← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 92

Sashe 82

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakuri ka yafemun.."Saikuma ta Kara fashewa da wani sabon kukan sosai baba ya nuna bacin ransa matuka.inda su ammy dasu baba har Hajiya Kaka hakuri kawai suke bashi kowa yayi mamakin irin yanda baba ya nuna bacin ranshi kasancewarsa mutum.mai hakuri dakyal da jibin goshi aka samu aka shawo kan baba Amma Kuma saiya gindaya sharadi akan Zahra bazata koma ba zata zauna a wajenshi har lokacin da zata yaye yaran ta mayar musu da Su "Nanfa hankali ya Kara tashi musamman na ammy da Chuchu "Hakuri ammy ta dinga bashi ta ce "Dan Allah malam kayi hakuri munsan mu masu laifi ne a gareka Amma ka sassauta a dauki abunnan matsayin kaddara Dan Allah malam kuyi hakuri a sasinta wlh yaron yayi matukar nadama kuma.yanzu haka Yana son Zahra Yana son idan kun amince ta koma a matsayin matarsa tahar abada Dan Allah malam kuyi hakuri kodan arzikin yaran Nan har ukku dake tsakaninsu"Ammy ta fada hankali tashe "Nanfa baba yace baisan wanna zancen ba Indai Zai yafawa Zahra abunda tayi mashi to zata zauna ne a wajenshi sannan ya Aiko mata takardarta tunda ba aure ne akayi na mutunci ba idan ba haka ba ta tashi ta bisu ya bar musu ita har abada"Sosai hankalinsu ya Kara tashi Banda Zahra ta taji sassauci gwara ta zauna a Nan din kawai "Baba tsoho ne ya saka Baki yacewa "Ammy 'kiyi hakuri Hajiya a barmata sudin Yana cikin fushi ne a Bari su huce kawai"Badan Ammy taso ba dole ta amince musu chuchu ko hada kukan Dan batason tayi kewar Zahra daidai da second yanda takejin zey a ranta haka takejin Zahra tamkar ciki daya suka fito Nan Hajiya Kaka ta gabatar musu da Baba matsayin kakan Zahra Sosai kowa yayi al'ajabi dajin wanna al'amarin baba ko yayi farinciki matuka na ganin mahaifin tsohuwar matar tasa Kuma kakan y'arsa Sosai yaji dadin bayyanuwar ahalin na Zahra dukda sunyi al'ajabi dajin wannan labarin na baba Mai rikitarwa Bayan sunci abinci an karramasu Wajen la'asr suka fito domin tafiya an cika musu ledoji da kindirmo Sosai Ammy da chuchu sukayi sanyi na barin Zahra mama habi da matar bappa suka rike triple chuchu ko ta garkame little Sosai sai kuka take ganin haka ya Sanya Zahra kasa da kanta Tana hawaye sai yanzu takejin kewar su da zatayo ga Kuma baba tsoho da ko sabawa basuyiba Shima tare zasu koma har mota suka rakosu Wanda chuchu dakyal ta Mika little ta ruga da gudu mota Tana kuka Ammy ko dauriya kawai tayi Tana rike da hannun Zahra ta ce "To takwara mun wuce saimun dawo ganinku"Zahra batasan lokacin da ta fashe da kuka jikin Ammy ba duk kallonta suke Sosai ta dinga kuka Ammy da itama zuciyarta ta kusa karyewa dakyal ta lallasheta ta shige mota da gudu Zahra ta koma ciki Tana kuka girgiza Kai kawai baba tsoho yayi Bayan sun Kara bankwana suka wuce cike da kewa da jimamin barin Zahra chuchu ko har suka Isa gida Tana kuka Dan ba Zahra kadai zatayi kuka ba hada triple da tayi muguwar shakuwa dasu kwana tare tashi tare kullum suna hannunta Ammy ma hakan ta kasance baba tsoho ko Shi kadai yake sake sake a ransa bazaiso abunda mahaifin Zahra ya fada ya faru ba watau na rabuwar Zahra da md yasan muddin Zahra ta rasa yaron Nan to fa tayi babban Rashin miji na gari Dan Shi kanshi yasan yaron mutumin kirki ne tashin hankalin da md ya shiga Najin labarin baro Zahra da da yaran baya musaltuwa Sosai ya burkucewa Ammy kamar Zai musu hauka su kansu mamakinshi suka dingayi yanda yake magana kasan Yana cikin tashin hankali ya ce "Ammy me yasa zaku baromun mata meyasa Ammy na fada maki ina son matata meyasa Zaki maida ita Gashinan kin lalata komai Ammy Ana neman rabani da matata wallahi bazan saketa ba kome zakuyi kuyi haba Ammy saikace Ba d'anki ba kinsan Sarai ina cikin tashin hankali shine saida kikayi yanda kikayi Kika rabani da mamy na Baki hakuri ba iyaka Ammy nayi regrade duk abunda nayi Ammy Amma kikaki hakura saida Kika rabani da matata why Ammy me nayi maki"Ya fada kamar Zai fashe da kuka"Ba Ammy ba hattababa tsoho saida ya tausaya Masa "Cikin kwantar da murya Ammy ta ce "Babu Wanda yafini sonka da Zahra babana nafi kowa kaunarka da Zahra saboda bazanso rabuwarka da itaba duk abunda nayi make nayine saboda tayi daraja da martaba wajenka ka gane amfaninta Amma bawai Dan karabu da ita ba ni zanfi kowa shiga bakin ciki ace ka rabu da Zahra In son Zahra tamkar yanda nakeson su chuchu "To Ammy meyasa Zaki Baro musu ita meyasa Zaki kaita wajensu Ammy yanzu kina gani sun amshe mun mata Ammy duk laifinki ne meyasa tun farko Baki sasintani da matata ta ba Kika dinga jamun Rai ni mamy tun ranar Dana fara haduwa da ita nasan darajarta da mahimmanci ta da amfaninta a cikin rayuwata.."Kasa karasa magana yayi saboda wani daci dayakeji a cikin zuciyarsa "Ammy ce ta ce "ka nutsu baba na dole ne a kaita Wajen iyayenta ayi musu bayani Susan halin da ake ciki saboda su sukafi kowa hakki a kanta kaga ko Baba da kagani shiya haifi mahaifiyarta to baikai dangin mahaifinta da mahaifinta hakki a kanta ba kayi hakuri harsu huce " bai tankawa Ammy ba saboda baima San abunda zaice mata ba Kuma, fuuuu yabar dakin kamar Zai tashi sama cikin tsananin bacin Rai "Chuchu ma Tana kuka ta Mike ta ce "Daman Ammy duk laifinki ne tun lokacin da yace yanason momcy kikakiya yanzu Gashinan kinja iyayenta sun amshe Mana ita"ta fada Tana tashi da gudu ta Ruga"Tagumi Ammy tayi ta ce "Oh ni !Fatima yanzu Kuma laifin Nan duka sun maidoshi kaina......... *07026166536 domin magana da marubuciyar* ...........*91 & 92* & ..........*93 & 94* "Ki kwantar da hankalinki Hajiya insha Allah zai huce idanma bai huce ba ni da kaina zankoma na basa hakuri"Baba tsoho ya fada kafin yayiwa Ammy bankwana ya koma masaukinsa Da aka saukesa a gidan"Sosai Md ya burkuce ya shiga tsananin tashin hankali na rashin Zahra da yaransa gaba daya baya cikin nutsuwa cikin kwana biyu harya zabge ya rame saboda tashin hankali da rashin bacci Ga ko abinci baya iyaci saidai ruwan Lipton idan ya zauna ba Wanda yake tunanin irin Zahra Shi kanshi baisan Yana mata so har irin haka ba sai yanzu da tayi nesa dashi Gaba daya yashiga tashin hankali rasa Wanda zaiyi shawara dashi yayi sai jabir ya bude wayarsa ya Kira Dan tun Kiran da iyayen amira suke mashi ya dameshi ya sanyashi kashe wayarsa .....bangaren Zahra Itama Bata da wata walwala Sosai dukda kannen babanta na kokari a kanta Sosai baba ma Yana nuna mata ya hakura Dan har yaran saiya daukesu su yini wajenshi Amma Kuma har yanzu batajin Tana da walwala Sosai takejin kewar su Ammy ga Kuma tunanin Md da tarasa dalilin da Indai ta zauna ba Wanda take tunawa da irin rayuwar da sukayi a baya irinshi yauma Tana kwance Tana tunani batasan lokacin da wasu hawaye masu dumi suka zubo mata ba Haka kawai data zauna saita dinga tunaninsa ta rasa fahimtar abundanda ke damunta game dashi lura da rashin walwalar na Zahra ya sanya Mama habi tafiya da ita gidanta katsina Dan taci gaba da Kula da ita Komawarta katsina Zahra ta danji sassauci saboda koba komai akwai yaran mama habi Sa'anninta da Wanda suka fita sun zauna su danyi hira ta rage kawaici triple ko Daman idan ba yunwa sukaji ba tofa ba a kawosu wajenta suna hannun mama habi da yaranta haka dai rayuwa taci gaba mama habi naci gaba da yiwa Zahra gyara Sosai dukda damuwar da tasa a ranta ta rame yaranta ko sunyi b'ul b'ul abunsu gwanin sha'awa kamanninsu da mahaifinsu na Kara fitowa....a halin yanzu md kullum cikin zazzabi da ciwon Kai yake ya rame Sosai gashi yaki yaje asibiti Ammy ko itama duk hankalinta ya tashi ganin yanda beloved son din nata ya koma ita kanta batasan md Yana yiwa Zahra har irin wannan son ba sai yanzu lallashi ba irin Wanda batayi Masa ba Amma yakiji Baba tsoho ko Yana daya daga cikin gidajen Baki na md inda Ammy ta saukesa kafin Shima su waiwayi jigawa wajen ahalinsa sun Bari dai a gama da matsalar Zahra Ranar da Zahra ta cika sati ukku da tafiya idan ka kallesa saikayi Masa kuka saboda yanda ya firgice kamar ba mr MD billonia ba matashi da kudi Ranar ji yayi bazai iya jure rashin Zahra ba saboda yanda yakejin zuciyarsa kamar zata tarwatse a daddafe ya Kira chuchu a waya Koda tazo saida tayi hawaye ganin yanda Yayan nata ya zabge Address din garin da suka Kai Zahra ta basa tare da fada mashi drivern da ya kaisu baiyi wata wata ba ya Kira drivern a tare da jabir suka tafi garinsu batsari Wanda tafiyar sirri sukayi Allah yasa Drivern ya gane Gidan Koda sukayi sallama da bappa ya fito ganin Baki ne ya sanyashi masu iso har cikin gida Md kanshi Kasa ya gaishesu Har baba da yake zaune baba ya Gane jabir cikin girmamawa suka gaisa Yana tambayar jabir ya mutanen gidan sannan yayi mashi godiya akan Abunda yayi mashi Lura da shine baban Zahra ya sanya mD Kasa had'a ido biyu dashi dakyal jabir ya iya bude Baki ya ce "Baba Daman magane ce tafe damu akan Zahra"Inajinku wace magana kenan"Baba ya fad'a"saida jabir yayi Jim kafin ya. Dago ya ce "Daman hakuri ne muka zo mu Kara Baku akan Abunda ya faru Dan Allah Baba kuyi Hakuri wannan abokina ne Kuma shine mijin Zahra baban yaran shine mukazo mu Kara Baku hakuri "Kallon md baba da bappa sukayi kafin Bappa ya ce "Allahsrk shine yaron kenan To Ai komai ya wuce Hakuri an Riga anyi d'an Adam ai baya wuce rubutun Allah duka abunda ya faru ya faru ne a bisa kaddara da Kuma rabon yaran Nan dan haka daga bangarenmu ya wuce yaro tunda dai ba Zina sukayi ba Aure sukayi har aka haifi yaran ta hanyar sunna kaga ai komai yazo da sauki "saida ya md ya sauke boyayyar ajiyar zuciya "Baba Shima cewa
Chapter 82 · 0% Book details