y'ar uwa kar laifin yayana ya shafeni" Kirkirar murmushi Zahra tayi ta ce "Kibar maganar nan Chuchu babu abunda kikayimun mubar maganar kawai" Chuchu najin haka ga sauke ajiyar zuciya kwanciya zahra tayi kan makeken bed din Chuchu ta lumshe ido bacci take so ya d'auketa amma tunani ya hana....bangaren MD tashin hankalin daya shiga bana wasa bane cikin Sauri ya kira Jabir a waya bai samesa ba Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai yake maimaitawa kafin yayi Sauri ya fito ya kwalawa driver dinsa kira kai tsaye Airport ya nufa ya wuce Kaduna koda isarsa gidansa dake nan din g r a ya nufa Yana son zuwa gidan Ammy amma baisan me zata masa ba saboda yasan tsananin fushi Ammy take dashi sosai yayi mamakin ya akayi Ammy tasan da maganar nan d'ayar number Jabir ya kira nan yaci sa. a ya d'auka baima jira komai ba ya ce "Kana ina Jabir ka maza kazo gidana dake gra ina kd akwai matsala babba" Daga bangaren jabir yasan daman da haka Koda Jabir yazo gidan Cikin tashin hankali MD ya ce "ya akayi Ammy tasan da maganar nan Jabir Bayan kasan dagani saikai sai Dr Aliyu sai ALLAH daga bangarena suka san da maganar nan taya akayi ta fita" Nan Jabir ya bawa MD labarin yanda sukayi da Ammy Shima yayi mamakin yanda sukasan maganar"Sosai MD ya shiga tsananin damuwa Daren ranar da idonsa bacci gagararsa yayi....washegari Around 9:am Ammy ta sanya Chuchu ta kira mata zahra tare suka isa palourn da Ammy take Wanda zahra kasa yarda ta had'a ido da Ammy tayi saboda wani irin nauyinta da take ji "A sanyaye kanta a k'asa ta ce " Ina kwana Ammy"Lafiya qalu takwara ya bakunta"Ammy tafada fuskarta d'auke da murmushi"alhmdllh "Zarah ta fad'a a hankali" shiru Ammy tayi kafin ta ce "D'ago ki kalleni zahra zamuyi magana" Sai sannan zahra ta iya d'agowa amma bata yarda sun had'a ido da Ammy ba tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Tohm Ammy"saida Ammy taja numfashi kafin ta fara magana da cewa" Nasan Chuchu tayi maki bayanin komai Ba saina Kara maimaitawa ba ina mai baki hakuri akan dukkan abunda Babana yayi miki Dan banga laifinki ko Kad'an ba Kiyi Hakuri ki d'auki hakan a matsayi jarabawa ce kuma insha Allahu kinkusa cinyeta abunda nake so dake ki kwantar da hankalinki waje Daya ki nutsu kiyi hakuri Nasan anyi miki ba daidai ba ki daukeni tamkar mahaifiyar da ta haifeki karkiyi d'ari_d'ari dani ina son ki zauna a wajena ne Har ki haihu kafin muga yanda Allah zaiyi na bincika na samu labarin mahaifinki yanzu yaji sauk'i yana garin danginsa kiyi hakuri ki zauna damu har zuwa lokacin da zaki haihu saimuje tare ayiwa iyayenki bayani sannan a basu hakuri Sannan Abu na gaba da nakeson fad'a maki Ko babana yazo gidannan kar wani Abu ya k'ara hadaki dashi ko ganinsa kikayi kibar wajen kada wata alaka kota magana ta kara hadaki dashi karki sake ki sake masa fuska koda wasa kinji na fad'a maki " gyadawa Ammy kai tayi Alamun taji"Ajiyar zuciya Ammy ta sauke ta ce "Yawwa to Allah yayi miki albarka ya Rabaki da abunda ke cikinki lafiya " Shiru tayi Chuchu ta amsa da ameeen "ga Dr nan zaizo ya duba ki yanzu ki tabbatar kin karacin abinci sannan ta kalli Chuchu ta ce " ki kulamun da ita sosai Kuje Kuyi break fast an shirya muku a dining dake sama "Daman zahra so take Ammy tace Su tashi saboda jinta take kamar a k'aya tare sukayi break fast da Chuchu kafin Su fara hira sosai Chuchu ta dinga Jan zahra da Hira Wanda har saida ta samu da wartsake wayarta Chuchu ta jawo ta ce " Bari na kira Asmy nayi mata albishir"Lokacin da Chuchu ta kira Asmy tana kwance zazzabi ya rufeta daga bangaren Asmy ta ce "Tun jiya nake jiranki bakya d'auka nakagara Naji yanda kukayi dashi" murmushi Chuchu tayi ta ce"AI Albishir na kira na miki gama momcyn nan a kusa dani"Asmy batasan sanda ta mik'e ba ta ce "Da gaske ko wasa" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ga kat ki gani" ta fad'a tana bawa zahra wayar murmushi tayi ta k'ara wayar a kunne a hankali ta ce "Hello sis" Ai Asmy batasan sanda ta buga ihu ba ta ce "wayyo Allah Alhmdll Alhmdllh Zahra kece kuwa" Murmushi zahra tayi ta ce "Karki batamun dodon kunne da Allah Malama " Dariya Asmy tayi ta ce "ba dole nayi murna ba karkiga yanda nayi kewarki Kina ina" chuchu ta mik'awa wayar Chuchu ta ce "tana gidannanmu" Gidanku kuma ina kika sameta "Dariya Chuchu tayi ta ce " akwai labari baya fad'uwa a waya"Aiko gani nan zuwa yanzu"duk daukarsu wasa take basu yarda ba da zatazo sai Bayan two hours data kira Chuchu ta ce "Na Iso kizo ki tafi dani security sun hanani shiga" Da mamaki Chuchu tace "waida da gaske kike gani nan" Tana fita suka shigo Tare da chuchu Asmy na ganin Zahra batasan lokacin da taje ta Rungumeta ba ta ce "I really miss you so much My Dear nayi kewarki over kafin kuma ta Goge hawayen da suka zubo mata ta ce " kina ina tsawon watannin nan zahra"Shiru zahra tayi mata saikuma ta sauya hirar da cewa "Yagida yasu Mama Ya jikin Baba" murmushi d'auke da fuskar Asmy ta ce "kowa lafiya qalau Baba yanaji sauki yana Batsari jiya ma su Mama sunje duba sa sunce ya warke sosai Dukda yana tambayarki " Goge hawayen da suka zubo mata zahra tayi sosai takeson ganin Baban Nata ko taji sanyi a ranta Sosai suka sha Hira da Asmy Sosai sukaji dad'in ganin juna dukda Zahra bata da wata sakewa sosai da fara'a fuskar asmy ta kalli cikin zahra ta ce"tubarakalla sis ji yanda cikinki yayi girma saikace yanzu ne lokacin haihuwar"Harararta Zahra tayi tare Jan tsaki ta kauda kai "Dariya Asmy tayi ta ce " Daga magana Sorrry Harna k'agara naga Unborn d'innan Na *Auren wata Tara* sosai zahra ta k'ara shakuwa tsaki taja tare da mik'ewa ta shige ciki Dariya Asmy tayi ta ce "Wlh Chuchu zahra duk ta sauya hali dukta zama wata jarababbiyar karfi da yaji" inaga fa Cikin nan ne ya sanyata haka"Uhm kuma hakane Allah dai sauketa lafiya "Ameen Chuchu ta fad'a Asmy ce ta ce " bakiban labarin yanda akayi kuka sameta ba "A sanyaye Chuchu ta labartawa Asmy cewar yayantane " Sosai Asmy tayi mamaki jin cewar da Yayan Chuchu akayi haka no wonder kamarsu da Ammy daman ta baci Dan tun sanda sukaga Ammy suka San tana tsananin kama dashi ta wani bangaren Asmy taji dad'i da abun yazo da sauki tasan Ammy mutuniyar kirki ce Zata kula da Zahra sannan zata fahimtar dasu Baba Ita yanzu chuchu Tsoranta bai wuce Zahra ta gane Yayanta shine MD d'innan data tsana tasan tsanarsa ninkuwa zatayi a ranta "Sai yamma Asmy tayi musu bankwana zata wuce bayan taje ta gaishe da ammy Inda Chuchu ta sanya driver ya kaita har gida sosai Asmy taji Kashi tamanin na damuwarta ya ragu zahra ko saitaji ba dadi da asmy ta tafi koda taje gida ta yanke shawarar fad'awa iyayenta Maganar Gaskiya dukda tasan zasuyi mata fad'a mamanta ta samu a tsorace ta labartawa mata komai " salati mamansu tayi ta salamce "sosai ta shiga yiwa Asmy fad'a kamar ta doketa ta ce " daman ashe kece kikayi silar shigar zahra wannan halin kece silar komai Dan Ubanki ita kuma ta biyeki to ai gashinan kinja mata "fad'a sosai maman su Asmy take Inda asmy ke bata hakuri daga karshe kuma ta godewa Allah da Cikin zahra ya kasance ta hanyar aure aka samesa ba hanyar banza ba dukda dai tasan mutane ba kowa zai fahimta ba har videon d'aurin Auren saida Asmy ta nuna mata Dan ta tabbatar.....Shiru MD yayi gaban Ammy yama rasa abunda zaice mata saboda tun gaisheta da yayi ta amsa a takaice bata Kara ce masa komai ba " Dak'yal yayi jarumtar cewa "Ammy Dan Allah kiyi hakuri" Me kayimun da zaka bani hakuri "Ammy ta fada'"Shiru ya sake kafin ya ce " Ammy nasan fushi kike dani Dan Allah kiyi hakuri Bazan iya jurar fushinki ba "murmushin da yafi kuka ciwo Ammy tayi ta ce " Ah ah ni ai baka tsoron fushi na ga Amira uwarka data haifeka ta kawoka duniya ita kake shakka kake tsoron fushin ta baniba "Omg MD ya fad'a ya ce " Ammy ba haka bane nasan ban kyauta ba ki tsaya nayi maki bayani"Daga masa hannu tayi ta ce "ba bayanin da zakayimun " duk yanda yaso Ammy ta sauraresa kin sauraransa tayi kullum.MD saiyayi zarya gidan Dan son shawo kan Ammy amma bata kulawa wani lokacin ma tashi take ta basa wajen Dan ba abunda yafi mata ciwo kamar idan ta tuna wai Dan Matar d'aya aura a boye ta haihu suce mata Dan ko d'iyar ya mutu ya kaiwa Amera ace ita ta haihu
Chapter 73 · 0% Book details