Sashe 12
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanzu sun gama Shirya koma yau Jabir ya kaisu Shopping mall Wanda shi ya biya musu kudin sayayyar komai itadai Zarah a sanyaye take yayinda Asma'u ke d'aukar musu komai da zasu buk'ata. Bayan sun gama ya biya kudin suka kama hanyar gida Bayan shigar Asma'u gidan sun tab'a Hira sosai tsakanin Zarah da Hafiz Bayan nan tayi mishi Godiya akan irin hidimar da yake mata murmushi ya sakar mata ya ce. "Komai nayi miki ban fad'i ba matata har na k'agara ranar nan tazo bansan wani irin farinciki zan shiga ba ranar da muka zama mata da miji" Murmushi Zarah tayi tare da rufe fuska kunya ta baibayeta. "Cikin Sauri ta bud'e murfin motar tare da fita " Dariya yayi tare da girgiza kai Dan kunyar ta Zarahn tashi ba k'aramun burgesa take ba yanason mace mai kunya a rayuwa(exectly wlh kunya ado ce ga y'a mace maza da dama suna son mace mai kunya Rashin kunyar y'a mace ba wayewa bace Allahsa mu dace") yaune tafiyar su Zarah makaranta tunda suka tashi cikin farinciki suke su dukansu Bayan sungama Parking d'in komai d'insu an saka a boot din motar hafiz . nasiha sosai mai shiga jiki Malam ya dinga musu Bayan suma su maman su Asmy sunyi musu nasiha Mama Rabi ko ko Allah ya kiyaye batace ba sai bak'inciki take dubu goma Malam ya basu tare da cewa sunyi wani abun dashi. Dukansu sosai sukayi kyau cikin manyan hijabai Asmy ma tayi kyau Dan itama masha Allah badai kyauba a hanya Hafiz sai satar kallon Zarah yake har suka isa Zaria kai tsaye cikin Makarantar A B U suka nufa. Asmy ita ta dinga shigar musu da kayansu hostel din da aka kama musu Zarah ko tana gaban motar Hafiz ne ya mik'o mata kwalin waya biyu Duka iri d'aya Tare da cewa . "ga wayarki keda Asmy please dia karkice bazaki amsa ba saboda bazan juri Rashin jin muryarki a kusa dani ba Kuma hasalima An sanya mana Aure ina da hakkin da zan d'auki hidimarki" Amsar kwalin wayar Zarah tare da cewa "Hakane ya Hafiz nagode Hakika kaid'in ka taka rawar gani a cikin rayuwa ta babu abunda zance dakai Sai fatan alkhairi da nasara a rayuwa mungode" Murmushi yayi najin dadi tare da mik'a mata 20k yace gashi ba yawa ku fara chachaftawa da wannan" "girgiza kai tayi tare d'ago da dara daran idanuwanta "a a a ya Hafiz wlh bazan amsa ba hidimar tayi yawa." "kamo lallausan hannunta yayi tare da damk'a mata kudin a hannu Wanda tunda ya tab'a hannun Zarah taji wani irin shock saida ta rumtse ido kafin ta daidaita nutsuwarta tayi saurin kwace hannunta Tare da b'ata fuska ta ce " "Meyasa zaka rik'emun hannu ya Hafiz Bayan ni ba maharramarka bace"hade hannayenshi waje biyu Alamun rok'o ya ce "am sorry my Zarah by mistake ne bansan nayi ba" " Uhm" kawai tace tare da bude motar ta ce "Ka tafi karkayi dare fa kaga hanya ba kyau" "korata ake kenan"cikin murmushi ta bashi amsa da "Nina isa Banki mu shekara haka ba" 'ta fad'a ta na rufe fuska " murmushin jin dad'i yayi cike da kewarta Hafiz ya juya yabar makaranta Inda Zarah ta kama hanyar hostel d'insu. ta na shiga ta samu Asmy Harta cire hijab din ta na shirya musu kaya "Kallon d'akin tayi ta ce. " wai nufinki mu kadai ne kenan a dakin" "Wlhko Nima haka nagani naga duk ba a fara zuwa ba Kinsan Monday ake fara lectures ba kowa zai zo kamar haka ba" "Kice mu iyayen azarb'ab'i mune farko farko ta fad'a tana cire hijab din jikinta " Dariya asmy tayi ta ce "Keko abunka ga farin shiga Dariya Itama Zarah tayi tare suka kimtsa komai kafin Zarah ta mik'awa Asmy wayar da ya Hafiz ya saya musu zo kuga murna wajen Asmy hada tsalle ta Rungume Zarah. " itama Zarah cikin farincikin take bud'e wayar suka ga iPhone 6+ ce Duka iri daya dubawa sukayi kowacce Duka an sanya sim ganin ba chaji gashi ba wuta ya sanyasu ajewa sai Chan wajen 8 aka kawo wuta nan suka sanya wawowin chaji salla Zarah tayi tare tare da hayewa kan bed tace. "nikam bacci zanyi wlh nagaji" Asmy ce ta ce "Chab aini nan inkinga na kwanta to wayar nan ta cika Na duddura abubuwa a ciki har what's app saina bud'e komin dare. " Dariya Zarah tayi ta ce "aifa abun nema ya samu nikam bacci ma zanyi waya bata dameniba sosai Idan kin d'auko abubuwan nima ki daukoman amma what's app kadai zaki budemun sannan kiyimun down load din Qur'an na ji da na karantawa" " To" Asmy ta fad'a ta ce "Mu sarakan zumudi Allah sama akwai data a sim din " Juyawa Zarah tayi tare da kwanciya ta ce . "Allahsa ma babu muga ta tsiya kiyi ,zaman hofi" "Insha Allahu ma akwai muguwa Asmy ta fad'a tana Mikewa itama tare da Fara Sallar bacci ne ya kwashe Zarah cike da gajiya. Ranar Monday suka fara Lectures Sosai Dukansu suka maida hankalinsu ga karatunsu Zarah suna waya da Hafiz Sosai Kuma suna chat dukda ba Sosai take hawaba saboda ba wasu mutanen chat gareta ba. danma Asmy tayiwa wata kawarsu da sukayi sec magana ta bada number su aka sanyasu grp din makaranta anan ne ma wasu ke binsu PC har suke chat amma dukda haka Zarah saita yini bata hau online ba. Karatu suke sosai ba kama hannun yaro yanzu hostel din ya fara cika da mutane Dakinsu ma sunsamu Karin wata Mutum guda zaituna. <Kaduna> Cikin marairaicewa ta ce "Yaya Dan Allah ka bari na tafi A B U din wlh yaya banason karatu a America plx harfa sun bani admissions kuma ma har anfara lectures yaya Dan Allah" "Chuchu bazan barki kiyi karatu anan k'asar ba fa Ga yanda na tsara tare zamu tafi america a gidana zakiyi karatunki amma ban lamunce na barki ki tafi Zaria karatu ba Nafison kiyi a gaba na na sanya miki ido saboda wannan rawar kan naki Dan kiyi abunda kikeso shiyasa ai kikak'i cike KASU kika zab'i ki tafi Zaria sannan banason kiyi karatu a kasar nan sanin kanki ne to bazaki ba A B U din ba na gama magana" "kuka Chuchu ta sanya tare da Fara birgima ta sangarta sosai ta ke kuka da diddira kafa Ammy ce ta shigo ta ce . " Subhanalla Me akayiwa Auta ta ke wannan kukan "MD dake zauna baice uffan ba sai maida hankalinshi ga kallon da yake yayi" Chuchu ce cikin sangarta ta ce"Ammy yaya ne ya ce "Wai bazan tafi Zaria karatu ba dole sai dai mu tafi america tare Bayan ni banason nesa dake Ammy plx ki ce ya barni " "Kallon MD Ammy ta yi ta ce " me yasa bazaka barta ba babana tunda harta samu kuma ta nuna Chan din take so ka barta ta tafi kawai nima banason tayi nesa dani saboda kaga gidan kadaici zaiyimun yawane ba Abbanku Zainab na gidan mijinta kaima ka tafi sai anganka please Babban yaya ka barmun ita " Jan numfashi Yayi tare Dagowa ya harari Chuchu dake Kuka jikin Ammy ya ce. "Allah Ammy kin sangarta Yarinyar nan jifa irin tabarar da takeyiwa mutane" Dariya Ammy tayi ta ce "Ah muka sangarta ta dai duk gidan nan wa ya fi sangarta Maryam sama da kai " "Ummmm to Taci arzikinki Ammy na yarda Tayi Chan d'in Allah kiyaye Amma Tana cigaba da irin wannan shigar Saidai taga na cireta Nayi mata Aure " ya fad'a yana kallon matsatsun Riga da wandon dake jikinta Tsallen murna Chuchu ta buga tare da rugawa ta Rungumeshi ta ce. "Thnks Babban Yaya Uba Allah ya k'ara girma bazan sake ba sannan tayi Dariya ta ce hhh yaya Ai ko kayimun Auren bazan zaunaba y'ar k'arama dani kuna kaini kafin ku dawo ma na rigaku gudowa " Duk miskilancin MD saida ya d'an dara tare da Kai mata "Dukan wasa a baya ya ce. " Kin rainani ko chuchun yaya shiyasa kika fad'amun haka" "Ammey ma tayi Dariya tare da girgiza kai ta ce "Allah shiryaki Auta" Dariya Chuchu tayi tare da mik'ewa ta Ruga cikin tana tsallan murna nan ta kira Aunty Zey ta mata albishir yaya Ya amince.. A nan take MD ya kira Wani Abokinshi dayake lecturar makarantar ta Cikin waya yayi mishi bayanin komai take ya ce Ai ba matsala tunda ta samu registration Banki kawai za Aje ayi" PA d'inshi Ya kira Tare da sanyashi yaje yayiwa Chuchu registration saida yaga ya gama yi mata komai tukwana Ammy ce ta Kalleshi da damuwa a fuskarta ta ce. "Baba na wai ya maganar bincike game da kisan mahaifinku naga Har yanzu bakayi wani Abu ba yaci ace angano kowaye yayi mana Wannan d'anyen Aikin" "numfashi Ya fesar tare da cewa " Insha Allahu Mamy Gaskiya zatayi halinta inaji a jikina nan kusa akwai abun al'ajabin da zaizo bada jimawa ba akwai shirin da nake akan Lamarin " Goge hawayen da ya zubo mata Ammy tayi tare da cewa"Allah dai ya Toni.Asirin ko suwaye sukayi mana wannan d'anyen aikin insha Allahu bazasu gama da duniya lafiya ba Sannan asirinsu saiya tono" "Ameeeen MD ya fad'a tare da mik'ewa zai shiga Bedroom d'inshi dake gidan " da mamaki ammy ta Kalleshi ta ce "Ina kuma zaka Bayan Matarka na gari"...... *Domin magana da marubuciyar 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ *AUREN WATA TARA* MALLAKAR *Hajara L Sadeq* *_TEAM GAWURTATTU BIYAR_* .........*15 & 16* Ta na gidansu Ammy"tsaki Ammy