← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 92

Sashe 20

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ba wani kyau na azo a gani ba ba diri ba ba komai ba Abu k'ashi duk a waje Ko ina ma jin dad'i a wannan abar Har Kake like mata malam ga mata Duma Duma a gari sai ka zaba ka darje amma ka tsaya kana shashanci to wlh ka fita ido na in rufe Dan idan bakayi wasa ba idan bansa ka saketa ba kace ban haihu cikin Uwata da uba na da ruwan zamzam aka haifeni bada jini ba" Tunda Hajiya ta fara maganar MD ya cika yayi famm ga haushinshi na kushe masa mata da take Hade rai yayi sosai tare da kauda kai " Ammy ko shiru tayi sai d'an murmushi da tayi Dan gwara da Allah ya kawo Hajiya ko zata gyarawa MD zama " Mikewa yayi ba tare da ya k'ara kallon ko d'aya daga cikinsu ba ya fita Ya na Jan tsaki. "Da harara Hajiya ta bisa ta na tab'a hannu ta ce " ohh ni Rukayya kujibi dai don Allah a haka a ido kamar zai tab'uka abun kirki nanko ba asan Solon Soson wanka bane dani kake zancen aini ba tsohuwar banza ba ce da zan zuba ido ina ganin tabaranci shekara Tara ana Abu d'aya to Abu yazo karshe na gaji kuma munsanya k'afar wando d'aya daku. MD koda ya koma gidansa ba abunda yake ja sai tsaki tsohuwar nan kwata kwata zuwanta ya rikita masa lissafi gashi ba abun ya koma America ba Ta aiwatar da abunda takeso Dan yasan halin Hajiya sarai bata magana biyu sannan kome ta fad'a saita aikata sa Tsaki ya kumaja tunowa da wai zata aura masa y'ar kauye a ransa ya ce . "dako kinyi babbar nadama dagake har y'ar kauyen sannan ya kumajan tsaki ya na ganin kiran Amera itama duk haushinta yakeji bai d'auka ba saima kashe wayarsa da yayi Dan baya son damuwa tayi masa yawa". <Zaria> Waya ce k'are a kunnanta ta na Waya da Hafiz Bayan fitowarsu daga lectures cewa ta yi " ya Hafiz ka bari na isa hostel sai muyi magana" "Okay ya fad'a daga bangarenshi tare da cewa " ki kulamun da kanki" Saida suka fara biyawa capteria ita da Yusuf sukaci abinci tukwana ta wuce hostel d'insu shima. Ya wuce nashi. "ta na isa ganin su Asmy na lecture Gado ta mimmike tare da yi mishi flashing ya na kira nan suka shiga hira mai dadi Sosai hirar ke yiwa Zarah dadi a haka su Chuchu sukazo suka sameta Asmy ta ce " Uhm manya y'an love kenan' "Chuchu ko taja tsaki ta ce "Uhm Nifa na tsani wannan Hafiz din wlh momcy da yayana kika dace badashi ba please Ki auri yaya na" "Saurin katse kiran Zarah tayi ta na Dariya Dan karyaji abunda Chuchu ta ce ta ce " "kinganki daughter ki barni da ya Hafiz Dina ni yayimun ni wannan Yayan naki da kike kodasa har yau kinki ki nuna mana shi" Turo baki Chuchu tayi ta ce "Wlh da gaske karkiga yaya na ya had'u y'an mata da yawa ridinsa suke ya had'u ta ko ina gashi halinki d'aya dashi Shima miskili ne na Bugawa a jarida wlh kunyi match ta ko ina Shima ya na da irin larurarki Kinga Abu yazo daidai kenan" "Tab'e baki Zarah tayi ta ce " please ki daina had'ani dashi tunda dai ni yanzu na kama ya hafiz dina daurin aure kawai ya rage Ki hada sa da Asmy ta fad'a ta na Dariya " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ai kece halinku yazo d'aya Kinga Ko dake yafi dacewa sannan ya Hafiz din da kike magana Ai ba daura Aure akayi ba sa Aure ba Aure bane kika sani ma ko ke rabon Yayan nawa ce" Nanndai sukaci gaba da Gardandaminsu suna Dariya Asmy ce ta ce "nikam zanso naga wannan yayan da ake fad'a sannan baki fad'a mana sunansa ba ? Gaban Chuchu ne ya fad'i tunowa da MD din da Zarah ta tsana Wani tunani yazo mata Ai basusan sunansa na Gaskiya ba hakan ya sanyata cewa. " sunansa yaya Mustapha"Nice name Asmy ta fad'a Zarah ko bama ta saurari sunanba Inda Chuchu tayi saurin barin zancen Dan kar suce ta nuna musu hotonshi dukda basu sanshi ba wata rana zasu iya cin karo da hoton a wani wajen ko media kuma Su gane ita Kanwarsa ce. <Kaduna> Daga ranar nan MD bai Kara zuwa gidansu ba Dan Ya ce Sai Hajiya ta tafi saida ya kira Ammy kullum ya gaishe ta. Amera ma suna y'ar waya akai akai kewarta bata wani damesa ba Dan Inda sabo sun saba Suna ma aurata amma wani time d'in saisuyi wata hud'u basu hadu ba ita ala dole batason zuwa 9ja Wanda shikuma bazai juri hakan ba Dan family dinsa sun fiye masa komai a rayuwa . sannan wani karinma in ta tafiyarta yawo kashashe sai anganta shi kanshi wani Karin mamaki yake shin wani irin zaman aurene suke da Amira? Kowa haka yake da matarsa daman(nikam na ce MD ka tambayeni Kira ne ya shigo wayarsa dubawa yayi ya ga Chuchu d'auka yayi Inda yaji sautin muryarta cikin shagwaba ta ce "I really miss you yaya please yaushe zaka kawo mani ziyara nayi missing naka sosai " numfashi yaja kamar bazai magana ba saikuma ya Ce . "ke meyasa bazaki zo duka ina Kaduna ina Zaria " Ta na shagwaba ta ce "Yaya wlh lectures ce ta dau zafi kasan level 3 akwai azabar karatu yanzu haka ko weekend din da nake samun zuwa ba Dama saboda yanzu har Saturday muna da lectures Friday da Sunday ne kad'ai ba ma lectures" "Okay Zan duba naga cikin week d'innan idan zan samu dama me kike buk'atar nazo miki dashi" tsalle ta daka tare da buga ihu su Zarah dake gefenta saida suka done kunne ta ce "Thnks so yaya na bana buk'atar komai kai kawai nake buk'atar gani" Kayataccen murmushi ya saki Dan a rayuwarsa ba abunda yakeso sama da farincikin ahalinsa musamman Chuchu da yake mugun ji da ita ya ce. "Zaki fasa mun kunne fa chuchun yaya " Dariya tayi ta ce "Sorry yaya duk murnar zakazo ne ta zautar da ni please yaushe zaka shigo" "Yau yaushe " Friday "okay to Sunday zanshigo insha Allah " Cikin d'okin farinciki ta ce Allah ya kaimu yaya na I love you so much". .suna gama wayar ta shiga d'okin murna nan Duk ta ishi su Zarah da zancen Yayanta zaizo ya kawo mata ziyara Dariya ma su Suka dinga mata Dan yanda duk ta rikice musu. Ran Sunday tun asuba Zarah ta dinga jin ciwon Mara Alamun zuwan perioud dinta sosai cikinta ke murda mata. su Asmy basu sani ba saida safe suka ganta ta na juyi wayyo cikina kawai take cewa duk Sannu suka shiga jera mata Zarah iya ciwon cikin da take bata tabajin irin na yau ba fashewa tayi da kuka ta ce. "Zan mutu ku taimakamun Mara ta ciki na wayyo Allah Baba " Cikin tashin hankali su Asmy suka sanya hijab d'insu Tare da kamata Chuchu ma duk ta rude fito da ita sukayi ta na murkashi kamar mai nakuda "Asmy taje ta taro napep Bayan sun fito daga hostel Chuchu na shirin shiga Asmy ta ce " ki koma kiyi mana Girki sis zata samu sauk'i zamu dawo ba jimawa" Badan Chuchu ba taso ta koma Dan ta tsorata da yanda ta ga Zarah Kai tsaye asibitin da ake kaita suka nufa Gado aka basu danshi kanshi Dr d'in dake duba ta wannan Karin yayi mamakin yanda take. allura yayi mata amma kamarma Kara ciwon ake Asmy duk ta rude banda hawaye ba abunda ta ke "Bayan Dr ya fito kallon Asmy yayi ya ce " me yasa tun farko bakuyi amfani da shawarar da na bayar ba Akwai fa matsala sperm ne ya tarar mata Wanda inba sa a ba sai anyi mata Aiki " "Ta na hawaye ta ce " Dr ba yanda zamuyi ne sannan Shi Wanda zata Aurar saura shekara bikinsu yanzu ya jikin nata"dage kafada yayi ya ce "nadai fad'a muku Gaskiya ta na ciki ki shiga munmayi mata allurar da ake mata ta daina yi mata Aiki ki shiga muga abunda Allah zaiyi. Ta na kuka Asmy ta shiga d'akin Inda ta samu Zarah a bakin toilet sai sheka amai take ita ta taimaka mata ta gyara wurin kafin ta koma gadon ta na kukan ciwon cikin Dan yanzu ta ma fara fita daga hayyacinta Ita kanta ji take yau kuma kila sunyi bankwana da duniya sabbatu kawai take yayinda Asmy na rik'e da hannunta ta na hawaye. Shigowarsu kenan garin zaria Inda suka nufi hanyar A B U da mota d'aya suka taho Dan baisan duk Inda yaje asan yazo gari wayar Jaber ce ta yi ringing ,dubawa yayi yaga number mahaifiyarsa cikin Sauri ya dauka cikin muryar tashin hankali ta ce " kana ina jabir kayi Sauri ka wuce Zaria mahaifinka yayi assident yanzu aka kirani aka shaidamun suna asibitin Zaria ina ma hanyar Zaria yanzu haka nayi ta Kiran layinka tun d'azu bata shiga " Cikin tashin hankali jaber ya ce "Subhanallahi Umma wani asibitin ai ina Zaria ma yanzu haka" bansan sunan asibitin ba Amma bari na baka Aisha ta fad'a maka kila ita ta rik'e wayar Umma ta bawa Aisha Inda ta fad'a masa sunan asibitin kafin ya katse kiran " Kallonta MD yayi ya ce "Lafiya" da damuwa a fuskar jaber ya ce "Ina fa lafiya wai Abbanmu yayi assident a hanyarsa yanzu haka ya na nan Zaria asibiti kawai ka wuce makarantar ni bari na sauka na wuce Asibitin" Da damuwa MD ya ce "Subhanallahi Allah ya takaita wahala mu wuce tare kawai ina ai tafiya ta zama biyu kuma" juyar da motar sukayi suka nufi asibitin. Sunsamu jikin na Abban da sauki raunuka ne ya d'anji kuma harma anyi masa d'inki tare da treatment a lokacin ma har ya samu bacci duk Ajiyar zuciya suka sauke Office d'in Dr d'in suka wuce kafin Su jira farkawarshi . suna nan harsu mamansu Jabir da Kanwarsa sukazo Inda su suka tsaya wajen Abban nasu su kuma sukayi zaune a office d'in Dr Aliyu
Chapter 20 · 0% Book details