Sashe 41
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a bakin mota ya tarar da Zarah tare da Asmy suna ta hira suna Dariya Gaisheshi Asmy tayi ya amsa ba yabo ba fallasa horn yayiwa Zarah Bayan ya shiga Sakin hannunta Asmy tayi ta ce " Sai gobe kawai karki tsaidashi "Harararta Zarah tayi tana turo baki ta shiga gaba " Har suka isa ba mai cewa uffan suna isa ta iske dogayen riguna a palourn jibge kuma duk masu manyan kudi sai hijabai "ki kwashe ki kai bedroom d'inki " yana gama fad'ar haka ya wuce ciki..washegari Bayan tayi shirin tafiyarta makaranta 5k ya mik'a mata har zataki amsa tunowa da maganar da yayi mata rannan ya sanyata amsa tare da cewa "Thnks" Karfe nawa zaku gama lecture din?Karfe biyu?Okay "tana fita ta samu driver na jiranta cikin girmamawa ya ce " Hajiya barka da fitowa nine sabon driver d'in naki da zai dinga kaiki"Da mamaki take binshi da Kallo tana tunanin me.MD yake nufi koda suka gama lecture tana fitowa taga driver d'in tana Jan tsaki ta ce "Gaskiya nidai nema ake a takura rayuwata wlh" Cemashi tayi bari ta fito tana zuwa hostel ta samu Chuchu da Asmy cikin Sauri ta Ruga ta rungumesu ta ce "Daugher yaushe kikazo" dazu na shigo wlh duk nayi kewarki momcy sosai suka dinga hira Zarah harta ma manta da driver sai wajen 3 ta tuno Firgit ta mik'e ta ce "Subhanallahi na manta nabar driver waje sai Allah ya kaimu tayi saurin fad'a tare da barin dakin tana zuwa ta samu driver d'in bai tafi ba yana can Inda ta barsa tana shiga ya ja suka nufi gidan Bayan fitar Zarah d'akin da mamaki Chuchu ta ce " ina zata wai naga ta fita "Karyar da zatayiwa Chuchu Asmy ta nema ta rasa Chan kuma kome ta tuno tayi firgit ta ce......... *07026166536* _Masu fitarmun da Littafi bazanyi Allah ya isa ba saboda littafi amma ku sani hakkina kuke fitarwa batare da izini na ba duk Wanda ya saya kudin karantawa kadai ya biya ba na mallaka ba kusani dai sarai akwai hakki kowa yana da damar karantawa indai ya biya 300 kachal cikin nutsuwa da kwanciyar yafi ka tsintseshi a gantali ka karanta a gantalewa cikin Rashin nutsuwa _ *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* *_Miss Hajo ce_* .........*51 & 52* "Kinsan na Fad'a maki akwai kanwar mamanmu anan to shine takoma gidanta da zama ta na d'an rage Mata ayyuka saboda mijinta baya nan" ayya kice yanzu munzama mu biyu Gaskiya zamuyi missing nata sosai wlh"cewar chuchu"wlhko ai bama kadanba danma ai ba koda yaushe take Chan ba zata dinga dawowa nan" dukda haka dai Chuchu ta fad'a...washegari Bayan dawowarta daga lectures around 5pm tana kwance Kan sopa ta na Karatun exams din dake tunkaro musu shikuma yana operating a system "Kallonta yayi yaga ta maida hankalinta ga karatun da take Bayan ya gama aikin da yake a laptop ya linke ya Aje tunani ne yake karfa yayi gudun gara ya fad'a gidan zago taya za ayi Ace wata biyar yanzu da Auren amma bata samu ciki ba gashi har saura wata hudu yarjejeniyar su ta kare a ranshi ya ce " kodai matsalar daga gareni take?Amma ai Duk asibitocin da naje sun gwadani lafiya ta qalau to me hakan yake nufi "wani tunani yazo masa ya ce " Karfa aikin banza nake Yarinyar nan da abunda takesha tunda wayayyace zaiyi wahala ta yarda ta dauki ciki "wata dabara ce ga fado masa yace bari nayi mata low nagani idan hakane " Mamy"ya kira sunanta a hankali "Aje littafin dake hannunta tayi ta ce " Na'am"Karatun nan tund'azu kike yaci ki bari inba so kike ki hardace littafin ba "murmushi tayi ta ce " Ai da zan samu dama ma na hardace book din da zanji dadi sosai "Uhm kaji dictionary" y'ar Dariya tayi Kad'an ta ce "Uhm"Na tambayeki zaki bani amsa"? Gyada mashi kai tayi ta ce " idan har na sani zan baka ,insha Allah"kina son yara kuwa?Murmushi tayi ta ce "Ina so mana sosaima kuwa " kice mijinki yaji dadi zaki Haifa mai yara da yawa"Gabanta ne ya bada daram tunowa da Hafiz "murmushin da ya lotsar da dimple dinta ta ce " insha Allah"tana rufe fuska "murmushi yayi ya ce " Kenan ni bazaki Haifa mun ba "Wara idanu tayi saikuma ta turo baki ta ce " Matarka kaima ta Haifa maka mana nima mijina zan haifawa "yana jinjina Yarinta irin ta Zarah ya ce " Ayya ni ai matata bata haihuwa shekararmu Tara da Aure amma ko b'atan wata bata tabayi ba "cikin muryar tausayawa ta marairaice ta ce " Ayya wlh harkun bani tausayi Allah ya baku mai amfani Amma kuma kai kana son yara ne"ina sonsu sosaima kuwa tun kafin nayi Aure nake da burin Son yara ina sonsu sosai Wanda har nake tunanin sonsune da yayimun yawa yasa Allah ya jarabceni har yanzu bai bani ba"girgiza masa kai tayi ta ce "kadaina wannan tunanin kasa a ranka lokacin samun sune kawai baiyi Aure,Da Haihuwa Abu ne da Allah ya sanya musu lokaci dole sai lokacin Su yayi tukwana sukan zowa bawa ina maka fatan Allah ya baka masu amfani" Murmushin da baiyi niyya ba ya sakar mata ya ce "Hakane To Allah ya kawo lokacin" a ranshi ya ce "Ga dukkan alamu ba abunda take sha amma Indai hakane Tabbas ina cikin jarabawa ya zanyi da Hajiya kaka?Tabbas dole ne duk yanda za ayi Amera ta koma America kafin na samu mafita " Tunanin me kake ?ya tsinkayi Muryar Zarah "murmushi ya sakar mata ya ce " bakomai Please zaki iya girkamun tuwo irin na rannan"Shiru tayi kamar bazatayi magana ba saikuma ta ce "akwai kayan Had'in ne?Eh akwai komai a ciki" Okay Badamuwa ta fad'a tana Mikewa da Kallo ya bita harta shiga kitchen din kafin ya sauke ajiyar zuciya a ranshi yana mamakin yanda yake sauya wasu dabi'un game da halayyarshi idan yana tare da ita har yake tsayawa yayi doguwar Hira da ita ko Dariya da murmushi Wanda ko a gida bakowani lokaci ba yake yinsu a ranshi ya ce "Saboda Yarinyar simple ce bata da hayaniya?wata zuciyar kuma ta ce " saboda ka chutar da ita a farkon mu'amularka da ita Wanda idan bangyara mu'amula ta da ita ba ko Bayan rabuwarmu zata rikeni mugu a cikin ranta "da wannan tunanin har aka kira Sallar magriba sai Bayan isha'i Zarah ta gama Tuwon da miya ta juye a warmer a dining ta jera Kafin taje tayi Sallar isha'i Bayan tayi wanka ta sanya doguwar Hijab d'inta ta fito Zaune ta tarar dashi a palour yana cin tuwon cikin nutsuwa sosai MD yaji dadin Tuwon fiye da na rannan sai lumshe ido yake da hannu yayi mata nuni da good kafin ya furta " Thnks"a hankali"murmushi kawai Zarah tayi batace komai ba "Bazakici ba ?Sai anjima ta fad'a " a hankali"Zoki zauna muci tare"girgiza masa kai tayi ta ce "A a a " Sanin kanki ne banason musu ko?a sanyaye ta k'arasa ta samu guri gefen k'asar da yake ta zauna "ko kefa mumu girl" Wata irin harara ta banka masa kafin ta maida kanta kasa tana turo baki"murmushi kawai yayi "Cike da jin kunya Zarah takecin abinci bata wani ci da yawa ba ta ce ta k'oshi ba yanda baiyi da ita ba akan tadawo amma takiya ganin zata sanya masa kuka ya sanyasa cewa" Shikenan rigimammiya"tana turo baki ta koma Daki wayarta ta janyo ganin missed call ya Hafiz ya sanya tabi kiran saida ta katse kafin ya kira Hira suka fara Sosai cikin Sauk'i da k'aunar juna sosai suke waya Zarah na kwance saman bed tayi rubda ciki batasan har lokacin da MD ya shigo dakinba ba saida ta tsinkayi muryarsa da cewa "bani wayar " Cikin kid'imewa Zarah ta kashe wayar tana addu'ar Kar Hafiz yaji muryar MD "Dan Alla meye haka wai dan Allah idanfa yaji muryarka me kake tunanin zai faru" tsaki yaja ya ce "so what Dan yaji muryata baki da Gaskiya kenan" Shine fa Wanda zan aura"ta fad'a kamar mai shirin yin kuka"Ni kuma Wanda kike Aura a yanzu ba ?saiki bambance ni dashi wayafi matsayi "Tana turo baki ta ce " Kai ai mijin wucin gadi ne shikuma shine mijina na har abada "kwabe mata bakin yayi ya ce " Ki dinga sanin maganar da zakiyimun hope kin fahimta ko nayi maki kama da sa an wasanki sannan ya fusge wayarta dake ringing yabar dakin"takaici ya ishi Zarah rasa me zatayi tayi kawai sai ta fashe da kuka ta ce "Allah ya isa mugu azzalumi saikace shine ya sayamun wayar da zai amshe wlh nidai an cuceni da aka lakabamun wannan alkakaidin ya zamemun k'arfen kafa ke Asmy kina Chan kina rayuwarki hankali kwance ni kin barni da kunci tana wannan sabbatunta a haka har bacci ya kwasheta MD ko Shima kwanciya yayi yana buk'atar Ta amma wannan Karin bazai jeba Dan karyaja raini a wajen yarinya k'arama harta gane larurarshi ta kawo mashi raini Irin yanda Amera tayi masa Dukda Amera intayi masa babbace ita ko wannan karamar yarinyar da auren wuri ya haifi kamarta bazai yarda ta samu damar raina sa ba...washegari koda ya tashi a daddaure ya tashi ya koma MD dinshi na ainahi Zarah na ganin haka ta kasa masa Rashin kunyar da taso masa akan wayarta saboda muddin tana ganinshi a haka tofa bazata iya gaya masa maganaba ta rasa ya akayi mutumin yake mata kwarjini duk maganar da taso fad'a masa wani lokacin saita kasa a haka ta tafi lecture d'inta batare da ko magana ta