← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 92

Sashe 7

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bana nan " Zarah ta fad'a tana yamutsa fuska mamansu Asmy ce ta ce "je kace gata nan" Kallon Zarah tayi ta ce "y'ata jekiga waye ne Ai ba a haka " ",to Mama ta fad'a tare da mik'ewa ta sanya hijab d'inta har k'asa ta fito Rungume da hannayenshi ta sameshi A jikin motarshi kirar corolla L E sanye yake cikin shadda ash Bak'ine amma coculate colour bashi da muni haka bazaka kirashi da kyakyawaba. " k'arasawa wajen Zarah tayi tana jin d'ari_d 'ari Hafiz ko tunda ta fito ya kafeta da idanu ya na k'ara yabawa da zubi da kyan sura uwa uba kyau irin na Zarah dan tunda ya ganta a wajen safka ya kwallafa rai a kanta. Dan lokacin da suka haduma arashi akayi yaje unguwar wajen wani abokinshi Hakan yasa ya bi mai napep din Har ya gano gidansu Zarah Inda ya nemu information a kanta kuma ya samu bayanin komai a kanta. tundaga tarihinta da irin wahalar da take sha sosai ya tausaya mata hakan ya k'ara sawa yaji soyayyarta a ranshi. "Da fara'arshi yayi mata sallama tare da cewa "fatan na sameki lafiya sarauniyar mata " Batasan lokacin da murmushi yazo mata ba ta ce "wa'alaikumussalam yaushe na samu wannan mukami haka Ba nad'i ba komai a nadani har sarauniyar mata anma bansaniba wannan mukamin ai sai manya ". ai kin fi ma a kiraki da sarauniyar mata saboda ked'in ta musamman ce a cikin mata"K'asa da kanta zarah tayi ta na wasa da zoben hannunta. "Da farko dai su na na Hafiz ma'aruf Mahaifina tsohon Dan kasuwane kuma.manomi a wannan garin namu nine Third thild d'insa A yanzu na kammala Degree d'ina a Umyuk Inda yanzu ina shirin jonawa masters wannan shine takaitaccen tarihina" "Tsaki Zarah taja a ranta ta ce " ji shegen surutu kowa ya tambayesa a fili kuwa cewa tayi"masha Allah Nice to meet uh". gyaran murya Hafiz yayi ya ce "da farko dai tun ranar da na fara ganinki Naji kin tafi da imani na kuma ina sonki so na aure inason ki zama uwar y'ay'ana duba da tarbiyarki,hankalinki da nutsuwarki a Gaskiya Zarah ki godewa Allah a zamaninnan samun kamarki sai antona Allah yayi miki komai a rayuwa kina da kyau tarbiya ga kuma ilimin addini both side boko da arabi kafin nazo wajenki saida nasan wacece ke ina fatan za amshi tayin soyayya ta" " uhm Zarah kawai tace tare da cewa"Gaskiya zan fad'a maka ka fara zuwa wajen mahaifi na ka nemu izini a wajensa Dan bai bani ikon kula kowaba har sai an nemu izininshi sannan nagode da soyayya" "ta na gama fad'ar haka ta juya ta shiga gida Dan ta tsani namiji mai yawan surutu . " Hafiz ko yaji dadi a ranshi tunda da kanta ta ce yabi ta iyayenta hakan ba k'aramar dama ce ta sameshi ba". "Zarah na komawa gida Nan Tabawa Asmy labarin yanda sukayi ta na Jan tsaki " Dariya asmy tayi mata ta ce "Uhm nikan banga makusha a wajensa ba wlh daga gani yana da nutsuwa" Harararta Zarah tayi ta ce "Ke wani ganin baki da hankali ma wlh Haba mutum sai shegen surutu ke nifa sanin kankine bansan surutu " . Chab nikam zanso naga mijinki zarah kowa yazo saikince ga aibunshi Asa Nura ma wannan ba Mate d'inki bane amma hakafa kwanaki wani daga katsina yazo wajenki saida kika koreshi Kinga Zarah kiyiwa kanki fad'a ". Kamar yanda ta fad'a masa da daddare yaje ya samu mahaifinta a waje Inda Yayi mashi bayanin abunda ke tafe dashi Malam yaji dadi sosai Dan dukda a dare ne baiga fuskarsa ba kasancewar duhu amma a kalaman yaron yasan yana da nutsuwa". ce masa yayi ba damuwa zai iya fara zuwa Wajenta hakan sosai yayi wa Hafiz dad'i. Washegari Baba saida ya sanya aka masa bincike akan Hafiz kuma aka tabbatar masa da yaro ne mai hankali da nutsuwa hakan yayiwa Baba dadi sosai . Ranar da daddare ya samu Zarah a d'aki Inda ya shiga mata nasiha tare da cewa " Kinga Zarah yaron nan da alamu ya na da hankali kuma na bincika an bani kyakyawan zato a kansa zai dinga zuwa wajenki har Allah yasa ku daidaita kanku kinji" Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce "Bab." shit karkice komai Zarah kice "Allah ya zab'a miki alkhairi Dan ba abunda nake da burin gani a rayuwa da raina sama da aurenki na k'agu naga ranar da zan Aurar dake zarah kema ki huta da wahalar gidannan shi yasa kullum Addua ta da buri na naga ranar Auranki Allah ya baki miji na gari Wanda zai rikemunke da amana" kasa da kanta Zarah tayi Bayan Baba ya fita daga d'akin saida tayi hawaye ita harga Allah Hafiz d'innan bai mata ba Amma yanda taga Baba yana yabonshi kuma ya nuna yanason alakanta dashi dole ta kula shi ko Dan son farincikin mahaifin nata. Soyayyace da shakuwa ta fara shiga tsakanin Zarah da Hafiz Sosai yake nunawa Zarah soyayya da kulawa a nata bangarenma ta fara sabawa dashi saboda mutum ne mai barkwanci kullum yazo sai ya sanyata Dariya hakan yasa ta fara sabawa dashi Saidai duk wata sayayya ko kudi da zai bata bata tab'a amsa ba ba yanda baiyi da itaba amma bata amsar abun hannunshi. ta bangaren Mama Rabi ko bakinciki take da Hafiz d'innan dake zuwa wajen Zarah ba irin Karfar da batayiwa Zarah a wajenshi ba Anma yace Eh yaji ya Gani yana sonta Dan kafin yazo wajen Zarah an bashi labarin Mama Rabi ko ita wacece da samarin da take korarwa Zarah. Washegari Zarah ta tashi da ciwon Mara Wanda hakan ya tabbatar mata da perioud d'inta na kusa sosai hankalinta ya tashi Dan duk wata a darura takeyi saboda tsananin wahalar da take sha cikin Sauri ta sanya hijab d'inta tare da fitowa ta nufi gidan su Asmy Dan bata mance irin sharrin da Mama Rabi take mata ba akan ciwon marar da take akwai lokacin da tace k'ilama cikine aka zubar mata ake mata rufe rufe hakan yasa ta maza ta zame tana zuwa gidansu Asmy Bayan ta gaishe da Mama a daddafe ta shiga d'akin Asmy Inda ta sameta ta na guga kwancewa tayi kan gadon ta na maida numfashi . "Asmy ce ta ce " Lafiya Besty"Gyada mata kai Zarah tayi tana ida kwanciya kan gadon ta ce "Da sauki dai perioud d'ina ne zaizo wlh na farajin ciwon Mara" Cike da tausaya Asmy ta ce "wayyo my Zarah Allah dai ya yaye maki wannan larurar Dan larurace wlh ace duk wata sai ka sha bak'ar azaba hada su suma " . bata Kara cewa komai ba Zarah saboda murdawar da cikinta ke mata ruwan zafi Asmy ta d'auko tare jika tsumma take Dan shafa mata a ciki sannan ta had'a mata tea mai zafi ta bata ta sha ciwon sai gaba yake Inda Zarah duk ta firirice ta fara fita hayyacinta kafin ka Ce me sai amai nan ta fara kwararashi Asmy dai Sannu kawai take mata Bayan ta gyara wajen mamansu Ce ta shigo ta ce. "Lafiya Asma'u" cike da damuwa ta ce "Mama perioud din Zarah ne yazo" cike da kulawa Mama ta ce "wayyo Allah sauwake amshi ki maza ku tafi Asibiti ayi mata allurar ta fad'a tana mik'a mata d'ari biyar amsa tayi tare da kama Zarah dake murkashi . mai napep ta fara tarowa tukwana ta zo ta kamata suka tafi asibitin da suka saba zuwa suna zuwa nurse din tayi mata allura daman ita ke mata duk wata ita kanta tana tausayawa irin wahalar da yarinyar takesha. Sai wajen magriba Zarah ta samu kanta Taji ciwon ya lafa Asmy itake jinyarta kamar kowani lokaci harta gama perioud d'inta. Yau ta na zaune tsakar gidansu ta na sintar gashinta aka Aiko akace ana kiranta " to ta amsa " Mama Rabi na banka mata harara saida ta ida sintar tukwana ta mike tare da sanya Hijab ta fita . " kamar yanda tayi tunani shi d'inne dai murmushi ya sakar mata Itama ta mayar masa da murmushin yak'e sun tab'a Hira sosai kasancewar yamma ce Sai wajen magriba da zai tafi kwalin waya kirar hot10 ya mik'o mata ya ce. "tata ce saboda su dinga waya ko baya nan" nanfa Zarah ta ce bata San wannan zancen ba ba irin yanda baiyi da ita ba akan ta amsa amma takiya saboda bata da sha'awar abun hannun namiji kuma Baba ma yayi mata wannan kashedin Hafiz badan ranshi ya soba ya juya. Zarah na d'akinta ta na karatu taji Asmy ta Banko k'ofar batayi aune ba saiji tayi ta Rungumeta cikin farinciki ta ce "Sis ki tayamu murna ina applying da Mukayi a wayar Mama kwanaki na A B U zaria to yanzunnan sukayo message sun amshemu sannan daman kinga ita ce first choice dinmu s jamb Ranar Monday ma zamuje muyi PUMB kai sis Kinga farincikin da nake ciki" "Wow Zarah ta fad'a ta ce " Gaskiya ni kaina nayi farinciki Sai kuma tayi sanyi ta ce "Sis nadai tayaki murna ammani kinsan bamu da halin da zantafi wata makarantar gaba primary da secondry dinma a yaya na yita ina da burin karatu mai zurfi amma dole na hakura saboda karatun yanxu na masu da shi ne " Lokaci guda asmy ta hade rai Tare da cewa "Insha Allah tare zamu tafi yanda muka fara tun daga pri tare haka zamu cigaba har university ai idan babuke nima wlh Saidai na hakura da makarantar kuma bari naje nayiwa Baba Bayani " sakin firar Zarah tayi ta Kama wata sun jima suna Hira kafin Asmy ta tafi. Babansu Asmy ya samu Baba da maganar makarantar da su Zarah suka samu Inda Baba ya nuna masa baida ra'ayin tura Zarah karatun gaba Aure yake da burin yi mata tayi a gidan mijin ta " shi kanshi babansu asmy baiji dadiba ace yanda yarinyar nan take da tsabar kokari da baiwa Ta tsaya iya sec Dan shi kanshi yasan Asma'u ma Zarah ta taka rawar gani sosai a rayuwarta Dan yasan ba wani kokarin kirki gareta ba Amma tare da Zarah ya sanya itama take dagewa take kokari saboda kunsan ance shi abokin
Chapter 7 · 0% Book details