← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 92

Sashe 56

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karkiji irin yanda nakeji idan na tuna da yaya wlh Rashin mata ta gari babbar illa ne ta Riga ta lalata rayuwar Dan uwana ni kad'ai nasan irin zafin da nakeji a raina yaya baiyi dacen Aure ba ammy" murmushin da yafi kuka ciwo Ammy tayi ta ce "Ni kadai nasan irin yanda nakeji a cikin Raina Maryam nidin uwa ce Addu'a kawai zan Kara dagewa da masa Dukda kullum cikin masa nake kema ki raya Yayanki da addua".... A sanyaye Zarah ta shiga cikin gidansu Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba Mama Rabi tsakar gidan Sai Baba yanajin radio cikin farinciki da murna Baba ya tari y'ar tasa ba irin albarka da bai sanya mata ba. Sosai ya nuna mata jin dadinsa na kammaluwar karatun nata lafiya sannan ya bata hakuri akan Rashin halartarsa wajen " Murmushi tayi ta ce "Bakomai Baba wannan Karin Mama Rabi batayi alkaba'in da take yiwa Zarah ba saboda ganin Baba a takaice ta amsa gaisuwar da tayi mata Bayan Fitowarta daga d'akin Bayan Zarah ta huta Tayi wanka da dare Baba ya sanya aka kirawota Bayan ta zauna kallonta yayi ya ce " Zarah yau zan baki wasiyar da mahaifiyarki ta bani dukda na fad'a maki na adana maki ne har zuwa lokacin da ta wa'adanta watau lokacin Aurenki Alhmdllh yanzu ne lokacin da ya kamata na baki"Ya fad'a yana mik'a mata Awarwaron da zobanyar da ya sanya cikin k'aramun box hawaye ne suka zubowa Zarah tare da amsa sosai taji k'aunar awarwaron da zoben kuma tayiwa kanta alk'awarin kula dasu kamar ranta "Allah ya jikan mahaifiyarki yasa tana cikin Rahama " Ameen Baba"Zarah ta fad'a kafin ta ce"D'an Allah Baba kana da hoton Mamana ko d'aya ne?Yanajin tausayinta a ransa ya ce"Banda hoton mahaifiyarki Zarah ni kaina Inajin Haushi Rashin hotonta da bani dashi a lokacin bamu damu da hoto ba Tunda muka hadu da ita batayi wani hoto ba Saidai nakanji dadi idan na kalleki ked'in hoton ta ce Zarah idan kinason Kallon fuskar mahaifiyarki to ki kalli kanki ita zaki gani wani gamin idan ina kallonki sainaji kamar mahaifiyarki nake kallo saboda har zubin jikinki ba banbanci da nata sannan a lokacin ma da ta rasu Bazata wuce shekarunki ba kamar yanda kike d'innan har abun nan na gefen bakinki da suka lotsa (Dimples) ita ma haka suke banbanci nata d'aya ne ke kuma Duka biyun ni kaina nakanyi mamakin tsananin kamarki da mahaifiyarki ta baci zarah "Dan murmushi Zarah tayi sosai takanji dadi idan akace tana kama da mahaifiyarta sosai takejin dadi idan Baba na bata labarin mamanta cewa tayi " Baba Itama tana da hakuri ko?Murmushi Baba yayi ya ce "Hakurinta ya ninka naki Zarah kinsan dai rayuwa Ana cewa zomu zauna zomu saba ko ?To bantaba samun sabani da mahaifiyarki ba b'ata tab'a fushi dani ba ,bata tab'a yimun gardama ko musu ko kuma na fad'a magana ta mayar ba bamu tab'a fada ko na dak'ik'a d'aya da mahaifiyarki harta rasu shiyasa har kullum bazan tab'a mantawaba da mahaifiyarki ba Bantaba salla biyar ba ban roka mata Rahama wajen ubangiji ba Zarah y'ar aljanna ce ,tayi mutuwar shahada sannan ta rabu da mijinta lafiya ta rabu da mak'wafta da duk Wanda tayi mu'amula dasu lafiya Wanda nake da tabbacin iyayenta ma lafiya ta rabu dasu mutuwar mahaifiyarki ba mata ba hatta maza da idanunsu suka dinga kuka unguwar nan babu Wanda baiji mutuwar mahaifiyarki ba Allahsa ta huta"" Ameeen Baba "Ina son kiyi hakuri a gidan mijinki kamar yanda mahaifiyarki tayi zakici ribar zaman duniya Zarah har ko yaushe na kanyi alfahari dake matsayin kyautar da Allah yayi mun Na mallakamun ke a matsayin y'a ked'in y'a ce da kowani uba zaiyi alfaharin da kasancewarki y'a a gareshi Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki Albarka Sannan ina son na sanar dake mun tsaida Ranar Aurenki da yaron nan d'an mutunci Hafiz Sati Ukku masu zuwa" Wata irin faduwa gaban Zarah yayi Jin an tsaida Aurenta Da Hafiz sati Ukku Bayan da Auren wani a kanta"kanta yayi wata irin sarawa Wanda ta kasa control d'in kanta a matuk'ar rude ta d'ago ta kalli Baba dake mata kallon mamaki ta ce......... 07026166536 domin magana da marubuciyar kai tsaye *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ .........*67 & 68* "Sati Ukku fa baba"ta fada idonta na cikowa da k'walla " eh sati Ukku m uka tsaida saboda shekara hud'u ba wasa ba munriga munshirya komai na biki da kayan daki tuni na tanada komai Saidai jiran rana Kina da matsala ne da hakan"Goge hawayen tayi ta ce"a a a Baba naga yayi kusa ne"Murmushin dattaku Baba yayi ya ce "baiyi kusa ba Zarah Iyayen yaron sun nuna yana son ne ayi abun wurwuri shiyasanya muka barshi a haka din " kasa tayi da kanta saida Baba ya k'ara mata nasihohi sosai kafin ya bata umarnin fita Zarah kamar jira take yace ta fita tana zuwa d'akinta tayi rubda ciki ta fashe da kuka Cikin kuka take cewa "Na shiga ukku ya zanyi da rayuwata taya ina musulmai zan yarda A daura mun Aure Bayan akwai Auren wani a kaina sannan ba idda ba komai ka cuceni Musty tsakanina dakai Sai Allah ya isa mugu azzalumi" Sosai take kuka Daren ranar bacci sai barawo ne ya d'auke ta washegari koda ta tashi da ciwon kai ta tashi saboda kukan da tasha Bayan tayi wanka d'akinta ta koma Dan yanzu kwata kwata zaman gidansu baya mata dadi Khairat ce Daman Suke Dan Hira da ita gashi itama Bata gidan bare Safiya yunwa takeji Amma tashin hankalin da take ciki tasa ta manta da abinci sosai ta Lula duniyar tunani "tana cikin wannan tunanin Asmy ta shigo saida ta daddabata tasan da zuwanta Firgit tayi ta mik'e tare da kallonta da Itamadin ita take kallo a sanyaye Asmy ta ce " Kinji Sati ukku aka sanya Aurenki da Hafiz yanzu nakeji wajen Mama"Naji"zarah ta fad'a kamar zata fashe da kuka "Tagumi Asmy tayi tare da lulawa duniyar tunani Wanda itama Zarah tagumin tayi Sunkai minti goma ba Wanda yayi magana kafin Asmy ta ce " nayi Danasanin *Auren wata taran* wannan da Akayi Zarah Bacci da idona jiya ya gagareni nasan duk ni na ja maki wannan tashin hankalin ji nake inama akaina wannan Abun ya faru bake ba Zarah akwai babbar matsala Bazaiyu ayi Auren nan ba muddin bai sakeki ba sannan koya sakeki dole saikinyi idda "murmushin da yafi kuka ciwo Zarah tayi Dan yanzu idanunta sun fara k'afewa da kukan ta ce " Hmmmm"Hawaye na sauka daga idon Asmy ta kamo hannunta ta ce "Dan Allah Zarah ki yafemun da nazama silar shigarki wannan hatsarin wlh tallahi da nasan haka zata faru da ko makamanciyar haka bazaiyu ba A lokacin sonki da tsoron rasaki ya sanya harna amince da Auren nan bansan abun nan zai zama Haka ba Zarah na cuceki naci Amanar.....rufe mata baki Zarah itama hawayen take ta ce " Kidaina cewa haka Asmy wlh ban rik'e ki da komai a zuciya ba na d'auki hakan a matsayin kaddarata kidaina cewa haka Wannan din ya zama sirri a tsakanin nidake karmu sake wani yaji labarin nan Asmy mun tafka Babban kuskure duk laifi na ne "Ba laifinki bane Zarah laifi nane yanzu menene mafita kwana nayi ina tunanin mafitar da zamu samu Amma kaina ya kulle" Bamuda mafitar da ta wuce Addua Komai ya Riga ya lalace Mafitarmu d'aya Allah shi kadai zamuyi ta roka Dan ba abunda yafi karfinsa shine kawai zai kawo mana mafita"cewar Zarah "wayarta ce tayi ringing kamar bazata dauka ba saita d'auka tana ganin Hafiz ne saida gabanta ya fad'i saida ta kusa gama ringing tukwana ta d'auka tana daidaita muryarta karya gane tana kuka " A sanyaye ta gaishesa ya amsa cikin so kauda tare da shaida mata yana k'ofar gidansu"ina zuwa"ta basa amsa tare da katse kiran kallon Asmy tayi ta ce "Hafiz ne yazo" Okay gyara fuskarki mu fita tare daman Mama tace mutaho tare saina wuce gida idan kin sallamesa kije gida Mama na nemanki"To"Zarah ta fad'a tare da mik'ewa saida ta wanko fuskarta kafin ta dawo ta sanya k'atuwar hijab d'inta Tare suka fita da Asmy Bayan Asmy ta gaishe da Hafiz tana shirin barin wajen ya ce "a a dawo babbar kawar Amarya ai wannan zuwan Naku ne ku biyu Naga Amaryar tawa bata shirya ba har yanzu gwara mu mu fara shirin karmu biya tata" murmushi Asmy tayi ta ce "Hakane kam" Zarah ko bata tanka ba saboda wani iri da take ji"Mota Hafiz ya shiga Ya d'auko invitation masu yawa mik'awa Asmy yayi ya ce "gashi Dan ku fara rabo da wuri" Saida Asmy ta wara idanu kafin tayi Dariya ta Ce"lallai ango wannan zumudi haka invitation da wuri to shikenan"murmushi yayi ya ce "Ai dole nayi zumudi kam Abun shekara hud'u ya rage sati Ukku ina zama ya ganni" hakane kam to Allah ga kaimu "Ameeen Sai Maganar event ko walima da kukeso Kuyi duk abunda kuke buk'ata ki rubuta gobe idan nazo saina amsa" To shikenan ranka ya dad'e"Asmy ta fad'a"Bayan barinta wajen sai sannan ya maida Kallonshi ga Zarah da tayi kasa da kanta cike da kulawa ya ce "Yadai my wife lfy?lafiya qlau ya Hafiz Ina kwana" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla an kammala sch lafiya ko to Allah ya taimaka jiya din naso zuwa wlh Wani kiran gaggawa ne akamun katsina shi ya hanani zuwa am sorry Kyautarki tana gida na mance da ita " murmushi ta kirkira ta ce "Ba komai Ai " Duk yanda Hafiz
Chapter 56 · 0% Book details