Sashe 5
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga Inda ta samesu kowanne da earpiece suna Waya sai huci take Salamatu ce ta katse wayar tare da cewa. "kema Mama ki daina tada hankalinki akan komai meye akayi akayi wata banzar Zarah kina da mu " Tsaki Rabi taja ta ce "ba dole na damu kaina ba yarinya duk tazo tana neman muku zarra Kuna nan zaune bakinku primary amma yarinyar nan shegiyar da bala i na da komai Amma saida har ta gama secondry school sannan gashinan har tana hardar alk'ur ani amma ku shaggun ko izif d'aya cikakke bana ce zaku kawoshi ba ga shegen farinjini tsiya yarinyar nan Duk ta na neman ta rikitamun lissafi " "Habiba ce ta turo baki tare da cewa "kema Mama meye abun damuwa anan har waccen figaggiyar yarinyar y'ar shekara 16 zata dameki sannan da kike maganar Karatu har wani amfani ke gareshi a zamaninnan Mama Me muka nema muka rasa Muma dai daidai gwargwado muna da namu farinjinin tunda manyan yaran da suke zuwa wajenmu da kud'in da ake kashe mana ma kadai ya isa ki gane munyiwa yarinyar Chan zarrah Mama" "Kullum maganar kenan kuna tare da manyan yara yau a sauke ku a wannan mota gobe a saukeku a waccen amma har yanzu an rasa na aure guda d'aya gaisuwa ma suzo abun ya gagara". Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yaune ranar saukar su Zarah Duka daliban makarantar sanye suke da ankon atamfa tare da hijab Blue Sabbi sai tag din shaidar su a wuya manyan malamai sosai aka gayyato a walimar . Wanda wurin ya cika sosai kowa da d'an uwanshi iyaye da abokan arziki sunzo Zarah na zaune ita da Asmy Dan Mamansu Asmy ma tayi musu ankon kayan A gidansu Babu Wanda yazo Sai Baba Dan tanajinsu khairat da tace ma.zatazo Mama Rabi ta hanata . Hakan bai dameta ba Dan daman ba buk'atar zuwan nasu take ba Fuskarta rufe take da nikab nan aka shiga kiraye kirayen dalibai Bayan sunyi karatu a basu kyaututtuka har akazo kan sunanta. *Zarah yusuf*Gaban Zarah saida ya bada daram saboda sosai takejin kunyar ratsa mutanen nan Saida aka k'ara kiran sunanta sau biyu tukwana ta mik'e Shima saida Asmy ta zungureta tana mata Dariya kamar wacce batason ta taka kasa Haka take ratsa wajen Wanda duk Inda ta gitta sai an bita da Kallo dukda kwayar idanunta kadai ake gani fuskarta rufe take bai hana Kyaunta bayyanuwa ba . a haka harta isa kan step din mik'a mata abun karatu akayi amsa tayi tare da Fara rero qir'a cikin zazzak'ar muryarta Mai dadin sauraro tsakiyar suratun bak'ara take karantawa babu mahalukin dake wajen da zaice karatun Zarah bai ratsa sa ba Mutane har wani lumshe ido suke iyaye da dama sunajin inama y'arsu ce jin irin yanda take fitar da tajwidi. Baba ko wani farinciki da annashuwa ce yakeji na shigarsa yana Godiya ga Allah da ya mallakamai Zarah a matsayin y'a tayi minti ashirin tana karatu batare da gargadaba tukwana Aka amshi abun maganar tare da yi mata kabbara . Duka wajen kabbara ya d'auka Inda manya daga cikin bak'i suka mik'e tare da Fara yiwa Zarah kyauta Bayan ta amsa tayi musu Godiya Malam ta mik'awa jinjina mata Malam yayi da hannu Dan daman sunsan Zarah zata fiddasu kunya a taron nan Bayan nan Aka shiga bada kyautar karramawa ga d'alibai Inda yawaici Duka Zarah ta amshe kyaututtukan saboda duk fagen da akazo ita d'ince saida taci kyauta ukku d'aya ta wacce tafi kowa kokari a ajin ta biyu kuma Wacce bata fashi ,ta Ukku nutsuwa da girmama malamai. ,itama Asmy ta amshi kyauta biyu d'aya ta maida hankali a karatu d'aya kuma ta Rashin makara Bayan nan suma sauran dalibai aka shiga basu nasu kyaututtukan sai around 2:pm aka k'are taro Bayan baki sun tafi Ya rage daga dalibai sai malamai . nan Malaman suka bawa Zarah kyaututtukan da ta samu duk a emblem ne wasu Ba yanda batayi ba akan malaman su rik'e sukace a a a nata ne Sosai Malaman sukeson Zarah saboda kwazo da kokarinta Tabbas Zarah tabar makarantar zasuyi Babban rashi Dan duk musabaqar da ta tashi da ita ake turawa kuma ita ke ciyo musu na daya. Bayan sun taho daga Makaranta kai tsaye gidansu Asmy suka nufa a kofar gida Zarah ta tarda Baba Dan ya rigasu tahowa Wajenshi suka nufa Kallonsu yayi ya ce "Allah yayi muku albarka Zarah ked'in y'a ce ta gari da kowani uba zaiyi sha'awar kasancewar ki y'arshi ina matuk'ar alfahari dake Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari mai tausayi da jin k'ai". murmushi Zarah tayi tanajin dad'in addu'ar Baba ta ce "Ameen Baba nagode mik'a masa kyaututtukan da ta samu tayi " nan ya shiga d'agawa emblem na farko kud'ine tsabarsu dubu Hamsin na biyu kuma turmin atamfa na Ukku alqur'an ne sai sallaya a ciki da charbi"Cikin fara a Baba ya ce........ Ga masu buk'atar a tallata musu hajarsu su tuntub'eni akan number wayata kamar haka 07026166526 Ko masu buk'atar shiga grp sharhi ko tambaya hanya a bude take *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ *AUREN WATA TARA* MALLAKAR *Hajara L Sadeq* .........*5 & 6* "Masha Allah natayaki murna y'ata Allah sanyawa karatunku albarka " Ameen suka fad'a ita da asmy Mik'a mata kyaututtukan Baba yayi da niyar ta amsa. "girgiza kai tayi ta ce " a a a Baba banason komai a ciki komai na sama na sameshine ta dalilin tarbiya da jajircewar da kayi a gareni ". girgiza mata kai yayi ya ce " na sani Zarah ta amma Bazan amsar miki Komai ba nasan kina da buk'atar abubuwa da dama bakya tambayata Dan haka ki biya bukatunki dasu . "Girgiza kai tayi ta ce " a a Baba wlh bana buk'atar komai kafini bukatarsu Dan Allah ka amsa ". Duk yanda Zarah tayi Baba ya amsa kin amsa yayi saida Asmy tasa baki dak'yal ya Anshi Dubu ashirin Inda ya mik'awa Asma'u sauran kudin ya ce " "Amshi ku tafi Sannan ya kalli Asmy ya ce "kiyiwa mamanki Godiya kice nagode Allah ya saka da alkhairi Tabbas Saratu ta cika y'ar mutunci kuma ta cika Alkawarin aminiyarta mariganyiya Kinga yarinyar nan saboda kawaici bata fad'amun akwai maganar Anko ba Allah sarki ashe har tayi muku saida safe take fad'amun angode Allah bada lada". Murmushi Asmy tayi ta ce "To Baba " Barwa Baba sallayar sukayi tare da Qur'an din Inda suka koma gidan su Asmy sai tayasu murna ake nan y'an uwa da abokan arziki suka shiga shigowa tayasu murna da Yamma suma sukayi y'ar k'aramar walimar su Wanda mamansu Asmy ce ta shirya hakan. Bayan magriba isha'i Asmy ta kalli Zarah ta ce "Wai kudinnan sis me za ayi miki dasu" ki bawa Mama kawai ni ba abunda zanyi dasu"Mama ce dake jinsu ta ce "Har ance babu abunda za a yi da kudi Zarah zandai Aje miki " . Girgiza kai Zarah tayi ta ce "Mama Dan Allah ki rik'e wlh babu abunda zanyi dasu ke ai tamkar uwa kike a gareni Dan Allah Mama ki rike " . girgiza kai Mama tayi ta ce "a a fa Zarah Aje miki kawai zanyi karki k'ara cewa wani Abu " shiru Zarah tayi badan taso ba Dan a abunda maman asmy take mata ko jininta ce ita sai haka . "Asmy ce ta ce " Mama babansu zarah yace nayi maki Godiya "girgiza kai tayi ta ce " " Ai Tsakani na dasu ba Godiya Komai nayiwa Zarah Ban fad'i ba irin zaman mutuncin da mukayi da mariganyiya da amintar da mukayi a lokacin bamu da hali amma Matar nan bata ci banci ba akwai lokacin da saimun kwanta bacci haka zata buga mana gida na bud'e naga abinci ne ta kawomun a lokacin muna cikin wani hali da haka zamu kwana bamuci ba muna halin Rashin babu Amma Matar nan bata tab'a cin Abu Bancishi ba Munyi zama na amana da mutunci da mahaifiyar Yarinyar nan ". Goge hawayenta tayi ta ce Har yau idan ina tuno da zahara'u bazan daina kukan rashinta ba mac e mai kirki hakuri da juriya Allah dai ya jikanta yasa ta huta". Sosai sukayi sanyi Cikin k'asa da murya Zarah ta ce Ameen ganin ta na shirin yin kuka ne ya sanya Mama barin maganar tare da kama musu hirar duniya Har ta samu ta d'an warware Bayan sunci abinci Cire kayanta Zarah tayi tare da sanya rigar baccin Asmy Dan daman nan gidan take Aje sabbin kayanta saboda su Habiba suke lalata mata su sanye mata kuma bata isa tayi magana ba hakan yasa take ajewa gidansu Asmy . nan gidan kawai take samun walwala da farinciki Sai wajen 10pm ta wuce gidansu har bakin kofar gidan Asmy ta rakata tukwana ta Koma Zarah koda ta shiga Zaune ta tarar da Mama Rabi na girgiza k'afa tana ganinta ta taso tare da Wanke da Mari Dan da bakincikin kyaututtukan da akace Zarah ta samu ta yini hakan ya sanyata huce haushinta na dalili marar ma ana da tushe nan tahau dukanta tana bala i tana cewa . "Y'ar iska tun safe rabonki da gidan nan Sanadin mutane su dinga zagina suna kin lalace a hannu na Bayan duk yanda zanyi inayi iya kokari na Amma kullum baki da aiki sai jamun Zagi cikin unguwa Itakuma saratun in gidanta zaki koma saitazo ta daukeki Dan kazar kazarta kuma daga yau bazaki kara fita ba daga gidan bare ki fake da islamiya na kara ganinki gidan saratu wlh duk tsiyar da na shuka maki ke