← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 92

Sashe 57

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake yiwa Zarah Hira kin sakin jiki tayi dashi Ganin hakan yasa ya tafi saita d'auka ko kunyarsa ce takeji Dan ya Santa akwai kunya Koda ta shiga gidansu Asmy Bayan ta gaishe da mamansu nan ta zaunar da ita ta fara bata magunguna Wanda tunda ta bata Zarah ta fahimci na meye ba ason ranta ba ta fara sha sai Dan batason yi mata musu Bayan nan ta d'ora tayi mata dilka ta amare sosai ita kanta tayi mamakin karuwar sanyin na Zarah Saita lak'anta hakan da Bikinta dake karasowa tundaga ranar kullum Zarah tana gidan su Asmy mamansu tana yi mata Dilka da magungunan gyara bangaren Mama Rabi ko Sosai Zarah tayi mamakin yanzu wani mutunci da take mata ba zagi ba komai har tana mata maganar shirye shiryen biki itama ta bata invitation tayi tata gayyatar ranar Zarah sossai mamaki ya cika ta Nan ta d'auko invitation din da chungum din da ya kawo mata daga baya ta bata tana mamakin wannan saukowar mutuncin na Mama Rabi na lokaci guda bangaren Baba ma sosai yayi mamakin yanda take nan nan da bikin kamar za ayi bikin diyarta a tunaninshi Zatayi bakin cikin kayan d'akin da akayiwa Zarah saiyaga itace mai cewa ma a k'ara wani abun ayi Abu na fita kunya sosai a ransa yaji dadin sauyawar tata har yana murnar kila yanxu ta sauya hali. <Abuja> Kallo d'aya zakayi masa ka lura yana cikin tsananin damuwa har wata rama yayi idonshi lumshe kamar mai bacci nanko tunani ne chunkushe a ransa Ya Lula duniyar tunani yaji wayarsa tayi ringing saida tagama ringing bai daga ba wani kiran ya k'ara shigowa kamar bazai duba ba saikuma ya janyo wayar a hankali tare da Kallon screen din wayar Ganin number Ammy ce ya sanyashi saurin picking a sanyaye ya gaishe ta ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da cewa "kana ina?Ina Abuja " Okay to kazo Hajiya na nemanka "yana kwance baisan lokacin ya Mike zaune ba a matuk'ar makance ya ce " Hajiya kuma Ammy tazo garin ne?Eh tazo tun jiya kuma tace kome kake karka wuce gobe bakazoba"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un "ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa Ammy bata jira amsarsaba ta kashe wayarsa dafe kansa dake tsananin sara masa yayi ya ce " Oh my god"Ya Hajiya takeso nayi da rayuwata ne Wai,dalilinta na shiga halin da nake ciki yanzu kuma ta k'ara zuwa ta k'ara jagula lissafi cikin Sauri ya lalubo number Amera ringing biyu ta d'auka "bai saurari abunda take cewa ba ya ce " kome kike kiyi gaggawar dawowa gida kafin nan kafin 12:na ranar gobe "Daga bangaren Amera ta ce " Subhanalla honey lafiya"Lafiya nadai fad'a maki ki baro k'asar nan "Saboda me honey wlh gobe ake fara bikin Chichilayo" MD ji yayi kamar ya shak'eta da wayar baisan lokacin da yace "uwar bikin chichilayo Dan Iskanci ina Miki maganar Serious zaki sakomun maganar wata tsinanniyar arniya ki zauna karkizo ki saurari abunda zai faru kishiyar da bakiso ita zaki tarar"Daga bangaren Amera wani irin bugawar zuciya taji batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Ta ce " nashiga Ukku ni Sadiya me kake nufi honey bangane yaren naka ba "Tsaki yaja ya ce " ki sameni a Abuja gidana Dake life camp buzu quarters Hajiya tazo kuma kinfi kowa sanin zuwanta"yana gama fad'ar haka ya katse kiran yana jan tsaki Sosai yakejin haushin kansa da na kowama yanzu ta ina zan nemo yarinyar nan?ya tambayi kansa "lumshe ido yana tuno da Dadin yarinyar lokaci guda mood dinsa ya sauya dak'yal ya iya hada ruwan tea tare da matsa lemon tsami kusan goma Dan tun Bayan rabuwarsa da ita kullum saiya sha sa yake iya samun bacci ga tunaninta da yaki barin kwalwarsa daidai da second guda washegari tun karfe shida na safe MD yaji bugawar part din da yake tundaga bedroom dinsa yajiyo saboda wani irin knoking da ake da karfi jallabiyarsa ya zura tare da fitowa palourn yana bud'ewa yaci karo da Amera kallo d'aya yayi mata yasan a matuk'ar firgice take ga idanunta da sukayi ja jawur Fadowa jikinshi tayi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsananin gaske sosai take kuka kamar ranta zai fita Wanda MD Jin kuka nata yake har cikin ransa sosai ya tausaya mata wannan nadaga cikin abunda yasa ake ganin kamar Amera ta gama dashi Bayason ganinta cikin wannan halin hakan yasa ko maganar Karin Aure bayaso Daddab'a bayanta yafara cikin sigar lallashi Dak'yal ya samu har suka k'arasa palourn Inda ya zaunar da ita Cikin kuka ta ce " Honey karkaga tashin hankalin Dana shiga ban iya bacci ba Jiya da Daren da ka kirani na tafi Airport Sai 1am jirginmu ya tashi dak'yal na iya kawo kaina nan honey mutuwa zanyi a kanka "Numfashi mai zafi MD ya fesar kafin ya d'ago ya Kalleta ya ce " kibar kukan nan bashi da amfani kalleni muyi magana ta fahimta "Cikin Sauri ta Goge hawayen tace ina sauraranka honey" Hajiya ce tazo kuma take nema na kinsan zancenta bai wuce na Rashin haihuwar da banayi akan na k'ara Aure to shine nake son mu samawa Kanmu mafita tun kafin Abu yazo yafi karfinmu kinsan halin Hajiya sarai"ya nemu ya biye mata maganar ta ta baya Dan karta k'ara shiga tashin hankali "Dukda haka saida hankalinta ya tashi cikin kuka ta ce " to yaya zamuyi Honey ina mafita Bansan yanda zamuyi da ita ba ni kaina na k'agara naga jini na Ina son haihuwar nan fiye da yanda baka zato honey Allah ne bai bani ba "ta k'arasa fad'a cikin kuka " cikin sigar lallashi ya ce "Akwai mafita" Firgit ta d'ago ta Kallesa ta ce "Wace mafita ce Honey" Zamu cewa Hajiya kina da ciki zamuje tare yanzu kiyi pretending din ciwo akwai maganin da zakisha Zai sanyaki amai Dan duk su tabbatar da abun kafin mu nemu mafita"cikin tsananin mamaki ta ce "Idanfa suka gane honey nan gaba Bayan munsan ba cikin garan ba" Ajiyar zuciyaya ya sauke yace kibarmun sauran abunda nakeson kiyi yanzu kenan kawai"Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Shikenan honey zanyi hakan Allah yasama na samu cikin gasken kafin Su gane" Murmushi ya sakar mata ya ce "Ameeen My Merah" k'arfe 11am tayi musu a Palourn Ammy a lokacin kowa na palourn har Hajiya Har Aunty Zey da tazo Bayan an gaggaisa Amera ma wannan Karin cikin ladabi ta gaishe da su Hartana tambayar Zey ina su Mema Zey Ta ce "suna gidan kakarsu sunje mata yini" masha Allah na kwana biyu bangansu ba ai da sun yarda da sunyi mana Hutu muma"Murmushi zey tayi ta ce "Aikam dai" Chuchu ta k'asar ido take Hararar Amera a ranta ta ce "munafuka batayi mamakin yanda ta gaisa da zey ba saboda daman Chan ita Zey kamewa gareta har mutane suna cewa duk gidansu itace mai girman kai hakan yasa Amera ke shakkarta Dan tasan halinta ba shiga harkar mutane take ba Amma aka shiga tata akwai masifa " Ammy ce ta ce "Chuchu ki kawowa Amera abun Tabawa mana ga Alamun sunshawo hanya" Badan Chuchu ta so ba ta tashi tare da dauko mata juice ta koma Inda take tana Danna waya A cup Amera ta zuba ta fara sha tana cikin sha taji maganin da MD ya bata a mota ya taso mata cikin Sauri ta Aje cup din tare da yamutsa fuska "Ammy ce dake lura da ita ta ce " Lafiya dai ko?Tana yamutsa fuska tace "Naji Inajin amai....bata k'arasa fad'a ba Taji ya tunkaro mata da gudu ta Riga toilet din palourn nan ta fara kakarin amai harta samu ta danyi Kad'an Duka mutanen dake cikin palourn da Kallon mamaki suka bita Hajiya ta ce " Ikon Allah itafa wannan aman me take"Shiru MD yayi ya kyale ta "Har Amera ta fito daga toilet din tana Murmurdewa irin anji jikin nan cike da kulawa Ammy ta ce " Sannu yaushe kika fara irin haka?nafi sati biyu ina yi amma kwanannan yafi matsamun?kuma kunje Asibiti "?girgiza kai tayi ta ce " a a a Ammy bamuje ba"Hajiya ce ta ce "Kinji sakarkaru abunda ake nema shekara da shekaru ya samu shine zaku watsar kunjimun Sakarkarun yara kai kasan da haka shine baka sanar mana tun wuri ba " MD yasan sarai da shi Hajiya take ya kauda kai yana maida Kallonshi ga television "kaji da mugun halinka dai Hajiya ta fad'a tare da Kallon Amera ta ce " Sannu ko bari a kira likita ya duba ki "Murmushin jin dadi Amera tayi ta kwanta kan doguwar sopa tana maida numfashin karya Kallon Ammy Hajiya tayi ta ce " Fatima kirayo likita yazo ya duba yarinyar nan Allah sa abun alkhairi da muka jima muna jira ne ya samu"Murmushi Ammy tayi ta ce "To Hajiya " Nan Ammy ta kira Family Dr d'insu Akan tanason ganinshi zai duba patient "Har lokacin MD hankalinsa gabak'i baya ga y'an d'akin Har Dr yazo Wanda gaisawa kawai sukayi da MD ya shigo Inda Hajiya tayi masa bayanin gwajin da zaiwa Amera nan ya shiga gwadata Inda ya dauki jininta da awon fitsari yaje baima bar gidan ba ya tsaya a mota Bayan few minutes ya dawo rik'e da paper da murmushi a fuskarsa Hajiya na ganin haka ta washe baki ta ce " Kardai kace mun ciki ne Dr "Da fara a a fuskar Dr ya ce"Tana dauke da cikin Wata Biyu " Ai gudar da sukaji Hajiya ta rangadane ya kawo kowa ya maida hankalinta Wajenta "Alhmdll Alhmdllh Allah nagode maka ranar da nadade ina jira gashi tazo da raina da rayuwa kai amma yau rana ce da bazan tab'a mancewa da ita ba a rayuwa ashe da rabon zanga jinin Mustapha a rayuwa kai Allah na gode Maka " sosai Hajiya ta shiga sabbatunta na murna Ammy ma ita kadai tasan farincikin da ta shiga haka su Chuchu da Zey MD ta ido yayiwa Dr d'in jinjina Irin aikinsa yayi kyau murmushi dr yayi masa "Hajiya ce ta kalli MD da babu Alamun yayi farinciki da abunda aka fad'a ta ce " Ikon kaji mai mugun hali ayi maka wannan Babban Albishir da muka dad'e muna jira ka zauna haka sototo
Chapter 57 · 0% Book details