Sashe 85
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dayayi mugun amsar fatarta kitso ta Sanya akayi mata shima Mai shegen kyau Tsadadden lace da yasha dinki Ta Sanya da yayi mugun yi Mata bala'in kyau simple make_Up asmy da tazo tayi Mata sai zolayarta suke ita da chuchu suna ce Mata amarya saidai ta hararesu ko ta musu Tsaki"Sosai ta fito tayi kyau kamar wata wacce zata zaben sarauniyar kyau ni kaina Saida na ce"Tubarakallah Masha Allah "saboda wankan ta wanku kallo daya zakayi Mata kasan eh ba karya ta cika Mrs MD a palour Ammy ta zaunar da su ta dinga yi musu nasiha sosai gami da nusarwa cikin hikima Ta dinga Musu nasihohi bayan nan ta ce "Iyayen Zahra shekaranjiya sunzo sunyi Mata jere dukda ba yanda bamuyi da su ba Akan su Bari karsu wahalar da kansu sukakiya jiya sunje sunyi Mata jere a Sabon gidanka daka cemun chan zaku tare sannan Nima nayi Mata nawa Allah yayi muku albarka yasa mutuwa ce zata rabaku"kafin Shima baba data Kira Dan yasa musu Albarka ya Dora Akan nashi Saida suka gama musu wa'azi sannan baba ya Kara Masa da nasiha akan yayi adalci a tsakaninsu duka matansa "Sai sannan ya tuno da Amera "Bayan sungama yi musu Nasiha Zahra kanta na kasa Ammy ta ce "Allah yayi muku Albarka "Kutashi ki tafi"A sanyaye Zahra ta Mike ta Ce "Nagode Ammy " MD ko jinshi yake cikin wani irin farinciki marar musaltuwa ya kasa kyafta Ido da kallon Zahra Masha Allah kawai yake fada a ransa Dan shikanshi yasan sai yanzu yayi Mata d'aya da d'aya rike hannun Zahra Ammy tayi har bakin labceciyar motar MD Zahra Tana tunanin Ammy batayi Mata maganar yaran ba MD ya kasa daurewa ya ce "Ammy Triple fa"Ga sunan su chuchu sunshirya su Marar Kara"Ammy ta fada Tana Kai Masa dankwashin wasa"d"an Kara yayi tare dayin dariya ya kauce "Suna tsaye Chuchu Da Asmy suka fito rike da yaran Sunsha Kayansu Suma masu mugun Kyau iri daya sosai sukayi bala'in Kyau chuchu ce ta ce "Wow Yaya gaskiya sainayi muku hoto irin wanna show haka"Murmushi yayi ya ce"Yi sauri kiyi to Kinsan banason hoto sosai"Hannunshi chuchu ta hada Dana zahra ta ce "Yawwa Ku rike a Fara muku Ku biyu"Nan chuchu ta shiga kyalla musu hotuna masu mugun Kyau a dalleliyar wayarta Kafin a Basu yaran a musu Baki d'aya wa'iya zubillah zo kuga irin kyaun da wanna couples din sukayi da yaransu kamar ka sacesu ka ruga Saida chuchu ta Gama kyallarasu kafin ta barsu sai dokin hotunan take Ganin Ammy tabar Wajen ya Sanya Zahra sakin jiki kallon asmy tayi kasa kasa ta ce "Dan Allah Anjima kuzo"Dariya asmy da chuchu sukayi suna tabawa asmy ta ce "So kike ya koromu da karnika kenan ana Shan amarcin Rana kawai zaimuzo muku ai harya hadomu da Kare"Dariya chuchu tayi ta ce kinsan ko yaya wlh ya aika"harara Zahra ta Galla musu kadin ya tsunkini Asmy ta ce "Saura ki tafi yau"Horn din da MD yayi Mata ne ya sanyata rabuwa dasu chuchu Dan ta lura shegantaka suke Shirin yi Mata kafinma ta bud'e taga ya bude Mata Shiga tayi tare da rufewa kallonshi tayi day rike little a Gabansa a ranta ta ce "Da itazaiyi tukin kenan it's kanta tasan cikin yaran yafison Little saidai ilimi yasa baka taba ganewa "motar yayiwa horn a hanya sai kallon Zahra yake da take d'an yiwa amar da Akhbar wasa dukda ya lura kunyarsa takeji kallonta kawai yake gwanin burgewa Yana Murmushi ji yake abun tamkar almara hannunshi daya ya saki tare da Kamo hannunta daya dake dauke da Lalle Abunda yafiso kenan Yana Murmushi yayi sama da hannun tare da kissing din hannun ya ce "I love this"Ganin Yana Shirin karkace tuk'in ya Sanya Zahra Jujjuya Masa idanu tare da shagwabe fuska ta ce "Karka kadamu fa"ai MD ji yayi kamar zai narke Saida tsikar jikinsa ta tashi irin yanda tayi maganar sosai ta rikita Masa lissafi lura da hakan Saida yasanya Zahra ta kusayin dariya tare da zame hannunta "Shima marairaicewa yayi ya ce "Zaki rikitani da yawa babe kija na kadamu a mota"d'an Murmushi Zahra tayi batace komai ba "Har suka Isa Yana kallonta gwanin burgewa yanda take komai cikin class sosai yake son komai nata musamman class dinta Dan shikanshi yasan ajin Zahra bana kananan Yara bane yana son mace Mai aji Daman Shi a rayuwarshi Koda suka isa Sabon tafkeken gidanshi da Shima anan gra din yake ni kaina Saida nayi kauyanci ganin irin wannan gidan aljannar duniya kenan ai duk yanda nake santin gidan md wancen wannan ya Shanyeshi ya Dame ya gidan yanda kasan kazo wata katafaren compony ko Kuma villa tafkeken gidane daya more da kayan alatu da more rayuwa girman gidanko bazan iya cewa ga kwatankwacinshi ba unguwa guda ita kanta Zahra Saida ta tsorata da ganin kyau da girman gidan yanda kasan wata tafkekiyae estate Yana rike da hannunta har suka nufi parlourn bayan ya umarceta da ta shiga da kafar Dama ai shigowar Zahra parlourn Saida ta raina kanta ganin irin turkey da Korea furnitures din da aka lafta a dakin to ai ko gidan shugaban k'asa kayan Nan da gidannan sai Haka rufin selin din dakinma kanshi abun ayi masa kauyancine tiles din Zahra ta kalla Taga Tana ganin kanta Kamar madubi Murmushi kawai MD keyi bayan isarsu tsakiyar palourn A lausassan carpet din da Saida na kusayin sumar tsaye danaga zai Dora twins kanshi ganin yanda yake sawaya ita kanta Zahra Saida ta kusa tsorata ajesu yayi gabaki daya a wayance ta take carpet Jin laushi ya sanyata sauke ajiyar zuciya itadai a rayuwarta Bata Taba ganin duk Abunda ta gani a palourn ba Bata karasa tunanin Nan ba taji ya janyota ya rungumota ta baya tare da rankwafar da kansa Yana shinshinar wuyanta ya Ce "Alhmdllh thanks you so much my all above kingamayimun komai a rayuwa Babu Abunda zance da ubangiji sai hamdala sannan nace ya barmu tare na har abada "Murmushi kawai Zahra tayi Tana kasa da kanta "Marairaicewa yayi ya Ce "please muje ciki muyi sirri aji Dani"RauRau tayi da idanu tare da juyasu ta shagwabe fuska "Suma Ce kawai md baiyi Ba ai baima tsaya wata wata ba yayi sama da ita bai direta ko Ina ba Sai bedroom ya sauketa a kataferen bedroom dinta...sosai ma'auratan Nan suka jiyar da junansu Dadi Kamar zasu cinye juna kunsan mutanen namu duka gwanayene a fagen Nan mD ko haukane kawai baiyiba Jin yanda Zahra ta Kara nice ta dawo Masa sabuwar budurwa Ai iya rikicewa ya rikicewa Zahra sai Wajen magriba suka samu komai ya lafa, fitowa Zahra tayi daga Wanka kallon MD tayi da har lokacin Yana gado kwance, wardrobe ta d'aga sosai tayi mamakin ganinta cike da Kaya na sawa wata Riga marar nauyi a cikin English wears din da ta gani iya gwuiwa ta Sanya sosai rigar tayi Mata kyau musamman data Dame ta bawa albarkatun jikinta damar bayyanuwa jikin mirror taje handrayer ta jona ta Fara busar da lallausan Gashin kanta cikin nutsuwa Daga kwancen da yake ba Abunda yake in banda kallonta Yana Kara godewa Allah d'aya mallaka Masa ita a matsayin Mata Shi kansahi yasan yanzu yayi aure yanzu yasan menene aure Yana Murmushi ya Ce "Kingamayimun komai Mamy bani da kudi ko bakin dazan iya biyanki da alkhairan da kikayimun shigowarki rayuwata kinsauya komai kedin haskece a cikin rayuwa ta data iyalaina kin bani farinciki da ba a taba bani Shiba a rayuwa kedin Allura ce cikin ruwa Ni Allah ya bawa damar chafka I love you so much my wife Ina sonki sosai Ina sonki son da Ni kaina bazan iya kwatanta adadinshi ba "kalamai masu sanyi da sanyayar zuciyar masoyi MD ya dinga zuba Mata Kuma sosai suke tasiri a zuciyar Zahra Saidai kunyarsa ta hanata mayar Masa saboda wani irin nauyinsa takeji Ganin magriba na Shirin gotawa ya Sanya Zahra Ce wa"Za ayi magriba fa ya musty kana kwance"Murmushi yayi tare da mikewa ya Ce "sorry malamata yaufa sai kinyimun karatun Nan Nak'i Mai narkar da zuciyar Mai sauraro cikin zazzakar muryar Nan Taki har nayi bacci sannan ki chanza sunan Nan kibani wani"Murmushi kawai Zahra tayi ta Ce "Uhm"kafin ya fito daga Wanka Harta tada sallar Magriba ganin Tana salla ya Sanya md Shima Sanya jallabiya lokacin magrib ya gota dan yasan yanzu masallataima sun Gama yasanyashi tada Salla a kusa da ita Zahra ta rigasa gamawa a ranta ta Ce"Insha Allah saina sauyaka daga sallar gidan Nan Dan ta Lura ko da sukayi zamansu a gidanshi na Zaria akwai lokutan da yake salla a gida dukda dai taga Yana da kokarin ibada sai idan ya makara Saida suka Gama salla md ya tuno da yaran mikewa yayi ya Ce "Subhanallah na Manta munbar yaran Nan a palour "a rude Zahra ta Mike ta Ce "Sai yanzu na tuna" ta fada Tana nufarr palour da gudu binta yayi kasancewar akwai tazara tsakanin parlourn da bedroom din ya Sanya basuji irin kukan da yaran sukayi ba wajensu suka karasa inda sukaga fuskar little Zahra zabe zabe da hawaye ita da Amar sun hade waje guda suna baccin wahala daga gani ba karamun kuka suka Sha ba Akhbar ko sai tsala kuka yake har Yana kakkafewa a matukar rude Zahra ta daukesa ta Fara jijjigashi da lallashinshi dakyal ta samu ta lallasheshi harta samu ya karbi mama ajiyar zuciya ta sauke MD ko little da Amar ya dauka a hankali ya Ce "Sorry my kids parent din ku sunbarku a palour sunmanta daku "Daidai lokacin da little ta farka itama ta tsala kuka dakyal suka samu suka lallashi yaran sai Wajen isha'i suka samu sukayi shiru bayan kowa ya koshi su kansu sai sannan suka tuna da yaran sunjima a palourn dole susha kuka su suna chan wata duniyar bama suji kukan ba "Da Dare Ammy ta Aiko driver da cooler abinci MD ya fita ya amso Bayan Zahra tayiwa yaran Wanka Wanda MD ya taimaka Mata da shiryasu Kaya ta Sanya musu Bayan ta feshesu da turarruka na Yara masu santin kamshi itama Daman tunda tayi Wanka ta feshi gashi Daman a gyaran da Ammy tayi Mata hada na kamshi Dan ko wake ta zauna saiyayi akamshi