← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 92

Sashe 23

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fad'a tare da tashi ta miko mata ta ce "anyi ta Kiranki ganin kiran yayi yawa ya sanya na ma kashe ". bud'e wayar Zarah tayi ta ga missed call d'in ya Hafiz Kusan goma cikin Sauri ta Danna masa kira Ring biyu ya d'auka ta na jin Ajiyar zuciyar da ya sauke tare da cewa . "ina kika sanya wayarki my love jiya na yini da darura " Ajiyar zuciya ta sauke ta na lumshe ido ta ce "ta mutu ne ba chaji ya Hafiz ina kwana ya sch din" . Alhmdllh Habibaty har Naji sanyi kinsan na d'auka ko ba lafiya ba sai tunaninki nake"murmushi tayi ta ce "Lafiya qalau nima da tunaninka na yini" ta fad'a ta na rufe fuska ". Daga bangarensa yayi Dariya ya ce " ai dai nesa ta kusa zuwa kusa nan da one year munzama mata da miji"rufe fuska Zarah tayi kamar ya na gabanta tare da katse kiran Dan ya bata kunya ma . Ganin yinin ranar yanda Zarah ta share Asmy ya sanya bataji dad'i ba Ta ce "Na ce Kiyi Hakuri Zarah Daman zaki iya fushi dani tunda maganar ta wuce ba shikenan ba" murmushi Zarah tayi ta ce "Ya wuce Asmy kinban Haushi ne nayi mamaki da maganar ta fito daga bakinki saikace baki da hankalii" . turo baki Asmy tayi ya ce "Naji dai yanzu abar maganar" a take suka shirya sukaci gaba da hirarsu Wanda asmy hankalinta duk baya gurin. "To ba saurin nake ba bloody kaifa komai kafison ayishi cikin ujila ba ina hanyar zuwa gidan ba minti biyu yayi yawa na iso " " jaber ya fad'a daga wayar "tsaki MD yaja tare da katse kiran ya na tsaye harabar gidan flat house ne Me kyau baida wani girma sosai Saida ya tsaru parking space d'in gidan zai d'auki mota Ukku ya na tsaye motar jaber ta shigo gidan Bayan yayi parking shiga gaba yayi da zasu fita ya tsaya ya mik'awa me gadin kudi tare da cewa . " A cigaba da kula da tsaftar gidan yanda ya kamata "to ranka ya dad'e insha Allahu Nagode Allah ya k'ara girma" kai tsaye Hanyar kd suka nufa jaber ya Kalleshi ya ce "bazamuje mu gaisa da Chuchu ba" Bana ra'ayin hakan "ya fad'a yana cigaba da latsa wayarsa " Girgiza kai kawai jaber yayi tare da cigaba da driving Dan ya lura ranshi kamar bace tafiyar 30 minutes ta kaisu garin kd Wanda kai tsaye gidan sa suka nufa Bayan ya saukesa jaber ya wuce gidansu Dan tun safe aka Sallami babanshi shi kuma md ciki ya shiga Dan ya huta. Kwance yayi kan makeken Royal bed dinsa mai matuk'ar d'aukar hankali ya yi pillow da hannayenshi biyu bacci yake so ya daukesa amma ya rasa dalilin da muryar qiri'arta yarinyar ke dawo masa a kunne lumshe idonsa yayi. Jin ringing d'in wayarsa da ya bude ba jimawa ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya Lula d'aukar wayar yayi ganin Chuchu ce ya sanyashi d'auka "yaya na jiya shine ka shanyani nayi ta jiranka har girki mai dadi nayi maka amma bakazo ba " ta k'arasa fad'a cikin shagwaba " Cikin muryarsa da bayason yin magana ya ce "wani uziri ne ya hanani zuwa chuchun yaya next time na tashi zuwa Saidai kawai ki ganni kwatsam" Yana jin ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "To shikenan yaya Ai Inajin next week ma zanzo gida saboda munyi waya da Ruky tace next week zasu tafi Dan naje muyi bankwana " to shikenan Allah ya kawoki lafiya "ya fad'a Dan bayason hayaniya. Kiran Amera ne ya biyo baya Bayan gama wayarsa da Chuchu kamar bazai daga ba saikuma ya d'auka " kuka yaji ta fashe dashi Wanda yakejinshi har cikin ransa tsayawa yayi ya na sauraronta har saida ta gama kafin ta tsagaita cike da kissa ta ce. "Haba Honey Bayan kasan nayi missing naka shine zakayi zamanka anan please yaushe zaka dawo kasan banason zamanka a Nigeria ko wace banza ta dinga kallemunkai please mijina ka dawo kewarka duk ta isheni. " Ke me zai hana bazaki taho ba Inda nake Dan in kin ganni a America to fa saina gama muhimmin aikin da ya kawoni " "Haba honey yanzu ka na nufin bazaka dawo ba yanzu akwai muhimmin aikin da ya fini daman me zai hana bazaka k'arasa aikin a nan America ba dole sai Nigeria " ta k'arasa fad'a ya na jin shashekar kukanta". Don son kwantar mata da hankali ya sanyashi kasa da murya ya ce "Aikin bazaiyu ba a Chan my meera ki taho kawai nima ina bukatarki kusa dani kinfi kowa sanin haka Gobe ki taho saiki sauka Abuja" "Ni wlh honey bazanzo Nigeria yanzu ba idan nazo dinma in banda chazamun kai ba abunda ake sannan a isheni da maganar Rashin haihuwa Bayan ta Allah ce Nifa tun last time da nazo Sunan Daddyn Zey karkaga irin Rashin mutuncin da tsohuwar nan tayimun Hada cewa wai Aure zata sanyaka kayi na shanyeka na gama dakai sannan itama Ammy Ai Naji kwanaki kus_kus din so take kayi Aure to wlh ba abunda zai maidoni Nigeria kusa wancen zuwan ma da kaga nayi Dan nayi kewar iyaye na ne kawai akanme zanzo Bayan family dinka ba k'aunata suke ba dan wlh tsohuwa ko yarinya ta kawomun wargi ba kyalewa zanyi ba Hakanan kawai a doramun hawan jini da yarintata" Sosai ran MD ya b'aci Cikin b'acin rai ya ce "Da Allah iya mutane shiru stupid kawai iyayen nawa kike fad'awa haka Dan baki da kunya kar alasa kizo din kiyi shekara ta Annabi nuhu tunda America din garin ubanki ce " ya k'arasa fad'a ya na Jan tsaki. Kuka Amera ta fashe dashi ta ce "ni kake zagin uba na MD yau Ni ka zaga" tsaki ya ja tare da katse kiran Dan ta bata masa rai ya jima ya na Jan tsoka. Kasancewar ya rike ranar da chuchu ta fada masa su hajiya zasu tafi around 11am ya shiga da motarsa harabar gidansu Hango motar Adil tare da su Hajiya da su Chuchu a wajen ya sanyashi karasawa"Ina kwana hajiya "Lafiya qalau Mustapha mu kuma muntafi sai Allah yayi mana d awowa ko kuma kunje dukda Bason zuwa kuke cikin dangin Ku ba kowa gareku ba a Kaduna in banda Aikin gwamnati da kasuwanci da ya kawo mahaifinku duk dangin mahaifinku suna Maiduguri amma tsabar shak'iyanci saiku Shekara biyu ko Ukku baku taka garinba Dan lalacewa Ai wlh duk laifin Fatima ne Ai lokacin da ran Mariganyi yana tiso keyarku kuna zuwa" Murmushi yayi ya ce "za a gyara Hajjajunah " itama Ammy murmushi tayi ta ce "Insha Allah Hajiya zamuzo nan kusa " Allah yasa Hajiya ta fad'a ta na sanya akwatinta cikin boot da Adil ya fito mata da ita tare da Chuchu hannu Adil ya mikawa MD sukayi musabaha ya ce "Yaya zamu wuce " "Okay Allah ya kiyaye Ya tsare hanya yanzu tundaga Chan Saida Hajiya ta tiso ka Dan Kawai ka d'aukesu maimakon A musu booking Fly hankali kwance". murmushi Adil yayi ya ce "Wlhko ya na iya na musa cibi ya zama Kari" Hajiya ce ta ce "Naji dai Komai zakace kace amma banga tukin da zan hau ba idan ba naka ba Sauran duk y,an kasada ne ka maza ka shigo mu tafi maiduguri ba zuwa kano bace karmuyi dare hanyar nan da ba kyau gareta ba". Ruky ta fara shiga Bayan sunyi hug din juna da Chuchu da takejin kamar tayi kuka Bye bye tayiwa Adil ta na narkewa jikin Ammy murmushi yayi mata na so da k'auna ya ce " Bye Dear sai munyi waya"itama mayar masa tayi ta ce "Allah ya maidaku lafiya " . Har zasu tafi Hajiya ta juyo ta kalli MD ta ce"kai kuma Ka fara lissafi yanzu saura wata sha d'aya ka bari lokacin da zan dawo garin nan zakayi mamakin d'anyen aikin da zanyi "ta na gama fad'a ta shiga Mota Adil ya ja har suka bar gidan suna daga musu hannu". Cikin suka koma Chuchu ta zauna gefen Ammy ta d'ora kanta bisa kafadarta " Gaishe da Ammy MD.yayi Bayan ta amsa Kallonnshi Chuchu tayi ta ce "Ina kwana yaya" Lafiya qalau "ya bata amsa tare da cewa jeki hadoman break fast " "to" ta amsa tare da wucewa kitchen. Kallonshi Ammy tayi ta ce "yaushe zaka koma ka baro Matarka ita kadai kayi zaune a nan" Ba yanxu ba Ammy bazan bar k'asar nan ba har sainagano Wanda sukayi kisan Alhaji sammani saboda sak irin harin da suka kawowa Abba Shima daidai zai shiga gidanshi da mota aka harbeshi akwai binciken da nake saina k'arasa tukwana". Saida Ammy ta Goge hawayenta tunowa da uban Yayan nata ta ce "Tabbas Wanda yayi kisan Alh sammani shi ya kashemun miji saboda alh sammani da Mahaifinku aminai ne bashi da aminin da ya fishi kuma insha Allahu asirinsu saiya tonu har kullum bazan daina muguwar addua a kansu ba Asirinsu zai tonu insha Allahu wlh karkaga yanda iyalanshi suka shiga wani hali abun tausayi har yanzu na tuna da Alhaji ji nake kamar mutuwar ta dawomun sabuwa " ta k'arasa fad'a ta na Goge hawayenta. Nan suka ci gaba da hirar rayuwar baya har Chuchu ta kawo masa Break fast din Bayan ta Aje d'akinta ta shiga sai ganinta yayi ta fito da hijab tare da hand bag a hannunta Kallon Ammy tayi ta ce "Na wuce ammy" MD ne ba wasa a fuskarsa ya ce "Ina zaki ? "Makaranta zankoma tun jiya nazo kuma muna da lectures Gobe" ki koma sai gobe "Ta na turo baki ta koma ciki Dan tasan Halin Yayan nata baisan musu Kallon Ammy yayi ya ce. " me akayi mata naga ta na bata rai"Tab'e baki Ammy tayi ta ce "Baiwuce akan Tafiyarsu Ruky da Adil ba kasan halinta indai suka tafi tazo tanayiwa mutane fushe fushe Saikace in cewa akayi ta shirya taje Chan tayi ma musu Hutu iyawa zatayi". ***** Tsaye take ta na gyara Tsayuwar hijab d'inta Bayan ta gama Kallon Asmy dake chat ta ce "Zanje bank na ciro kudi tunda bazaki raka ni ba" "A dawo lafiya " ta fad'a ta na
Chapter 23 · 0% Book details