← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 92

Sashe 67

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba saboda kartai zargin wani Abu tunani na general hospital d'innan da na gansu a nan ne asibitin da yake yanzu zanje garin na bincika tunda nasan gidansu kaga komai mai sauki ne karka samu damuwa" numfashi MD yaja yanajin yarage y'ar Kad'an daga cikin abunda ke damunsa ya ce "sainajika idan ansamu yanda akeso ka kirani" yinin ranar ba abunda zahra taci a cikinta dukda irin yunwar da takeji har juya ke daukarta amma batajin zata iya cin abunda ya fito daga hannun mutumin nan da takejin tsanarsa a ranta bangaren MD ma hankalinsa tashe yake bai iya sanya komai a cikinsa ba sai fresh milk yinin ranar daga ita harshi Cikin tashin hankali Suka yishi Dan sosai ta d'agawa MD hankali washegari ma haka zahra harta fara fita daga hayyacinta da komai bibbiyu take ganinsa kwana biyu kenan ba abinci cikinta sai ruwa da Takesha yanzu babu abunda take da muradin sama da tasamu hanyar da zata zubar da kadararren cikin nan Kallon cikin tayi Wanda da a haukanta kiba ce ta fara taga harya so ya fara fitowa batasan lokacin da ta fara bugun cikinta da hannu bibbiyu ba iya karfinta sosai take bugun cikin dukda azabar zafin da takeji tana cikin Bugawa taji wata irin azaba batasan lokacin data k'walla wani uban k'ara ba Wanda daga nan bata Kara sanin Inda kanta yake ba ta zube a wajen summammiya MD daga palour ya jiyo Karan da tayi ba shiri ya Ruga d'akin yanda ya sameta ne ya yi tsananin tayar masa da hankali kwance k'asar tiles ga jini da ya ga ya fara fitowa daga kasanta a matuk'ar tashin hankali ya nufi Inda take tare da Fara jijjigata yana kiran sunanta shiru Ba shiri ya sungumeta a guje yayi waje da ita makullin motarsa dake kan centre table ya d'auka cikin tashin hankali yayi waje yana bud'e motar ya sanyata a baya tare da Juyawa gidan Gaba a 360 ya figi motar tare da dannawa mai gadi wani Mahaukacin horn kafin ya isa da motar get dinma an wangale masa gudu yake sosai Cikin tashin hankali yana driving yana waigawa yana kallonta ikon Allah ne kawai ya kaisa Asibiti.... *Domin magana da marubuciyar 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss hajo ce*_ ..........*77 & 78* Da isarsu asibiti ma emergency aka wuce da ita idan hankalin MD yayi dubu a tashe yake zirga zirga kawai yake yana cikin wannan tashin hankalin wayarsa tayi ringing baima duba mai kiran ba ya daga daga dayan bangaren amera ta ce"Hello honey ykk daman zan fad'a maka ne gobe zanyi tafiya Dubai dan wlh jina nake kamar a k'aya k'asar nan dan karkaji na tafi"md ji yayi kamar ya shakota ta cikin wayar ya wanke ta da mari ba karamun haushi ta basa ba cikin bacin rai ya ce "Ba london ba kitafi bangon duniya stupid mahaukaciya kawai kije gaba da bangon duniya " baijira amsarta ba ya katse kiran yanajan tsaki shi yana cikin wannan babban tashin hankalin wanda duk silarta hakan ya faru ita tana ma masa zancen tafiya wata kasa baimasan ya zage ta ba ,babban Dr d'in mai asibitin kanshi kasancewar da kansa ya shiga duba ta tare da taimakon nurse saida yayi awa Ukku a ciki kafin ya fito yana shafce zufa da Sauri MD ya taresa ya ce "ya ake ciki dr tana lafiya Kardai kace mun abunda ke cikin ta ya zube" Calm down ranka ya dad'e Babu abunda ya samu abin cikin ta Gaskiya kayi Namijin kokari da kukazo da wuri asibiti Dan da aka kai wani lokaci Abinda ke cikin ta zai fita ita kanta zata wahala sosai Dan dak'yal da taimakon Allah yasa Muka ceci cikin daga zubewa Amma yanzu alhmdllh cikin iko na ubangiji Munyi aiki da kwarewa har muka tsaidar da jinin sannan muka yi control d'in matsalar dake shirin faruwa Amma Gaskiya next ka kula sosai Dan Abu Kad'an ba fata ba Zai iya Affecting cikin ayi asararsa sannan ta dinga cin abinci please "nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke Jin cikin bai zube ya ce " Thank you so much Dr itafa ya jikin nata"Alhmdllh da sauki amma zata kwana biyu kafin a sallameta saboda ta k'ara warwarewa yanzu munsanya mata Karin ruwa tana bacci ne "Okay Zan iya samu na ganta" ba matsala ranka ya dad'e "Dr din ya fad'a yana masa nuni Dan kallo d'aya yayi masa ya ganesa saboda suna cin karo da hotonsa a Internet sannan MD ba boyayyan mutum bane dukda yayi mamakin Kawo yarinyar da yayi Saiya d'auka matarsa ce tunda bakowa yasanta ba " Bayan shigar md d'akin da zahra take kan kujer dake gaban gadon ya zauna kallonta ya shigayi ba kakkautawa kwance take tana bacci hankali kwance Fuskarnan tata tayi fayau yanayin yanda take baccin sosai ya basa sha'awa a hankali ya kamo hannunta mai d'auke da bakin lalle da ratsin ja sosai lallen yayi masa.kyau Kallon lallen ya shigayi ba kakkautawa yana Dan shafa lallausan hannunta a hankali A rayuwar MD yanason yaga matarsa na masa lalle wayarsa ce tayi ringing ganin jaber ne yasanyashi saurin picking Daga bangaren jaber ya ce "Yadai najiki kamar baka cikin yanayi mai dadi"da sauki ya fad'a yana matsawa daga Inda take ya ce " ya ake ciki kaje asibitin?Eh naje komai ya tafi yanda akeso kuma sun bada Had'in kai Sunji dadi sosai da taimakon sannan munyi magana da Dr d'in a jiya ma ina Chan yace Zuciyarsa ke ke shirin kamuwa da ciwo amma idan aka tallabi abun da wuri bazai kamu ba "Innalillahi MD ya maimaita a ransa duk shi yayi sanadin shigar mahaifinta wannan halin kafin ya ce " Dan Allah Jabir kamun kokari duk yanda za ayi ayi kar wani Abu ya samu mahaifinta muddin wani Abu ya samesa bazan tab'a yafewa kaina ba duk yanda za ayi ayi chuku_chukun da za ayi kafin gobe a fitar dashi daga kasarnan na shirya kashe ko nawa ne wajen nema masa lafiya"insha Allahu babu abunda zai samesa amma ga shawara mezai hana a jaraba akwai wata Dr Najmat Kwararrar likitan zuciya ce har daga kasashe kawo masa patient ake Inma anfitar dashi wajen tofa abunda zatayi zai iyafin ma na Chan din saboda itama gwanace har Asibiti gareta a India a Gaskiya indai muka sameta tofa insha Allahu za a dace "cikin Sauri MD yace " To yaza ayi a sameta cikin Sauri kar wani Abu ya kuma samunsa sannan wani gari ne take "a nan kaduna itama take gidansu shima cikin GRA yake babu matsala insha Allahu saboda akwai abokin mijinta Habib to Abokina ne kuma matarsa Amera Y'ar uwar ita Dr najmat d'ince yanzu insha Allah zankira Habib din zanje har gidansa ta hanyar amerar zata hadamu da Najmat d'in Insha Allahu" (Only najmat abiy fans can related masu buk'atar cmplt book din *Najmat Abiy* su tuntub'eni akan wannan number 07026166536 Na Batin ne )Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce "Nagode Jabir komai Kenan ka sameni a waya zan maka transfer kudi kome ya kamata ayi sannan Dan Allah ka sayi kayan abinci da komai na Buk'ata ka kai gidansu ka d'ora musu da isassun kudi kayi abunda koda ina nan haka zanyi Dan Allah" Bayan sun gama wayar kujerar da yake ya koma ya kafeta da idanu kamar zai cinyeta yana jiran farkawarta da akayi Sallar Azahar yaje yayi salla d'aya daga cikin restaurant dinsa ya kira drivern sa akan yaje ya amso abinci Bayan ya fad'a masa asibitin d'akin da take ya koma kafin 1hour drivern ya kira number d'akin ya fad'a masa Akan idan yazo yayu knoking karya shigo haka ko akayi yana zuwa yayi knoking MD yafita ya amso warmers din yazo ya Aje sai wajen la'asr zahra ta farka dak'yal ta iya bud'e idanunta saboda wani irin nauyi da sukayi mata Ga jikinta da duk yayi tsami takejin ko tashi bazata iya ba MD yana lura da tashinta Ajiyar zuciya ya sauke suna hada ido hud'u zahra ji tayi kamar ta kashesa saboda a halin yanzu ba Wanda ta tsana sama da mutumin nan da yayi silar rugujewar farincikinta Dana mahaifinta "MD na shirin tab'ata cikin b'acin rai Ta ce " karka sake hannunka ya tabani"Kamar Wanda aka tsaida haka MD yayi dukda yaji ciwon abunda tayi masa Telephone din dake d'akin ya d'auka tare da kiran Dr din akan yazo ya duba ta ta tashi ba dau lokaci ba likitan yazo Nan yashiga tambayarta irin yanda takeji tana basa amsa a takaice Dan duk haushin kowa takeji "y'an rubuce rubuce dr yayi a paper tare da mik'awa MD ya ce " gashi a saya wannan magungunan ta fara sha daga yanzu amma kafin nan a tabbatar taci abinci "kin amsar paper MD yayi ya ce "a saya a pharmacy din asibitin bani acco no dinka zanmaka transfer kudin"take MD yayiwa dr din transfer kudi masu yawa dukda Dr baiyi mamakin hakan ba Dan MD zaiyi fiye da haka ba dukda asibitin mai mugun tsadane dan kwana daya ma kudin gado kaji kudin saikayi mamaki amma saida ya ninka kudin sau hud'u dr din na shirin taba hannun zahra dan ya cire mata karin ruwan da ya kare md ya daga masa hannu yace " kaje zancire mata"okay dr din ya fada tare da yin hanyar fita zahra ta ce " Dan Allah Dr cikin ya fita"Murmushi yayi mata ya ce "Ki kwantar da hankalinki madam ba abunda ya samu cikinki ya na nan Saidai ki k'ara kula wajen rainonsa " Wani irin bak'inciki ne ya tokare zuciyar Zahra batasan sanda ta fashe
Chapter 67 · 0% Book details