Sashe 63
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take kamar ranta zai fita tama kasa magana Baba ne da hankalinshi yayi mugun tashi yana dafe da saitin zuciyarsa ya ce "me yake faruwa Habiba kiyimun bayani me zahrar tayi " Cike da takaici ta Kalleshi ta ce "Saidai kayi hakuri Malam abunda na kiyayar ne Ya faru Yaron nan yaudararta ya yi yayi mata ciki shiyasa yazo lokaci guda yace ya fasa" A matuk'ar tashin hankali Baba ya furta "Ci ki" a rarrabe "Mama Zainabu ce " Cikin b'acin rai Ta ce "Meye haka kike Habiba wai kasancewar itace gaba da ita ta ce " wannan Abun da kika fada kai tsaye ai sai kija kuma zuciyarsa ta tarwatse shida daman ba kosashshiyar lafiya ba tun mutuwar mahaifiyarta ba lafiyar kirki ta ishesa ba "To idan ban fad'a masa ba an nemu mafita shiru zanyi dole yayi hakuri muzo mu nemu mafita tunda Mai faruwa ta Riga ta faru Wlh Zarah kin kunyatamu bantaba tunanin haka daga gareki ba " Kasa magana Baba yayi sai Dafe saitin zuciyarsa da yayi cikin k'arfin hali ya ce "Habiba Nasan halin Zahra sarai na san irin tarbiyar da na yi mata ba zata aikata wannan Abun ba kodai likitan ya gwada ba daidai ba kafin ya kalli zahra data durkushe kasan kujera tana kuka ya ce " Zahra taso ki fad'a mana Ba Gaskiya bane bazakiyimun haka ba nafi kowa sanin halinki da irin tarbiyark...kasa k'arasa maganar yayi sakamakon wani irin daci da yake ji a a makogaransa na tashin hankali "Cikin muryar kuka zahra ta d'ago ta ce " Ba Ba "Saikuma kuka yaci karfinta " Cikin b'acin rai Mama Habi ta nufi Inda take ta ce "Fad'a mana ubanda yayi miki wannan abun" Kasa Dagowa tayi saici gaba da kukan da tayi tana tsinewa Musty a ranta ta ce "Ka cuce ni ,ka zalince ni,ka tozartani ,ka sanya mutanen da suka yarda dani yanzu bazasu tab'a aminta dani ba ,bani da bakin da zan k'are kaina Allah ya isa tsakani na dakai" cikin Zafin rai Mama Habi ta nufi Inda take tare da shakota ta ce "Zaki fad'a mana ubanda yayi miki ko saina illataki yau d'innan" dukda zahra taji shak'ar sosai kasa magana tayi sai kuka"Kasancewar D'akin tsakar gidan yake gashi da karfi suke magana ya sanya mutanen dake tsakar gidan suka Fahimci halin da ake ciki kowa Salati kawai yake Asmy ko tashin hankalin data shiga baya musaltuwa har Chuchu da taji abun tamkar almara saida tayi kuka ta ce "Asmy ban yarda ba Momcy zata aikata haka Dan Allah kije kiyi musu bayani kila Dr dinne ya rubuta ba daidai ba " tagumi Asmy tayi hawaye na sauka daga idanunsu Cikin tsananin b'acin rai Mama Habi ta ce "Magana ta ta tabbata amma yaron nan anyi Dan iska ba kama ,ya cucemu aiko wlh bai isa ba yanzunnan bazan zarce ko ina ba sai gidan uwarsa da ubansa suji abunda dansu yayi yasa ya ce ya fasa Auren ta fad'a tana yin hanyar waje kamar wacce aka tsunkula haka Zarah ta zabura tare da saurin Kamo K'afar Mama Habi " mama Ba shi ba ne "Ta fad'a a rarrabe duk juyowa sukayi suka Kalleta yanda ta rik'e kafarta tana wani irin kuka mai cin rai sai sannan Mama Rabi da shigo d'akin Bayan ta gama shewarta da hamdala a d'aki d'auke ta da Mari Mama Habi tayi ta ce " To Dan Ubanki idan ba shi ba uban wa yayi miki ko fyad'e aka miki"Nan ma shiru Zarah tayi saici gaba da kuka da take "Daidai lokacin da Baba ya fara tari dukansu cikin tashin hankali Suka nufi Inda yake sosai ya shiga tari ba kakkautawa yana dafe da saitin zuciyarsa" Salati duk mutane suka fara "Mama Rabi ta ce " Shikenan kin kashe sa kin kashemun miji bakincikin ki ya kashe ubanki Munafuka duk sanya hijab din da zarya Islamiya ba fashi Ashe na banza ne na kariyar iskanci ne ni daman Nasan An Rina jami'ar nan da ta tafi nasan da bura'ubar da take yo yarinya ce Daga shiga Jami,'a ta waye tana ganin kowa a daddage sai wani kyau da take Da kiba kamar ba karatu take ba Ai yanzu ga ranar tonuwan asirinki nan muna fuka algulguma "Kannen Baba sunajin abunda Mama Rabi take cewa Amma hankalinsu yana ga Dan uwansu dake tari hankali tashe sai sannan zahra ta lura da Baba da gudu taje Inda yake tare da Rungumesa da fashe da wani irin kuka ta ce " Dan Allah Baba karka tafi ka barni kai kad'ai ka ragemun a duniyar nan kai kad'ai ne mai sona kuma nasan kai kad'ai zaka fahimceni Dan Allah Baba karka mutu kodan ni ka tausaya mun "Mama Rabi Ce cikin zafin nama Ta fardo ta dagaa kan Baba ta ce " Dan Ubanki k'arasa kashe shine zakiyi y'ar iska karuwa cike da muganci ta hau Bugunta Karan da Zarah tayi ne ya sanya su Asmy da chuchu dake daki Sauri fitowa ba shiri suka shiga d'akin ganin irin dukan da Mama Rabi ke mata ya sanya suka isa wurin da Sauri tare da fardar Zarah Cikin b'acin rai asmy ta ce "Ke kuma ina ruwanki da ita Munafuka har zakiyi mata irin wannan Dukan Muguwa" Nuna kanta Mama Rabi tayi ta ce "Dan Ubanki ni kike fad'awa haka ohhh kungama yawon iskancinku tare shine Asirin d'aya ya tonu zaki Fara borin kunya to saura ke " Cikin Tsawa Chuchu ta ce "Shut up Malama Annabi MUHAMMAD (s a w) ya ce falyakul khairan auli yasmut " ka fad'i alkhairi ko kayi shiru amma daga ganinki bakinki baya fadar alkhairi wannan dukan da kika hauta dashi kasheta zakiyi Dan muganci "Salati Mama Rabi tayi ta ce " watau tsabagen yanda zahra keyi dani har kawayenta ta sanya zasu Zage ni lallai Ta haihu duk ruk'on da nayi mata tun yarinta"Mama Habi ce Dake kokarin tada Baba a kaishi Asibiti ta juyo ta ce "Da Allah Malama fita kiba mutane waje waya sakoki ma d'akin nan muna ta lafiyar Dan uwanmu kin zauna kina wasu banzayen maganganu marar tushe da ma ana ke in kina da kunya har kince kin Riki zahra wlh idan baki bar d'akin nan ba zanyi miki rashin mutuncin da bakiyi zato ba " Tsaki Mama Rabi taja kasa kasa ta ce '"yo ina zani mijina na wani hali yanda yake Dan uwanku nima haka yake mijina kuma uban y'ay'a na Dan haka ba Inda zani kuma ta kashe mun miji kotu Ce zata rabamu da ita "Ohhh haka kike ce kenan to bari nazo mu fidda Raini " Mama Habi ta fad'a tana tunkarar Inda take cikin Sauri Mama Rabi tabar d'akin tana tsine mata kasa kasa "tsaki taja tace k'aramar y'ar iska kafin ta kalli Asmy ta ce " Dan Allah jeki taro mana mai napep"Asmy dake Kuka Rungume da Zarah da ta sume ta ce "To Mama Chuchu ma hawaye take ganin kawar tata sume kamar ba rai " Sai sannan su Mama Habi suka lura da zahra ta suma "Ruwa suka kawo suka yayyafa mata amma taki tashi Sosai hankalinsu ya k'ara tashi ga zahra sume ga Baba dake tari ba kakkautawa yana fara fita hayyacinsa koda mai napep suka zo da taimakon Baban Asmy aka saka Baba Inda sai sannan suka samu labari sosai maman Asmy ta shiga tashin hankali jin wannan Abun tamkar almara wata napep din aka taro Inda aka saka zahra da Chuchu Da Asmy na gefenta Asibitin da aka kai Baba Chan aka kai zahra sosai likitoci suka fara iya kokarinsu wajen ganin sun ceto rayuwar Baba wajen ganin hawan jinin nasa da yahau sosai ya sauka Allurar bacci suka masa kafin su daura masa drip Wanda aka zuba magunguna a ciki" Zarah ko cewa sukayi ba wata matsala tashin hankali ne Yayi mata yawa sannan suka horesu da yadaina shiga irin wannan tashin hankalin zai iya Sanadiyar zubewar D'an cikin ta "A zuciyar Mama Habi ta ce " Ai dama zubewa yayi me za ayi da shege Allah yasa ya zube ma "Chuchu da Asmy ko har lokacin hawaye suke musamman Chuchu da takejin zafin irin abunda Mama Rabi da dinga aibantawa kawartata da take jinta har ranta " Su kadai aka bari a d'akin da zahra take hawaye cike da idonta ta kalli Asmy ta ce "Sis nasan bata boye maki komai a baya ban gaskata cikin nan gaske bane sai yanzu da Dr yayi bayani na k'ara tabbatarwa Nasan halin zahra Bazata iya aikata wannan mummunan abun ba Dan Allah Ko Fyade wani yayi mata Dan Allah ki fad'amun wlh bazan iya jurar ganinta cikin wannan halin ba ki fad'amun kowaye yayi mata fyaden wlh sai Inda karfinmu ya k'are " Asmy bata iya bata Amsa ba saici gaba da Kuka da take "Ganin ba amsa ya sanya Chuchu yin shiru sai wajen Bayan magriba Zahra ta farka koda ga farka da bakin cikin abun ta tashi sosai taci gaba da rera kuka abun ban tausayi Cikin su ukkun bamai Lallashin wani cikin Muryar kuka Zarah ta ce " Asmy ya cuce ni ya zalince ni Allah ya isa tsakani na dashi ban tab'a tunanin Abubuwa zasuzo da haka ba a yau ji nake daman Allah ya karbi rayuwata babu abunda nake da Buk'ata sama da mutuwa na sanya Mahaifina mafi soyuwa raina Wanda yafi kowa kaunata cikin wani hali ina Baba Asmy yana cikin wani hali da wani ido zan Kallesa,,,kuka ne ya k'ara cin karfinta Inda ta shiga rerasa ba kakkautawa "Rungumeta Asmy tayi tana kuka ta ce " Duk ni na janyo wannan din zahra ni na cuce ki na zalunceki"Chuchu da duk hankalinta ya tafi akan fyad'e akayiwa zahra cikin Sauri ta mik'e ta ce "Wlh ko waye yayiwa Momcy wannan Abun bai isa yaci lilis ba wannan ai zalinci ne babba wai garinyama haka ta faru" Cikinsu ba Wanda ya iya bata Amsa sai kuka Banko k'ofar da akayi da karfi ne ya maida hankalinsu gamai shigowa d'akin Mama Rabi Ce ta shigo daga ganinta kasan ba mutunci Kai tsaye gadon da Zarah ta nufa ta shakota iya karfinta ta ce "Wlh baki isa ba kika kashemun miji nima saina kasheki kingama yawon karuwancin naki