Sashe 14
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kunji takaitaccen Tarihin MD matashi da kudi Wannan shine kirarinsa". Tunda ya fara maganar Zarah take Jan tsaki Inda yana gamawa ta kuma Jan wani tsakin tare da cewa "To waya tambayeka Tarihinsa ina ruwanmu dashi ka zauna sai zuba kake mana akan wani chan banza " wara idanu Yusuf yayi ya ce "MD dinne banza Zarah" Tsaki taja Dan sosai takejin zafin tsayuwar nan tasu ta ce. "To me zankirashi dashi Bayan ya tsaida mu a titi yanzu haka Ina tunanin Banki sun tashi" ta fad'a ta na Jan tsaki tare da kauda kai tanajin haushin wannan banzan MD din da aka fad'a Wanda ya tsaida su kusan Awa guda a titi" "Chab ba ruwana wlh security dinsa suka jiki Saidai kiji ina cewa A mota muka hadu " "Asmy ce ta kwashe da Dariya tare da cewa " lallai Abbanmu kace duk uba da d'iyar da ake ajesa za ayi" "Chab ina ake ta uba idan ta fito lafiya sai acigaba da ubantakan" "Dariya Asmy tayi ta ce " Kaidai anyi matsoraci wlh nima saida ka fad'a na tuna da shopping mall d'insa da na tab'a gani a kano sannan a funtua ma ai akwai gidajen mansa har biyu Saida ka fad'a nagesu" "Chab ai yana da Mahaukatan gidajen mai kalli Chan ya fad'a yana nuna mata wani had'adden gidan mai sabo mai d'aukar kai Ashirin Ya ce " Karanta Chan ma me aka rubuta wancen ma nasa ne"dagawa Asmy tayi ta Kalla ta ce "Aikuwa wlh amma dai nima nayi mamakin Mahaukatan kudin matashin nan ya na da mata amma? " Wara hannu Yusuf yayi ya ce "wannanne dai bansaniba Anya ya rasa mata ma kuwa Amma dai ko wacece Matar zatasha miskilanci" Dariya asmy tayi ta ce "Gaskiya kam " sai sannan motocin MD suka gama wucewa Mai napep d'insu ya tada suka isa Zarah ta cika tayi Fam Asmy na mata Dariya ta ce. "Ran manya ya b'aci ayi hakuri ya muka iya k'asar nan Indai kai talaka ne Ai saida kayi hakuri" "koda suka isa Banki harsun tashi sosai Zarah ta k'ara k'uluwa tana tsinewa wannan shegen MD din da ya tsaidasu ji take kamar ta kurma ihu Dan Haushi Wata napep din suka Tara tare da komawa Zarah sai cika take batsewa Dan taji haushin b'ata lokaci ta da sukayi a banza a hofi. Dan ita tana daraja lokaci da ace tsawon lokacin da suka 'bata a tsaye da ko karatu ta tsaya tayi bata amfana ba. saida suka tsaya kasuwa sukayi sayayyar kayan miya da Abubuwan da zasu buk'ata Dan karsuyi fitowar banza sune basu koma makaranta ba sai wajen magriba . Koda isarsu makaranta sosai sukayi mamakin chinchirindon student wasu ana wawwatsewa ita dai Zarah bata tsaya ma kallonsu ba . Cikin jin Haushi ta isa hostel d'insu Asmy na mata fad'an akan ita da ta sani da hakuri yanzu kuma itace take mita akan Abunda baikai ya kawoba Ta ce " gobe ba saimuje mu bud'e ba Tunda safe ba" "Zarah bata kula taba saboda ita kanta batasan ya akayi ba takejin haushin b'ata lokacin da sukayi suna isa hostel sunyi mamaki ganin bak'in kaya a Bangaren da ba kowa Uban jibgin kaya akwatuna kamar Lefe banda uban provison Kallon juna sukayi da mamaki Asmy ta ce " to fa ko bakuwa muka samu a d'akin namu '". Basu k'arasa magana ba sukaji shigowarta dukansu Juyawa sukayi tare da Kallon matashiyar budurwar da baza wuce sa'anninsuba sanye da Doguwar Riga mai shegen tsada da kyau sai fara'a take sosai daga ganinta kasan tana da tsananin fara'a Murmushi ta sakar musu tare da karasa shigowa d'akin saurin fusgewa sukayi da Kallon da suke mata suka zauna bakin gadon su suna huta gajiyar da suka kwaso cikin girmamawa ta ce sannunku ko kune Wanda muke d'aki d'aya"...... *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ *AUREN WATA TARA* ```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* ............*17 & 18* Murmushin suka mayar mata Asmy ta ce "Eh mune Sannu da zuwa" Yawwa Chuchu ta fad'a tare da cewa. "suna na Maryam Dikko ana cemun Chuchu ko kuma ku kirani da chuchun yaya dan nafison a kirani da haka kufa". "Ni suna nan Asma'u ana Cemun Asmy ita kuma wannan " Zarah y'ar uwata ce"Asmy ta fad'a ta na nuna Zarah "Wow nice name Sunan Ammy na ne Fatima Zarah" Saidai na kirata da momcy "Chuchu ta fad'a cikin iyayinta da ya zame mata jiki. " Murmushin da batayi niya ba Zarah ta sakar mata tare da cire hijab Dan taje tayi sallah "Asmy ta ce " Wow kice ke y'ar gata ce Gaki ga mom d'inki" "Ah sosai ma a gatana nazo school d'innan Saidai naga momcyn nawa kamar batason magana dani? "An d'an bata mata rai ne shiyasa " cewar Asmy Zarah ko Smile ta sakar mata tare da cewa"Ba haka bane Daughter Ykk anzo lafiya " "Alhmdllh momcy sorry ko Naji ance an bata maki rai ko waye dai Wanda ko wacce ta bata miki ran nan bata kyauta ba gsky kiyi hakuri ko" "Dariyar da bata shirya ba Zarah tayi Dan ta lura akwaita da surutu ta ce " shikenan na hakura daughter sunci arzikinki" "Wayar Chuchu ce ta yi ringing Cikin Sauri ta d'aga kiran Ganin ammynta ce ya sanyata " murna ta ce. "Hello my Ammy na " Daga bangaren Ammy ta ce "Na am Autar Ammy kinganni nan daga tafiyarki har na fara kewa" "Dariya Chuchu tayi tare da cewa" Wayyo Ammy na tun ba Aje ko ina ba har kin fara missing Nima da banjima ba Amma kadaicinki duk ya isheni "ta fad'a ta na turo baki. Sun tab'a Hira da Ammy cikin so da k'aunar juna Daga nan kuma ta kira Yayanta Bayan ya d'auka ta ce " yaya Ya hanya kunkoma lfy" "Alhmdllh ya fad'a tare da cewa " ki tsaya kiyi karatun kirki karki sake na kamaki da matsala na sanya a sa miki ido sosai banda biyewa kawayen banza da samarin banza na sameki da haka cireki zanyi" "toh yaya bazanyi ko d'aya ba daga ciki " Shima sun tab'a Hira tukwana ta kashe. Washe gari tare da Asmy suka wuce lectures saboda course d'insu d'aya itakuma Zarah ta tsaya tayi musu girki saboda sai 10 take da lectures. Cikin k'ank'anin lokaci Su Asmy suka saba da Chuchu Wanda duk ita Chuchu din take shishige musu ita dai tunda taga Zarah taji ta kwanta mata a rai. Itama Zarah din Chuchu ta kwanta mata a rai Saidai Abunda ke bata Haushi game da ita irin shigar da take kullum da k'aramun gyle bata tab'a ganinta da hijab ba sannan bata tab'a ganin ta dauki Alquran da sunan wai tayi karatu kullum cikin jin kid'a take ta lura yarinyar sangartattace ta Bugawa a jarida Saidai Inda take burge ta ta na da kamun kai sosai. Sosai y'an mata keson abokantaka da Chuchu saboda lokacin da MD ya kawota sunsan Kanwarsa ce ta bangarenta ko bata kula kowa saboda ita daman haka take bata fiya mu amula da mutane ba sai Wanda jininsu ya zo d'aya. Da Yamma suna zaune a Harabar hostel din suna shan daddad'an iskan dake kadawa Yayinda Alquran ke hannun Zarah cikin zazzak'ar muryarta Mai dadin sauraro ta ke rerawa ". " Chuchu ce dake sauraronta sosai ta burgeta yanda take zuba kiri'a shiru tayi ta na sauraronta wayarta ce Tayi ringing saurin dubawa tayi ta ga yaya MD aiko cikin farinciki ta daga tare da cewa. "Yaya na I really miss you so much yaya " Daga bangaren MD yaja numfashi tare da cewa "miss you too chuchun yaya Ya kike ya school d'in kina dai maida hankali kuma ba wata matsala ba abunda kike bukata" "alhmdllh yaya na ba wata matsala kuma ina maida hankali sosai " good girl haka nakesonji wani karatu nake ji daga gefenki ko? "Eh yaya momcy ce Ke yin karatu sunan Ammy gareta yaya karka ganta ta had'u da kyau Ga Ilimi Ko na baka ku gaisa" Tsaki yaja daga bangarensa tare da cewa "kin fara rainani ko ni zaki cewa zaki bawa wata mu gaisa " yana gama fad'ar haka ya kashe wayar . Chuchu ko Dariya tayi ta ce "Allah barmun kai yaya na " Asmy ce ta ce "Na lura dai kina ji da wannan Yayan naki sosai fa" "Kamar mai jira Chuchu ta gyara zama tare da cewa . " kaiii ai fin sosai ma ina son yaya sosai shidin ba matsayin yaya kadai yake a wajena ba shi din uba ne ya na sona da kaunata sosai nima ina sonshi sosai matsayi biyu yake a wajena yaya kuma uba Dan tun wata na biyu a ciki mahaifina ya rasu bansansa ba yaya na kadai ya mayemun gurbinshi shidin na musamman ne a cikin mutane" "Allahsrk Allah ya jikan Baba ya mishi Rahama Gaskiya dole kiso Yayan nan naki da yawa Allah ya k'ara had'a kanku" Cewar Asmy " "amen Chuchu ta amsa ta na cigaba da sauraron karatun Zarah" Dukda karatu ta ke amma Zarah na sauraronsu Taji abunda Suke fad'a saida takai daidai Inda takeson tsayawa tukwana ta ninke Alk'uran din Chuchu jira ta ke ta gama daman cewa ta yi" "Gaskiya momcy kin hadu ta ko ina wlh bantaba Jin kiri'ar karatu mai dad'in wannan ba kina da murya mai zaki Dan Allah Ko zaki dinga yimun k'arin karatu Dan wlh hizif d'ina ko Talatin bankai ba " "Da murmushi a fuskar Zarah ta ce " me zai hana daughter insha Allahu indai kina so daga yanzu ma saimu fara" Cikin farinciki Chuchu