← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 92

Sashe 13

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taja tare da cewa "Allah ya kyauta " D'an murmushin gefen baki yayi tare da girgiza kai ya wuce ciki. <Zaria > "Kwance take saman bed din Dakinsu ta na chat da Hafiz d'inta ya na bata labarin abun Dariya labarai masu sanya nishad'i sosai takejin dad'in chat d'in " Asmy ce da ke Dafa musu indomie a k'aramun gas d'insu ta ce " "Uhm Manya chat yayi dad'i sai Murmushi ake " "Kede bari wani labari ne ya Hafiz yake bani na ban Dariya" ta na sauke indomie d'in Asmy ta ce. "Ai naga alama kam Sauko muci kafin ta huce " kashe datar tayi tare da Saukowa nan suka faracin indomie d'in kasancewar dare ne. "suna cikin ci y'ar d'akin su zaituna ta dawo K'arewa shigarta kallo Zarah tayi taci uban attachment ta sanya matsatsun kaya girgiza kai tayi tare da Cigaba da abunda take Dan ta lura yarinyar ba tarbiya gareta ba hakan yasa ko maganar kirki bata had'asu inba Sannu ba . Sannu tayi musu Zarah ta amsa da yawwa " Asmy ce ma dayake suna Dan mutunci suka Dan tab'a Hira yayinda Zarah tayi kwanciyar ta dan gobe tun 8 suke da lectures . Washegari tunda safe ta shirya 7:40 tayi mata a class saboda 8 suke da lectures Bayan lecturer d'insu ya fita Mikewa tayi tare da fitowa jikin wani block ta zauna tare da fiddo hand out d'inta ta fara Duba abubuwan da akayi musu sosai. Sallama taji anyi mata batare da ta d'agoba ta amsa "zan iya zama Malama Zarah " Dagowa tayi tare da Kallonshi class mate d'insu ne amma tayi mamakin yanda yasan sunanta " "Matsa masa tayi tare da cewa zaka iya zama mana" Bayan ya zauna Har lokacin karatunta take "cike da burgewa ya ce " Gaskiya Malama Zarah kin burgeni wlh Tunda kika shigo makarantar nan na lura da kwazo da nutsuwarki Da yawan dalibai ba karatu ke.kawosu ba makaranta amma ke yanda kike dagewa yasanya nayi sha'awar Ko zakiyi abota dani Dan nima na k'aru saboda course d'inmu d'aya kuma math tana bani wahala sosai " Murmushi Zarah tayi masa tare da kallonta ta lura yana da nutsuwa daga ganinsa kasan d'an Babban gidane ta ce "Badamuwa Allah sa mu karu da juna Saidai bansan sunan malamin nawa ba " Cikin barkwanci ya ce "Ah dalibinki dai ai kece malamar sunana Yusuf muna zaune a garin Abuja tare da iyaye na karatu ya kawoni Zaria bansan kowaba" "Ah kace Babana ne Saidai na kiraka da Baba " Dariya Yusuf yayi ya ce "Wow kice da y'ata nake tare Gaskiya nayi sa'ar haihuwar wannan santaleliyar d'iya Kinga dole ayimun biyayya Sannan Abban na zaki dinga Cemun ba Baba ba " Duk yanda Zarah taso ta fusge saida ya sanyata Dariya ta ce "Eh Gaskiya ne Abba na Amma naga Abban nawa akwai iyayi da surutu fa " Dariya yayi tare da bude book dinsa ya ce "Wlh daughter karatun da akayi yau kwata kwata bangane ba idan kin gane ki koyamun please" bari na duba naga ko zan iya ta fad'a ta na amsa tare da Fara gwada masa dalla_dalla kamar ita ce lecturar sosai Yusuf ya gane fiye da yanda Malam ma ya koya a aji shi kanshi ya sake da baiwar kokari irin na Zarah gashi dai tare aka koya musu amma saika rantse malamin ma a Wajenta ya koya. Saida ta gama koya masa komai "wow amma daughter nagode Wlh daga yau kinzama malamata ki godewa Allah yayi miki baiwar da ba kowa ya sameta ba Kyau Ilimi tarbiya uwa uba addini " "Muje dai yanzu class za a shiga wata lectures ba surutun ba Abba na" ta fad'a tana Mikewa Shima Mikewa yayi yana Dariya tare da Amsar jakar dake hannunta "wara idanu tayi ta ce . " so kake ace y'a ta sanya uba rik'e jaka ai sai a sanyamu a news "Shima dariyar yayi tare da amsar jakar ya ce " Kinga sai muyi suna yanda za ayi ta zancenmu muzama cele". Har suka isa Class din suna Hirar barkwanci duk miskilancin Zarah har mamaki nayi yanda ta sakarwa Yusuf kodan ance Gamon jini daban yake. Da suka gama lecture ma tare suka fito Inda sukaje capteria sukaci abinci kafin Zarah ta wuce hostel Bayan ya amshi numberta. Shakuwa ce da abokantaka ta shiga tsakanin Zarah da Yusuf yazama closed fried d'inta Asmy har mamaki ta ke yanda Zarah ta sakarwa Yusuf fuska duk sanda bai gane wani Abu ba ita take zaunawa ta fahimtar dashi sosai yake amfanuwa da Zarah. Cikin sati guda da Fara lecture a makarantar har amfara sanin Zarah saboda kokarinta Inda tayi wasu kawaye su biyu hibba da Jamila suma yabawa da tarbiyarsu ta sanya Zarah fara abuta dasu amma fa ba wai Chan ba saboda Har yanzu miskilancin ta ya na nan na Rashin son magana idan y'an maganar sukazo saikayi mamakin yanda take magana . A yanzu Hankalinta kwance yake Hartama fara mancewa da su Mama Rabi Saidai tunanin babanta da take. Suna waya da Hafiz Ya ce "Dear wai bazakije ku bud'e account ba Yaci ace kun bud'e ko Dan saboda scholarship sannan idan za ayi muku aike fa account yafi sauki akan Sai an Aiko muku" "A rufda cikin da take a kwance ta ce " To ya Hafiz Insha Allahu gobe Monday sai muje mu bud'e ko" "Yawwa matas Shiyasa nake sonki gobe kuje ku bud'e Ki bud'e a access " "To ta fad'a tare da cewa gashi ba musan ko ina ba bamu tab'a fita ba " "Ina abokin naki da kike bani labari Abba ko to shi zai iya sani kice ya rakaki " "To " ta fad'a sun tab'a Hira Kad'an kafin ta kashe wayar a yanzu Hafiz ya Riga ya fara zama wani bangare na jikinta tun bata sonshi yanzu har taji ta fara sonshi saboda soyayya da kulawa da yake nuna mata. Washegari Bayan fitowarsu daga lecture suka shirya Fita domin Suje su bud'e account around 1 suka tafi Yusuf yayi musu rakiya Napep suka hau su Ukku Inda shi Yusuf ya hau gaba. Nan napep d'insu ta fara tafiya Yusuf ne ya jiyo cikin barkwanci ya ce "Daugher Kinga kuwa Yanda kikayi kyau na jima banga macen da hijab ke yiwa kyau kamarki ba ked'in ta musamman ce fa " "Dariya tayi tare da cewa " baka rabo da barkwanci Abba na Kana uba amma ka maida y'ar jikarka" "Y'ar Dariya yayi ya ce " Ai Gaskiya Ce dole a fad'a y'artawa ta daban ce Shiyasa idan na tashi Aurar da ita mutum na daban zan aurawa saboda ked'in Matar manya ce ba yara ba wlh daughter " "Murmushi tayi tare da girgiza kai ta ce " kadai kalli gabanka karka fad'i kaja mana " Bayan Asmy ta gama waya Ta ce "Ai Gaskiya ka fad'a ko Abbanmu"Dariya yayi tare da cewa " Eh mana Bestynmu "nan suka cigaba da hirarsu su Ukku yawaici duk ta barkwanci ce. Sunzo daidai round din da zasubi ya kaisu Banki Sukaji mai napep d'in ya tsaya " Abun hankalinsu duk yana dumin da suke "Asmy ta ce Lafiya Malam yanaga ka tsaya" Mai napep d'in ya ce "Kuyi hakuri Hajiya Inajin wani Babban mutum ne zai wuce a wajen shiyasa chunkoso yayi yawa sai motocinsu sun gama wucewa tukwana a bamu hanya". Cikin jin Haushi Zarah ta ce " Yanzu haka zamuyi ta tsayuwa a titi saboda kawai wani zai wuce dan fin arziki za a tsaida mu". "Kuyi hakuri Hajiya ya muka iya " Daidai lokacin da wulfa_wulfam motocin suka fara gittawa ta wajen "Kallon motocin da tunda uwarta ta haifeta Bata tab'a gani ba Asmy ta gani wara idanu tayi tare da cewa " Kan uban Chan waiko shugaban k'asane ya shigo garin? Yusuf ne dake gaba ya ce "Kan ube Wlh MD ne ya shigo garin nan Chab dole a tsaida mutane Innalillahi inama zan gansa ido da ido MD a Zaria to me ya kawosa" "Zarah ce ta ja tsaki Ta ce " Shi waye da za ace sabodashi za a tsaida mutane saboda shi yanzu fa Banki suna gab da tashi ta fad'a ta na duba Agogon hannunta " "Yusuf ya jiwo ya ce " "Wai kina nufin bakisan MD ba kina Nigeria Amma baki Kallon Television da labarai ko? " Tab'e zarah tayi ta ce "nidai ban wani sansa ba Asmy ma ta ce nima kam " Yusuf sarkin bada labari juyowa yayi yare da cewa aiko yau zan baku labarinshi saboda ni fans dinsa ne ina karanta tarihinshi sosai". wani shahararren matashin mai kud'i ne iyayenshi suna zaune a garin Kaduna Mahaifiyarshi asalinta y'ar India ce a Chan mahaifinshi ya ganta ya auro ta shiyasa da kin gansa zakiga asalin ba indiye kannansa biyu mata sosai yake sonsu da ji dasu na manta sunansu , Compononyn da gayen nan ya mallaka nan Nigeria da ma k'asashen k'etare da kadarori gidajen mai kudade na ban mamaki ke kanki saikinyi mamaki gashi matashi Dan bazai wuce 38 years ba Amma wlh Inajin gayen nan shi yazo na biyu a kudi a negeria su kansu manyan durkusa masa suke Dan wasu Mahaukatan kud'ine ke garesa duk wajen Da kikaje kikaga an rubuta MD to mallakinsa ne wajen Shopping mall ko da park_park babu jahar da baya dasu a wannan k'asar tamu Ga shi ya had'u Iya had'uwa y'an mata da dama karkiga yanda suke rudewa a kansa Kwanaki a labarai da nagani Wata tana shirin kashe kanta saboda iyayenta zasu aura mata wani Dan uwanta shegiyar yarinyar nan wai MD takeson mutumin da baisan da zaman ta ba Mutum ne mai matuk'ar ji da kansa d'an gayu ne na Bugawa a jarida miskili ne na karshe Dan Ance a waje saiya yini baiyiwa mutane magana ba Amma ance yana magana da family dinsa sosai nidai tunda nake bantaba ga dariyar MD ba a hotunan da nake gani nasa Dan bantaba ganinsa ido da ido ba yana da manyan company a Abuja Amma ance mafi yawan harkokinsa a America ya ke yinsu yanzu haka a Chan yake da zama Saidai Naji ance Allah yayiwa mahaifinshi rasuwa shekaruun baya sosai Wanda ake zargin kashesa akayi to
Chapter 13 · 0% Book details