Sashe 77
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hotunan yaran da sunansu cikinta galleliya Atamfa Holland banda Callender sai Tab d'in yara a ciki Kirar Iphone wacce kudinta ma saiya girgiza mai karatu mutane ganin amfara basu wannan Abun duniyar nanfa aka rude Wasu Dasun fito suke kiran y'an uwansu akan suzo kar ayi basu Babu alamar karewar kayan rabo saboda daman masu uban yawa akayi Chuchu itace gaba gaba kan rabo ita da Asmy duk anshiga busy ga ba ruwansu da wai sai Wanda suka sani Kowa bashi ake saboda ranar farinciki ce acewarsu duk Wanda yazo murna yazo tayasu hakan yasama suka sanya security barin kowa ya shiga amma fa sai anyiwa mutane bincike kafin Su shiga saboda karsu shiga da mugun Abu Chan na Hango *Auren wata tara*Fans Gungunsu guda Ni kaina nayi mamakin Ganin irin yawan sunfi a kirga Wanda ba ma zan iya kiran sunan su ba chan na hango khadyn sp ana yagar cinyar kaza Rachel ko ina kallonta tana zuba wasu kajin a ledar da tataho da ita su ummu suhaif sai washe baki ake banza ta samu,su halimatu ko an sha goggoro yanda kasan itace chuchu su fatima sai zazzakewa ake tana sune kirjin biki sunan ammy da amarya zahra gareta yan uwansu ne ai,chan na hango quen faridat suna fada da wata tana cewa zata sa security su fitar da ita batasan yanda suke da md ba to cousine brother dinta ne nikam hajjo ina rike da takarda da alkalami nace zu 'i,su tsohuwa maman Siddiqa sai shafce zufa ake,su aisha,zainab oum ibisam ,jikalle ruky ,rahama ,maman nana,su nafisa kai sauran bazasu fadu ba wollah anyi kara Maman Khairat ita ce gaba Wajen yi musu jagora Akan suma suje su Amso nasu kason raba su gida hud'u tayi ta ce"Kunga ku bari mu kasu hud'u karsu ganmu gayya guda suce daman kayan suka kawomun kashi d'aya mu fara shiga kafin Sauran tunda Kunga munyi yawa "Ummu shugaba ce tayi k'araf ta ce " Wlh bazaiyu ba maman khairat kawai mu shiga gaba d'aya sanadin wanda suka fara shiga su su samu kawai mu mu rasa wlh bazaiyu ba "Ganin suna shirin yin sama ya sanya maman khairat cewa to shikenan muje mu Duka din Tunda bakusan ayi Harkar da baza a raina mu ba dukansu suka runkuta suka shiga kowa ya fito zaka kalli fuskarsa cike da farinciki sai wage baki suke kowa sai murna yake banda Sherston ghayu da ta fito hawaye jabe jabe da fuskarta wai bata samu rabo ba sosai na tausaya mata ganin yanda take kuka cikin bila'adadin mutane ita kadai ta rasa Allah sarki maman ummy da tausayi cewa tayi Dan Allah mu hada mata ko wani Dan abun ne a bata ,mutanen namu najin haka aka fara sassanfewa chan na hango lolos ta maida nata cikin hijab ta dukunkuneta ,mom shukurama cewa tayi tofa mu ma'assalam dadyn shukura yayi kira ,ummu suhaif da ummu rafi a sukace jiramu muma sun kira bansan yanda yan auren wata tara fans suka wansheba saboda barin wajen da nayi na kutsa ciki chan na hango zahra tasha tsadadden lace da yayi mata mugun kyau yanda kasan matar president Tripple dinta ko sunsha kyau cikin tsatsadan kayansu zey ta kasa ta tsare akan yaran ba a daukarsu kar a jagular su ganin Zahra a matukar gajiye take ga cs dinta da bata warke ba ga kaya masu nauyi da ta sanya ya sanya Ammy da itama tasha kyau kama hannunta ta kaita wani part din ac ta kunnawa dakin bayan ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya kan gado ta kwanta daman gajiye take saida ammy taga bacci ya dauketa tukwana ta fita bayan ta rufe mata dakin taro ya tashi lafiya cikin girma da dattako anyi Abu na bajinta da nuna sa a md ma lunch suka shirya hatta abokanan kasuwancin shi na kasashe saida sukazo wajen lunch dinma haduwar da yayi bata baki ne iya maza kadae akayi anci ansha kafin dare ma labarin sunan triplet din,md sun baza duniya sakamakon yan jarida da suka ziyarci wajen event din da wajen sunan kuma md ba boyayya mutum bane da dare abban amira yaga bikin sunan a news cikin tsananin mamaki yacewa matarsa me nake gani haka hajiya itama tana mamaki ta ce "nima abunda na gani md yana da wata matar ne daman bayan amira"cikin tsananin tashin hankali ya dannawa amira kira a layin ta na chan kasar lokacin amira na bacci ringing din wayar ya tasheta cikin muryar bacci ta ce"hello dad cikin tashin hankali ya ce "Kina ina daughter labarin Me nake gani wai an haifawa mijinki triple yaushe kika haihu mu bamu sani ba"a rude amera ta mike ta ce "what daddy daman jita-jitar nan gaskiya ce tun last week friends dina ke kirana sunamun barka daga karshe har kashe wayata nayi nama dauki abun a rainin wayau Innalillahi wa inna ilaihiraji'un wai meke faruwa shima honey din nayi ta kiransa baya dagawa"kome kike ki maza ki dawo kasar nan akwai gagarumar matsala "cikin tashin hankali ta ce "To dad ganinam"a take ta ,Mike ko bag dinta bata tsaya dauka na passpord da wayarta kawai ta dauka ta fito kai tsaye Airport ta nufa hankali tashe zuciyarta chunkushe da tunani kala^kala ba bata lokaci tayi clearing din komai a daren jirginsu ya d'aga daga London zuwa Nigeria......... *domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Misa Hajo ce*_ .........*85 & 86* Amera koda isarta jikin dadynta ta fad'a ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah dad ku fad'amun me yake faruwa bansan abunda ya faru ba hankali na bai kwanta ba " Lallashinta ya dingayi akan ta nutsu ba komai bane ta Bari ayi bincikike tukwana washegari dak'yal ta Bari gari ya waye ba yanda Mamanta batayi.da ita ba akan ta Bari a bincika aji gaskiyar Lamarin ta kiya ta ce "saitaje gidan Ammy tunda shi tayi ta kiransa kusan 1 week baya dagawa abunda baitab'a yi mata ba " girgiza kai mamanta tayi ta ce 'Ai daman Amer a na fad'a maki tun ba yanzu ba akan ki tsaya kiyi zaman Aure kwata kwata rayuwar da kika zab'awa kanki ba rayuwar y'a mace mai mutunci bace"da Allah mom Ni kibarni Naji da abunda ke damu na fisabilillahi"ta fad'a tana yin gaba tana gunguni "Girgiza kai Hajiya Farida tayi ta ce "Allah ya kyauta"Dadynta ko zirga zirga kawai yake...k'arfe 7:am zaune suke a palourn Dagashi sai Ammy Bayan kiran gaggawa da tayi masa shiru yayi ya maida hankalinshi ga sauraron abunda take son fad'a masa fuska ba wasa Ammy ta ce " d'ago ka.kalleni babana"ba shiri ya d'ago yana fuskantar mahaifiyar tasa "Hannu Ammy ta mik'a masa ta ce " bani takardar Saki ukkun zahra "Lokaci guda MD yaji wani irin tashin hankali ya ziyarce sa a matuk'ar rude ya ce"Ammy saki kuma" Eh saki ko kana da wata maganar ne daman ba Dan ka saketa ka aureta ba,ba Dan ta Haifa maka d'a ko y'a ka aureta ba to ai burinka ya cika ta Haifa maka yara har Ukku kaga ko amfaninta a wajenka ya k'are dan haka ka saketa ta kama gabanta itama taje tayi Aurenta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa "Cikin tsananin tashin hankali ya ce "Ammy kiyi hakuri kibar maganar nan please ni har yanzu Mamy matsayin mata ta take kuma haka zataci gaba da zama insha Allah please Ammy kiyi hakuri kawai ki barmun matata kodan yaran nan Ammy kinsan d'an sai uwa please Ammy ina begging d'inki kidaina maganar sakin nan ba Ni Gaskiya bazan iya sakin Uwar y'ay'a na ba" ya fad'a kai tsaye "Sakato Ammy tayi tana kallon ikon Allah kafin ta tab'a hannu ta ce " ikon Allah daman Kasan da ruk'on d'a sai uwa ka shirya rabata da Y'ay'anta ka kaiwa Matarka Matar so da.kafi sonta da kowa inbanda asirinku ya tonu to wlh baka isa ba saika saketa"Hankali tashe ya d'ago ya ce "Ammy Dan girman Allah ki daina maganar sakin nan nifa bazan saketa ba period magana Zan zauna da ita na bata kulawa kodan yaranta Dan Allah Ammy naci darajan yaran nan"baka isa ba wlh watau nufinka Zama ka zauna da ita zaman Y'ay'anta lallai Babana kai harka isa ka zauna da zahra zaman Y'ay'anta zahra harta isa tayi zaman ,y'ay'a to bazata zauna dakai ba sannan zata baka Y'ay'anka kaje ka kaiwa duk ubanda zaka kaiwa ka kaiwa Amera uwarka ko iyayenta su rik'e maka y'ay'an amma.koni bazan rik'e maka su ba Tunda baka da mutunci sannan zahrar ma bazata rik'e maka su ba bari naje na D'auko maka su sannan na k'ara ganin k'afarka a gidannan Zakaga mamakin irin Rashin mutuncin dazan maka tunda Haihuwarka nayi bakai ka haifeni ba " ta fad'a a fusace tana Mikewa"Cikin sauri ya yi Sauri ya riko k'afar zanen Ammy Ya ce "Baki fahimce ni bane.Ammy Dan...bai k'arasa abunda yake son fad'a ba ta fusge zanenta cikin Sauri ta haura sama " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ya fad'a yana dafe goshinshi Daidai shigowar Amera d'akin a matuk'ar rikice "kallonta yayi yanda tashigo da itama d'in shi take kallo kafin ta karaso palourn cikin tsananin tashin hankali ta fashe da kuka tare da kama.hannunshi ta ce " Ka fad'amun Gaskiya MD me yake.faruwa Wasu Yara ne ake zancen an Haifa maka Bayan Banida masaniya ka fad'amun gaskiyar cewar bakai bane wasune kawai suke.karya da yaranka ne"Ba karya bace Yaransa ne halak malak Shiya haifesu da Matarsa da ya aura kina Chan kina yawon tambadewa a jirgi harta haihu baki saniba ta Haifa masa Yara Ukku reras lokaci guda ko kina da abun