← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 92

Sashe 32

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce " Bari Naje na girka maka tunda akwai kayan hadi Dan tasan Dan nata bayacin abincin Maid House idan yana nan daman Chuchu keyi masa girki ko kuma yaci na restaurant "(nikam nace meye marabar dambe da fad'a") kamo hannun Ammy yayi ya ce "da wasa nake maki Ammy taya zan wahalar da Ammy na guda "indai kana so babana ka bari nayi maka " girgiza kai yayi tare da mik'ewa ya ce "Da wasa nake Ammy Hug d'inta yayi ya ce " Good night Dear mom"Shafa kanshi tayi ta ce "Have a nice dream my Beloved son god bless you " koda ya kwanta Kasa baccci yayi tunanin mood dinsa da yarinyar na Daren jiya ya shiga dawo masa lokaci guda yaji Yana neman burkutawa kansa lissafi Tsaki yaja a ranshi ya ce "Stupid kawai marar Kunya mata matsala ne Wlh " Kafin kuma ya ce "Amma yarinyar ta na Da dad'i over" Lumshe ido yayi ya ce "Zan kwashi gara kafin 9 months din stupid kawai villager girl " (Nikam nace kaidai ka sani MD). Washegari Azahar a Gombe tayi masa Daga shi sai Jaber kamar yanda suke zuwa haka suka isa a sirrance. Kallon dattijon dake kwance kamar ko yaushe MD yayi shiko yana ganinshi ya Fad'ad'a fara'arsa dukda baya iya komai Amma daga ganin fuskarsa zakasan yana cikin farinciki "Shima murmushin MD ya mayar masa tare da kamo hannunshi ya murza a hankali ya ce " Sannu ko Baba"Lumshe masa ido yayi tare da bud'ewa "Kamashi MD yayi ya tasar dashi Fruit ya dinga bashi a baki yana ci yana yi masa murmushi Har saida ya koshi ya daina Amsa tukwana ya d'auko Handchiep ya Goge masa baki kafin ya kwantar dashi Kallon dattijon dake gefenshi yayi ya ce " jiki ya fara sauki sosai naga"Da fara a tsohon ya ce "Alhmdllh yanzu kam Kamar ma ya dawo hayyacinshi Dan wani lokacin saika samesa yana kuka wani lokacin kuma murmushi sannan yanzu har motsa hannunsa yanayi ya ma fara amfani da hannun" jinjina kai MD yayi ya ce "Insha Allahu zai dawo daidai da yardar ubangiji Ai Babu Abunda yafi k'arfin Allah Sannan Shima na Asibitin a dinga basa magungunan Baba Karka gajiya Kaima Ladarka na wajen Allah " Tsohon ya ce "Insha Allahu kaima dai Allah yayi maka albarka ya kareka daga sharrin makiya da mahassada " Ameen MD ya fad'a Koda ya Mike Zai tashi sai na kwancen ya kamo hannunta Juyawa MD yayi ya Kallesa saiyaga hawaye nabin kumcinsa cikin Sauri ya koma ya zauna tare da Rik'e hannun tsohon cikin muryar girmamawa ya ce "Kayi hakuri Baba Zandawo insha Allahu bada jimawa ba zaka samu sauk'i da yardar ubangiji"Ta ido dattijon ya nuna masa da ya gamsu kafin ya saki hannun nasa.....a hanyarsu ta zuwa Airport Jaber ne ya ce " bawan Allan nan yana bani tausayi wlh tsawon shekaru A haka Kaiba matacce ba kaiba mai rai ba Kuma ga dukkan Alamu sihiri ne mai k'arfi akayi masa Allah dai ya basa lafiya"Ameen Kawai MD ya ce "Jaber ne ya ce " Bloody ya maganarmu ta rannan Ina takardar sakin Zarah"Ka cire hannunka a maganar kawai "Cewar MD " da mamaki jaber ya ce "ohh haka kace amma dai kasan nine jadanin Shirin ko ?lumshe ido MD yayi kafin ya bud'e ya ce " Eh nace ka cire hannunka kawai "Jinjina kai Jaber yayi ya ce " Hmmmm Na cire daga yau insha Allahu"koda suka isa kd Gidansu ya wuce Ammy ce ta Kallesa ta ce "ya naga kamar akwai alamar gajiya a tattare dakai"eh Wlh Ammy daga Gombe nake " Ammy ta ce "Ah dole ka gaji kam Ya Jikin na Baban to?dan tasan shi kadai ne ke kaishi gombe"Alhmdll Ammy Da sauki za ace yanzu kam an fara samun cigaba sosai" Cikin tausayawa Ammy ta ce "Allah sarki Bawan Allah ana ta kankarar zunubi Allah dai ya basa lafiya nima ina son Samun lokaci naje ba dama ya kamata ace munkoma mun dubasa Allah dai ya basa lafiya Gaskiya duniya ba Gaskiya wlh A kassara mutum shekara da shekaru tsohon Allah wata Allah Dan tsohon nan a k'alla zaiyi uba dani aka kassara bawan Allah a zaune Allah dai yayi mana tsari da makiya na fili Dana boye Shiyasa nake ta ce maka ku dage da addu'a babana mutanen yanzu ba Gaskiya Allah ya kare munkai ya tsaremun kai babana ya k'ara maka zuciyar imanin irin taimakon da kake Allah ya k'ara maka budin da zaka ninka fiye da na da " ameen Ammynah "MD ya fad'a... Washegari Zarah ce zaune tanayiwa Chuchu kitso Wanda dak'yal ta samu ake mata wai batason kitso kodan yawan gashin da sulbi Dan Sai a daure ita Zarah har mamaki take gashin Chuchu sak na India wa amma Kuma gata ita Bak'a ce bata da Haske sosai Bayan ta gama yi mata Wayar ta ce tayi ringing ganin ya Hafiz ne ya sanyata saurin d'auka Hira suka shigayi sosai yake zuba kalamai masu dadi dukda ba maida masa take ba Sosai Dan kunyarsa take ji kawarta ce Hibba ta shigo Bayan sun gaisa da Chuchu Da Asmy da ta gama sallar la'asr kusa da Zarah ta zauna katse wayar tayi tare da kallonta ta ce " Manya daga ina "Murmushi kawai hibba tayi ta ce " Gaku manya turoni akayi Malam Umar ya ce Kije wai "Da mamaki Zarah ta ce " Mlm Umar kuma Niko me zai had'ani dashi kofa magana bayi muke ba "Wara hannu tayi ta ce " Nima kin tambayeni kije kiji"chuchu ce tayi dariya ta ce "Ko shima yana ciki dai wai ya maganar mlm sulaiman dinnan ya kuka kare dashi" Asmy tayi dariya ta ce "Nima na manta nayi mata wannan tambayar " Hibba tayi dariya ta ce "Kila yaga ba sarki sai Allah ya hakura" Tabe baki zarah tayi ce "Ni harnama mance dashi bana yarda ma mu hadu dashi idan ya aika a kirani kuma ba zuwa nake ba " Hibba ta ce"Ki daibi a hankali wlh karya kada ke"chuchu taja tsaki ta ce "kufa duk laifinkune ma da kuke tsorata da irinsu wlh dan sunga ba a kaisu sama shiyasa suke wannan iskancin ya kada ita d'in ya gani wlh sainayi hanyar da za a kaisa sama sai yayi ta aikinsa" duk dariya sukayiwa chuchu wai zaiyi ta aikinsa Hijab d'inta ta sanya har kasa tare suka isa har office d'in Inda hibba ta tsaya daga waje shiga Zarah tayi Bayan ta gaishesa ya amsa tare da nuna mata kujera da ta zauna a sanyaye ta zauna wayarsa dake kan table tayi ringing cikin Sauri ya d'auka Ita dai bataji me sukace ba saiji tayi ya mik'o mata wayar akan ta amsa"Nuna kanta tayi ta ce "Ni,?Eh amshi zakuyi magana " a sanyaye ta amshi wayar tare da karawa a kunnanta "ki sameni a Gidan da na kawoki Rannan karki wuce 30 minutes "ta tsinkayi muryarsa daga cikin wayar" satar kallon Mlm tayi taga hankalinsa baya ma wajen "Murguda masa baki tayi tare da cewa " Idan fa naki ?ki ganni a makarantar yanzu na daukeki ta karfi"tsaki taja tare da cewa "to bazanzo ba aini ba y'ar iska bace " Sosai yayi mamakin jin furucin nata ya ce "Okay nine d'an iskan kenan?turo baki gaba tayi ta ce "oho dai Sai Anjima nidai ba Inda zanje " okay kijirayi zuwana Nan da 1 hour bakizo ba Zakiyi mamakina villager girl kawai"Yana gama Fad'ar Hakan ya katse kiran....... 07026166536 domin magana da marubuciyar kai tsaye *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ ..........*41 & 42* bin wayar tayi da Kallo tana mamakin k'arfin hali irin na mutumin nan ya dinga Abu gadara_gadara kamar wani ubanta Tsaki taja Ta ce "Ko ina ma yasan Mlm Umar" Tsoro ne ya kamata tunowa da ya ce nan da 1hour zaizo karfa da gaske yake karyazo yayi mata abunda zaija mata adinga mata Cece kuce Dan ta lura ba kunya ta ishi mutumin ba kar mutane suna ganinta da mutunci suzo sun fara zarginta Tsaki taja tanajin haushin Abunda yace mata wai villager A sanyaye ta mik'e tabar office d'in Bayan ta mayar wa da Mlm Umar wayarsa kai tsaye hostel ta nufa a sanyaye daka kalleta kasan tana cikin damuwa shiru tayi tare da Yin tagumi Asmy ce ta ce "Lafiya naga tunda kika dawo kinyi shiru" Tana turo baki ta ce "da sauki dai" Satar kallon Chuchu tayi taga hankalinta nakan waya chat take tana Dariya ya sanya Ta fad'awa Asmy Yanda sukayi a waya k'asa da murya Asmy tayi ta ce "Ki shirya ki tafi kawai karki yarda yana zuwa school d'innan Dan last time ma da aka saukeki wlh wasu harsun fara cece kuce wai daman ustazan nan Kunfi iskanci a boye har fad'a saida mukayi da wata Kiyi Sauri" Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce "To shikenan Chuchu fa yazamuyi da ita" Ki barni nasan Abunda zance mata "Cewar Asmy cikin k'ank'anin lokaci Zarah ta shirya cikin atamfarta Riga da sicket Ta d'ora hijab d'inta doguwa mai hannu Pink Fuskarnan tata fresh ba komai sai kwalli Bayan ta dauki hand back d'inta da wayarta zata fita Chuchu ce ta ce " ina zuwa momcy"Asmy tayi. Charaf ta ce "Cikin gari zataje gidan kanwar mamanmu Mijinta yayi tafiya zataje ta tayata kwana" okay Adawo lfy"cewar Chuchu"Koda Zarah ta isa cikin gidan tayi minti biyar tana tsaye ta kasa knoking Dak'yal dai ta tattara jarumta tayi knoking sau d'aya Saida a ka dau kusan Minti Bakwai kafin taji karar bud'ewa duk Haushi ya isheta tana
Chapter 32 · 0% Book details