Sashe 76
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biyu akayi mata ba yasanyata bata tuna ba har yanzu allurar bata saketa ba saboda bibbiyu take ganin komai daidai lokacin da Nurse biyu suka shigo suka duba ta kafin a sauya mata daki aka maida ita wani koda su Ammy suka shiga Sannu kawai suke mata bata iya magana ba sai daga musu kai Goge hawaye Asmy tayi taje gefenta ta ce "Sannu sis" Itama gyada mata kai kawai tayi tana lumshe ido Dan kanta duk Juyawa yake "MD ko daga jikin kofa yake kallonta Ammy ce ta ce Ku Aje mata yaran ta gansu gefenta aka aje mata su Kafin Ammy ta ce " Bud'e ido kiga kyautar da Allah yayi maki daughter "a hankali zahra ta bud'e idanunta har lokacin ba komai take gani ba " Kallon Yaran ta dingayi dukda ba Sosai taga fuskarsu ba Amma har a ranta sosai taji k'auna da soyayyar yaran na ratsa ta kenan y'an Ukku Ta Haifa kallonsu kawai take Ammy na ganin haka saitayi murmushi ta jima tana kallonsu kafin ta daga hannunta d'ayan dake rik'e da drip Da niyyar ta tab'a na kusan nata Daga tsayen da MD yake ya matso ya ce "Ki bari Mamy drip ne hannunki bayason motsawa" Harararsa kasa kasa Ammy tayi ya sanyashi yin shiru amma har lokacin hankalinshi na Wajenta kallonta Ammy tayi ta ce "Zaki iya" gyada mata kai zahra tayi D'aukar shi tayi Ammy ta Aje mata shi a gefenta a hankali zahra tasa hannu ta zagayosa ta matsesa gefenta tana Kallonshi tana kallon sauran Maman Asmy ce ta ce "karfa ki matse sa zahra" Bazan masa komai ba "ta fad'a kasa kasa " Girgiza kai Ammy tayi ta ce 'Allahsrk d'a da uwa kenan sai ALLAH "Dr ne ya shigo Bayan ya duba ta ya tambayeta Saidai ta gyad'a masa kai Dan maganar nauyinta takeji " Ammy ce ta ce "Dr kamarfa har yanzu bata dawo daidai ba " Eh daman bazata dawo daidai yanzu ba ita hakanma da sauki wasu allurar tana dad'ewa tana daukarsu sosai zakiga har suna wasu maganganu kamar marassa kai da ta ido biyu ce akayi mata zata tashi normal amma itama zuwa gobe zata dawo normal please a barta ita da mutum d'aya Ta samu Hutu sosai "Ammy tace zata zauna da zahra sauran duk su koma gida dukda maman Asmy taso zama Wajenta MD ma yaso ace shiya zauna Wajenta Dan hankalinshi yanzu yana ga samun Lafiyarta Ga damuwarshi na abunda za Aba yaran Dan sun fara kuka Sosai Ammy ta kula da Zahra da Yaran tamkar kwai Bayan ta had'a mata Malta da isashshiyar madara Abu mai ruwa ruwa dai ta dinga bata sannan aka bata maganin da tasha dan asamu abincin yaran yazo sai wajen 8pm aka samu ruwan yazo Ammy ta d'ora mata su ta dinga feeding d'insu dukda taji zafi da kunyar ammy haka dai ta daure saboda k'aunar yaran da takeji ta musamman washegari zahra ta dawo normal ta dawo hayyacinta har tana iya zaunawa a danyi Hira da ita dukda nauyin Ammy da maman su Asmy da takeji MD ko ko kallo bai isheta ba Koda yayi mata ya jiki a takaice ta amsa masa da yawwa Wanda baijin dadin hakan ba Ganin yawan matan a d'akin yasanya suka fita shida Jabir shi kanshi Jabir ya girgiza da jin zahra tripplet ta Haifa Sai sannan MD hankalinshi yadan kwanta ganin jikin zahra da sauki sai sannan ya fara tashi sayayyarsa Wanda ba iya yaran yakeyiwa ba hada Momynsu Hajiya ma ranar tazo zo kuga murna da doki Da farinciki Saidai tayi mamakin da ba Amera ta gani ba Koda ta tambayi Ammy ya haka ce Mata tayi kiyi hakuri Hajiya idan muka koma gida za ayi miki bayani su Asmy da mamansu kullum sai sunzo sai yamma suke tafiya Funtua sosai aikin na zahra yayi kyau a kwana na hud'u aka sallamesu suka koma gida Inda Ammy ta ninka kulawar da take mata kafin kace me labarin haihuwar Tripple. D'in MD ya baza gari har internet sosai abokan arziki suke kiransa abokanan kasuwansa dama manya suna kiransa suna masa Barka har gajiya yake da d'aukar wayar wasu daga cikin y'an uwan Ammy ma.dake.india duk sunzo banda y'an uwan Abban su MD na Maiduguri suma sosai suka taho kwansu da kwalkwatarsu ranar daga Ammy sai Hajiya ta labartawa mata abunda MD yayi Dan shaida har videon d'aurin Auren ta nuna mata "Maimakon Ammy taga Hajiya ta daga hankalinta saitaga ta sauke ajiyar zuciya ta ce " na godewa Allah da ba a hanyar banza akayi cikin ba daura Aure sukayi dukda ba Abi shara'a ba Amma Naji dad'in ma da Ba wacce y'ar iskar ya haihu da ita ba yarinyar mutunci mai tarbiya da nutsuwa ta haifa masa kuma insha Allahu zahra saita zama tauraruwar mustapha saita kwacesa daga hannun waccen yar iskar yar marassa tarbiya da izinin ubangiji saiya so zahra ya kaunaceta tamkar ransa"Girgiza kai kawai Ammy tayi a ranta ta ce " hakan ta faru da nafi kowa farimciki "kafin ta ce " Ni yanzu damuwata Hajiya bansan me zancewa mutane ba"Barni dasu ni nasan me zance musu zance matarsa ce Zuwan da nayi na aura masa jikar Aminiya ta akwai ubanda ya isa ya ce Ba haka ba "Ajiyar zuciya Ammy ta sauke ta ce Hakane " Haka ko suka fad'awa mutane wanda ba Wanda bai yarda da hakan ba Saidai suce ba a gayyacesu bikin ba Nanfa aka fara shirin yin suna Wanda sosai MD yake rawar kafa ganin mutane sun fara yawa gashi baya samun damar ganin Zahra saboda d'akinta Ammy ta sauketa take kula da ita saboda d'inkin ta Saida ya kira Chuchu ta d'auko masa yaran idan ya gama liliyarsu ya bata ta koma dasu sosai yakeson ganin ,Zahra amma ba dama dinkuna masu kyau Chuchu da Zey suka kaiwa zahra kala"_kala tamkar Lefe kowa dai sai yaba amayar ta MD yake a yanda Ammy tayi musu bayani Asmy ko nan ta dawo take kwana Saboda kula da aminiyarta mamansu ma kullum sai sunzo Dukda sanyin da zahra tayi ana jibi suna Bayan MD yazo part dinsa na gidan yake sauka daman saboda mutane Chuchu Ya kira lokacin tana gefen Ammy dake bawa Babyn ruwa Ya ce "Ki kawo mun triple yanzu " To yaya gani nan"Ammy dake jinsu ta ce "Kice masa Bazaiyi musu hud'u ba " Daga bangaren MD yanajinta ya ce "Kice Hudubar ce zanyi musu" Kallon Ammy tayi ta ce "Yace hud'ubar ce zaiyi musu" Mika mata shi Ammy tayi ta ce "Saiki kai masa su" Zahra ko tanaji tasan da Wanda ake waya daga kwanciyar da tayi ta rumtse ido Tanajin wani iri a ranta rukayya ta dauki d'aya Chuchu ta rik'e biyu koda suka isa part dinsa Gaisheshi sukayi Tare da mik'a masa su "Kamar ko yaushe saida yayi musu addua Sannan yadanyi musu wasa kamar wasu manya Kallon su Chuchu dake shirin fita yayi ya ce " Ku jira ku koma dasu "Dawowa sukayi suka zaune sunzaci y'an mintuna ne amma saida suka kusan shafar awa suna jiransa ga ba damar su tafi saida ya gama liliyar yaranshi ji yake kamar kar atafi dasu Bayan yayi musu Huduba sai sannan ya ce " Zoku tafi da su "Cikin Sauri Chuchu taje ta amshe Su tana Dariya ta ce " Yaya me ka sanya Musu "Namijin d'aya fara mik'a mata ya ce " Yusuf"Sannan ya mik'a mata dayan ya ce "Shi kuma sunan Abba" Macen ya mik'awa Ruqayya ya ce "ita kuma Ammy" Wow Chuchu ta fad'a ta ce "Aiko yaya Harnayi musu nickname " Akhbar,Amar,Ammy kuma little zahra"Murmushi yayi mata ya ce "sunan yayi chuchun yaya Amma takwarar Ammy a sauya bazanso a dinga kiranta da sunan haka ba " hakane yaya Amma ai kaga Ammy ba zahra ake ce mata ba Fatima ake Ce mata"baice komai ba sai lalubo wayarsa da yayi ya ce "Zan miki transfer 10 millions "Kafin jibi ki shirya kayan da za a bawa bak'i jakunkuna, calendar, Turamen atamfofi super Holland da duk abunda kikaga za a raba karki sake ayi harkar karanta kafin gobe komai yazo sannan Jabir yayi wasu jakunkunan anjima zai kawo miki tare da wayoyin da nayi order daga compony duka a sanya a jakar rabon ki tabbatar komai ya tafi successful idan kudinma basu isaba kiyimun waya zanmuku transfer wasu " insha Allah yaya komai zaitafi yanda ake.so"Ajiyar zuciya ya sauke tare da Danna mata transfer Take suka shigo wayar Chuchu koda suka koma Ammy ta tambayesu ta ce "Me.Ya sanya musu" Cikin doki Chuchu ta ce "Ammy baby girl din takwararki ce kuma takwarar momcy Baby boys din kuma wannan Yusuf (Akhbar) wannan kuma Takwaran Abba (Amar)Murmushi Ammy tayi ta ce " masha Allah Ubangiji ya raya "Zahra tana daga kwance kamar tana bacci sosai tayi mamakin karar da yayi mata na sanya sunan mahaifinta tunowa da Baba da tayi ko yana wani hali yanzu ya sanyata Goge hawaye Wurinta Chuchu tayi ta ce " Tashi momcy kinji sunan yaran yayi ko "Bud'e ido tayi a hankali tare da sakar mata murmushi Dan bazata iya magana akan yaran gaban Ammy ba Sai gyada mata kai tayi alamar sunan yayi Ranar suna tunda safe aka yanka gardama gardaman shanaye Guda goma.reras raguna shidda Wanda naman shanayen.duk sadaka aka babbada gidajen marayu da gajiyayyu Sosai MD.ya taka rawar gani a wannan sunan y'an uwan Shima haka uwa uba Ammy data k'asa zaune ta kasa tsaye zahra ko duk yanda bataso tayi kwalliya ba saida Chuchu ta sanyata tun safe take sauyin.latsa latsan kaya hoto ne dai dak'yal ta yarda akayi mata tare da Yaran sannan akayi mata da Ammy da kuma Chuchu da Asmy dukda a sanyaye take saboda sosai taron mutanen ya bata mamaki Sosaifa aka shiga shagali da fidda abinci da baza Naira a bikin triplet gidan Ammy duk Inda ka hanga cike yake da mutane Wasu ma basu sansu ba haka suke zuwa Dan aci banza" Kaji ko yanda kasan Tuwo haka aka maidashi a gidan duk Wanda yaje sunan nanfa tofa ya shaida Sunzo gidan kudi sunzo Inda ba a tausayin naira Duba ga irin Abubuwan da aka rarrabama kansu ya isa mutum girgiza K'atuwar jika mai d'auke da