Sashe 16
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abunda ke damun Zarah allura akayi mata Bayan Bacci ya kwasheta ta na tashi taji da sauki haka suka koma hostel Chuchu dukda tsorata Dan ita duk perioud din da take bata tabajin ciwon ciki ba Saidai taji kasala. Tundaga lokacin abun Zarah ya k'ara worse a halin yanzu har suma ta ke Asibitin da suke zuwa Dr d'in harya ganesu wani zuwa da sukayi ya cewa Asmy . "a Gaskiya ko yarinyar nan ta na samun sauki tofa dole sai wani Abu ya shiga tsakanin ta da wani?wara idanu Asmy tayi ta ce. " What Dr kenan yanzu ba maganin da za a bata"Babu maganin ciwon nan kamar yanda na fad'a hakan ne kawai maganin da zan baku shawara tayi Aure zata daina " "Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce " mungode dr"Ranar sun koma hostel Asmy ta kalli Zarah lokacin ta na kurbar tea ta ce. "Sis waikinsan me dr ya ce Ko kina daina ciwon cikin nan sai kiyi Aure sainakejin inama saida akayi aurenki da Hafiz kafin ki fara makaranta Dan wlh ciwon nan naki ya fara bani tsoro da safe fa har suma kikayi" "Cike da damuwa Zarah ta ce " Ni kaina ciwon nan ya na damuna karkiga idan perioud d'ina ya matso irin fad'uwar gaban da nakeji Asmy Aikin gama ya Riga ya gama dole ne nayi hakuri har na k'arasa karatu na Shima ya k'arasa nasa" <America> Tsaye ya ke waya na K'are a kunnansa daga ka gansa ka San ranshi a matuk'ar b'ace yake tashin hankali k'arara a fuskarsa ya ce. "what ka na nufin an sanya an kashe Alh sammani?banji me akace daga d'ayan b'angaren ba saiji nayi cikin Sauri ya ce. " gani nan zuwa k'asar yanzunnan ka sanar da DPO abunda ke faruwa a maza a tari abun da wuri kafin Su gudu a tabbatar an kama su" Ya na Gama fad'ar haka ya katse kiran Tare kiran PA dinsa ya ce a shirya masa tafiyar gaggawa daga Inda yake tare da Escort dinsa suka wuce Aiport ba tare da ya koma ma gida ba yayi wa Amera bankwana Dan Zuwan emergency ne. <Zaria> Kasancewar kwazo da dagewa da kuma ilimin addini ya sanya aka bawa Zarah Amera ta makarantar Sauri take sosai Dan zasuje wata musabaqa ta students din makarantu a Polytechnic Kaduna Sosai tayi kyau cikin Zumbuleliyar Hijab d'inta har k'asa mai hannu maroon" Tare da daura Nik'ab tare da Asmy suka tafi Dan tayi mata rakiya Chuchu ko ta na gida Dan weekend ne kuma yawaici a kd takeyinsa. Kasancewar a motar makaranta suka tafi cikin k'ank'anin lokaci suka isa Inda aka fara gudanar da Musabaqa ko wasu makarantu har akazo kan makarantar su Zarah Inda Zarah ta wakilcesu cikin muryarta mai dad'in sauraro tare da qiri'arta ta fara karatun da aka tambayeta duk Inda aka janyo saita k'arasa batare da gargadaba ba Kuma zallar tajwid take fitarwa Sosai ta burge mutane da dama dake wajen. Motocin Escord dinsa Guda goma suka sanya motar da yake ciki tsakiya shi kadai ne a motar sai driver . sunzo daidai zasu gitta ta poly MD yajiyo karatun muryar da ta kasa barin kwalwarsa cikin Sauri ya cewa "Driver ya tsaya" tsayawar yayi yayinda sauran motocin ma suka tsaya gabaki d'aya ya mayar da hankalinsa ga zazzak'ar muryarta karatun da yake jiyowa har wani lumshe ido yake Sosai muryar ke shiga ta na ratsa duk wani sassa na jikinsa suna nan tsaye ya na sauraronta muryar da tabbas ya San muryar da yaji ce a lokacin da yake waya da Chuchu. sosai yaji ya na son cigaba da sauraron karatun daga mamallakiyar wannan zazzakar muryar saida suka kwashe minti Talatin tsaye kafin ta gama karatun sai sannan MD ya dawo hankalinsa. ji yake kamar ya dawwama cikin sauraron muryar ta Cikin Sauri kuma ya tuno da abunda ya kawosa Umartar driver yayi da yaja su tafi. Zarah ko Bayan ta gama karatu kabbara kawai ake daga karshe dai ita ta ciyo musu na d'aya Wanda hakan yasa makarantar suka kara alfaharin da ita Dan sannan ne karo na farko a Musabakar makarantu state din da aka fara ciwo musu na d'aya Zarah ta samu kyautoci da dama daga wajen manyan da suka halacci wajen. Koda za a koma A motar makaranta kin shiga sukayi Dan suna son su biya gidan su chuchu Dan tun d'azu ta ke kiransu akan d'an Allah Ammy tace suzo Mai napep suka Tara Inda sukayi ciniki da shi akan ya kaisu G R A. Gudu sosai suke shararawa a titi yayinda waya na K'are a kunnansa DPO ne ya ce . "Ranka ya dad'e sun Kufce mana Yanzu haka Suna Hanyar da kake bi karka yarda su tsere zaka gansu a mashin sun rufe fuska su biyu suka rage sauran sun gudu" Cikin masifa MD ya Ce "Aikinme kuke har zaku kasa kama k'ananan y'an iskan da basu da aiki sai kashe jinin y'an uwanmu musulmi bil'adama ". tsaki yaja tare da katse kiran yace driver Kara gudu "Sunzo daidai Wani round about MD ta Cikin glass ya Hango su cikin Sauri ya zage glass din tare da fiddo bindigarsa Ya saitasu ji kake tassss ya harbesu a gefen hannu d'ayanma haka Shi kanshi MD rumtse ido yayi Dan wannan ne karo na farko da ya tab'a harbi a rasuwarsa. Hakan yayi daidai da isowar su Zarah wajen Akan idonsu Harbin ya afku saida basuga mai Harbin ba Sosai suka rude Zarah ta kankame Asmy tare da fasa Kara Dan iya tsawon rayuwarta bata tab'a ganin irin wannan ba Mutane filis a kasa jina jina akan idonsu aka harbesu. Ita kanta saida Asmy ta girgiza karkame juna sukayi tare da karanto duk addu'ar da tazo bakinsu dan basu tabajin anyi harbi a gabansu ba lura da hakan mai napep din ya juyo ya ce "Ku nutsu Wannan abun ba Bak'on Abu bane a Saidai kawai Allah kyauta" Asmy ce tayi k'arfin halin cewa "da gangan fa aka harbesu suna Tafiyarsu Dan zalinci ," girgiza kai napep din yayi ya ce " a Lamarin k'asar nan sai dai addua MD ne a cikin motar kuma ina kallonsa ta cikin glass shi yayi harbin Kunga ko a kudin sa ba abunda aka isa ayi hatta gwamnatin a hannunsu ta ke Saidai hakuri kawai " MD Zarah ta maimaita a cikin zuciyarta lokaci guda taji wata irin matsanancin tsanar mai sunan a rayuwarta ta tsani mutumin da baisan darajar d'an adam ba bazata tab'a mance da sunan ba mutumin da ya tsaidasu a Zaria da zasuje Banki. Sosai taji wata irin tsanarsa dukda bata sansa ba a fuska Amma taji a duniya babu mahalukin da ta tsana sama dashi cikin rud'u ta ce "mai Napep juya damu ka maidamu tashar motar Zaria" Juyasu mai napep din yayi har lokacin Zarah A rude ta ke Har suka isa Tasha Inda suka hau motar Zaria Dan komawa school jikinta bai bar kyarma ba "Ajiyar zuciya ya sauke daga zaunen da yake tare da maida bindigar ma ajinta a take nan motar y'an sanda suka ido DPO da kanshi ya lek'a ta glass tare da sarawa MD ya ce. " da ana samun irinka a cikin k'asar nan da an zauna lafiya Allah ya k'ara tsarewa sannan ya k'ara girma yanzu zamu wuce dasu police station ko asibiti bazamu kaisu ba harsai azaba ta ishesu sun fad'a ogansu dake sanyasu wannan aikin". "Jinjina kai MD yayi tare da cewa " kar ayi Sakaci dasu a matsesu har saisun fad'a ko waye duk bayanin da aka samu a kirayeni " <Zaria> Har suka isa hostel Zarah na kyarma Inda suna isa ta lulluba saboda zazzabin tsorata da ya zubar mata Asmy ta dinga Lallashinta akan karta sanya abun a ranta ya hanata bacci "Zarah na hawaye ta ce " dole na damu Asmy Jinin musulmi fa aka kashe a gaba na Asmy bantabajin tsanar wani d'an adam ba a rayuwata sama da MD d'innan da aka fad'a na tsanesa na tsana jininsa na tsani Wanda ya shafesa saboda duk mutumin da zai iya kashe jinin musulmi ya chancahnci tsana mai muni daga wajena "ta fad'a ta na rumtse ido. Ta na ganin abunda ya faru na dawo mata a cikin kwalwarta. <Kaduna> Lumshe ido yayi jikin Ammynsa ya na jin dad'in zama kusa da mahaifiyar tasa Albarka Sosai Ammy ta shiga sanyawa d'an nata a bisa Namijin kokarin da yayi Dan kafin ya Iso ma Har sungani a television live Chuchu ma sosai tayi alfaharin da irin taimakon da yayan nata yake bayarwa ta fannin Yak'i da y'an ta'addan da suka hana k'asarmu zaman lafiya. Ammy ce ta kalli chuchu ta ce " Wai har yanzu su momcyn taki Basu iso ba lafiya". Lalubo wayarta Chuchu tayi cikin damuwa tare da cewa"nima tun d'azu jiransu nake jira Bayan na shirya musu abubuwa ta fad'a ta na kiran Zarah" Asmy ce ta d'auka dan zarah duk ta rikice mata cikin shagwaba Chuchu ta ce "Wai me ya tsaidaku nasanfa tun d'azu aka gama Musabaqa kufa kawai nake jira " cikin sanyi Asmy ta ce "am so sorry sis wlh matsala aka samu wani Abu ne ya firgitar damu yanzu haka muna Zaria Kinga Zarah nan ma bata lafiya zazzabi ke damunta" Cikin tsananin damuwa Chuchu ta ce "Subhanallahi me ya faru ya jikin momcy din " da sauki Haba ai yau munga tashin hankali maganar bata fad'uwa a waya bace saidai kindawo"Cewar Asmy . Sosai Chuchu ta rude "Ammy ce ta ce " Lafiya Kuwa"wlh Ammy wai wani Abu ya rud'ar dasu suka koma yanzu haka momcy ba lafiya bari kawai na wuce school din yanzu hankali na bai nutsu ba " Ta fad'a tare da saurin Rugawa ta sanyo k'atuwar hijab din da suka dinka tare da Zarah tundaga Fitowarta MD ya bita da Kallon mamaki Kasa shiru yayi ya ce . "Ammy yau Chuchu ce da hijab " Dariya Ammy tayi ta ce "Au ashe ban baka labari ba Ai yanzu Chuchu an nutsu kawa tayi Malama Yanzu haka ta tafi hizif arba'in Karin karatu takeyi mata wannan shigar banza da kide kide da raye raye duk ta dainasu " "wow but Gaskiya Naji dadi ko wacece wannan