← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 92

Sashe 22

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya kaka ce kawai ta jawo masa matsalar nan " Jabir ne ya ce . "to saimu jirayi farkawarta muji Amincewa daga gareta " Girgiza masa kai Asmy tayi ta ce. "a a a Karku jirayeta kawai a D'aura Bayan an daura zansan yanda zanyi na shawo kanta har ta amince amma yanzu kawai a daura ba matsala " "To alhmdllh komai yazo cikin Sauki yanzu zamuje masallaci a daura Auren Bayan fitowar Sallar La'asr sannan zanyi muku video din d'aurin Auren Dan ya zama hujja da shaida a garemu" "to mungode Allah saka da alkhairi Asmy ta fad'a tare da mik'ewa tace bari na koma Wajenta" murmushi Dr d'in yayi mata ya ce"muke da Godiya sis " ta na fita MD ya kalli Dr ya ce . "me yasa ka boye musu Gaskiya Dr da ka fad'a musu bukatarmu idan sun amince idan kuma basu amince ba a hakura kar ashiga hakkinsu fa" Mikewa dr yayi tare da cewa "karka damu Aboki ba wata matsala insha Allahu idan muka fad'a musu Gaskiya ba lalle su yarda ba amma kaga haka sun yarda cikin sauki" Zai sake magana Jaber ya Mike ya ce"is okay bloody ka tashi muje a d'aura kawai"Harararsa MD yayi tare da Jan tsaki ya Mike Dan haushinshi yake ji na lika masa koma wacece da zaiyi baima ganta ba Tsaki yaja Dan baidama buk'atar ganinta. Kai tsaye Unguwar su Dr Aliyu suka nufa Bayan MD ya rufe fuskarsa da face marks mahaifinshi sukayi sallama dashi ya fito Bayan sun gaisheshi ya amsa Dr Aliyu ya ce. " baba kaga wannan ya fad'a ya na nuna masa MD Baba ya ce Eh na gansa "yawwa to Abokina ne zaiyi jahadi na Auren wata y'ar gudun hijira to iyayensa sunki su amince da Auren shine ya taho wajena Dan mu taimaka a daura musu Aure inyaso daga baya Ya nemu yafiyarsu" "Kabbara mahaifinshi yayi ya ce " Allahu akhbar da ace ana samun irin wadannan ai da anzauna lafiya Gaskiya ne wannan jahadi ne zaiyi babba Sannan ya kalli MD ya ce . "yaro Allah yayi maka albarka Tabbas kaid'in da ne na kwarai insha Allahu a yanzu yanzunnan ba anjima ba za a daura muku Aure " murmushin k'arfin hali MD yayi jaber ko Hamdala kawai yake yanda komai yazo musu yanda basuyi zato ba. Bayan kammala Sallar la'asr Mahaifin Dr Aliyu ya bada sanarwa da akwai d'aurin auren da za ayi Nan ko mutane suka tattaru aka cika masallacin harda wajensa Dan Malam ashiru sananan mutum ne Bayan an kawo Goro Inda Liman ya zama wakilin Zarah shi kuma mahaifin Dr aliyu Malam ashiru ya zama waliyin MD. ganin An fara d'aurin Auren ya sanya Jabir saurin d'auko wayarsa tare da Fara yin video a take a nan aka Daura Auren *Zarah Yusuf* tare da Angonta *Mustapha dikko* Akan sadaki Naira Dubu d'ari biyar....... yanzu salon wasan zai soma wakana fans wancen duk sharan fagene yanzu muka shiga chakwakiyar Auren wata Tara Kudai ku kasance dani miss hajjo danjin karashin wannan K'ayaitaccen littafin da yazo da salo mai rikitarwa* *kamar yanda kuka sani littafin nan d'aya yake daga cikin gawurtattu biyar page d'aya ya rage mana mu gama free page daga page 30 zan tsaya da free page Wanda ya biya ne kad'ai yake da daman k'arasa karanta wannan zazzakan labarin da yazo daga zazzakan alkalamin miss hajo ga tsarin yanda biyan nan yake a kasa idan kun duba don neman karin bayani ku tuntube ni Akan number wayata kamar haka 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* *AUREN WATA TARA* ```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* ............*29 & 30* Daga wajen d'aurin Auren MD ko jaber bai Kara waiwaya ba ya wuce Gidanshi dake nan low-cost Zaria Dan kanshi duk Sara masa yake. Bayan komawarsu jaber asibitin kiran Asmy Dr yasa akayi a office d'inshi jaber ya mik'a mata wayarsa tare nuna mata video din amsa tayi ta na Kalla gabanta na fad'uwa Dan batasan yanda zasu wanshe da Zarah ba " Tura video din tayi a wayarta itama Dan ya zame.mata hujja sadakin a embleme ya mik'a mata tare da cewa . "ga sadakin dubu d'ari biyar ne chif" Amsa Asmy tayi tare da Sanyawa jaka duk tayi sanyi ta kalli Dr ta ce "Sai Abu na gaba da bamuyi ba takardar yarjejeniya " girgiza mata kai sukayi jaber ya ce "Ba ma buk'atar wannan ma'u sannan ki bani numberki mun k'arasa sauran maganganun a waya" Kwafe masa numberta tayi Bayan yayi save tata Shima tayi save a sanyaye ta koma d'akin da Zarah take har lokacin Bacci take tagumi tayi hawayen tausayin aminiyar tata na zubo mata Zarah ita ce bata farka ba sai Asuba koda ta tashi jikin nata Alhmdllh ba ciwon cikin sosai. A hankali ta mik'e ganin Asmy gefenta ta na bacci toilet ta nufa ta gyara jikinta ta na fitowa ta iske Asmy ta mik'e ta na mika Kallon juna sukayi Asmy ta ce. "Harkin tashi kenan ya jikin to" Alhmdllh kenan saida muka kwana Asibiti"Wlhko ai ciwon nan naki ya tsoratani Zarah ta fad'a tana shiga toilet Dan yin alwala Bayan ta fito tayi salla ita dai zarah ta yi tagumi Tun lokacin Asmy take son yiwa Zarah bayani amma ta kasa Sai tazo zata mata bayani sai ta kasa Wajen 7:00 Zarah ta ce "waike meye kikeson ki fad'amun tun asuba kin kasa karkija inyi zaton ko wani abun ne ya faru". Numfasawa Asmy tayi dak'yal ta iya d'aga baki ta ce " daman Zarah "saikuma tayi shiru daman me?ta fad'a ta na tsatsareta da ido" Dak'yal ta iya jarumta ta ce "ta ce . "Daman Dr ne ya ce ciwon cikin naki yayi worse sosai sannan Allurar da ake maki ta daina maki aiki muddin next month yazo a haka batare da wani Abu ya shiga tsakaninki da wani ba to dole sai anyi miki aikin 30 millions kuma aikin ya na da hatsarin gaske" Sosai tashin hankali ya bayyana k'arara a fuskarsa Zarah ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Wannan wace irin jarabawa ce Asmy yanzu ni me.zai had'ani da wani namiji kafin one months Ni da ba Aure gareni ba Sannan Aikin 30 millions fa kikace Asmy wani irin aiki ne wannan". Numfasawa Asmy tayi ta ce " Eh Zarah haka Dr ya ce Saidai akwai mafita "cikin sauri ta d'ago ta ce " wace mafita Asmy?Wani abokin Dr ne da yazo ya tausaya halin da kike ciki shine ya ce Wai idan zaki amince zai Aureki na wata Tara kafin lokacin bikinki da ya Hafiz saiya sakeki Kinga Asiri ya rufu hankali kwance". Wani banzan kallo ta dinga bin Asmy dashi kafin ta d'ago ta ce "bantaba sanin baki da hankali ba Asmy sai yanzu wannan wace irin banzar magana ne angaya miki Aure abun wasa ne ko kuma ciwo hauka ne to Bari kiji ko zan mutu bazan tab'a yarda da wannan shirmen banzan ba ko a garin gab'a gab'a anyi haka wlh ni kinma b'atamun rai yanda baki tunani " ta fad'a ta na Jan dogon tsaki. Sosai gaba Asmy ya bada daram hankalinta in yayi dubu ya tashi ta ce "Amma Zarah...daga mata hannu tayi ta ce " ya isa indai akan wannan banzar maganar ce Karki sake mun maganarta " Ta fad'a ta na mik'ewa tare da sanya Hijab d'inta ta ce "Kinja Asibitinma ya fita a raina tashi mu tafi " Amma aikin bari Dr d'in yazo ya sallamesu"Ke saiki jira har ya zo ya sallameki ni na tafi ta fad'a ta na nufar hanyar kofa. Daidai fitarta yayi da daidai da shigowar Jaber d'akin da Kallo ya bita harta fice daga Ward din wanda ko fuskarta bai gani ba juya Kallonshi yayi ga Asmy da tayi tsuru a d'akin ya ce . "hartaji sauki kenan naga fitarta ina zata?hostel wlh ya jaber taki amincewa nan ta fad'a masa yanda sukayi da ita " kallonta yayi ya ce "Karki damu sannan karki fad'a mata ki barta a haka din duk abunda zai wakana ya zamana muna shiryasa ni Dake tunda na lura Amaryar tamu kamar ta na da taurin kai". Murmushi kawai tayi ta ce " haka take in ta burkuce amma tana da saukin kai bari na bita "Ledar da ya shigo da ita ya mik'a mata ya ce " daman break fast ne na shigo muku dashi"Da farko kin amsa Asmy tayi saida taga yana ta mata magiya kafin ta amsa Bayan taje tayiwa Dr bankwana ta bar asibitin kafin ma ta isa wajen asibitin har Zarah ta tafi wata napep din ta tsaida ta wuce makaranta. koda ta isa kwance ta tarar da Zarah Chuchu na gefenta ta na bata ruwan tea ta na shigowa Zarah ta kauda kai ta na kunbure kunbure girgiza kai kawai Asmy tayi tare da zama Chuchu ta Kalleta ta ce . "ya mai jikin jiya nayi ta Kiranki ki fad'amun asibitin da kuke nazo amma kashe " wlhko chaji ne bandashi har yanzu wayar tawa ta mace gashi tata Kinga bamu tafi da ita ba " "ayya shiya sanya Ai da sauki ma wlh karkiga jiya banyi barcin kirki ba duk hankali na na wajenku sannan Yaya na ma da yace zaizo nayi ta kiranshi Shima kashe duk raina ya gama b'aci jiya da kadaici na yini na kwana". Murmushi akwai Asmy tayi ta ce " kilan wani uzurin ne ya rikeshi"Wama ya sani kuma fa wlh yaya baya magana biyu abun yaban mamaki sosai "duk maganar da suke Zarah bata ce uffan ba saima Kallon Chuchu da tayi ta ce " kin sanyamun wayata chaji?eh
Chapter 22 · 0% Book details