← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 92

Sashe 58

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko fara'a babu a fuskarka"Sai sannan MD ya kalli Hajiya Yana hade fuska ya ce "me kikeso nayi nagodewa Allah a cikin zuciya ta Bayan haka me zanyi kuma"tsaki Hajiya taja ta ce Wlh tunda nake rayuwa bantaba ga mutum mai irin bakin halinka ba shekara goma Kana neman haihuwa yanzu Allah ya kawo kaki nuna farincikinka ai nazata likitan dinnanma yau sai anyi mishi tukuici babba" Shiru MD yayi baice komai ba danshi hankalinshi ba anan yake ba "Ammy tayi mamakin yanda MD yayi da murmushi a fuskarta ta ce " Congratulations Baba na Allah ya rik'a"Ameen Ammy"ya fad'a ba walwala a fuskarsa "Zey ce ta ce " Congratulations yaya Gaskiya munyi murna wlh Allah ya raba lafiya"Murmushi itama ya sakar mata ya ce "Ameen sis" Cikin farinciki Chuchu ta ce "Congratulation yaya nayi farinciki Sosai wlh kaima zaka zama Daddy harna k'agara naga fitowar Babynka" Murmushi ya sakar mata Itama Mikewa yayi Ya ce "Ina zuwa Ammy " yana fita da Kallo Hajiya ta bisa tare da tab'e baki ta ce "Allah ya yaye maka wannan mugun Abu" nan fa Amera taga tarairayar wajen Hajiya da da bata kaunarta yanzu ita ce hada cewa me take so a girka mata Chuchu ma dukda basa shiri da Amera sosai taji dad'in samun cikin nata kuma ta tayata murna MD na fita suka had'u da Dr Jinjina masa yayi ya ce "Nagode Dr Dan Allah wannan din ya zama sirri tsakaninmu" Karka samu matsala ranka ya dad'e insha Allahu daga wajena bamaijin wannan maganar"Ajiyar zuciya Md ya sauke Bayan yayi de transfer 200k motarsa ya shiga tare da hade kansa da sitiyarin mota Jaber ne ya fad'o masa arai Tabbas dole ya neme sa dukda yasan har yanzu fushi yake dashi amma dole ya nemesa Dan shine kawai zai iya sama masa mafita dukda waccen mafitar tashi ita ta ruguza komai.. Yau tunda ta tashi takejin jikinta ba dadi ga wata irin kasala da takeji haka dai take daurewa amma ita kadai takejin yanda takeji ga bata iya cin abinci yanzu Kowa daka Kalleta saikagane ta zama so silent ga wani fari da kyau data Kara kowa sai ya lakanta hakan da dilkan amare ce da aka fara mata Sosai hankalinta yake tashe kasancewar Bikinta da Hafiz dake k'aratowa Dan yanzu idan bazata mance lissafin ba saura kwana goma ba wani shiri da take daga bangarenta Dan ko Anko bata fiddo ba haka rabon invitation daga ita har aminiyarta ta basa cikin walwala Musamman Asmy da har wata irin rama tayi Dan kullum da abunnan take kwana take tashi sai kowa ya lakanta hakan da rabuwa ce da zasuyi ya sanya sukayi sanyi yauma Zarah tana kwance Kanta keyi mata ciwo sosai Kamar zai tsage da gudu taji shigowar khairat tana cewa Aunty Zarah"Dukda ciwon kan da Zarah take bai hanata farincikin tarbar y'ar uwar tata ba Rungume juna sukayi Zarah ta ce "Badai har kunyi Hutu ba " Eh Aunty dawowata yanzu kenan bakiga ko unifoam ban cire ba ke na fara nema "Kama hannunta Zarah tayi ta ce " Gaskiya ne Autar Baba Ke boarding dinma amsarki tayi naga hada su kiba kikayi"Dariya tayi ta ce "Kai Aunty wlh ba dadi boarding din Bari naje na cire kaya akwai labari Allah ya taimakeni Ina nan za ayi bikin ki " Murmushi kawai Zarah ta mata tana barin d'akin ta koma ta kwanta koba komai taji dad'in zuwan khairat Dan ta samu Mai d'ebe mata kewa dukda Asmy kullum tana gidan ko kuma idan taje gidansu amma khairat ita har daki daya zasu iya kwana "ya rage saura sati d'aya biki aka kawo Lefe Sosai kowa ya yaba irin kokarin da Hafiz yayi kala hamsin ya zuba mata a akwati dangin babanta da makwafta sai yaba kayan suke Mama Rabi ma ko itace uwar zakalkalewa hada guda " A lokacin Zarah na kwance a gidan su Asmy Dan yau da zazzabi ta tashi Kiran Hafiz ne ya shigo wayarta Bayan ta d'auka ya ce "My love Kinga kaya sunyi maki dai ko ko a sauya sannan dinkunanki da zakisa da biki suna wajen tela katsina insha Allah gobe zasu Iso ina fatan suma zasuyi miki Dan na lura baki da shirin badawa shiyasa na bada maki"Banshiga gidan ba na Kalla ya Hafiz amma nasan sunyi Allah ya k'ara budi " Ai komai nayi maki ban fad'i ba Zarah kin chanchanci fiye da haka "Bayan sun gama wayar sosai Zarah ta fara hawayen tausayin kanta Hakika ta cutar da Hafiz ,ta yaudareshi,taci amanarsa ,batayi masa halacci ba yayi mata Rana tana shirin yi masa dare "dukda tasan ita kanta bada son ranta Hakan ya faru ba K'addarar ce ta zaba mata hakann taya zata iya fuskantar wani da wannan Maganar?Taya Kuma zata yarda A daura mata Aure kan Aure ?wannan wace irin kaddararriyar rayuwace ta tsinci kanta Batasan lokacin da hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata ba Maman su Asmy ce ta shigo d'akin da take kwance kasancewar Asmy ta fita Sayayya kasuwa cike da kulawa ta ce "Taso Zarah ki daure kisha Maganin nan " Goge hawayenta tayi tare da mik'ewa zaune ta ce "To Mama" Girgiza kai Mama tayi ta ce "Yauma kukan ne kikayi ko Zarah?na rasa abunda yake damunki keda Asma'u tunda kuka dawo daga makarantar nan bana gane kanku idan tunanin rabuwa kuke ai baku rabu ba kuna tare Har abada Aure baya raba Abuta to na lura abun naku ma ya wuce yanda nake tunani" Shigowar Asmy d'akin ya sanya Mama kallonta tare da cewa "kema shigo" a sanyaye ta shigo d'akin duk ta rame itama zaunawa tayi gefen gadon dukansu sukayi kasa da kansu kamar wasu munafukai "Mama ta d'ora da cewa " Dan Allah ku saki jikinku ayi bikin nan cikin walwala Ke yanzu Asmy bake ce aminiyarta ba ko ita bata saki jiki ba aike yakamata ace kinzama kirjin biki kin jajirce a bikin kawarki amma sainaga kema din kamar kin fita solancewa sakarcine yanzu ina tsammanin ko rabon katin gayyata baku kaiwa kawayenku ba bacin Anko da baku raba ba wannan Asama kun lakanta hakan da kurewar lokaci To wlh nidai ina fad'a muku tun wuri ku nutsu kusan abunda kuke"a sanyaye Zarah ta ce "Insha Allah Mama" Asmy ma ta ce "Insha Allah Mama zamuyi rabon IV din Tunda da sauran time" Da dai yafiye muku maza ki Shanye ta fad'a tana mik'awa Zarah cup din da tunda taji warin abun taji zuciyarta na wani irin tashi tana kafawa a baki kurba d'aya tayi taji wani irin amai na tunkaromata a Guje ta tashi tare da rugawa tsakar gidan a makwararo ta durkushe nan ta fara sheka amai kamar zata amayar da y'ay'an cikinta daga Asmy har Mama biyota sukayi Inda suka sameta durkushe sai kwarara amai take kamar zata amayar da y'an cikinta......... *Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo Ce*_ .........*69 & 70* Da taimakon Asmy da mamansu ta gyara jikinta sosai ta d'an galabaita sannun kawai maman Asmy ke mata ta ce "Baki da lafiya daman?Gyada mata kai tayi ta ce " amma ba Sosai ba "Ikon Allah ai bamuga ta zama ba amarya ba lafiya maza shirya mu tafi Asibiti" A sanyaye ta ce "Mama Bafa wani Abu bane kaina ne kawai ke ciwo kuma nasha magani basai anje Asibiti ba " A a ban yarda ba shi kuma aman na meye ?rasa me zatace tayi ta ce "Wannan maganin ne Mama daman banason shansa shine kawai ya kawomun Tashin zuciya har nayi aman" to shikenan tunda kinki Aje asibitin Maganin nan kam dole ki dinga shansa saboda yafi kowanne amfani bazaki gane amfaninsa ba sai nan gaba "shiru tayi tana kasa da kanta Asmy da duk gabanta fad'uwa yake itafa zargin ciki takeyiwa Zarah Dan duk wasu alamomi na masu ciki take gani a tattare da ita tun a sch bare yanzu da suka dawo gida abun yayi gaba kama hannun Zarah tayi suka koma daki tare da rufe d'akin cike da damuwa Asmy ta ce " Zarah yaushe rabonki Da Perioud? saboda me kikamun wannan tambayar?saboda cire kokonta ki fad'amun Gaskiya "Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Rabon dai da nayi cikakken perioud wata Ukku idan yazo Kad'an yake zuwa kuma kwana daya ya tafi wata biyu baya nayi irin haka Wannan watan ne banyi ba ko kadan kuma naga lokacin ma da zanyi kamar ya wuce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Asmy ta shiga nanatawa ta ce " na shiga ukku Zarah Kardai ace ciki ne dake"a matuk'ar rude Zarah ta ce "Ciki kuma?Eh ciki ni duk alamomin masu ciki nake gani kamar tattare dake " dukda gabanta dake fad'uwa bai hanata Jan tsaki ba ta ce "Lallai baki da hankali Asmy me zai had'ani da ciki nikuwa Bayan nafada maki Watanni biyu baya nayi perioud kuma rabo na da Azzalumin mutumin nan wata Ukku taya kuma zan dauki ciki please kibar maganar nan kar tashin hankalin yayi mana yawa ga wancen bamu gama ba ki b'ullo wani"tagumi Asmy tayi ta ce " Zarah Bazan tabbatar ba har saimunje asibitin ki tashi muje a gwadaki idan akaga babu sannan ne hankalina zai kwanta Amma yanzu babu ni babu kwanciyar hankali"tsaki Zarah taja ta ce "Ba Inda zanje wlh Kuma ba wani ciki jikina Allah ya kiyaye Ya tsareni da Cikin azzalumin mutumin nan macuci ya cuce ni ya yaudare ni Allah ya isa tsakani na dashi " ta k'arasa fad'a hawaye na zuba daga idanunta "Naji ba ciki jikinki Zarah akwai matsala fa Auren nan na gabatowa na
Chapter 58 · 0% Book details