← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 92

Sashe 80

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa Ina tibka kina warwarewa kin mayarmun da aiki baya zahra me.yasa kika saki jiki dashi haka bakison yasan darajarki da martabarki yagane matsayi da muhimmancinki zahra "Cikin kuka zahra ta ce " Dan Allah Ammy kiyi hakuri nima banason yana zuwa kuma ki tambayi Chuchu kiji "tab'a hannu Ammy tayi ta ce " kenanma wannan bashine karo na farko ba kafin ta dallawa Chuchu harara ta ce "Ke kuma Munafuka watau duk hudubar da nayi maki akan karki sake ki barsa yana zuwa Wajenta bakiji ba to ai shikenan gaba d'aya yau zata koma part Dina sai Inga in d'akin nau zai dinga binta " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ammy ni karkiga Laifina Miji da matarsa kuma saina hanasa shigowa" Dundu a baya Ammy takai mata ta ce "ja'ira" Dariya Chuchu tayi tana kaucewa ..tundaga ranar Ammy ta mayar da zahra part d'inta ta kasa ta tsare sosai akan MD ko Yaransa Saidai taba Chuchu takai masa sosai MD ya damu da hakan hankalinshi ya k'ara tashi Dan koba komai yana da buk'atar ganin matarshi sosai Ammy ta burkuta masa lissafi gabak'i d'aya ...yana kwance a makeken Royal bed dinsa kamar koyaushe indai ya kwanta shi d'aya to ba tunanin da yake idan ba nata ba yaji wayarsa tayi ringing kamar bazai daga ba saikuma ya d'auka ganin Baba na gombe ne Cikin girmamawa MD ya gaishesa ya amsa masa ya ce "jikana ashe haihuwa akayi maka baka fadamunba Abun farinciki ya samu ashe har anyi wata guda bani da labari sai dazu Jabir Daya kirani muka gaisa yake fad'amun gsky banji dadi da baka fadamunba kasan ai nazo naga y'ay'an nawa amma dukda haka insha Allah na shirya gobe gani nan zuwa kadunar zanzo nayi maka barka naga yaran kaga harmun gaisa da Hajiya sannan nayi mata Godiya"Cikin girmamawa MD ya ce " ba haka bane Baba lokacin wani uzurine ya mantar dani fad'a maka ai Baba dama ka barsa karka wahalar da jikinka idan sukayi kwari a kawoma maka su kaga jikin naka bai gama warwarewa ba"murmushi yayi ya ce "a a jikana jiki kuma ai ya warware gobe insha Allah Zanzo naga y'ay'an tunda tafadamun haihuwar Naji ina son ganin Yaran " cike da murmushi MD.ya ce "To shikenan Baba gobe da safe driver zaizo ya tafi dakai saika biyoshi zai kawoka har gida " haka ko akayi washegari tunda safe driver yaje ya taho da Baba na gombe da Yakejin gabanshi na fad'uwa tunda suka taho suna isowa garin Kaduna Baba ya dinga bin garin da Kallo yana murmushi Har suka isa tafkeken gidan su MD Daman tun jiyan MD.ya sanar da Ammy da zuwan Baba anshirya masa komai na tarba a Babban palourn bak'i aka saukesa Bayan an cika masa gabansa da abubuwan makuleshe sosai MD ya nuna jin dadinsa na zuwan Baba Bayan Ammy ta shigo tana rik'e da Amar Hannunta da fara'a tayi welcoming din Baba cikin girmamawa tamkar mahaifinta haka ta dinga girmamasa Bayan sun gaisa Baba ya k'ara yiwa Ammy Godiya akan irin taimakon da MD yayi masa murmushi Ammy tayi ta ce "Bakomai Baba Ai anzama daya kaid'in ai tamkar uba kake a gareni shiko jika ne a gareka" fara'a cike da fuskar Baba ya ce "na jima banga mutanen kirki mutane na kwarai ba irinku ba Allah dai yasa a gama da duniya lafiya ya kareku daga sharrin makiya ya raya zuri'a Ameen Ammy ta fad'a tana mik'awa Baba Amar ta ce " Ga d'iyan naka Baba Biyun yanzu za a kawo maka ana shiryasu"Murmushi Baba yayi yana amsar yaron Ya ce "kai kai masha Allah Tubarakalla Allah ubangiji ya raya ya karesu daga sharrin makiya " shidai MD yana mamakin Baba tsoho da duk addu'ar da zaiyi ko waya suke saiya ambaci makiya da mahassada "Kallon yaron kawai Baba yake yanajin k'aunar yaron haka kawai yakeganin yaron tamkar ya rik'e jininsa Chuchu ce tare da zahra suka shigo tana sanye cikin zullubebiyar hijab har kasa ita na rik'e da Akhbar Chuchu kuma little gefen Ammy Zahra ta zauna Hakanan yau ta tashi a sanyaye kallon ta kawai MD yake tunda ta shigo sosai yaga ta k'ara yi masa kyau da kwarjini baisan lokacin d'aya saki kasaitaccen murmushi ba tare da sauke ajiyar zuciya Dagowar da Baba zaiyi daga Kallon Amar idonsa ya sauka akan zahra dake mik'awa Ammy akhbar Ammy ta ce " To Baba ga sauran an kawo maka kaga maman yaran"ta fad'a tana nuna masa Zahra"A matuk'ar firgice Baba ya Mike Hankali tashe yake kallon zahra yana rik'e da Amar ya fara nunata da yatsa kasa magana yayi sai nuna ta da yatsa da yadingayi muryarsa gaba d'aya ta sartsa ya kasa furta abunda yakeson fad'a duk Kallon mamaki suke binshi dashi har zahra da ita yauma ta fara ganinsa Rumtse idonsa yayi da karfi kafin ya bud'e yana nunata da yatsa a rarrabe ya ce "Ma my y'a ta Zahra'u da man kina raye ba ki mutu ba Zahra'u kece nake gani ko ko mafarki ne nake........ *Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ .............*87 & 88* & .............*89 & 90* Duk Kallon mamaki suke bin Baba dashi shiko nuna zahra kawai yake "MD ne yayi k'arfin halin cewa " Dan Allah Baba kayi mana bayani ina kasan wannan "hawaye na fita daga idon Baba ya ce " y'ata ce d'aya tilo dana mallaka Nina haifeta a tare Nida ita akayi mana harin da har kuka tsinceni tsawon shekaru bansan Inda take ba a tunani ma ta rasu saboda Bansan Inda sukayi da ita ba "cike da mamaki Ammy ta ce Ka nutsu dai Baba wannan ba y'arka bace Mahaifinta Yana Chan Funtua kuma wannan yarinya ce ma bata kai shekarun da kake Tunani ba kadai duba Baba" mik'awa MD yaron Baba yayi ya nufo Inda Zahra take da duk a tsorace ta ke kama hannunta dake d'auke da zoben da awarwaran da tunda Baba ya bata yake hannunta yayi Kallon zoben da awarwaran yake Yana murmushi yana hawaye ya ce "Kece Mamy ashe daman idona zai sake nunamun ke ina raye Mamy na nine Mahaifinki Mai kaunarki ko kin manta ni zahra'u ko kema sun juye miki kwalwar ne Dan karki tona musu asiri kamar yanda suka juyemun tawa Mamy ki tuna mahaifinki Malam Abdussalam sai kuma ya Rungumeta tsam a jikinsa ya ce " Alhmdllh Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nuna mun wannan yara y'ata da na shekara da shekaru ina begenta yau gashi Allah ya had'amu ta yanda banyi tsammani ba "ido ido kawai ake tsakanin Ammy da MD har Chuchu zahra ko Itama kuka ta fashe dashi Tabbas wannan din shine kakanta shine mahaifin Mamanta dukta k'are MD ne ya taso yayi kokarin raba su ya ce " ka nutsu Baba kayi mana bayani wannan ba wacce kake tunani bace "Sassauce ruk'on da Baba yayiwa zahra yayi ya juya ya kalli MD ya ce " Haba yaro ya zakamun gardama na haifi y'ata na kasa ganeta"Juyawa yayi yana kallon zahra dake Kuka ya tallabo Fuskarta kallonta ya dingayi yana son yaga banbanci tsakanin ta da mahaifiyar Ta" motsa bakinki "ya fad'a a hankali zahra ta motsa mamaki ya kama Baba ya ce "To ya haka da sanin da nayi mata tun yarinta abun nan d'aya gareta amma yanzu naga biyu " Cikin muryar kuka zahra ta ce "Ba waccen Da kake magana bace y'arta ce " ta fad'a tana hawaye"duk mamaki yagama. Cikasu Ammy ce ta ce "Kamarya y'arta ce kunsanyani cikin duhu fa Dan Allah ku warware mana " Zaunawa Baba yayi jibis yana mamakin jin Abunda ya fito daga bakinta MD ne yaja numfashi ya ce "da Alamun akwai wani Abu a kasa please ku nutsu ku warware mana muna cikin duhu " cikin muryar kuka zahra ta ce "Babana ya bani labarin mahaifiyata yana aikin noma.ya tsinceta a lokacin Bata cikin hayyacinta har aka samu akayi mata magani Dan da ko magana batayi sai daga baya da aka dage da rokon Allah kasancewar gidansu babana duk malamai ne koda ta farka bata iya tuna komai ba sai sunanta ta ce Musu sunanta " Zahra"a haka har Allah ya sasinta kansu da babana sukayi Aure Wanda suka zauna a funtua wajen sana'arsa yace bata tab'a tuna wani nata ba ko ita kanta wacece Sai lokacin da ta haife ni Wanda a nan ta ciro zoben wannan da awarwaro dake hannu na ta basa ta ce idan na girma ta bani zasu taimaka mani wajen gano danginta daga nan bata Kara ce dasu Komai ba game da asalinta Har Allah yayi mata cikawa"Ta k'arasa fad'a cikin kuka "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ashe karshen saduwata da Zahra'u kenan a rayuwa ,ashe bazan sake ganin y'ata ba d'aya Dana mallaka Allahu akhbar Su mudan basu samu damar kasheta ba kenan Allah mai iko zahra Har saida ta haihu ashe Allah sarki zahra'u Allah ya jikanki yayi miki rahama yasa kina cikin rahama hakika mamy baki mutu da hakkin iyaye ba Kinyimun biyayyar da bakowani d'a zaiyiwa mahaifansa haka ba allah ya jikanki Ashe bazamu kara saduwa ba sai a darussalam Zahra'u ke kika rigani tafiya ashe ba rabon mu sake ganawa yana hawaye ya kamo hannun zahra ya ce " Tabbas ni nan nine kakanki Nina Haifi mahaifiyarki Wannan awarwaron da zoben Tabbas nata ne ko babu su kamanninki da mahaifiyarki kadai sun isa duk wani ahalinmu ya ganki ya shaidaki Allah ya taimaka Mudan bai ganki ba na tabbata da ya ganki tofa da ya zama dole ya kasheki "Mudan " Ammy ta
Chapter 80 · 0% Book details