Sashe 70
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya MD ya sauke a boye ganin bata tsiro mai wahala ba Mikewa yayi ya ce "give me 30 minutes please kibar kukan nan" Shiru tayi harya fita kafin ta bisa da harara A waya MD yayi browsing Dan ko simple indomie bai iya girkawa ba tsawon rayuwarsa bai tab'a girki ba baima San ya ake ba dan ko school baiyi girki ba Saidai yaci na restaurant Saida ya kwabe manyan kayan jikinsa kafin ya shiga kitchen din waya na rik'e hannunsa daman video ne nan ya shiga Kalla ba laifi MD yayi trying sosai dukda yasha wahala Dan ji yake kamar an sanyashi aikin gini haka dai ya samu ya gama girkin Inda ya juye a plate sai shafce Zufa yake yana fitowa ma kai tsaye d'akin da take ya nufa Inda ya sameta tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Allah mai iko yau nine MD da shiga kitchen akan Aiken wannan y'ar kankanuwar yarinyar saikuma ya tuno da ai kome yayi saboda cikinsa yayi hakan ya sanyasa Aje warmers din tare da Fara kiran sunan da yake kiranta dashi watau Mamy saida ya kira sau Ukku kafin ta tashi Tana murza ido " ta ce "Meye " Abunda kika buk'ata"ya fad'a yana hade fuska "Tura baki gaba tayi tare da mik'ewa taje toilet tayi brush tana dawowa ta iske harya zuba mata d'aukar plate din tayi ta na yatsine fuska kamar taga kashi ta nuna Alamun baiyi mata dadi ba nanko ba laifi saidai magi da yayi yawa kauda kai tayi ta ce "na koshi"murtuke fuska ,yayi ya ce "wlh kinji na rantse saikinci aini ba bawanki bane ki sani bakar wahala kuuma kiki ci abunda bazaiyu bane"bata tanka masa ba sai jujjuya spoon din take kafin ta dauka ta faraci MD na ganin ta fara ci har tayi rabi ya sanyashi sauke ajiyar zuciya Tare da ficewa daga d'akin da harara ta bisa sosai taci abincin Daren ranar zahra karfe d'aya ta tashi ta hau salla Sosai ta daga hannu tana rokon Allah ya kawo mata mafita hawaye na sauka daga idanunta ta ce '" ya Allah kaika jarabceni da duk wannan Abun kuma kana sane dani ya Allah ya kawomun mafita Ya Allah kasan banyi abunda zai tab'a mutuncina da na iyayena ba ya Allah ka fitar dani daga zargin da mutane ke yimun ya Allah ka wanke ni,ya Allah ina kamun kafa da masoyinka fiyayyan halitta Wanda babu kamarsa a duk duniya ya Allah ka bawa mahaifina lafiya Allah ka sanya cikin nan ya zube ta k'arasa fad'a cikin kuka gwanin ban tausayi sai wajen 2 ta ji bacci ya fara daukarta Kallon MD dake bacci kan gadon hankali kwance tayi Dan baya yarda ko daki daya Suki kwana Saboda baisan abunda zata kuma yiwa cikin ba Sosai takejin haushinsa kamar ta kashesa gefen gadon Chan karshe ta ja ta kwanta ba b'ata lokaci bacci yayi awon gaba da ita Cikin baccin ne tayi mafarki Gasu a wani tafkeken lambu Wanda ya cika da kayan marmari da alatu iya rayuwar zahra bata tab'a ganin irin wannan lambun ba waigawa ta dingayi taga ba kowa ba Tana cikin waigawa ta Hango wata mata na kusantowa Inda take fuskarta cike da murmushi da annuri tana sanye da fararan kaya kallonta zahra take har ta karaso Inda take sak Matar taga kamarsu d'aya rai da rai Kallon kanta tayi ta kalli Matar taga sak komai nasu iri daya Karasowa tayi tare da kama hannunta tanayi mata murmushi ta ce "bakisanni ba ko Zahra?Gyada mata kai tayi ta ce " Eh"Kama hannunta ta kumayi suka zauna kan wani lausassan waje da bata Tantance menene ba Matar ta ce "Ni ce Mahaifiyarki Zahra shine suna na nima" sosai zahra ta tsorata saikuma ta Rungumeta ta fashe da kuka ta ce "Ina kika shiga Mama kika barni ina ta shan wahala gashi yanzu ma bata rabu da ni ba Dan Allah Mama Karki k'ara tafiya ki barni ina matuk'ar buk'atar ki a rayuwata ina shan wahala a sanadin rashinki Mama Dan Allah ki daina tafiyar nan Mai nisa karki sake komawa ki zauna tare dani"sai taga hawaye na zuba daga Idanun mahaifiyartata tare da murmushi a fuskarta ta ce "Nasiha nake son nayi miki zahra rayuwa cike take da k'alubale da jarabawowi iri_iri a duk halin da kika tsinci kanki kiyi hakuri sannan ki k'ara kusanta kanki Da ubangijinki shine kawai Wanda zai yaye maki dukkanin damuwarki kiyi hakuri da jarabawa Allah yana jaraba bayinsa ne Dan yaga iya imaninsu karki karaya y'ata ki zama mai tawakkali da godewa Allah a duk halin da kika tsinci kanki sannan ina son ki nemu yarda a wajen Allah ko Duka mutanen duniya basu yarda dake ba indai Allah ya yarda dake kingama samum komai a wajen Allah ake neman yarda ba d'an Adam baa sannan ba mutumin banza Allah yake jarabta ba ni kaina bada son raina nayi doguwar tafiyar nan Ba batare da na rayu dake ba kiyi hakuri da rayuwa kiyi hakuri da rayuwa y'ata ki sani ked'in Haske ce a cikin duhu Ked'in alkhairi ce a rayuwar duk wanda kika rayu dasu zahra ina matuk'ar alfahari da kasancewar ki y'a gareni ina matuk'ar kaunarki kedin yace ta gari " Rungumeta sosai tayi tana kuka ta ce "Mama Dan Allah karki sake tafiya ki barni" murmushi tayi tana Hawaye ta ce "taso nayi miki Albishir" tasowa tayi ta ce "Kalli Chan ta fad'a tana nuna mata wani waje" wajen zahra ta Kalla bata fahimci komai ba saboda wani haske daga gani guda biyu hannunsu rike da juna ta juya ta kalli maman tata ta ce "Mama Haske ne na gani" Murmushi ta kuma ta ce "Kinsan meye hasken can" a a a "" To hasken Chan kece Tare da abokin rayuwarki kudin haskene mai maganin duhu "Da mamaki ta ce " bangane ba Mama"Zaki gane nan gaba kawo hannunki"Mik'a mata hannun tayi "Wasu irin kwandalolin kudi ne taga ta fiddo sai Haske suke guda Ukku kamar zinare har wani Wal_Wal suke ta damk'a mata a hannunta Tare da rufewa ta ce " Ki bawa jikokina kowa d'aya idan sunzo kice ina gaishesu kuma ina sonsu sannan ta bata fuska ta ce "Bazanji dadi ba muddin kika asarar da alkhairi nan dake cikinki zahra ina son kiyi rayuwa Me kyau ki Tara zuri'a mai albarka da zakiyi alfahari da ita ko Bayan ranki sudinga maki addua y'ay'a da kike gani duki ya ce mai daraja Wacce ya kamata mu darajasu mu martaba su sannan inayi miki murna da samun abokin rayuwa na gari kuma Haske a cikin rayuwarki dama ta all'umma Zan Tafi Y'ata sai wata Rana " Cikin kuka Zahra ta ce "Dan Allah Mama karki k'ara tafiya ki dawo ina sonki ina tsananin bukatarki cikin rayuwata " Hawaye na zuba daga Idanun Matar ta na murmushi ta ce "Kalli Chan hasken chan dake rike da hannunki shine mamayina a wajenki zaibaki farinciki insha Allahu tamkar Wanda zan baki " zahra na kallar wajen ta kuma ganin hasken dazu kafin ta juya taga babu Matar babu alamar ta a wajen "Kara sosai ta fashe dashi cikin kuka ta ce " Mama Mama Mama "A matuk'ar firgice da gigicewa ta farka tana Kiran " Mama Mama Mama da karfi"A rude md ya farka yana kallon yanda ta firgice tana ihu tana Mama "Rik'eta MD yayi sosai tare da Fara tofa mata adduo'i a Amma bata fasa kuka ba Tana kiran Mama Wanda MD dukya shiga kogin tunani Har aka kira asuba yana tofa mata adduo'i karatun qur'ani ya shiga rera mata cikin zazzak'ar muryarsa A haka ya samu tana sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali ta fara dawowa hankalinta har tagama nutsuwa tana shirin barin jikinsa ya ce Ina kuma zaki" a sanyaye ta ce "Salla zanyi" Ajiyar zuciya ya sauke tare suka Mike Bayan tashiga toilet tayo alwala Shima sai sannan ya samu damar zuwa yayi shiya jasu salla suna gamawa zahra ta hade kai da gwuiwa ta shiga rera kuka sosai mafarkinma dayazo mata a abun al'ajabi ya tsaye mata a rai tsawon rayuwarta koda wasa bata tab'a mafarkin mahaifiyarta ba sai wannan Karin sosai tashiga kuka tana tunwoa da Abubuwan da suka faru a mafarkin gani take kamar gaske ji take kamar gaske ne gata ga mahaifiyarta ji tayi inama bata farka ba Sosai take kuka tanajin wata irin soyayyar mahaifiyarta na ratsa kowani sassa na jikinta MD lure yake da ita yasan kukan take kuma yasan irin yanda ta tashi Tabbas tayi wani mafarki ne ganin kukan nata yayi yawa ne ya sanyashi cewa"Me ya sanyaki firgita lokacin tashinki a bacci da kuma wannan kukan da kike ko kinyi wani mugun mafarkin ne"fuskartat jab'e jab'e da hawaye ta ce "Nayi mafarkin Mama na ne bantab'ayi ba Sai yau ina son na sake mata magana saita tafi" ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai"Lokaci guda Jikin MD yayi sanyi a sanyaye ya ce"Bata raye ne?kanta sadde ta daga masa kai"Sosai MD yaji wani irin tausayinta ya kara tsarguwa a ransa Tabbas yasan Rashin uwa Babban gibi ne su kansu mahaifine suka rasa suna damuwa duk sanda suka tunashi bare ita data rasa Mahaifiya Sosai yakejin tausayin yarinyar na ratsa duk wani sassa na jikinsa "Shi mamaci har kullum Addua yake buk'ata ba kuka ba Addua da Sadaka itace kawai take buk'ata wajenki a halin yanzu shine Babban gatan da zaki mata tayi alfahari dake Na Haihuwarki da tayi kuma taji dad'in barin baya da tayi ki daina zubar mata da hawaye har kullum mamaci baya son kuka addua kawai yake bukata " Kasa tsaida kukan zahra tayi ta ce "wannan shine karo na farko dana tab'a ganinta Shima kuma a mafarki ba zahiri ba zanso kullum ta dinga zuwamun koda a mafarkin ne" ta k'arasa fad'a cikin kuka"Janyota jikinsa MD yayi ya fara Lallashinta a hankali ya ce"Kina nufin bakisan mahaifiyarki ba?Gyada masa kai tayi tana Hawaye "Ko baki da wayau ta mutu" muryarta na rawa ta ce "a haihuwa ta ta mutu wai" Allahsrk Allah ya jikanta yasa ta huta yasanya tana cikin Rahama ki daina mata kuka please Addua take buk'ata "Gyada masa kai tayi har lokacin hawaye take lokaci guda kuma Ta firgita