Sashe 45
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dinga gaisawa a hanya sai Farinciki yake yana mamakin wani irin Abu ne akayiwa tsohon nan da har yake gudun garinsu na haihuwa shi kanshi saboda tsaron tsohon ya sanya yake tahowa a sirrance koda suka isa kd har dare ya fara gidansu ya fara zuwa yayima Ammy albishir da samun lafiyar Baba Inda ya bata labarin abunda ya basu a takaice sosai Ammy tayi farinciki kuma tayi adduar Allah ya k'ara masa lafiya ta ce Insha Allahu Zata samu lokaci taje ta ga jikin nasa daga gidan ammy gidansa ya wuce lokacin Amera hartayi bacci saida ya shiga d'akin ta gane yadawo cikin hammar bacci ta mik'e ta ce " yaushe ka dawo honey"yanzu harkinyi bacci kenan"wlhko na gaji da jiranka na kwanta wai ina kaje haka "Wani waje ina tsohon nan da nake baki labarin mun tsinceshi da dad'ewa tun kafinma muyi Aure " Eh nagane"Shine ya warke ya samu lafiya"Tab'e baki Amera tayi ta ce "Kaidai honey baka gajiya da kwashekwashe wlh a tunanina tuni ka wurgar da talakan tsohon nan saikaje ka kwaso mana alkakai daga tsintar mutum a titi kawai ka daukeshi ka dinga hidima dashi Haba wannan Abu Dame yayi kama sai wahalshe da kanka da kayi ba dangin iya bana baba Nifa banason harka da talakkawa wlh Haba su goga maka karnin talauci " ta fad'a tana yamutsa fuska"girgiza kai kawai MD yayi Dan baiyi mamakin abunda ya fito daga bakin Amera ba Tun fil azal ita daman ta tsani talakka Wanda hakan d'abi'ar da ta taso da ita daga gidansu ne duk yanda yaso ya sauya ta amma hakan ya gagara "Baice mata uffan ba sai rage kayan jikinshi da yayi yanajinta tana gunguni a haka har yaji ta koma bacci girgiza kai kawai yayi yana mamakin yanda Amera ta tsani talaka take wulakanta mutane da batasan darajarsu ba " Bayan ya watsa ruwa gefenta ya kwanta baccin gajiya ya daukesa..washegari around 11 dare MD na kwance Amera na gefenshi tana chat da kawayenta Sai dariya take shiko ya lumshe ido babu wacce ke fad'o masa a rai sai Zarah a Gaskiya yana da buk'atar ta koba komai tana bashi abunda baya tab'a samunshi a wajen Amera koda kuwa zai shekara suna Abu d'aya "Lumshe ido yayi ya bud'e sai yaji Yana son jin muryarta tsaki yaja a ranshi , "Tunani yayi yanzu ai ko yaje zaria suna Hutu tunda ba sanin garin da take yayi ba Yasan dai tunda take zaman hostel to ba yar garin bace Kallon Amera yayi dake gefenshi tana chat ya ce " My Merah chat d'in ya isa kizo mu kwanta"Sorry honey ka kwanta wani labari ne luzy take bani ba yanzu zan kwanta ba "Shiru yayi bai kuma ce mata komai ba " Duk yanda yaso bacci ya d'auke sa kasa daukarsa yayi saboda a matuk'ar bukace yake sai wajen 12:00 yaji kwanciyar Amera janyota yayi jikinshi koya rage zafi Amera najin haka ta ce "Haba honey Dan Allah ka barni na gaji Wlh bacci nakeji" Kyaleta MD yayi badan komai ba saidan bayason takurata a ranshi yana mamakin saita dinga cewa ta gaji saikace wace ke wani aikin wahala na farko dai ita ba ma'aikaciya ba,ba y'ar kasuwa ba,ba wani aikin gida take ba macen da ko shara bazata ce ta tabayi ba ,Amma duk dare saita gama chat d'inta da kawaye tace ta gaji"Da wannan tunanin dak'yal ya samu bacci ya kwashesa washegari da misalin 4pm yana zaune a kujerar palourn su suna Hira da Ammy Chuchu ta shigo gidan "da fara'arta ta ce " Lah yaya Kaine two days bana ganinka karkaga yanda nayi missing dinka "murmushi ya sakar mata ya ce " Daga ina Haka Auta na ganki da jaka"gefenshi ta zauna ta ce "Daga gidan Aunty Zey nake kwana na biyu a Chan " Kice ziyara aka kai mata "Murmushi tayi ta ce" Eh Yaya "Ammy ce ta ce " Tofa keda kikace zakiyi sati me ya maidoki"Dariya tayi ta ce "kewarki ta dawo dani ammy Gani nayi bazan iya ba ina gari bana ganinki sainayi ta tunanin kewa zatayi miki yawa gasu y'an rainin wayan yaran nan na Aunty Zey nayi da su taho mu taho suyi maki kwana biyu sukaki wai Saidai in gidan Uncle zankaisu shiyasa na tahowata watau ni sun rainani"ta fad'a tana turo baki" murmushi Ammy tayi ta ce "Ai yaran nan sarkafar iyaye garesu shiyasa nama hakura da a kawomun su Dan ba zama ba zasuyi sun fiso su jisu kusa da iyayensu sai suje Chan su karata Tunda ga Auta ai nasan ke kin bani Yaranki ko" Dariya Chuchu tayi tare da rufe fuska ta ce "Kai Ammy Saidai yaran Yaya dai" Ohhh bazakiban ba kenan kun nunamun Yayan shine kawai nawa ko to shikenan Shima Allah ya kawo nasan kuga yanda nima zan gwada muku banbanci Dan Ko halawa na sayawa yaranshi bazan bawa naku Ba "Dariya Chuchu tayi ta ce " Kai Ammy Bafa haka nace ba "MD najin hirarsu bai tanka ba saida Ammy takawo zancen yaransa Yaji zuciyarsa wani iri a ranshi ya ce " Allah yasa nima ina da rabon ganin nawa yaran"ganin hirar zata sanya MD tunani ya sanya su sakin hirar suka kama wata MD ne ya kalli Chuchu ya ce "Tunda kika dawo Hutu bakije gida na ba why" Sorry yaya Aunty Amera na gidan shiyasa bana son zuwa "Bata fuska yayi ya ce " Ita ga dodonki ko?girgiza kai tayi ta ce "Yi hakuri Yaya ba haka bane" Saura kwana nawa hutun naku ya k'are "3weeks" Okay shirya mu tafi ki k'arasa hutun a gida na "Kamar zatayi kuka ta ce " Yaya Za abar Ammy ita kadai fa "Sanin Halin Chuchu sarai ba jituwa Suke da Amera ba ya sanya ta cewa" Kayi hakuri Babban yaya tayi maka kwana biyu nima banajin dad'in gidan ni kad'ai sai masu aiki "To shikenan Ammy" ya fad'a Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke Kala biyu Chuchu ta d'auko suka tafi gidan MD dukda ranta bayaso a palour suka tarar da Amira ta harde kafa daya kan d'aya tana latsa waya y'ar aiki durkushe gabanta tana mata tausa a kafa "Tsaki Chuchu taja a ranta ta ce " kamar wata yar shugaban kasa mtwsss fuska murtuke ta zauna palour Bayan MD ya zauna Dagowa tayi tare da Fara Murmushi ta ce "Honey yaushe ka dawo" Yanzu "ya bata amsa yana lumshe ido " Tsawa ta dakawa me aikin ta ce "Bazaki tashi ki tafi ba kina ganin mijina ya dawo Dan kutumar ubanki zaki zauna a nan ban muku dokar cewar ko a bisa sabani idonku ya had'u da na mijina a bakin aikinka ba to kema yau aikinki ya k'are Dan haka kije na koreki daga yau na kuma ganinki a hanyar layin nan ma sai nasa an kama Duka ilahirin danginki " Cikin kid'imewa y'ar aikin ta fara kuka tana magiya ta ce "Dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri wannan Aikin shine madogarata idan na rasashi bansan ya zanyi ba kiyi hakuri ki yafemun ina tsoron tashi ne karkice kuma nayi laifi shiyasa kimun rai Hajiya" D'auketa da wani irin Mari Amera tayi Wanda Marin saida ya tsoratar da Chuchu ta ce "Ni zan fad'a magana ki musa mun Dan Ubanki y'ar matsiyata dake zanyi musayar baki tana shirin Kara d'auketa da wani marin Chuchu tayi Sauri ta shige gabanta " Wani banzan kallo ta watsawa Chuchu ta ce "Ke kuma ina ruwanki matsa kiban waje" bazan matsa ba idan ke bakisan darajar d'an Adam ba ni na sani me yarinya tayi miki Dan zalinci zakiyi mata irin wannan Marin Dan kina tutiya da arziki kifa sani arzikin nan da kike tak'ama dashi Allah ne yake rabawa ga duk Wanda yaso suma talakkawan basu sukayi kansu ba Allah ne yayosu haka haka masu arzikinma Duka yin Allah ne akanme zaki dinga wulakantar da na kasa dake dandai kawai suna karkashinki"wani banzan kallo Amera ta watsa mata kafin ta ce "Allahu Akhbar ke kuma yaushe kika fara wa azi bamu da masaniya" banza Chuchu tayi mata tare da kama hannun yar aikin sukayi waje kudinta 20k dake hand bag d'inta ta bata tare da bata hakuri "kafin ta dawo Inda ta samu MD haka ta barsa kamar komai bai faru ba a ranta ta ce Wlh hada laifin yaya da ya bari Matar nan take iskanci yanda taso" Bata kuma waiwayar Amera ba tayi wucewarta D'akin da take sauka tana Jan tsakin Haushi da tsanar halin Amera "MD ko sai Bayan barin Chuchu wajen ya rufe Amera da fad'a akan Abunda take bata kyautawa " Nanfa ta tubure tace wlh kome zaice Saidai yace Amma indai akan wannan ne yanzu ta fara ganin bata bakinshine ma zaiyi rabuwa yayi da ita kwanan Chuchu biyu a gidan Wanda kamar a k'aya tayishi ta koma gida Koda ta koma ta bawa Ammy labarin abunda ya faru girgiza kai tayi ta ce "Rabu da ita duniya ce " MD ko yananan yana lissafin kwanakin da ya ragewa su Chuchu su koma makaranta. Kowa idan zai koma makaranta bak'inciki yake na rabuwa da gida banda Zarah dake d'okin komawarta sch Dan wannan Karin ba k'aramar takura Tasha ba wajen Mama Rabi ba Bugu amma akwai zagi da bakaken maganganu ga aiyuka dukda wannan ba ya damunta saboda ta saba yaune komawarsu sch Wanda tunda safe ta shirya Bayan Baba ya sallameta da abunda ke aljihunshi dukda dak'yal ta Amsa nan yayi mata nasihohi kamar yanda ya saba yi mata Bayan fitarshi ba jimawa itama ta shirya sosai taji dad'in Rashin ganin Mama Rabi a gidan Dan yanzu ta tarki yawo gidan su Asmy suka wuce Inda daga Chan suka wuce Tasha suka hau motar Zaria minti hamsin me kyau ya kaisu har hostel Bayan sun huta wayarta Zarah ta janyo tare da dannawa Chuchu kira ta ce "Ya dai daughter munfa shigo bamu ganki ba " Daga bangaren Chuchu ta ce "Haba daman nafison saikunzo nazo nima gani nan tahowa gobe daman nagama parking d'in komai na " Okay to muna Kallon Hanya ki gaishe da Ammy"zataji Zan fad'a mata insha Allah "washegari Chuchu ta shirya ta taho makaranta Wanda driver ne ya Kaita MD Bayan ya shigo gidansu ganin baiga