Sashe 37
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zame mata jiki duk sanda tazo mata ta ce "Nifa ba da kai nake ba " ta k'arasa fad'a hawaye na sauka daga idanunta "Had'iye kukan ya fad'a yana kama hannunta " kamar an d'auke nefa haka ta Had'iye kukan shi kanshi har Dariya taso ta bashi ya fusge "harsuka isa katafaran palourn gaban Zarah na fad'uwa saida ta kusa kauyanci cin karo da hadaddun turkey furnitures d'in da suke shake a palourn komai na palourn y'an waje ne bazaka tab'a cewa a Nigeria kake ba "a rakube ta zauna d'aya daga cikin kujerun palourn tana ta kalle_kalle a wayance Wanda bazaka tab'a cewa tanayi ba a ranta ta ce " Wasu na cikin wahala wasu bama susan anayi ba jifa Dan Allah wannan lafcecen gida da kayan cikinsa kamar baza a mutu ba "zaki iya tashi kije kiyi salla kafin na dawo ga bedroom Chan" ta tsinkayi muryarshi data dawo da ita daga duniyar tunanin da ta Lula Firgit ta Kalleshi kamar mai shirin fashewa da kuka ta ce "Amma kuma ni kad'ai zaka bari a gidan nan ni tsoro nakeji wlh karnikan nan karsu shigo Su cinyeni ni kadai" murmushin da baikai fuska ba yayi ya ce "bazan jima ba zandawo babu abunda zasu maki bazasu shigo nan ba " Badan taso ba ta ce "To Amma karka jima Dan Allah " Ba tare da ya amsa ta ba yayi Hanyar waje tanajin fitarshi ta turo baki tare bin kofar da harara ta ce "Mugu Allah saiya sakamun ta fad'a tana nufar d'akin da ya nuna mata Dan tayi salla Nanma saida tayi kauyanci cin karo da kayan alatun dake dakin ga gaban mirror din dake shake da kayan shafa irir_iri tab'e baki tayi cikin Sauri ta shiga toilet tayi alwala ta fito Bayan ta tada salla cikin Sauri ta bar d'akin Dan ji take a tsorace take palourn ta dawo ta zauna Kan kujera tare da Yin tagumi sai Bayan isha i Taji tsayuwar mota lek'awa tayi ta window taga shine cikin Sauri ta koma ta zauna harya shigo Mikewa tayi ta ce " yawwa nazo mu tafi ya Musty?Batare da ya Kalleta ba ya ce "Sai gobe " yana gama fad'ar haka ya Aje take away din da ya shigo dashi tare da Yin hanyar dayan bedroom d'in da Kallo ta bishi har ya wuce Tana turo baki ta daga wayata da Asmy ke kira daga bangaren Asmy ta ce "Wai kina ina harna dawo tun d'azu " Ina kd "ta fad'a kasa kasa" Kd kuma to me ya zaunar dake "Ya ce sai gobe " ta fad'a tana shirin fashewa da kuka "Daga bangaren Asmy tayi Dariya " Au cewa zakiyi Amarci za a sha keda Angon naki"Dogon tsaki Zarah taja cike da jin Haushi ta ce "Banza y'ar iska Allah kiyaye wannan ya zama mijina " kit ta kashe wayar tana Jan tsuka Daren ranar dai taga MD baida shirin maida ita gashi tunda ya shiga bai fito ba Bayan tayi Sallar isha I a palourn bacci ya kwasheta cike da gajiya gararanbar da suka sha A waje MD ko daman tuni yayi bacci Dan yau akwai gajiya a tare dashi Dan dawowarshi metting kenan daga Abuja suka had'u dasu Zarah washegari Around 10 Zarah ta shirya tana palour Tana jiran fitowarshi ya fito ya maida ita Cikin tsadaddan shaddarsa ya fito yasha shiga ta alfarma ta manyan mutane kallo d'aya Zarah tayi masa tayi saurin k'asa da kanta saboda gabanta dake fad'uwa sosai taga yayi wani irin masifar kyau a sanyaye ta ce "Ina kwana" muntashi lafiya ya fad'a yana karasowa palourn "Tare da cewa " Kinyi break fast ko?gyada mishi kai tayi "eh " Okay to muje a saukeki "Cikin farinciki Zarah ta d'ago ta ce " Thnks "Dan tayi mamaki dazai maida ita cikin Sauri saikuma ta ce " Naga bakayi break ba fa"Eh bana ra'ayi ya fad'a "Dan azumi yake tab'e baki Zarah tayi tare da mik'ewa ta ce " kai ka sani miskili kawai" a tare suka jera suka fito gwanin sha'awa kamar wasu masoya Dan sosai naga matching d'insu Shigowar Mota ya sanyasu tsayawa bin motar MD yayi da Kallo harta karaso parking space d'in yana kallon motar Kafin yaga fitowar Amera cikin shigar da ta saba ta K'ananan kaya driver yana rik'e da Akwatinta shock a wajen Amera tayi ganin mijinta sun fito tare da wata daga cikin gidan lokaci guda idonta ya rufe wani azababben kishi ya taso mata dak'yal ta iya daidaita numfashinta dake sartse mata cikin bala'i da masifa ta tunkaro Inda suke Wanda har lokacin suma kallonta suke musamman MD da yayi mamakin zuwanta Zarah ko tuni cikinta ya Dori ruwa Ganin yanda take tunkarosu " Tsaye Amera tayi tare da daure k'aramun beil din da ta yafa a kugu ta ce "Yau akwai kutumar bura uba a garin nan kace yau akwai tashin bomb a kaduna wanda zai tashi da uban kowa Wace karuwar y'ar Iskar ce wannan Mustapha ?...... *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ .......*47 & 48* "Na ce Wace y'ar kutumar uban ce wannan Mustapha " Kallonta MD ya tsayayi da mamaki Ganin bazai bata amsa ba Amera ji tayi kamar a mafarki cikin zafin nama tayi kukan kura tare da shako wuyan Zarah cikin wani irin Hargagi ta ce "zakisan kin shiga gona ta Dan kutumar ubanki shegiya y'ar iska karuwa yau saidai uwarki ta haifi wata amma yau d'innan saikin bakunci lahira tunda har kika iya bin mijina bakisan Kallon mijina ma mace batayi bare har na ganku tare Tabbas ajaline ya kawoki gidan nan Dan saidai a fitar da gawarki daga gidan nan billahillazilla'ila illa huwa" iya rudewa Zarah ta rude ga ta kasa kwatar kanta daga shak'ar da Amera tayi mata Cikin b'acin rai MD ya daka mata Tsawa ya ce "Sakarta Amera kafin ranki ya b'aci banason hauka" Cikin kuka da Hargagi Amera ta ce "Wlh saina kasheta " Kokarin kwatar Zarah MD ya fara amma ya kasa saboda cike da zuciya Amera tayi ruko ganin zata illatata Dan harta fara numfaffashi ya sanya MD d'auke Amera da wani irin gigitaccen Mari Wanda ba shiri ta saki Zarah tana dafe kumcinta ta ce "Ni ka Mara Mustapha " An mareki din stupid mahaukaciya da kishi zai haukatar dake kasheta zakiyi ko Me?ka fad'a kome zaka fad'a indai akan wannan ne na shirya wlh kaji na rantse saina kashe tsinanniyar yarinyar nan saidai nima a kasheni munafiki maci amana ashe Fasik'anci kake shiyasa kake tahowa k'asar kak'i waiwayata ashe karuwai kake kawomun har cikin gida wlh da wani ne ya bani labari bani na gani da idona ba zan yarda ba fasiki maci ama....bata k'arasa maganar ba sakamakon Saukar Marin da taji Tass tass har guda Ukku "wani ihu ta buga tare da nuna kanta ta ce " ni ka mara akan wannan karuwar mustapha Aiko zakasan ka mareni ta fad'a tana tunkarar Inda Zarah ta durkushe ta na Maida numfashi sosai kalaman Amera ke dakar mata zuciya ganin tayo Wajenta ne ya sanyata saurin tashi ta boye Bayan MD sai Lokacin ta samu damar fashewa da kuka "Wlh Amera kika k'ara tab'ata zakiga b'acin raina yanda bakiyi tunaniba wai hauka ne kike kome me kike shirin aikatawa saboda kishi ya rufe maki ido" Cikin kuka Amera ta ce "zakaga hauka Mustapha zakasan ka taboni ka jira fitowa ta ta fad'a kamar wata mahaukaciya tare da Yin hanyar Ciki ganin haka ya sanya Zarah rudewa cikin kuka ta ce " Dan Allah ka fitar dani daga gidannan na shiga ukku "MD Yama rasa yanda zanyi Cikin Sauri ya nufi parking space tare da dauko mota Zarah hada tuntub'enta wajen shiga tana shiga sukaga fitowar Amera hannu d'aya da tabarya hannu d'aya kuma lafceciyar wuk'a mai kamar Adda iya rudewa Zarah ta rude Duk Addu'ar da tazo bakinta yi take cikin kuka ta ce " Kayi Sauri karta karaso na shiga ukku ni Fatima Wannan wace irin masifa ce "ta fad'a tana fashewa da kuka da karfi yaja motar Horn D'aya yayi mai gadi ya bud'e masa da gudu Amera ta nufo su tana ihu tabarya da wuk'a a hannunta ta ce " ka bud'e musu get suka Fita wlh a bakin aikinka"lokacin har motarsu ta fita Wata nauyayyar Ajiyar zuciya Zarah ta sauke amma dukda haka gabanta fad'uwa yake MD ko mamaki ne cike a ranshi bai tab'a tunanin haukan kishin Amera yakai haka ba wata irin zufa ce Ke keto masa Har suka isa Zaria cikinsu ba Wanda yace uffan daidai kofar A B U yayi parking Tare da ciro bandir din y'an Dubu dubu ya mik'a Mata girgiza kai tayi har lokacin gabanta fad'uwa yake ta ce "a a nagode " wani irin kallo yayi mata tare da cewa "Bana bada Abu a a mayarmun doka ta ce wannan ki kiyaye kinga damar ki yaddasu ko kiyi sadaka wannan ba damuwata ba ce " Amsa Zarah tayi harzata fita Ya riko hannunta Wand a dukda suna cikin tashin hankali bai hanashi jin shock ba makulli ya damka mata ya ce "Ki kwashe kayanki ki koma Gidana dake nan karna dawo na iske baki koma ba" Tana shirin fashewa da kuka ta ce "Dan Allah karkace saina koma wlh banajin dad'in zaman Chan" Umarni na baki ba shawara ba sannan karki koma kiga Abunda zai faru"hawaye na zuba a idonta ta ce "To taya zan iya zama a wannan gidan ni d'aya wlh ni bazan iya zama ba " wani tunani ne yazo masa kuma hakane bazata iya zama gidan nanba ita daya Dagowa yayi da