Sashe 78
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cewa ne zakizo kiwa mutane hauka da ba abunda kika iya sai bakin kishin jaraba to alkadarinki dai ya karye Duka Asirin da kika masa ya sakesa yayi aurensa ya rabu dake saiki koma Chan k'asar tambadewar taki kici gaba da tambadewa a sararin samaniya "Hajiya kaka ta fad'a tana shigowa palour" a matuk'ar rude Amera ta juya ta Kalleta kafin ta saki Hannun MD tanajin zuciyarta tamkar zata tarwatse ta ce "What sai kuma ta fashe da kuka ta ce " wlh Allah karya ne bazaiyu ba ,bazaiyu ba MD yayi Aure ya haihu da wata,karyane ,ihu ta k'walla iya karfinta tana girgiza kai kamar zata hau bori "tab'a hannu Hajiya tayi ta ce " ikon Allah to ko aljanu zata tada kihau bori Kece bishiyar kuka karewar iskokai mahaukaciya y'ar mahaukata Kaikuma Solon hofi tsayawa ma kayi kana kallonta"MD Yama rasa Inda zai tsoma ransa fitowa Ammy tayi tare da little zahra a hannunta Chuchu na biye da ita tare da biyun tana hawaye ta ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri karki basa yaran nan Momcy zata shiga wani hali Kinga koda kika amsosu kuka take Dan Allah Ammy kar fushi yasa kiyi aikin Dana sani" Daidai shigowarsu palourn Duk Kallon Amera suka tsayayi dake kwala ihu kafin ta chukumi MD iya karfinta ta shakesa ta ce "Daman kai Bakin Munafuki ne bansaniba,Mayaudari ne kai daman ,ashe duk kalaman da kake fad'amun na bazaka iyamun kishiya ba na karya ne to wallahi tallahi ka sani Mustapha baka isa ba kayi Kad'an ka yaudareni kaci bulus wlh baka isa ba ka hada matsayi na Dana wata ba karya ne Wlh zan kasheka zan kasheta zan kashe kaina Bayan na kashe shaggun yaran Dan wlh badai aure ba Saidai in y'an zina ne kuka haifa.Marin da taji an wanka mata ne ya sanyata Had'iye maganar da ta fito daga bakinta Dagowa tayi da kalli wacce ta maretar Ammy ta gani tsaye kanta tana huci rike da baby cikin b'acin rai Ammy ta ce " Duk iskancin da zakiyi ki tsaya iya mijinki shine Wanda zakiwa kici bulus amma ba zahra da yaranta da sukafiki matsayi da daraja a wajena ba baki isa ki shegantar mata yara ba sannan anfada Yayi Aure matarsa ta Haifa masa Yara ba karya akayi ba ko haramun ne Dan yayi Aure tunda ke kin kasa basa farincikin da kowace mata take bawa mijinta hakan yasa yayi Aure kuma da masaniyarmu yayi kece baki sani ba yanzu kuma ai kinsani"Wani irin kallo Amera Kebin Ammy dashi tana rik'e da kumcinta ta ce "Ni kika mara " An mareki Dan Ubanki ko ramawa zakiyi" "Kutumar uban nan to Inma na rama din ke uwata ce ko haihuwa ta kikayi munafukai ke mijinki har ya mutu ya taba miki kishiya ne da zaki sanya nawa mijin yayimun kishiya daman Nasan ba kaunata kuke ba shine har Kuka sanya yayi mun kishiya to wlh kusani ni Amera nafi k'arfin kishiya nafi k'arfin hada miji....d'auke da Mari har sau Ukku da taji anyi ne ya sanya ta kasa fadar abunda tayi niyyar fad'a cikin huci MD ya ce" baki da hankali ne Amera mahaifiyar tawa kike fad'awa hakan Dan iskanci ko ubanki ya isa ya fad'awa mahaifiyata haka bareke kodan Kinga Duk abunda kike ina kyaleki kina cin Darajar Abu biyu ne Inbanda haka da baki isa kiyi wani abun na kyaleki ba"kuka sosai Amera ta fashe dashi tare da k'walla Ihu duk saida suka toshe kunnuwansu Kafin ta bud'e ido Jaririyar dake hannun Ammy idonta yakai kukan kura tayi tare da nufar Ammy ta amshe Jaririyar Tana shirin timata da K'asa Zahra ta rugo A guje batasan sanda wani k'arfi yazo mata ba ta amshe y'ar daga fad'uwar da Amira taso kadata Huci kawai zahra take tana kuka Dan yau ita kadai tasan tashin hankalin data shiga da Amera ta kada mata yarnan da batasan yanda zatayi ba jijjiga yarinyar ta fad'a data fara tsala wani irin kuka kowa Ajiyar zuciya ya sauke ganin irin kokarin da zahra tayi saboda ba k'aramar shammatarsu amira tayi ba Cikin Hargagi Hajiya ta ce "Ka fitar mana da mahaukaciya Matar nan gidan nan Dan ubanka tunda ta shanyeka Ibanda sakarai ta zagi uwarka Ka tsaya kana kallonta baka sauke mata saki Ukku ba " cikin ihu Amera ta ce " da Allah iwa mutane shiru ke asuwa Ke ki sakeni d'in tsohuwar banza kawai" Ai MD baisan sanda ya k'ara d'auke Amera da wani Marin ba ya ce "Dan baki da hankali iyayen nawa da kakata kika zaga?Anzagesu din kaima wuce a zageka kayi banza d'an iska Mayaudari tana kallon zahra dake jijjiga y'arta tana kuka ta ce " Daman Y'ar Iskar karuwarka ka aura Macuci Mayaudari"waige waige ta fara tana neman mabugi Chan ta Hango Fankar K'asa cikin Sauri ta nufi wajen iya karfinta ta Karya Fankar ta d'auko K'asar da gudu ta nufi wajen zahra zata maka mata MD yayi Sauri Yarike cikin tsananin b'acin rai ya ce "Wannan wani irin hauka ne kike Amira" Kallon Chuchu da zahra Ammy tayi ta ce "Ku wuce ciki" Zahra hada gudu_gudu suka wuce Dan sosai ta tsorata da Amira Dan bata mance karansu na farko ba Cikin b'acin rai Hajiya ta ce "Bazaka saketa ba Sai kallonmu ka tsayayi ta zageni ta zageka,ta zagi uwarka ta shirya kashe maka y'ar da ka shekara goma Kana fatan samu ka tsaya kana kallonta Dan Kana Asararre"MD rasa Inda zai tsoma ransa yayi cikin bacin rai Ammy ta ce " ku barmun gida daga kai har ita inba so kake na yi muku abunda bakuyi tsammani ba "Cikin tashin hankali ya ce " Dan Allah Ammy kiyi hakuri idan sakinta kike so nayi sainayi"Daga masa hannu Ammy tayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba ya rage ruwanku amma Abunda nakeso ta barmun palour sannan a maida mun duk abunda ta lalatamun na palour " tana gama fad'ar haka ta haye sama da Kallo Hajiya ta bita kafin taja tsaki ta ce "Kaji d'ayar mahaukaciyar a tunani na zakice ya saketa ne ko ki tsine masa amma ke ta kayan Da aka lalata miki ma.kike Allah mai iko zaman gidannan ko kayan takaici Aiko zuwa zanyi na tattara kayana na bar garin haihuwa yau har tajamun Zagi" Hajiya ta fad'a tana goge hawayen takaici kafin tayi fuuuu itama tabar palour "Cikin b'acin rai MD.ya kalli Amira ya ce " Hakan da kikayi burgewa ce to hankalinki ya kwanta kin had'ani da iyayena sannan zakisan iyayena Suna da martaba da daraja sunfi k'arfin zagi a wajenki ki biyo ni"ya fad'a yana fita sai sannan tsoro da fargaba suka kama Amira ta tuno da abunda tayiwa Ammy da Hajiya kaka sai sannan hankalinta ya fara dawowa jikinta tasan karya take ta zagi mahaifiyarshi da kakarshi ta kwana Lafiya karfa ya saketa "Cikin tashin hankali ta bishi Inda ta sameshi cikin mota ya had'e kai da sitiyarin mota Cikin tashin hankali ta fashe da kuka ta ce " Dan Girman Allah MD.karka sakeni wlh tallahi bansan na zagesu ba zuciya ce kasan bata da kashi"Wani irin kallo ha dinga binta dashi cikin Tsawa ya ce "shigo nace" Cikin Sauri ta shiga da Sauri ya figi motar bai tsaya ko ina ba sai gidansu suna isa bakin get ya tsaya ya ce "Fita ki tafi gidanku " Kuka ta fashe dashi ta ce "Dan Allah honey karkace ka sakeni" Cikin Tsawa ya ce "Bakiji abunda nace ba " Ba shirin ta fita tana fita Ya rufe motarsa ya jata da gudu da gudu Amira ta shiga gidansu tana wani irin kuka ta fad'a jikin dad d'inta ta ce "Na shiga Ukku Dad shikenan md ya rabu dani daddy yayi Aure bansaniba Matar harta haihu naje gidansu na zagi mamansa da kakarsa yayi fushi ya maidoni gida shikenan dad nasan sakina zaiyi na shiga ukku wlh dad inason mijina ina kaunarsa bazan iya rabuwa dashi ba wata bata isa ta rabani dashi ba Dady zuciyata ji nake kamar zata tarwatse dad tana cikin wannan sai ganinta sukayi ta sulale a wajen summammiya hankalin iyayenta idan yayi dubu ya tashi a guje aka wuce Asibiti da ita hankali tashi Kafin likitoci su fara kokarin ceto rayuwarta.....MD ya rasa yanda zaiyi da ransa yasan Ammy ba k'aramun fushi ta k'ara dashi ba nakin sakin Amera Jabir ya kira a waya ya sanar masa halin da ake cikin hankali tashe Jabir ya ce " Innalillahi Abu dai baiyi dadi ba bloody me yasa kak'i sakinta Ammy fa da Hajiya ta zaga kishi hauka ne "Jabir bazaka gane bane ni kadai nasan yanda Naji zafin hakan a cikin raina Nafi su Ammy jin zafi naki sakinta ne saboda Duniya zata zageni babu Wanda zai duba abunda tayi za ace na saketa ne saboda Na auri wata harta haifamun yara nayiwa Matar data zauna dani tsawon shekaru goma ko shad'aya butulci" numfashi Jabir yaja yace "Tabbas hakane kayi tunani bloody amma dai abunda yafi kamata kaje kaba Ammy hakuri yanzu kayi mata bayanin nan zata fahimce ka" Kamar yanda Jabir ya fad'a masa haka yaje ya samu Ammy da dare ko gaisuwar da yayi mata kin amsawa tayi cike da damuwa ya ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri wlh bawai Dan banji ciwon abunda Amera tayi ba yasa ban saketa ba nayi hakan ne saboda gujewa surutun mutane za ace na saketa ne kawai saboda wata Matar ta haifamun yara na rabu da ita tsawon shekararmu goma ban rabu da ita ba sai yanzu za aga Rashin kyautawata Wanda kome tayi baza a ga nata ba Amma Ammy kiyi hakuri indai zaki janye fushin nan naki wlh zan saketa yanzu daman na Turata gidansu Saina aika mata takardarta indai hakan zaisa hankalinki ya kwanta" Tunani Ammy tayi tace tabbas hakane dagowa tayi ta Kallesa har saida yaso bata tausayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba Inama umartarka da kaje ka D'auketa ku koma gidanku Kamar yanda bazanso a saki nawa y'ay'an ba haka bazanso a saki nawasu ba ka mayar da Matarka gidanku sannan Ka lallasheta harka samu ka shawo kanta Tabbas kishiya da ciwo musamman baka San da ita ba har sai da y'ay'a dukda dai batasan dalilin Auren ba saboda soyayyarta ne