← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 92

Sashe 51

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi Kinga Ko yanda kika k'ara kyau da komai my Zarah Gaskiya nayi sa'a fa ba kadanba "murmushi Zarah tayi tare da rufe fuska ta ce " kai ya Hafiz kaima ka k'ara kyau wlh"ai ban kaiki ba ke fa komai kika kara Ai ji nake kamar na janyo gama sch d'innan naku fa ji nake kamar a daura mana Aure yau"Nan ma Kara rufe fuska tayi ta ce "kana bani kunya fa ya Hafiz " Ai Gaskiya Ce dole na fad'a "karan tashin motar da tajine ya sanyata Kallon wurin a guje taga motar tabar wajen tab'e baki tayi a zuciyarta ta ce " ko ubanme ya tsaya tun d'azu yi mtwss"hafiz ko baima lura da tashin motar ba dan gaba daya hankalinsa yana gurin zarar sa sosai Zarah suka sha fira ita da Hafiz Wanda sosai ya dinga fallasa mata sirrin zuciyarsa da yanda ya matsu lokacin bikinsu yayi lectures din da bataje ta ba kenan Har lokacin sallah yayi yana nan yaje yayi salla ya dawo Hafiz shine bai tafi ba sai Bayan la'asar sosai yaji dadin arba da abar k'aunar tasa Zarah ko hostel ta koma ina ta samu Chuchu nayiwa Asmy kitso waje ta samu ta zauna tana hararar Chuchu ta ce "Shine ko kije ku gaisa" Tana turo baki ta ce "Na hangesa da na dawo daga lectures keda kikasan ni bamun yayiba har zanje mu wani gaisa ni banga abunda kika gani kikeso a jikin wannan mutumin ba wlh kikaga yayana saikin manta da wani Hafiz yayana ya had'u y'an mata har tuntube suke a kansa dashi kuka dace wlh tako ina kunyi match har cikin zuciya ta nake maganar nan wlh Zarah zanzo ki zama mallakin yayana saboda kece type dinsa yayana yana son mace mai ilimin addini da na boko,yana son mace mai kamun kai da Jan aji da tarbiya ,yana son mace mai tsafta gayu iya girki da sauran duk abunda yake so game da mace kina da su momcy tako ina kin hadu baki da makusa wlh Ammy ma tana son ki zama surukarta Saboda karkiga yanda take sonki" girgiza kai kawai Zarah tayi ta ce "Mubar maganar nan Chuchu kiyi mana fatan alkhairi kawai" tab'e baki ta kumayi Chuchu ta ce"Allah ya kaimu lokacin A nan Funtua ai za ayi ko?Eh "Insha Allahu tun satin bikin zantaho dukda ba son Angon nake ba" Dariya Asmy tayi ta ce "Kina yanda kikaso Chuchu wai Bason Angon kike ba keda bake zaki zauna dashi ba ita ai ta gani kuma tana so" y'ar Dariya Chuchu tayi ta ce "Allah da gaske nake kawai ina taya yayana bakincikin rasa ta da yayi ne" Asmy na Dariya ta ce "Auta baki da dama to shi Yayan naki cewa yayi yana sonta da zaki dinga tada jijiyoyin wuya" Ai nasan idan ya ganta din zaice yana so shiyasa "Sosai Asmy ta shiga yiwa Chuchu Dariya Inda suka dinga hirar Wanda Zarah bama tasan sunayi ba Dan tuni bacci yayi awon gaba da ita kallonta Asmy tayi tace " ikon Allah Daga Hira sai Bacci baccinma na la'asr"Chuchu ce ta ce "Jiyama wlh bata gama lecture ba tataho wai bacci takeji saida tayi kusan awa Ukku tana bacci" zuwan driver d'inta ne ma yasa na tasheta saboda Yusuf ya kirani yace ana kiranta"Asmy ta ce "Kuma fa wlh da bata da yawan bacci Zarah baccin rana ma ba fiya damunta yayi bare na la'asr " Kilan hada gajiya"hakane kuma Asmy ta fad'a "Zarah itace bata tashi ba sai magriba Shima saida Asmy ta tasheta tayi sallah Ranar a hostel ta kwana " kwananta biyu bata koma gidan MD ba Wanda sosai taji dad'in Rashin waiwayarta da baiyi ba cikin kwana na hud'u ta fito daga lectures ta Hango wata dalleliyar mota a gab da hostel d'insu har tayi gaba "mamy" ta tsinkayi muryarsa daga mota "harta tsaya saikuma ta juya ganin ta Cikin mota yayi mata magana amma da.Alamun saida ya Zage glass din motar waigawa tayi gabanta na fad'uwa Allah yasa ba Mutane sosai a wajen da batasan wasu mutanen suyi mata fassara harzatayi gaba saikuma ta tuno karya biyota ko ya kamata a gaba mutane ta shiga ukku Juyawa tayi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi Inda motarsa take tana shirin shiga taji wasu y'an mata na gefenta wata daga cikinsu na cewa " Ai daman bana fad'a muku ba wlh salahan nan kamar na Allah sunfi shek'e ayarsu yanda suke so ana fakewa da hijab ana yanda akaso yanzu wlh idan ka fad'awa wani saiya karyataka amma da yake akan idonku ai kungani daman na fad'a muku amirar nan cikin wayau take barikancinta mune dai da muka fito namu fili aka fi gani"Juyawa Zarah tayi ta kallesu dukda maganar da ta jefe ta tayi mata ciwo girgiza kai tayi tare da yi musu murmushin da yafi kuka ciwo ta bud'e motar ta shiga taja ta rufe tana maida hawayen da suka zubo mata"Ko Kallon MD batayi ba ta hade kai da gwuiwa ta fara hawayen zarginta da wasu daga cikin sch din suka fara Wanda tasan duk shi ya ja mata Jan motar yayi batare da yabi ta kanta ba a hanya ganin har lokacin kamar kuka ta ke "ya sanyashi kallonta a takaice ya ce " me akayi maki"Kamar mai jira nan ta d'ago tana Goge hawaye Cikin muryarta ta shagwaba ta ce "Y'an sch d'inmu ne suka fara zargina akan daukata da kazo please kadaina zuwa sch d'inmu kar mutane su farayimun wani irin kallo" hankalinshi na kan driving din da yake ya ce "Bani naja maki suke zarginki ba samarin da kike kawowa suka ja maki yaushe na tab'a zuwa wajenki idan ba Yau ba?ni ba samarin da nake kawowa ko motar saurayi bantaba shiga ba ," ta fad'a tana turo baki"Shi Wanda yazo rannnan din har kina masa murmushi shiba saurayinki bane?ohhh ya Hafiz kake nufi?Harararta yayi ta gefen ido ya ce "Bansaniba" Murmushi tayi ta ce "Aishine Wanda zan aura wata guda da Gama school dina za Ayi bikin" tsaki yaja tare da cigaba da tukin sa "Tab'e baki Zarah tayi a ranta ta ce "Mai mugun hali kawai" Duk Auren da akace an daura Koda a wasa ne ya dauro kuma Aure ne ingantacce inhar ba rabuwa akayi ba Mu'amula da maza ko abunda yayi kama da makamancin haka haramun ne ki bari lokacin da Na rabu dake kinyi mu'amula da duk Wanda kikaga damar yi amma yanzu ina nusar dake girman zunubin da kike d'auka kuma nasan kema kinsan da hakan saboda kina da Ilimi karki d'auki nayi maganar nan da wata manufa a a in zakiyi mu'amula da maza dubu ba damuwa ta bace ina kiyaye miki ne fushin ubangiji"Yana gama fad'ar haka yayi parking tare da ficewarsa saboda sun Iso gida Zarah ko sosai jikinta yayi sanyi koda ta shiga cikin gidan harya shige bedroom dinsa tagumi tayi maganganun da yayi mata suna mata yawo a kwalwa ta jima kafin ta mik'e ta shiga tayi sallar la'asr da taji ankira a hanya Bayan ta gama sallah Qur'an ta d'auka tana cigaba da karantawa yunwar da tajine ta tuna mata da bataci abinci da rana ba yaye hijab d'inta tayi Kallon jikinta taayi taga doguwar rigar bata lafe ta ba Sosai taji dad'in ganin baya palourn Kitchen ta shiga ta girka Abu mai sauki sosai taci abincin Wanda har mamakin kanta tayi tasan dai bata da ci da Chan ma bare yanzu Bayan ta gama tayi hamdala kujera ta mik'e batasani ba har bacci ya d'auketa fitowa yayi daga Bedrom d'in sosai yayi mamakin ganinta tana baccin la'ar Wanda bai tab'a ganin haka a Wajenta ba Zaunawa yayi karewa sleeping face d'inta kallo yayi Yajima.yana kallonta wayarsa da tayi ringing ta dawo dashi daga duniyar tunanin d'aya Lula dubawa yayi yaga ,"My Merah"a jiki saida ta gama ringing kafin ya kirata sosai suka sha Hira irin ta mata da miji Wanda yawaici duk Amira ce mai surutun danshi ba ma'abucin son surutu bane har suka gama wayar bacci Zarah take Gashi yana son tashinta amma bayason katse mata baccin dayaje zai tab'ata saiya fasa sai Chan wajen 6 yaji farkawarta Bayan ta wartsake kallo d'aya tayi masa ta kauda kai tare da mik'ewa ta shiga d'akin cikin har isha'i bata fito ba Dan Sallama a Chan tayi tana gama salla ta kwanta bacci ya d'auketa Chan cikin dare taji MD nayi mata abunda ya saba kin biyesa tayi Dan kwana biyun nan abun ba dadi yake mata ba shi kad'ai yayi kidansa da tsalle Shi kanshi MD yayi mamakin yanda bata bashi attention ba ga kuma jin wani dadi da take karawa kwanakin nan haka rayuwa taci gaba Rabi a hostel rabi kuma a gidan MD Dan MD yanzu ya mayar da Zaria gida idan ka ganshi a kd tofa ziyara ce yakai musu A haka dai har wata guda Wanda yanzu wata Guda ya rage karewar yarjejeniyarsu A halin yanzu kallo d'aya zakayiwa Zarah kaga ta sauya saboda wani fresh da kyau da ta k'ara ta k'ara murjewa ga komai nata yayi b'ulb'ul saikuma bacci da take yawan yi Wanda ita kanta har mamakin wannan masifar baccin data sameta yauma tana kwance a gadonsu na hostel Tana bacci Chuchu ma tana gadonta tana karatu a Littafi kasancewar final exams dinsu dake tunkarowa duk sun maida hankalinsu ga karatun da suke Bayan dawowar Asmy daga Lectures Kallon Chuchu tayi ta ce "Badai Zarah yauma bataje lectures ba" Wlhko kinganta nan tun shigowarta da safe tana shiga lectures safe ta fito tun 10 take wannan bacci duba kiga yanzu har 2:15 na tashetama tayi sallah taki tashi sai rabuwa nayi da ita"Karasawa gadon Asmy tayi ta ce "Na rasa dalilin baccin nan da ta tarka na uban meye " ta fad'a tana bubbugar Zarah da karfi dak'yal ta samu ta tashi tana hade fuska Asmy ta ce "Ke yanxu Zarah Dan iskanci saida kikaga karatunmu yaxo karshe zakisa shiririta ki tarki wani bacci Ki dinga kin attending lectures to wlh bazan yarda da haka ba "Sorry uwata nadaina" Zarah ta fad'a tana Mikewa tare da Yin y'ar mik'a tayi hanyar toilet Dan ta dauro alwala "Chuchu ce tadanyi murmushi ta ce
Chapter 51 · 0% Book details