Sashe 19
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hada masa tea da lemon tsami gadon da Zarah ta ke ta koma Tare da kama hannunta ta ce. " sorry momcy ko na hada maki tea da lemon tsami zakiji reliep .girgiza mata kai tayi batare da tayi magana ba ta na nan zaune gefenta ta na mata Sannu har Asmy ta dawo kallonta sukayi da take Jan tsaki Chuchu ta ce "kinsamu maganin?tsaki taja tare da cewa. " inaga wai duk chemist din da naje sai suce gwamnati ta hana sayar wa wai saboda masu sha Dan maye " "da mamaki Chuchu ta ce " wai daman maganin tari ne zaki sayo mata?Eh mana shi kadai ne ake samu har bacci ya d'auke ta idan ba haka ba haka zata yini tunda ba mai d'auke mata Kewa gareta ba" "Mai zai hana a bata ruwan tea da lemon tsami idan yaya na ya na haka shi yake sha" Cewar Chuchu girgiza kai Asmy tayi ta ce "maza yake yiwa amfani banda mace daman Dr ya bada shawarar bata maganin kuma Kinga an Rasa" ta fad'a da damuwa. Cike da tausayi Chuchu ta ce 'wayyo sorry momcy to me zai hana ta d'an yi wasa da gabanta ko ta samu relief" "Kallonta Asmy tayi ta ce "Ko hakan kikeyi Zarah tunda Kinga a bisa larura ne" dukda azabar da Zarah takeji bai hana ta girgiza kai ba ta ce "Karku damu zan samu sauk'i ba sainayi wannan ba sanin kanku ne ba kyau" Sosai cuchu ta k'ara jinjina addini da tarbiya irin ta Zarah Dan a yanda take da feeling ba kowace mace bace zata samu kanta. A haka ba bata fad'a halaka ba. Ranar sai bacci barawo ne cikin dare ya kwashi Zarah koda su Asmy suka tashi suka tashi Sallar asuba kin tashinta sukayi saboda ta huta bata samu bacci ba sai wajen 8 ta tashi garas Sannu sukayi mata ta amsa da murmushi ta ce "kunjiku fa kamar wata mai ciwo sannan ta duba agogo ta ce " ya Allah shine kukaki tadani nayi sallah"Chuchu ce ta ce "Ai munga bakiyi bacci ba shiyasa" dukda haka din ai da kuntadani ta fad'a tana Mikewa Dan zuwa ta dauro alwala. <KD> Yau koda ya tashi duk rai ba dadi Bayan ya shirya kamar ko yaushe a palour ya hakimce tare da kwanciya kan sopa lumshe idonshi yayi ba abunda ke fad'o masa a rai sai muryarta lokacin da take karatu har wani lumshe ido ya ke shi kanshi ya rasa dalilin da yasa muryar ta kasa barin kwalwarsa saurin barin wannan tunanin yayi a ranshi tare da Jan tsaki wayarsa ce tayi ringing dubawa yayi ya ga Amera ce tsaki ya ja tare da Aje wayar ta karashi ringing d'inta harta gama. Kira ta shiga yimai sosai har 5 missed call bai daga ba Jin shigowar message ya sanyashi Jan tsaki tare da d'aukar wayar ba tare da ya duba message d'inba ya Danna mata kira ringing d'aya yaji ta d'auka. Sautin kukanta ya fara jiyowa ta cikin waya tare da cewa "Haba honey tun shekaranjiya nake kiranka kak'i dagawa Nifa ya kamata ace ma nayi fushi ka taho batare da kayimun bankwana ba Amma kai kake fushi me nayi maka baby ko ka daina so na ne" "Cikin sigar lallashi ya ce " Kiyi shiru kinsan banason kukanki yanzu dai ya wuce ykk" yanajin daga bangaren ta ta sauke ajiyar zuciya ita har mamaki take yanda MD bai iya bada hakuri ta ce "am okay dear please yaushe zaka dawo kewarka duk ta isheni" "Lumshe ido yayi tare da budesu ya ce " ba rana sai nagama muhimmin aikin da ya kawoni" .Kamar mai shirin yi kuka ta ce "Haba honey wani aiki ne da bazaka k'arasa yinshi ba a nan please kasan banason zamanka a Nigeria ina kishin yanda y'an iskan karuwan matan nan ke kallonka please my husband ka dawo" "Cike da kosawa da magana ya ce" bana magana biyu Amera Kitaho kawai ki sameni idanma Kaduna ce bakya son zama saimu koma Abuja finally magana ta k'arshe" "Cike da takaici Amira ta ce " Bazan dawo Nigeria ba Honey duk Randa ka dawo ina nan ina jiranka amma Bazan dawo k'asar da za a dameni a Takuramun ba" "Tsaki MD ya ja Dan duk ta k'ara masa Haushi tsaki yaja tare da katse kiran yayi Wulli da wayar Dan itama duk ta gama chaza masa kai a ce ya na da mata amma bata biya masa buk'ata ai gaskiyar su ammy ne da suke cewa da shi da gauro ba banbanci. Saboda Hajiya kaka ya dagawa gidansu Dan kullum ya je zance d'aya ne Fada kullum hakan yasa yayi zamansa a gidansa ya na hutawarsa Dan Yawaicin rayuwarsa hutunsa kadanne idan ba Kaduna ba yazo duk Inda yaje harkar kasuwanci bata barinsa sakat. Kamar yanda jaber ya fad'a a one week din ya zo a lambun gidan suka zauna suna kurbar drink " Aje lemon dake hannunsa MD yayi ya ce "Ina sauraranka bloody wace shawarace ka ce kazo da ita". Ya na fuskartansa jaber ya ce " Shawara ce Na yanke wacce nake tunanin ita ce mafita a gareka mafi sauki shine kayi *Auren wata Tara* ?da mamaki MD ya ce "What *Auren wata Tara* kuma Kamar ya ban fahimce ka ba ka kullemun kai ina gudun Karin Auren shine zakazomun da maganar da na guda" "Murmushi Jabeer yayi tare da cewa of course wannan ita ce kad'ai damar da na hasaso maka zata zame maka mafita" "Har yanzu ka sanyani a duhu fa kayi mun bayani me Kake nufi da inyi *Auren wata tara"* Gyara zama jaber yayi tare da cewa yanzu zanyi maka bayani kuma nasan zaka fahimta "sannna ya d'ora da cewa....... *07026166536 domin magana da marubuciyar* *hmm yanzu fa salon wasan zai fara fans Kudai muje zuwa* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* *_Miss Hajo ce_* *AUREN WATA TARA* ```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* ............*25 & 26* "Aure zakayi a sirri batare da sanin Iyayenka ko wani naka ba ka Aje Matar a sirrance har kayi mata ciki Kaikuma saikayi musu albishir da Amera ta samu ciki tunda ka ga ta na chan America ita kuma Matar zakuyi yarjeniya da ita ne akan Zaka aure ta na Wata Tara zata Haifa maka d'a ko y'a saika saketa sannan zaka biyata mak'udan kudi amma fa dole Saidai a samu y'ar talakawa nakasassu wacce basu da cin yau basu na gobe a rudata da kudi" "Wani irin kallo MD ya dinga binsa dashi na baka da hankali kafin ya ce " "amma bantaba sanin jaber baka da hankali ba sai yau wannan ai ba mafita bace maganar shirmece kazomun da ita Sannan ni kakeyiwa ikirarin da Auren y'ar talakawa neman haihuwa hauka ne wannan shawarar batayi ba nema ma kake duk ka b'atamun rai" "Dage kafada jaber yayi ya ce " tunda hakan baiyi maka ba Ai shikenan amma kayi tunani wannan ce kawai mafita mafi sauki" ya na gama fad'ar haka ya Mike ya ce "na Wuce Abuja akwai meeting din da zamuyi da wasu y'an kasuwa zan wakilceka Dan kwana biyun nan ka zama wani gashinan dai" "MD ko tsaki ya ja ya na jin haushin wannan banzar shawarar da jaber ya kawo abun ma ya zama hauka ya fad'a ya na Jan tsaki" Mikewa yayi kamar wani zaki tare da fitowa excort dinsa na ganinsa sukayi saurin bin bayansa tare da bude masa mota kai tsaye gidansu ya nufa. A palour ya tarar da Hajiya ta mik'e kafa ruky na gefenta ta na chat ta na ganinsa ta tashi tare da cewa "Ina yini Yaya MD " ba tare da ya Kalleta ba ya ce "Lafiya" fuskarsa a hade ya gaishe da Hajiya ta amsa da fara'a "Ammy ce ta shigo itama gaisheta yayi Bayan ta amsa ta zauna ta na Duba news a jarida. Yayi minti Talatin ba tare da ya ce uffan ba Hajiya ce ta lura da akwai magana a bakinsa cewa ta yi " Yadai Naga kamar akwai magana a bakinka ka fad'a ta cikinka mana Malam " "Cikin hade rai ya ce " daman akan maganar nan ce da mukayi Hajiya please ki janye shekara guda yayi yawa sannan fa haihuwa ta Allah ce Insha Allahu muna addua kuma kuka tayamu da addua za a dace" "Wani banzan kallo Hajiya ta bisa dashi kafin ta ce. " ka gama na ce Ka gama sanin Allah ne zaka gwadamun to tun kafin a haifi uwarka da ubanka nasan wannan nasan haihuwa ta Allah ce kajini da kyau da kunnan basira bari kaji dai nayi maka ta Mahaukacin kare " "wallahi tallahi billahillazilla'ila ha illa huwa Matarka ta shekara bata haihu ba ko bata samu ciki ba Ko a kauye ne saina samo mata na aura maka ," "Ka ganni nan ni ba tsohuwar banza bace bana magana biyu kuma ka zuba ido ka gani badai ka na tsorantaba ta salamceka ba bazaka iya mata kishiya ba To ni nan da kaina zan Aura maka duk wacce tamun kuma dole ka zauna da ita ko ubanka da ya ke raye na sanya yayi Abu dole yayi bare kai k'aramun kwari ni wuce kaban wuri kayan takaici kawai shine hada wani daure fuska to a ganinka tsoranka zanji kome ko nima fatimar ce da kake zare mata ido ta kasa maka magana," " to ni ba ita bace wani had'e ranka na banza Sololon hofi ,gadara da iko da isa sai a waje a gida kuwa Tsigaggiyar matar da a tsaye kamar iccen kabari ta na Juyaka ita bama macen kirki