← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 92

Sashe 69

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga wancen zuwa wannan Babban asibitin da daga gani za a chashi kudi masu yawa Wanda yayi musu jagora ne yace "Ya isa Haka su tafi kar wani ya gansu a ja masa ta aikinsa "hawaye d'auke da fuskar zahra ta ce " nagode "kudin da suka rage a aljihunsa MD ya basa masu yawa kafin Su koma mota sosai jikinsa ya mutu gaba d'aya kamar Wanda aka zarewa lakka Har suka isa motarsa nanfa zahra ta tubure tace batasan wannan ba ba Inda zata koma hankalin MD nanfa ya k'ara tashi yahau Lallashinta amma ta tubure ganin tana shirin guduwane baisan lokacin da karfi yazo masa ba ya fardota tare da sanyata mota yayi Sauri ya zagaya yayiwa motar lock kai tsaya ma bai tsaya saurarar komai ba ya juya Abuja sosai zahra ta dinga fasa masa kuka kamar ranta zai fita har suka isa Abuja tana kuka tana tsine masa Daren ranar sunsha dabu da ita Dan burkucewa tayi ya ce Wlh saiya maida ita gida kota jaza masa bala i dak'yal ya samu baccin gajiya ya kwasheta ....sosai Baba yake samun sauki a asibitin Dr Najmat kulawa.sosai Jabir yake basa bisa ga umarnin MD Bayan sati biyu jikin Baba ya warware Ranar da aka sallamesa y'an uwansa sukayi shawarar awuce dashi Batsari ya karajin sauki saboda sunsan halin Mama Rabi sarai zata Kara tayar masa da hankali ne akan zahra ta gudu Bayan sun boye masa sunce tana gida zuciyar Baba chunkushe da tunanin zahrarsa .....Cikin satin nan ba k'aramun dabi zahra da MD suke sha ba Sosai zahra ta birkitawa MD tunani ne yau inya tallabota nan gobe ya tallabota Chan sosai yake hakuri da jure irin abunda take masa shi kanshi baisan yana da hakuri har haka ba abinci ko Sai yayi kamar zai mata d'ure tukwana yake samu taci da bala'i da masifar saiya maida ita gida sannan ancire mata cikin nan har sukayi wata guda a gidan Wanda MD ko kd baisamu yaje ko gaishe da Ammy yayi ba Saidai ya kirata a waya ya ce uzuri ne yayi masa yawa .yauma yana zaune a palour around 9pm yana waya da Ammy tana masa complain Chuchu ta kasa gane kanta indai bashi ba yazo babu Wanda zata fad'awa damuwarsa"numfashi yaja Dan yasan damuwar Chuchu bata wuce ta abunda ya samu kawarta ba ya ce "Badamuwa Ammy Zankirata waya Naji meke damunta insha Allah zansamu nazo " Daga bangaren Ammy ta ce "Hmmm haka dai kake cewa Na rasa wani irin aiki ne wannan da zakayi wata guda kana k'asar bakaga ammynka ba " Shafa lallausan sumar gashin kansa yayi yana murmushi ya ce "Ba haka bane Ammy insha Allahu.muryarsa ce ta sartse ganin fitowar zahra daga ita sai rigar bacci cikin kayayyakin da ya sayo mata Wanda Hakanan take sanyawa d'an bata da wasu Cikinta ya fito yayi das a jikinta Cikin b'acin rai da hawaye ta ce " Waikai d'aukar me kayimun marar galihu ko.kuma me mi.kake nufi da ajeni a gidan nan da kayi kamar wace y'ar iska ....saurin katse.kiran md yayi gabansa na fad'uwa tsoransa Allah kada Ammy taji abunda zahra ta fad'a kallonta yayi fuska ba wasa ya ce "Zaman Aure kike?Tana binsa da wani banzan kallo ta ce " lallai kai baka da kunya ma.wlh har kana da bakin da zaka iya furta wannan Kalmar Wacece zatayi zaman Aure da mugu azzalumi Wanda baisan damuwar wani ba damuwar kansa kawai ya sani mayaudar....bata k'arasa fad'a abunda takeson Fad'a ba MD yayi sama da ita bai direta ko ina ba sai kan Bed yana shirin danneta ta k'walla Kara ta ce "Wlh tallahi ka sake kayimun wani Abu zanyi maka abunda ba a tab'a yi maka shi a rayuwa ba " banza MD yayi mata ya rungumota jikinta sosai tare da Fara Aika mata K'ananan sakwanni ganin zai birkitawa kansa lissafi gashi yayi alk'awarin bazan k'ara wani Abu da ita ba saboda cikin dake jikinta daidai kunnanta ya rada mata a hankali "ki kwanta kiyi bacci yanzu indai bakyaso wani Abu ya faru" Zahra najin haka ta Had'iye kukanta Batasan lokacin da wahalallen bacci yayi awon gaba da ita ba saida yaji saukar numfashinta tukwana ya sauke ajiyar zuciya ya zame a hankali saida ya sha ruwan liptop da lemon tsami tukwana ya samu bacci ya daukesa washegari zahra ta tashi bayan asuba dan ta makara salla shiko md koda yayi salla ya fita daga dakin ya koma nasa Bayan tayi alwala ta gabatar da salla Sosai ta rokawa mahaifinta samun lafiya dukda MD ya fad'a mata ansallamesa yaji sauk'i amma bata yarda ba Tana gama salla yunwa ta ciyota tsaki taja Dan yanzu wata irin jin yunwa takeji da taci kamar bataci ba hakan yasa yanzu ta daina masa zuciya da abinci Dan ita ke illatuwa kofa ta nufa tana turawa taji a rufe tsaki taja Dan sosai takejin haushin kulleta din da yake ko yaushe kamar a gidan yari tsaki taja tare da komawa ta zauna tana lazumi tana addu'ar Allah zubar da cikin nan dake jikinta ba ayi 30 minutes ba MD ya shigo d'auke da plate din wainar kwai kusan guda biyar sai cup din tea da bread a hannunsa kai tsaye gabanta ya nufa dasu a hankali ya ce "Good morning mummyn baby" Tsaki taja tare da kauda kai Dan murmushi yayi Dan ya saba da abun nata ya Aje kafinma ya ce ta ci tuni ta fara ci Dan yunwar data ciwo ta saida abun yaso basa Dariya ganin yanda ta murtuke takeci kamar an mata dole cewa yayi "ki gama ki shirya muje Asibiti ayi miki scanning sannan ya kamata mu fara zuwa awo" wani banzan kallo tayi masa cike da takaici ta ce "Allah kiyaye Allah tsari gatari da saran shuka a tunaninka ni zanje Asibiti saboda lafiyar cikin nan Dana tsana Aiko Inma kana wannan tunanin tun wuri ka bari Dan wlh ba haihuwar....saurin kwabe mata baki yayi cikin bacin rai ya ce" Da Allah yiwa mutane shiru "Dogon tsaki Taja Wanda MD Inda sabo harya saba da tsakin nata wanda duk duniya bayan ammy babu wanda ya isa ya masa su wanje lafiya ta ce" Satoni dinma da kayi Allah saiya sakamun wlh Dan laifinka d'aya da y'an kidnapping"tsaki MD yaja tare da mik'ewa ya ce "Idan kina buk'atar wani Abu ina palour" Da harara ta bisa har yaban palourn wajen Azahar zahra ta karajin wata yunwar koda ta fita palour zaune ta samesa yana aiki a laptop Wuri ta samu ta zauna tana shashan magani so take tace masa yunwa takeji ta kasa ganin baiyi mata magana ba ya sanyata cewa "yunwa nakeji fa Malam" Kamar bazai tanka mata ba ya ce "Me kike son ci a kawo miki" Bana son Cin abincin restaurant Dan ban yarda da tsabtarsu ba bazan sake ci ba"Yana mata kallon mamaki ya ce "To shiga ki girka?Harara ta banka masa ta ce " Wlh kaji na rantse ko hanyar kitchen bazanyi ba"Aje laptop d'in MD yayi yana kallonta ya ce "To wa kike tunanin zai girka maki" Kai da kayi cikin da ke sakani jin yunwar kai zaka dinga girkamun harya zube......... *Ohni wai yaushe zahra ta zama y'ar Rashin kunya haka* *Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR,5 TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ASA.. _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI.. _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA _Miss Hajo_ Guda aya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda hu u N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KU INKU TA WANNAN HANYAR Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 ........... .... AN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KU INKU Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* *_Miss Hajo ce_* ...........*79 & 80* Nuna kanshi da hannu MD yayi ce "Kina nufin ni zan shiga kitchen na girka maki abunda zakici" Tana binsa da harara ta ce "To kaid'in waye" Sosai Abun nata ya fara isar MD tsaki yaja yana maida hankalinshi ga aikin da yake ya ce "Baki da aikinyi shiyasa kike maganar nan ga abinci Chan a dining danayi order kala Ukku ne ciki ki zab'i Wanda zaiyi maki," Harara zahra ta banka masa tana kauda kai dajan tsaki ta ce "Bazanci ba Kuma wlh ka maidani gidan iyaye na na fad'a maka tun kafin nayi abunda baka tunani" Banza MD yayi mata kamar badashi take ba Sosai hakan ya bakanta mata dukda yunwar da take ji amma ta rantse bazataci na restaurant ba ciki ta koma Tare da hayewa Gado ta fashe da kuka MD ganin kusan har awa biyu da komawarta daki a tunaninshi ta fito taci abincin amma yaji shiru tunani yayi yarinyarfa yanzu ta tarki kafiya da zuciyar bala'i karfa wani abun ya samu cikinsa Dan yasan illace mace mai ciki na zama da yunwa Mikewa yayi Koda ya shiga daki kwance ya sameta tana hawaye yana ganinta yasan taci kuka gefenta ya zauna cikin sigar lallashi ya ce "Please Mamy ki daure kici abincin kar wani Abu ya sameki kinsan ban iya girki ba Sarai fa neman rigima ne" banza zahra tayi masa "Mamy ya k'ara kiranta Nanma shiru" Omg " ya fad'a a cikin ransa Kafin ya sake dauriyar cewa "Ko na kawo maki kici anan" Bazanci ba na k'oshi ta basa amsa kai tsaye"shiru MD yayi yana mamakin taurin kai irin nata Wanda da kwata kwata baiyi tunanin tana dashi ba shi damuwarshi bai wuce abunda ke cikinta ba da yakejin sonsa na daban yakejin zai iyayin komai indai zata Haifa masa cikin nan bashi da wani girman kai dole ya Aje ya ce "To ki fad'amun please me kike son ci " Na fasa bazanci komai ba "Cikin lallashi ya ce " na yarda zan girka maki din indai zakici "Sosai zahra tayi mamakin jin wai zai girka " shiru tayi masa "Kifadamun me kike so please" Saida taja mintuna kafin ta ce "jolloup d'in taliya da wake "
Chapter 69 · 0% Book details