← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 92

Sashe 4

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*Miss Hajo ce*_ *AUREN WATA TARA* MALLAKAR *Hajara L Sadeq* *FREE PAGE* ..........*3 & 4* Tana nan zaune tana jin yunwa har Ukku da rabi tayi cikin Sauri ta mik'e tare da sanya Hijab d'inta Dan daman Allah Allah take lokacin Islamiya yayi turaranta Wanda baiwuce Naira d'ari Ukku ba ta fiddo ta fesa Dan Ita daman Chan ma abuciyar son kamshi ce . Fitowa tayi ganin ba kowa tsakar gidan Tare da barin gidan Gidansu Asmy ta shiga gaishe da mamansu tayi har k'asa ta amsa mata cikin girmamawa Babansu ne ya fito Shima gaishesa tayi ya amsa mata cikin sakin fuska Asmy ce ta fito daga palour tare da kallonta ta ce. "Ki shigo yau kece da Shiryawa da wuri Ko y'ar jarabar bata nan " Dariya Kad'an Zarah tayi tare da girgiza kai ta ce "Kiyi Sauri dai yanzu " Kama hannunta tayi suka shiga cikin palourn su mai d'auke da kujeru matsakaita masu kyau sai madaidaiciyar plasma d'insu dake manne a d'akin Suna Kallon tashar arewa24 . ganin ana maimaicin dad'in kowa ya sanya Zarah maida hankalinta ga kallon da ake Asmy tunda ta shigo ta lura da Idanun Zarah yanda suka fad'a tasan bataci abinci ba gashi tasan ko mutuwa zatayi bazata tab'a cewar bataci ba Shinkafa da miya taje ta zubo dukda taci abinci Tazo ta Aje gabanta tare da kallonta ta ce "Sauko muci abinci my Besty" na k'oshi Kedai kawai kici mutafi?Harararta tayi ta ce "Aiko kice yau ba zuwa Islamiya Dan Allah sai kinci abincin nan idan ba haka ba Muyi ta zama a haka" Saukowa Tayi Dan tasan kawar tata ta aika Ta ce. "Uwar y'an jaraba to muyi Sauri" Sai sannan Asmy ta saki fuska ta ce "kokefa my Besty wai kinsan Waec d'inmu ta fito Kuma alhmdllh Duka na cinye yanzu jiran neco kawai muke tunda ita kikayi " Cikin farinciki Zarah ta ce "Wow alhmdllh sis a Gaskiya na tayaki murna wlh Allah sanya alkhairi kice itama neco tana gab da fitowa muyi ta addu'a" " Wlhko Besty Kinga murnar da nake "Har suka gama cin abincin suna Hira Inda Bayan sun gama sukayi sallah tare da wucewa Islamiya Dan duk shirye shiryen saukar da zasuyi ne nan da sati biyu ake. Sai wajen magriba suka bar makarantar Inda daga nan kowa yayi gidansu Tun a Soron gidansu Zarah ta farajin muryar Salisu gabanta na fad'uwa Ji take kamar ta juya Dan tana tsoron mashayin Chan. dak'yal tayi shahada ta shiga tun daga shigarta Salisu dake kan turmi yana busar sigari ya kafeta da idanu har wani lashe harshe yake Itako hade fuska tayi Tam Cikin muryar y'an maye ya ce "Daman tun d'azu nake jiran dawowarki Amaryata " dogon tsuka Zarah taja tare da Yin hanyar d'akinta janyo mata hijab yayi Wanda hakan ya k'ular da Zarah batasan lokacin da ta juyoba tare da wankeshi da Mari Salisu da saijin saukar Mari yayi a fuskarsa dafe kumcinshi yayi tare da nunata da yatsa ya ce. "Ni kika Mara Aiko yau zakisan kin tab'a cikakken d'an tasha Dan uwarki Dan kin samu ma ana sonki Aiko daga yau bazaki k'ara gigin Marin wani ba ya fad'a yana zare belt d'in jikin wandonshi tuni cikin Zarah ya Dori ruwa Dan ba abunda ta tsana irin a tab'a lafiyarta Cikin Sauri Ta maza ta Ruga d'akinta Tare da sanya sakata ta rufe sai huci take. " Salisu ko tsaye yayi ya na ta banka k'ofar ya ke kamar zai b'allata "Rabi ko shiru tayi Dan abunda yasa bata tanka ba Baba na bandaki tun daga Shigowar Salisu Kasancewar Tattare suka shigo da Zara da ido take masa nuni akan ya bari amma sai dura ashar yake ya na cewa yau sai ya raba Zarah gida biyu . Baba ne ya fito daga bandaki cikin b'acin rai irin nasu na masu hakuri ya dakawa Salisu tsawa " Juyowa yayi Dan duk iskancinshi yana shakkar Malam saboda mutum ne mai kwarjini Sosai Malam ya shiga F'ada ta Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sulalewa Salisu yayi ya bar gidan Inda ya koma kan Rabi ya ce. "Wlh na.k'araga d'an iskan yaron nan ya shigo gidan nan zaki kuka da kanki Marainiyar Allah ku sakata gaba Kuyi ta musguna mata wlh kedai Rabi kiji tsoron haduwarki da ubangiji Dan sanya bak'inciki a cikin zuciyar maraya ba k'aramun Abu bane kina daukarsa wasa hakkin wannan yarinyar kadai ya isa ya hanaki kwanta kabari ko Dan a tunaninki duk abunda kike bansaniba . "ina sane kuma ki kiyayi irin hukuncin da zan yanke nan gaba Dan Zarah ta fiyemun ke da kowa ma " Tsaki Rabi ta ja tare da Barin wajen ta na gunguni "Girgiza kai Baba yayi tare da Yin alwala Dan ya wuce masallaci ya Tada musu sallah. Zarah ko ta nan tana hawaye har taji fitar Salisu da yanda Baba yayi musu saitadanji sassauci Amma dukda haka tsoron bud'e d'akin take Dan tasan Rabi duk abunda Baba yayi mata akanta zata huce Ga tana son taje tayi salla ta na tsoro Gashi yau batayi musu girki ba tasan ta bani ta na nan rufe ta kasa fitowa tanajin irin ruwan zagi da masifar da Mama Rabi ke Surfa mata tayi mata banza sai da kanta taje tayi girki wajen 11 PM tukwana Zarah ta fito tayi alwala tana sanda ta koma daki tare da hade Sallar magriba da isha i tukwana ta nemu waje ta kwanta Dan Daman batasa ran cin abinci ba tama girka sai Anga dama dama ake bata Ko idan Baba na gidan bare ba ita ta girka ba Cikinta na kukan yunwa a haka har bacci barawo ya kwasheta. Washegari Tana kwance da Yamma tana bitar karatun Islamiya kasancewar Alhamis ce suna gida taji yaro yayi sallama tare da cewa ana kiran Zarah a waje " Mama Rabi Ce dake waje ta ja tsaki tare da cewa "kaje kace bata nan " Baba ne da shigowarshi gidan kenan ya kalli yaron ya ce "je kace gata nan" Fita yaron yayi yayinda Mama Rabi ke cika tana batsewa Kwalawa Zarah kira Baba yayi Bayan ta fito Ya ce "Jeki shirya Ana Kiranki kofar gida" " to "tace tana kasa da kanta dan bazata iya musu da mahaifinta ba Tare da komawa ciki ta sanyo k'atuwar hijab d'inta Ta fito Mama Rabi na binta da harara Dan tana bakincikin taji ankira Zarah waje zance. kamar yanda tayi tsammani shidinne sanye cikin wani bakin yadi gashi bak'i ga bakin yadi sai suka saje tsaki taja a ranta tana turo baki harta isa Inda yake tare da ja ta tsaya tana kauda kai . "Nura ko cikin farinciki ya ce " Yakike masoyiyata Yaudai Ranar ta musamman ce a gareni tunda kika amsa kirana "Wani banzan kallo Zarah ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce " "Malam idan ka gama zan wuce ina da Aikin da nake "a ah yi hakuri gimbiyar mata kinsan ke din ta musamman ce sai ana lallabaki Dan Allah Zarah ki amshi tayin Soyayyata tsaki Zarah taja ta ce " Inma kana wannan mafarkin Ka daina Dan bana sonka na fad'a maka ba sau d'aya ba basau biyu ba Amma ka nace ayi mutum ba zuciya ta fad'a tana Kara Jan tsaki tare da Juyawa ta shige cikin gidan ta na gunguni. Baba na ganin shigowarta rai bace ya ce "Lafiya y'ar Amanar Baba waya tab'amunke naga ranki bace " Cikin shagwabarta da tunda aka haife take da ita ta ce . "Baba Nura ne kuma nace masa yadaina zuwa wajena yak'i dainawa" Girgiza kai Baba yayi tare dayi mata murmushi ya ce "in banda abunki Zahra'u meye aibun Nura yaro mai hankali da sana'arsa da komai " Zarah ji take kamar tayi kuka ta ce "Ni Baba bana sonshi kuma ni da ba Aure zakamun ba Duka nawa nake" Dariya Baba yayi ya ce "to shikenan y'ar Baba kwantar da hankalinki ai ba a dole a soyayya Yawwa daman zuwan da nayi kauye jiya na sayar da akuyata Dubu sha Biyu Yanzu haka daga wajen malamin naku nake harma nakai kud'in sun bani receipt ya fad'a yana nuna mata receipt din" . Cikin farinciki Zarah ta d'ago ta ce "Kaii amma nayi farinciki nagode Baba Allah saka da alkhairi ya k'ara budi nagode Nagode" " Ameen y'ar kirki "ya fad'a yana Mikewa Mama Rabi Ce ta mik'e cikin Masifa ta ce " Amma dai Malam kasan Irin faman da muke a cikin gidannan kullum cikin cin tuwo Miyar kuka muke Maimakon da kud'in ko y'ar shinkafa ma auno mana Shine zakaje Ka biya asara Har dubu koma akan Saukar da bama ta kirki ba aka bibiya izif biyar bazata kawoshi a ka ba wlh abunda kake Malam ba adalci bane na tabbatar cikin yarana Khairat ko Safiya acire Habiba da Salamatu tunda ba yaranka bane Babu wacce zaka biyawa Har dubu goma idan zasuyi sauka amma ita y'ar gwal din ka lale Naira na dukan Naira har dubu goma ka biya mata". girgiza kai kawai Baba yayi Dan ba a komai ya fiye mata ba ya ce "Suma cikinsu Wata ta dage tayi saukar taga ko sama da dubu goma idan ban bayarba yaran da kin lalata su islamiyar ma na sanyasu amma ba zuwa suke ba Shine har zakizo kina kushe karatun yarinyar da ta shekara da shekaru tana gangariyar karatu ta gama sauka gashi yanzu har tayi harda Wanda iya tsawon rayuwa baxan iya tuna ince ga ranar da Zarah bataje makaranta ba ince Salamatu da Habiba ba sun girmeta ba cikinsu ba mai izif Biyu cikakke gwarama khairat shine zaki hadata da su wannan Abun da kike za a iya daukarsa a hassada ce " " Sosai maganganun baba suka b'atawa Rabi Tai masifa ta shiga surfawa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba hada kuka wai yayiwa diyanta gori Baba bai kulata ba ya ficewarshi tana ganin fitar Baba ta sauke ruwan masifarta akan Zarah saida tayi mai isarta itadai Zarah bata kula tab'a sai aikinta da ta kama . suko su Habiba ko akansu ita da da Salamatu suna Chan suna wayar batsarsu da samarinsu Bayan Mama ta gama masifarta daki ta
Chapter 4 · 0% Book details