← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 92

Sashe 54

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taji ta dawo normal saida ta kusa Rabi kafin ta mai nuni da ta k'oshi janyewa yayi tare da kallonta ya ce"Ko bakiji dadi ba karki sha wani maganin da ya wuce wannan"Saboda me?Saboda haka nace maki"Shiru tayi tare da kwanciya ta juya masa baya"Ki tashi daga baccin nan na fad'a miki"Tana turo baki dukda baya ganinta ta ce "ba bacci ba zanyi" Da Dare tanaji MD ya fara yamutsarta ta fashe da kuka "Sosai MD yayi mamakin abunda bata tab'a masa ba kenan " Hakan yasa ya rabu da ita yana tunanin ko jikin nata ne dayan d'akin ya koma Zarah najin fitarsa ta sauke ajiyar Zuciya raba dare tayi tana salla Wanda yawaici duk adduarta akan mahaifiyarta ne Sosai take roka mata Rahama A wajen ubangiji saida taji bacci ya fara daukarta tukwana ta lallaba ta koma ta kwanta MD ko tunda ya koma ya kasa bacci yana tunanin sauyin yanayin yarinyar abunda bata tab'a masa yau tayi masa A ranshi ya ce "Kodai itama ta fara gajiya ne?To amma me yasa da Chan bata tab'a nuna Rashin So ga abunba sai yanzu" Karfa ciki ne da ita?kai gsky ba ciki bane saboda tace tayi perioud? Meke damunta ne?haka dai MD yayi ta sake sakensa "washegari Zarah duk yanda taso taje lectures MD ya hanata saboda yana tunanin bata da lafiya ita dai tasan lafiyarta qalau yanzu kam ba yanda ta iya ta hakura ta zauna saboda yanzu batasan yawan musu dashi tunda dai kowa ya kusa kama gabansa Ranar da ta cika wata Tara Cif da yarjejeniyarsu Aurensu Wanda MD mancewa ma da lokacin yayi Zarah ko tana sane sarai tunda safe Ta hada duk abunta da tasan nata ne a gidan ta sanya a akwati Kayan d'aya saya mata ta barsu a ciki Wanka kawai tayi hijab d'inta har k'asa bata shafa komai a fuskarta ba zallar ainahin Kyawun da Allah yayi mata ne bata samesa a palourn ba hakan ya tabbatar mata da yana ciki zaunawa tayi zaman jiransa ya fito ya furta mata Kalmar saki ko kuma ya bata takardar sakinta ko ta samu nutsuwa a cikin zuciyarta gashi Allah ya taimaketa kafin lokacin bikinta ta gama idda tayi minti sha biyar zaune kafin taji fitowarsa cikin shigarsa ta alfarma tunda ya shigo Palourn k'amshin turarenshi ya kauraye Duka ilahirin palourn lumshe ido Zarah tayi a ranta ta ce " Baya ragawa Turare"cikin Tafiyarsa ta izza ya Iso palourn "batare da ta Kallesa ba ta ce " Ina kwana"Morning muntashi lafiya"Steady"ta basa amsa a kad'aice "Kallon akwatin dake gefenta yayi ya ce " wannan fa "Cikin k'arfin hali ta ce " kaya na ne zankoma hostel "da izinin wa kuma saboda me?saboda Yarjejeniyar *Auren wata tara* yazo karshe yau wata Taran ya cika nasan kaima.kana lissafi ina jiran ka bani takardar saki na ne kafin na tafi"wani irin kallo MD yake binta dashi Wanda bazata iya fassara yanayin da yake ciki ba lokaci guda mood din fuskarsa ya sauya cikin dauriya ya ce"Kina nufin wata Tara ya cika da aurenmu?"Eh mana Ka lissafa mana ina tunanin ma harya so ya wuce" shiru MD yayi kafin ya d'ago ya ce"Bai cika ba ki koma Lokacin da ya cika zan sallameki da kaina?wani irin kallo Zarah ta dinga binshi dashi na ka rainamun wayau ta ce "Kamarya me kake nufi wlh ya cika kuma yau d'innan saika sakeni tunda ba a garin gab'a_gab'a muke ba " Dukda MD yayi mamakin jin furucin ta Wani murmushi ya saki da bazaka iya sanin na meye ba tare yin shiru ya lumshe ido cikin nutsuwa Hankali kwance"da karfi zuciyar Zarah ta dinga Bugawa bata San lokacin da ta fashe da kuka ba Ta ce "Wlh baka isa ba saika sakeni aiba haka mukayi daku ba,wannan ba adalci bane,kamar yanda a baya lokacin da naki Amincewa da Auren nan Abokinka yayi mana gori bada son raina ba harna amince yanzu kuma wata taran yayi kace bazaka sakeni ba wlh baku isa ba " ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Sosai take kuka kamar ranta zai fita MD jin kukan nata Yake har cikin ransa "Bar kukan indai kinason muyi magana ta fahimta" cikin Sauri Zarah ta bar kukan tare da Fara Goge hawayenta "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Saki kike buk'ata ko?Gyada Masa kai tayi"Okay give me 2 minutes"ya fad'a tare da barin dakin ya shiga d'ayan ba ayi minti goma ba taga fitowarsa rik'e da takarda Yana linke ta dukda Zarah abunda take buk'ata a yanzu kenan saida gabanta ya fad'i k'arasa shigowa palourn yayi tare da makullin mota a hannunsa ya ce "Muje na saukeki" a sanyaye Zarah ta bisa parking space taga ya nufa ya fiddo mota nuni yayi mata da ta shiga Ciki ba musu ta shiga horn yayi mai gadi ya bud'e masa get tsit kakejin motar shiru bamai magana har suka isa cikin Makarantar daidai sanda yayi parking Dagowa yayi ya Kalleta daidai Shima ita d'in yake kallo Saurin kasa da kanta tayi "saida sukayi kusan 10 minute bame magana cikinsu kafin MD ya damko hannunta ya sanya mata takardar A hannunta Dagowa tayi tare da kallonsa ta kalli takardar hannunta da bai saki hannun ta ba har lokaci Bayan few minutes ta tsinkayi muryarsa da cew" Murna kike zamu rabu ko"Shiru Zarah tayi gabanta na fad'uwa "Murmushin da batasan ma anar sa ba taga ya sakar mata tare da sakin hannunta ya ce " Ina ne garinku?Shiru tayi saikuma ta ce"basaikaji ba"wani murmushin ya kuma saki ya ce "Bakison na halarci bikin naki kenan?Gyada masa kai tayi alamar eh"muga wayarki ya fad'a tare da amsa kwafar numberta yayi ya sanya a wayarsa Wanda duk bata lura da hakan ba kafin ya mik'a mata ya ce " Gashi Amarya sai wataran"Amsa tayi sosai tayi sanyi" Bud'e gaban motar tafi tare da fita a hankali harta fita MD baibar kallonta ba Itamadin so take ta Kallesa amma nauyi ya hanata Tanajin tashin motarsa ta juya ta dinga Kallon motar har ya bar wajen a sanyaye tayi hanyar hostel Asmy kadai ta samu a ciki tana ganinta ta taso tare da cewa "Ya sakeki dai ko?A sanyaye Zarah ta gyad'a mata kai" Alhmdllh "Asmy ta fad'a Tana shirin amsar takardar Zarah ta rik'e cikin rawar murya tace "bari na fara karantawa " Gabanta na fad'uwa ta warware takardar abunda ta gani ne a ciki ya kusan tarwatsa kwalwarta saida ta gama karantawa tsaf hannunta har karkarwa yake batasan sanda takardar ta zame kasa ba durk'ushewa a wajen Zarah tayi tare da fashewa da wani irin kuka mai cin rai kamar wacce aka aikowa sak'on mutuwa d'ora hannu aka tayi ta ce... 07026166536 *JUMA'AT KAREEM* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_: .........*65 & 66* "na shiga ukku na lalace Asmy shikenan na bani na lalace na shiga ukku na " ta k'arasa fad'a a matuk'ar rude tana d'ora hannu biyu aka "a d'imauce Asmy ta Dauki takardar ta ce " me akayi Zarah"Da hannu ta nuna mata da ta karanta "kafin ta k'ara rushewa da wani kukan Bud'e takardar Asmy tayi gabanta na fad'uwa Ta fara Duba good handwriting dinsa da bai wuce layi shida ba fara karantawa tayi kamar haka" Ko a addinin Christian ba a Aure kan Aure bare addininmu na musulunci da ya haramta hakan Har yanzu har gobe da Aure na akanki basaina yi doguwar magana Ba nasan kina da Ilimi kinsan abunda yake fari da baki Ki rik'e mutuncinki na Matar Aure ban Aureki Dan in sakeki yanxu ba har sai na samu cikar buri na nima kamar yanda kika samu naki zan waiwayeki nan bada jimawa ba ina Kara tuna maki karki sake ki yarda ki bari a daura miki Aure da wani Bayan da igiyar Aure na a kanki bye ki huta lafiya black beauty " "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" Asmy ta shiga maimaitawa tuni idanunta harsun cika da k'walla ta ce "Shikenan ya kashemu bake kika shiga ukku ba Nina shiga ukku Zarah Dana ja miki wannan Abun " ta fad'a itama tana fashewa da kukan sai ya zama.cikin su bamai Lallashin wani Asmy ce tayi dauriya ta mik'e cikin b'acin ran da tajima batayishi ba ta ce "Wlh basu isa ba Jirani naje gidan basu isa su maidamu y'an iska ba me suke nufi " ta fad'a tana wartar hijab d'inta ta fita Zarah ko sosai take kuka Tana Danasanin abunda suka aikata Tabbas sun tafka Babban kuskure da wauta yanzu yazatayi da rayuwarta?Bikinta da ya Hafiz fa ?Taya zai Aure ta Bayan da igiyar Auren wani a kanta?Taya zan iya yiwa Baba bayanin wannan Abun bak'inciki"da wani ido zan kalli mutane shikenan abunda nake gudun ya faru asirina zai tonu Baba banyi maka adalci ba naci amarka naci Amanar tarbiyar da yardar da ka ban....kuka ne yaci karfinta ta kasa k'arasa abunda take cewa a haka har Asmy ta dawo sai huci take "Kingansa?Zarah ta fad'a cikin muryar kuka" Ina fa gidan kulle da kwado ko get man babu "Innalillahi Mutumin nan ya cuceni ya gama da rayuwata Allah ya isa tsakani na dashi" Zarah ta fad'a tana kuka Wayarta Asmy ta dauka tare da dannawa jaber kira yana d'auka bama gaisuwa cikin jaraba ta fara cewa"Daman haka kuke ,K'ananan mutane ne ku daman bamu sani ba ,to wlh kunyi Gina kun tarda ruwa wlh baku isa ba wlh"Jaber da baisan wainar da ake toyawa ba cewa yayi"nutsu kiyimun bayani Dan Allah ma'u me yake faruwa wai"Ai kafi kowa sanin abunda ya faru tunda abokinka ne abunda nakeson ka sani wlh baku isa ba saiya saketa ya
Chapter 54 · 0% Book details