← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 92

Sashe 72

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kiyi hakuri sannan karkiyi fushi" Inajinka oya ka fad'amun karka dinga b'atamun lokaci"numfashi yaja kafin ya labartawa Ammy komai d'aya faru bai boye mata komai ba saboda daman yasan da irin wannan ranar dukda yayi mamakin yanda akai Ammy tasan da maganar Salati Ammy tayi ta tafa hannu ta ce "Naga ta kaina ni Fatima daman a saboda Amera ne kuka aikata wannan Abun kunji kunya kun rako maza wlh Babana yaban mamaki bantaba tunanin zaiyi irin wannan Rashin imaninba Ya sanya yarinya a cikin wani hali kawai saboda shegiyar amera kayan bannza kawai a saboda banzar biyan bukatarku kuje ku auri yarinya ba sanin iyayenta Kuyi mata wayau ku tsoratasu kuga mugaye azzalumai wlh babana sai yayi nadamar abunnan d'aya aikata zaisan mu yayiwa haka zaisan zahra ba a banza take ba wlh tallahi saina kwatar mata hakkinta zan mance cewa ni na haifeshi na kwatawa zahra hakkinta tamkar Nina haifeta bana zalinci sannan bana goyon zalinci Kenan so kukayi ku cuceta ta haihu ku kaiwa waccen y'ar Iskar d'an da ita kanta tarbiya bata isheta ba bare harta tarbiyar da wani mu kuma ayi mana lullubi ko to ai dayake a cikin abun ba Allah gashinan asirinku ya tonu hada had'o karyar Amera ta samu ciki toni bansan wannan wani irin so da tsoro ne babana yake yiwa amerarnan ba Abu saikace an asircesa A baka damar kayi Aure kawai saboda gudun b'acin ranta kaje ka yi Aure a b'oye ka zalinci yarinyar mutane wlh Duka a cikin abunnan banga laifin Zahra da Kawarta ba ko Kad'an kune manyan mugayen da kuka tilastasu suka amince muku macuta mayaudara Tsaffin munafukai Ka tashi kaban wuri wlh saikunyi mamaki na Akan Lamarin nan daga kai har shi Babban munafikin sannan Ka fad'amun gidan da yake idan ka fita saika kirasa ka fad'a masa ga yanda mukayi kace ya gudu da ita kaga abunda zai faru"Jabir dukya tsure ya ce "Dan girman Allah Ammy kiyi hakuri wlh nikaina nayi Nadama tsaki Ammy taja tace" ai nadama baku fara ba ma ka fad'amun gidan da yake da ita " kasa yayi da kansa yace "buzu quarters "Mikewa Ammy tayi ta ce " Saura kakirasa ka fad'a masa munyi haka tunda kunsaba munafurci tare "Kasa yayi Jabir da kansa yana muzurai saurin barin palourn Ammy tayi Chuchu dake tsaye duk tayi shock kafafuntama ji tayi sun kasa daukarta sosai Abun yazo mata yanda bata tab'a tunani ba wai Yayanta ne Mijin zahra kuma shine uban cikinta Shine sukayi *Auren wata tara* da ita idan ta tuna saitaji kamar almara Kallon screern din wayarta tayi ganin kiran da Asmy ke mata mema zata ce mata " Muryar Jabir ce ta dawo ita daga dogon tunanin data Lula ya ce "Chuchu please waya fad'awa Ammy zancen nan taya tasan wannan din" Turo baki gaba tayi Dan duk haushinshi takeji har yayan nata ta ce "Saika bi Ammyn ka tambayeta" tana gama fad'ar haka ta juya "Mikewa Jabir yayi zuciyarshi chunkushe da tunannika ta wani bangaren kuma yaji dadin da Ammyn sukasan da maganar ko ya fita daga sarkarkiyar d'aya shiga tsaka Baiyi yunkurin kiran MD ba Koda wasa Dan yasan yana fad'a masa guduwa zaiyi da ita koma subar k'asar Wanda bazaiso hakan ba Tunda asiri ya tonu gwara kawai ta fanjama " Ammy sosai ranta ya b'aci Hijab kawai ta sanya da takalmi ta fito Chuchu ta biyota ta ce "Ammy ina zaki kuma Yamma tayi fa" daga mata hannu tayi ta ce "Ki koma yanzu zandawo zanje na taho da yarinyar nan tun yanzu kafin abokin munafurcin nasa ya kirasa " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke Ammy na fita ta kwalawa driver kira Ta ce ya kaita Abuja cikin Sauri "Ba bata lokaci motarsu ta dauki hanyar Abuja ana gab da magriba Suka isa Kai tsaye buzu quarters suka nufa......MD na zaune a Palour ya na dafe da kansa Saboda yau ba k'aramun kuka zahra tayi masa ba akan ya maida ita gidan iyayenta ga Allah ya isa da ta dinga ja masa yau ko.abincin kin ci tayi duk ta chaza masa kai yajiyo knking Kamar bazai Mike ba saikuma yaje ya bud'e gabansane ya bada daram cin karo da Ammy tsaye fuska ba wasa lokaci guda Alamun Rashin Gaskiya suka bayyana k'arara a fuskarsa a rarrabe ya ce " Am my "ka bani hanya na wuce " Ammy ta fad'a a tsawace 'sosai yayi mamakin abunda baitab'a gani daga Ammyn nasa ba Hankalinsa sosai ya tashi waigawa yake Kar zahra ta fito Ammy ta ganta asirinsa ya tunu"tsawar da Ammy ta daka masa ce ta sanyashi matsawa ba shiri daidai sanda zahra ta fito daga daki cikin doguwar Hijab Fuskarta jab'e jab'e da hawaye Tsaye Ammy tana kallonsa tana kallon zahra sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammy a gidan Gabanta banda fad'uwa ba abunda Yake Sosai ran Ammy ya k'ara b'aci tunkarar wajen zahra Ammy tayi tare da kama hannunta tajata itadai zahra binta kawai take har suka isa Inda motar take ammy ta ce "shiga " ba musu zahra ta shiga motar Kallon Ammy MD d'aya biyosu yayi cikin tashin hankali ya ce "Ammy" Daga masa hannu tayi cikin Tsawa ta ce .............. *Domin magana da marubuciyar 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ .......*81 & 82* "karka Cemun komai baka da bakin da zaka fad'amun wata magana "Sannan ta kalli driver tace jamu" Bayan Inda Zahra take Ammy ta zaga ta shiga "Motarsu ta tashi sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammyn Chuchu me ya kawota gidan meye alakarta da Musty" Ganin ba amsa ya sanyata hade kai da gwuiwa tana hawaye "A sanyaye Ammy ta ce " Kidaina kukan nan kar kanki yayi ciwo"Duk yanda zahra taso shiru kasawa tayi Ammy na ganin haka ta janyota jikinta tare da Fara Lallashinta ta ce "Kiyi hakuri insha Allahu komai yazo karshe " Shiru zahra tayi tunani chunkushe a kwalwarta kafin bacci ya kwasheta a jikin Ammy tayi baccinta kallonta kawai Ammy take tana jin tausayinta na ratsa ta yarinyar abar tausaya wa ce Kamar yanda Chuchu ta bata labari ga maraici ga kuma halin da MD ya jefata Har mahaifinta ya shiga wani hali banda zargin mutane Har suka isa gida zahra batasani ba saida Ammy ta tasheta ta ce "Tashi Daughter munzo" a sanyaye zahra ta fito daga motar sosai tayi mamakin Ganin saukarsu gidan su Chuchu dan bazata mance gidan ba kama hannunta Ammy tayi a hankali take binta saboda cikinta da taga yayi girma har suka isa Babban palourn ita dai zahra na biye da ita Suna shiga palourn zahra tayi ido hud'u da chuhu Da gudu chuhcu ta Ruga tare da Rungumeta Da karfi saikuma ta sanya kuka Ammy ce ta ce "Ki bita a hankali Maryam bakiga yanda take " tsagaita kukan sukayi suka zauna Kan sopa Chuchu na dubar zahra dake hawaye Goge mata hawayen tayi ta ce "Kina.Lafiya sis?Gyada mata kai tayi har lokacin hawaye zahra take " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke ta ce "Kiyi hakuri momcy insha Allah komai yazo karshe Mikewa Chuchu sukayi tare da zahra Kallon Ammy da har lokacin ranta b'ace yake tayi ta ce " Ammy zamuje ciki"Okay tafada maki abunda take so a girka mata sannan ta huta sosai "To Ammy " Chuchu ta fad'a tana kama hannun zahra "Ki bita a hankali fa wajen hawa stairs " To Ammy Chuchu ta fada "koda suka isa d'akin Chuchu kasayin shiru zahra tayi Dan tun d'azu zuciyarta cike take da Tambayoyi Kallon Chuchu tayi ta ce " Sis Dan Allah na.tambayeki"Murmushi Chuchu tayi mata ta ce *bama saikin tambaya ba zanyi maki bayanin komai yanzu dai kiyi salla ki fad'a abunda kike so kici "numfashi zahra taja ta ce " Banason cin komai "wara idanu Chuchu tayi ta ce " taya zakice bakisoncin komai inke bakya so Unborn d'inmu yana so"Hararar wasa zahra tayi mata ita kunyar cikin nan ma take ta kauda kai Chuchu ta Kalleta ta sake cewa "please me kike son ci Dan Allah kinsan Na fad'awa Ammy Bazakici abinci ba fad'a zata maki " nafa koshi "ta bata amsa " okay bari naje na fad'awa ammy"Chuchu ta fad'a tana Mikewa saurin Rikota Zahra tayi ta ce "Ki bari mana karkije ki fada mata naji zanci koma meye " a a a ki fad'a a girka maki"girgiza mata kai tayi ta ce "Duk abunda kukayi zanci" Shikenan Chuchu ta fad'a ta ce "Bari naje na had'o maki ruwan wanka" gyada mata kai zahra tayi har lokacin mamaki take "Bayan Chuchu ta fito daga bathroom d'in Kallon zahra tayi ta ce " na hada kishiga kiyi bari naje na dawo"Okay "ta fad'a tana Mikewa a hankali Ta shiga toilet din sosai taji dad'in Wankan saboda ruwan dumin da Chuchu ta had'a mata Bayan ta gama ta d'aura towel a bakin gadon taga kaya marassa nauyi da Chuchu ta Aje mata d'auka tayi ta sanya tare da sanya Hijab tayi magrib da isha'i tana lazumi Chuchu ta shigo da plate din Farfesun naman rago d'ayan kuma lafiyayyan shinkafa da miya ce Samanta anyi yanke yanken kayan lambu da itama Tasha naman kaji a sama y'ar aikinsu da suka shigo Tare tazo gabanta ta Aje jug din dake d'auke da kunun Gyada da yasha madara cikin girmamawa ta ce " Ina yini Hajiya"Ina yini Zahra ta mayar mata Bayan barin mai aikin d'akin nan Chuchu ta tisata gaba saida ta kusa cinye naman shinkafarce ma ta kasa ci saboda kunun gyadar da ya cika mata cikin Dan sosai taji dad'inshi wajen 10 harsun kwanta ganin Chuchu bata da shirin mata
Chapter 72 · 0% Book details