← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 92

Sashe 81

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maimaita zahra ko jin abun take tamkar almara wai yau itace gata ga kakanta,yau itace taga jinin mahaifiyarta ,Allah sarki wasu hawayen farinciki ne suka zubo mata tana murmushi ta ce"Kana nufin kaid'in kaka na ne kai ka haifi mahaifiyata daman da rabon zanga dangin Mama a duniya "ta fad'a hawaye na zubo mata saikuma ta Rungume Baba ta ce " Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nunamun wannan ranar tamkar almara Baba najima da bakincikin Rashin sanin dangin mahaifiyata bantaba kawowa a raina ba zan hadu dasu Cikin Sauki haka meya kawoka gidan nan har yayi silar haduwata dakai Baba"ta k'arasa fad'a tana hawaye "Rungumeta sosai Baba yayi yanajin kaunarta kamar yanda yakejin k'aunar y'arsa data rasu " sosai su Ammy suka girgiza dajin al'amarin nan Chuchu da Ammy da Hajiya kaka da bata jima da shigowa ba hada hawaye MD ko mamaki ya gama cikasu cewa yayi "mezai hana Baba ka bamu labarin abunda ya raboka da garinku da wadanda sukayi harin rayuwarka da ta iyalanka " Saida suka saki juna daga rungumar da sukayi da zahra kafin ya goge hawayen bak'inciki da takaici ya ce "Yau zan baku labarin asalin waye ni da kuma silar shigarmu cikin wani hali ta dalilin d'an uwa Nida y'ata asalinmu haifaffun Jihar jigawa ne ina da mata d'aya Hajiya Saratu ina da kanne Shida Wanda muka fito ciki d'aya uwa d'aya uba d'aya sai Wanda muke uba d'aya Mudan Wanda shine autanmu shi kadai mahaifiyarsa ta Haifa har Allah yayiwa iyayenmu gaba d'aya a hankali a hankali rasuwa dalilin wannan ya sanya muke matuk'ar sonsa muke jansa a jiki bamu tab'a nuna masa y'an ubanci soyayyar da nake nuna masa ko Wanda muke uwa d'aya uba d'aya bana nuna musu t un ina yaro daman ni natashi mutum ne mai neman na kansa na kasance Dan kasuwa tun ina K'ananan kasuwanci da noma har Allah ya habaka na zama Babban attajiri a garinmu Wanda daidai ne zaka fad'a suna na Alhaji abdussalam Mai fata na samu sunan nan da dalilin Kasuwancinsu fatocin da nayi Mata ta d'aya Hajiya Saratu wadda tsawon shekaru bamu tab'a haihuwa ba sai Bayan shekaru har manyantaka ta fara kamani Allah ya bamu haihuwar y'armu Fatima wacce taci sunan kakarta ne ta wajen uwa hakan yasa Muka fiyan kiranta da "Mamy " Gata da soyayya ba irin Wanda bamawa Zahra'u kasancewarta y'a daya tilo a wajenmu amma dukda gatan da muke bata baihanamu bata ilimin boko da na arabi ba Gabak'i daya Na d'auki yarda na bawa Mudan Wanda Duka huldar kasuwanci na Shi na sanya a ragamar abun kasancewar girma ya fara kamani shi kuma lokacin yana tashen yarinta duk wasu garuruwa da nake huld'a dasu shi yake zuwa ya wakilceni sosai na dorasa akan dukiya ta saboda yarda Wanda a ido ya nunamun yafi kowa kaunata tare da iyalina ina son mudan har cikin raina Wanda har sauran y'an uwana sukance Nafi kaunarsa akansu Nayiwa mudan duk wani gata na Gina masa Gida Tafkeke na saya masa mota sannan koda ya tashi neman Aure Nina tsaye masa Akan hidimar komai duk wani gata da Dan uwa ke yiwa Dan uwa nayiwa mudan da gangan nake sakar masa kofar dazai samu alheri ina sane saboda ina son Shima yazama wani Abu ko Bayan raina ya zama shine zai kula da iyalina da dukiya ta hakan yasa bana boye masa komai yasan duk wani sirrina yana kanena amma bani da abokin shawara sama dashi ashe bansaniba soyayyar ido mudan yakemun bansani ba ashe mudan Makasar rayuwata yake nema k'watsam wata rana da bazan tab'a mantawaba ranar bak'inciki,ranar da ta kasa goguwa a cikin tarihin rayuwata muna kwance tare da iyalina a lokacin Zahra'u ta zama budurwa Har anfara shirye_Shiryen Aurenta Dan mutane da dama bama jigawa kadaiba har sauran jahohi sukan fito su nuna.suna son zahra Saboda yarinyace mai matuk'ar nutsuwa da hankali Ga kyau uwa uba tarbiya Dan zahra bata tab'a b'atamun raiba ita da mahaifiyar ta mariganyiya Muna cikin bacci mukaji barayi sun duro mana sosai hankalinmu yayi tsananin tashi ba wacce muka tunano sai y'armu Duk mun rikice mun dunkule waje guda a haka mukaga Shigowar garda_gardan samari Wanda bazan iya cewa ga yawansu ba saboda tashin hankalin da muka shiga gabak'i d'ayansu suka zagayemu da bindiga gaba d'aya fuskokinsu a rufe Na tsakiyarsu ne ya bud'e fuskar Wanda saida na kusanyi sumar tsaye ganin Mudan ne tsaye da bindinga ya saitani dak'yal na iya D'aga baki cikin tashin hankali na ce "Mudan ,mudan" Kecewa yayi da wata mahaukaciyar Dariya ya ce "Kana mamakin gani na a nan ko to ka daina mamaki nidinnan da kake gani makashinka ne da hannuna zan kasheka yau na kashe iyalanka gabak'i d'aya zan mallaka gabak'i daga dukiyarka Tun Asali daman ni ba Kaunarka nake ba dukiyarka kawai nake So kuma Alhmdllh lokacin amsarta yayi saboda Nasan Duka gaba d'aya ilahirin adadin dukiyarka da kadarorinka ina son Ka daukomun duk wasu takkadun kadarorinka da baka bani ajiyarsu ba ka mik'omun da hannunka kafin na kasheka" sosai hankalina yayi tsananin tashi Dan uwana Ace akan dukiya zai iya kasheni nashiga tashin hankali da rudun da bantaba shiga ba ranar ina hawaye na ce "Mudan zan mallaka maka Duka dukiyar daka buk'ata amma ka sani Amana Bazata barka ba mudan ka mance cewar ni jininka ne ka zab'i da ka kasheni Akan dukiya daudar duniya Tabbas yau na yarda da cewar d'an Adam bashi da Tabbas" wata irin Tsawa ya dakamun ya ce "Bana buk'atar jin wani Wa'azi daga gareka ka bani abunda na fad'a" Suna tisamun bindiga aka naje na D'auko masa gabak'i d'aya takaddun kadarorina sannan nasa masa hannu a wasu takaddun da tashin hankali baisa na tuna takaddun menene Matata cikin tashin hankali da bak'inciki ta ce "Amma kaidai mudan anyi butulu mugu azzalumi macuci insha Allahu karshenka bazaiyi kyau ba saikayi mutuwar wulakanci makaskanci " Harbin da yayiwa Matata ne A kirji ya k'ara rud'ar dani da shigar dani cikin tashin hankali daidai lokacin da naga shigowar zahra D'akin tana shirin shigowa Na ce "Ki gudu zahra karki shigo ki gudu karki yarda mugayen nan su kamaki zahra ina son ki tsira juyawar da zasuyi Su bita tana ji tana gani ta Ruga a guje inaga lokacin da wasu daga cikinsu suka mara mata baya kafin kuma Naji Jiniyar y'an sanda cikin tashin hankali Suka rude mudan yace mu maza mu tafi Harbin nan da nayi ne ya janyo hankalin jami" an tsaro d'aya daga cikinsu ya ce "To shikuma wannan yazamuyi dashi" mu tafi dashi mun kasesa a.hanya suka fad,a suna sungumata kamar wani yaro Cikin boot din mota suka jefani sosai nasha azaba kamar zan rasa rayuwata Kafin bansan Inda suka tsaya ba saigani nayi sun fiddo ni sun jefani cikin daji suna saita ni da bindiga daga lokacin bankara sanin abunda ke faruwa ba duk halin da na shiga na shige shi ne sanadiyar d'an uwa ya kashe mun mata a kan ido na yaso hallaka rayuwata inbanda Allah yasa ina da sauran kwana a gaba "ya k'arasa fad'a cikin hawaye " Kowa dake palourn saida ya girgiza dajin wannan labarin wai Dan uwanka ne yayi maka haka musamman zahra da yau ta had'u da kakanta sannan taji Tarihin mahaifiyarta sosai su Ammy da MD suka jajintawa Baba sannan sukayi Allah wadarai da wannan D'an uwan nasa ranar Baba jinshi yayi cikin wani irin farinciki ganin jinin y'artasa harda jikokinta md ko yasha alwashin saiya kwatowa baba hakkinshi a wajen Dan uwanshi duk inda yake bayan komai ya lafa Baba ta kalli ammy ya ce "Hajiya naji kince Zahra ce maman yaran Nan ko kina nufin ki cemun matar jikana ce "Murmushi dauke da fuskar ammy ta ce "Eh baba matarsa ce Allah ya kawoka a daidai lokacin da muke da bukatarka Kallonsu Zahra tayi har md ta ce "ku bamu waje zamuyi magana"A tare suka tashi Zahra jinta take cikin farinciki marar musaltuwa bayan ammy tayiwa baba tsoho bayanin yanda asalin aurensu Zahra ya kasance saidai ta boye musu na dalilin auren akan matarsa saboda batason Zahra ko danginta suji abunnan abun kunyarta ne Sosai baba yayi mamakin al'amarin ta wani bangaren Kuma yaji Dadi Sosai da ammy ta fada Masa yanzu md yanason Zahra Sosai itace dai take tunanin ko Bata sonshi bazata amince da koma Masa ba sannan batasan ta yanda zasu tunkari iyayenta ba sun tattauna Sosai tsakanin Ammy da Baba har Kaka kafin su tsaida magana akan jibi idan Allah ya kaisu za a tafi garinsu baba ayi masu bayani sannan a Basu hakuri haka ko akayi ranar suka shirya gabaki dayansu Ammy,kakan Zahra,Chuchu,Zahra,da triple dinta sai Hajiya Kaka ,md ne kadai ba a je dashi ba bayan isarsu batsari Kai tsaye gidan bappa suka wuce Wanda Zahra itace ta gwada musu hanya Banda faduwa babu abundan gabanta yake Sosai Aka karramasu Dukda zarha Bata yarda ta had a Ido da kowaba gabanta kawai ke faduwa A sace take Kallon baba da Shima tunda ya shigo ita yake kallo fuskarshi ba alamar walwala ganin da Zahra a tafiyar bappa yasan maganace Mai mahimmanci hakan yasa ya Kira Yan uwa baba su mama habi kowa duk ya hallara a dakin bayan an gaggaisa cikin mutunci Nan ammy tayi musu bayanin komai game da auren Zahra da sukayi da d'anta a boye har ciki ya Samu har zuwa haihuwarta suma dai Bata fada musu dalilin auren na md ba ta ce dai shirme ne irin na Yara sannan ta Kara kafa musu hujja da nuna musu video din daurin Auren sunyi mamaki matuka da gaske Jin wanna chakwakiyar su mama habi kuwa ajiyar zuciya suka sauke dukda sunji zafin aurar da kanta da Zahra tayi Amma Kuma sunji Dadi da diyan suka kasance y'an halak baba ko cikin bacin Rai ya ce"Kin bani mamaki Zahra ina tarbiyarki,ina iliminki,har ki aurar da kanki ba tare da izinin iyayenki ba kenanma bani da wani amfani a wajenki Dan haka. Ki tashi kibani guri tunda bani da wata daraja a wajenki har Kika iya aurar da kanki ba izininmu ki tashi ki tafi bana bukatar ganinki"Baba ya fada cike da takaici,"Kuka sosai Zahra ta fashe dashi ta ce "Dan Allah Baba kayi
Chapter 81 · 0% Book details