← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 92

Sashe 8

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai sayar da turare Shima kullum cikin k'amshi yake gashi yarinyar ya yaba da tarbiyarta 100%yasan ko makarantar suka tafi baida shakka a kansu saboda bazata bari Asmy tayi wani abun da bai kamata ba. Koda yaje ya fad'awa Mama yanda sukayi da baban Zarah itama bataji dad'i ba Asmy ko hada kukanta nan ta tubure ta ce itama ta fasa zuwa makarantar. gidansu Zarah taje tayi ta mata kuka akan dan Allah ta lallaba Baba ya barta sutafi tare idan kuma ba haka ba Itama ta hakura da karatun itama Zarah saida tayi hawayen d'an ba k'aramun so takeyiwa karatu ba. Da dare duk tayi sanyi baba ya shigo gaisheshi tayi ya amsa tare da cewa . " Dazu baban su Asma'u yake samuna da wata magana Wai ta karatu to Gaskiya na nuna masa Rashin amincewata saboda Har kullum burina Zarah bai wuce naga ranar Auranki ba naga na sauke nauyin da Allah ya doramun a kanki sannan na cikama mahaifiyarki burinta na Aurar dake sannan na had'aki da danginta kiyi hakuri Zarah bazan barki kije karatu har wani gari ba Kuma ma a halin yanzu bani da k'arfin wannan kiyi hakuri idan Allah ya sanya kinyi Aure sai kici gaba da karatunki gidan mijinki hankali kwance kinji" Duk yanda hankalin Zarah ya tashi bata yarda ta nunawa Baba ba kasa tayi da kanta ta na mayar da hawayen da suka zubo mata ta ce. "To shikenan Baba daman bansa haka a raina ba Allah sa haka shi yafi zama Alkhairi" Ameeeeern y'ar Amanata Allah ya yi maki albarka ya jikan mahaifiyarki" "Ameen ta fad'a kasa kasa saboda kar ya gane rawar da muryarta keyi ta na shirin fashewa da kuka Baba na fita daga d'akin ta fashe da matsanancin kukan da take rikewa . batasan ya akayi ba da bata sa burin karatu a ranta ba Amma daga lokacin da Asmy tazo da maganar taji yanzu duk duniya bata da burin da ya wuce Karatu Sosai take kuka har saida kanta ya fara ciwo sai wajen 2 wahalallen bacci ya kwasheta. washegari da ciwon kai ta tashi saboda kukan da tasha ranar sukuku ta yini ba walwala . da Yamma koda Hafiz yazo yana kallonta yasan akwai abunda ke damunta da damuwa a fuskarsa ya ce . "Me yake damunki ne my Zarah naga kamar kinyi kuka " Kamar jira take take nan ta fashe da wani kukan da batasan yazo mata ba. "subhanalla Zarah me yake damunki wani abun aka maki " Saida ta tsagaita kukan tukwana cikin muryarta ta shagwabar da batasanma tayi ba ta ce..... *Hmm Kudai muje zuwa fans ba a fara komai ba wannan shi ake kira somin tab'i bama mu shiga cikin wasan ba wannan duk Bayan fagene* _07026166536 domin magana da marubuciyar_ *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ~Share please~ _*Miss Hajo ce*_ *AUREN WATA TARA* MALLAKAR *Hajara L Sadeq* *TEAM GAWURTATTU BIYAR* .........*9 & 10* "Baba ne ya ce Wai bazanci gaba da karatu ba Aure yakeson yayi mun" Yanayin yanda tayi maganar ne ya bashi Dariya saida ya Dan dara tukwana ya ce "My Zarah kenan rigima to meye a ciki ba saimuyi Auren mu ba Kinga ni bazan hanaki karatu ba daga degree har masters. Turo baki tayi gaba ta ce " nidai banason Auren karatu nake so"To kwantar da hankalinki gimbiyar mata anjima zanje na samu Baba da maganar insha Allahu zai amince. Cikin Sauri ta d'ago ta ce "da gaske ya Hafiz" saboda haka take ce masa"murmushi ya sakar mata ya ce . "Insha Allahu" zokuga murnar da Zarah tayi kamar ance Baba ya amince.Aiko ranar Duk miskilancinta ajeshi tayi itace hada Hira da Hafiz Wanda hakan ba karamun mamaki ya bashi ba. Da daddare Hafiz yaje ya samu Baba da maganar karatun Zarah Inda ya nuna Rashin amincewarshi sosai Hafiz ya dinga yiwa Baba magiya akan dan Allah ya amince Zarah ta tafi karatun tunda ta na da hankali nutsuwa uwa uba Ilimi Sannan ya ce "Insha Allahu kuma Baba ni zan d'auki nauyin karatunta har ta gama". Shiru Baba yayi kamar mai nazari kafin ya d'ago ya ce " "bank'i taka ba yaro kozan iya Amincewa Zarah ta tafi karatu tofa Indai da gaske kake sonta ka turo magabatanka a tsaida maganar Aure duk lokacin da ta gama amma haka kawai sakaka bazanbar y'ata ta tafi karatu ba sannan Ko kana fara d'aukar nauyin ta tofa sainaji magana jinjina daga magabatanka" "Alhmdllh Hafiz ya fad'a a ranshi daman wajen da yake jira akai kenan " Nan take ya ce "Baba na Amince insha Allahu gobe magabatana zasuzo wajenka yanzu zanje na samesu da maganar". Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce " ba laifi"Ranar Hafiz cikin farinciki ya koma gida Koda ya samu iyayenshi da maganar basu wani kin Amincewa ba saboda sunsan Malam Yusuf Babban limamine da garin d'aid'aine basu sanshiba kuma sunsan mutumin kirki ne duk y'ar data fito daga wannan gidan tofa za a sameta da tarbiya. a washegari magabatan Hafiz sukaje wajen Baba Bayan an mutunta juna Inda suka tsaida magana akan Lokacin gama karatunta za ayi Auren shi ma lokacin sannan ya gama masters dinsa hakan yayiwa kowa dadi musamman baba. Zarah da bata San wainar da ake toyawa ba "saida dare Baba ya fad'a mata yanda sukayi " Baka iya Tantance yanayin da ta shiga farinciki ko akasin haka Amma kuma idan ta tuno da makarantar da Baba ya amince saitaji dadi a ranta batasan ya akayi ba dai maganar Auren bata kwanta mata a rai ba. Asmy ko koda ta samu labari hada tsallen murnar ta dan babanta dashi aka tsaida lokacin cikin farinciki ta je gidansu Zarah tare da Rungume juna suna murna ta ce. "Gaskiya nayi farinciki wlh sis bantaba tunanin Baba zai sauko haka ba inye kaga amarya a gidan Hafiz d'inta" turo baki Zarah tayi tare da "Kai mata Bugu a baya ta ce ". " kinsan bansan zolaya "Ranar kusa raba dare sukayi suna Hirar yanda Tafiyarsu makaranta zai kasance. Hafiz ko koda yazo Zarah kin fita tayi Dan kunyarshi take ji shiko sai fara a da farinciki ya ke ji yake kamar anmasa Albishir da gidan Aljanna bai tab'a tunanin zai samu Zarah ba cikin Sauk'i haka ba. Ranar Monday su Zarah suka shirya tafiya Zaria domin zana jarabawarsu ta FUMB Hafiz shi ya kaisu Har Zaria Inda ya jira saida suka gama tukwana Ya juyo dasu A hanya sai kallon Zarah yake yanda take sisinna kai a gaba " murmushi yayi tare da Kallon Asmy ya ce "Bestynmu yau fa mutuniyar Naga sarautar takeji " murmushi Asmy tayi ta ce "Naga alama kam inaga kunyarka takejifa " Harara Zarah ta watso mata daga gaban da take Wanda hakan ya sanya Asmy da Hafiz yi mata Dariya "Turo baki gaba tayi tare da Kallon hanya " har suka isa funtua suna Hira jefi jefi kasancewar ba wani nisa ke akwai ba tsakanin funtua da Zaria gidan su Asmy suka sauka Dan huce gajiya kafin ta wuce gidansu Ta na isa ta samu Mama Rabi na Surfa bala i ta na cewa. "Aikin banza aikin hofi ko anzata bamusan iskanci da karuwancin.da ake a jami'ar ba To ayi mugani idan tusa zata hura wuta Aikin banza aikin hofi " Sosai take jifar Zarah da mugayen kalamai Inda ita ko a kanta Dan itadai burinta bai wuce tabar gidan nan ta huta ba. Cikin ikon Allah jarabawar su ta fito Kuma duka sunci sun samu admission Inda Zarah mass com suka bata saboda daman shi ta cike ita kuma Asmy suka bata Biology education . zokuga farincikin da suka shiga Daga ranar suka fara sayayyar Tafiyarsu makaranta sun amshi kudin da Zarah ta samu a wajen sauka Inda suka sassayi kayan sawa dasu Komai iri daya suka saya da Asmy kala biyar biyar sukayi atamfofi suka saya Zane bibbiyu suka Kai d'inki ita kuma Mama ta d'inka musu manyan hijabai hurhudu saboda su Kara da nasu. baban su Asmy shi yayi musu registration ba yanda Baba baiyi dashi ba akan ya bari zai sayar da tumakishi a kauye ya rage masa ya ce "a.a daman shi yayi niyyar ni musu ai anzama daya " Sosai Baba yaji dadi kuma yayiwa babansu asmy Godiya sosai Zarah ma tayi mashi Godiya kwarai da gaske yanzu zaman gidansu ma gagararta yake saboda koda yaushe suna gidan su Asmy suna shirye_shiryen tafiya saboda Abun na tunkarowa Dan yanzu wata Guda ya rage musu su fara lectures Wanda ji suke kamar su jawo ranakun" *Wacece zarah* *Zarah Yusuf* shine cikakken sunanta mahaifinta Malam Yusuf haifaffen garin Batsari ne Noma da kasuwanci shi ya kawoshi garin funtua kasancewarshi malamin addini . ya samu karbuwa sosai a garin kasancewar lokacin Su ilimin addini bai wadatu ba Sosai sai ya kasance yana koyar da wasu manya magidanta karatu a masallaci Bayan kammala Sallar isha i kasancewar shine limamin masallacin Unguwar da masallacin juma'ar yankin" wannan dalilin ya k'ara sanyawa mutane da dama suka sanshi a lokacin sosai Malam Yusuf yake da rufin asiri saboda gona guda ya ke amsar haya yayi shukar masara da wake Wanda alkhairi da yake samu ba Kad'an bane . Bayan nan kuma daman yana kiwo a kauye ganin irin cigabar da yake samu a garin ya sanyashi sayan fili a unguwar jabiri Inda a hankali a hankali ya fara gininsa cikin ikon ubangiji har ya gama . ana haka ne wata rana yaje Noma Ya hadu da wata matashiyar budurwa sai gudu take ta na hak'i sosai hankalinshi ya tashi kuma yayi mamakin daga dajin da ta b'ullo ga Saran
Chapter 8 · 0% Book details