← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 92

Sashe 50

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mun harda Dan so nake na sauke kafin mu gama sch d'innan wlh"Murmushi Zarah tayi ta ce "Insha Allahu zama ki sauke kafin lokacin tunda Kinga yanzu hizif shida ya rage maki" Da daddare Zarah ta amshi haddar Chuchu Inda ta kuma Kara mata wani shafin driver ko tunda yazo yayi ta jira yaga bata nan ya koma ya fad'a ma ogansa bai ganta ba "Okay kawai md yace " Kd ya wuce Ranar Dan yanason ganin Ammynsa "washegari ya koma Zaria Bayan yayiwa Ammynsa bankwana " Zarah ko ranar ma so tayi ta k'ara kwana dandai kawai tana fitowa lectures ta had'u da driver da ba abunda zai maida ita tana zuwa ta samu MD ya hakimce a kan kujera a takaice ta gaisheta tare da wucewa ciki....after 3 weeks Rabin rayuwar md yanzu kam ta dawo Zaria saboda koda yaushe yana nanike da Zarah yana kwasar romo ko sch yanzu dak'yal yake barinta ta tafi Zarah ko tana nan tana lissafin sauran wata guda ra rage yarjejeniyarsu ta kare inda karatunsu ya rage wata biyu su gama tun daga lokacin da ta zubar da maganin nan bata Kara waiwayar sha ba kwata_kwata tunaninta ma baikawo mata komai a ranta ba harkar gabanta kawai take "Yauma dak'yal MD ya rabu da ita Dan a safenma yanzu ba d'aga mata yake ba cikin Sauri ta gama shirinta Zata wuce sch tana shirin fita Ya ce " kijira na saukeki hanyar nayi"to"ta fad'a a hankali tare da zaunawa gefen gadon tana nan harya gama shirinsa ya fito Cikin shigarsa ta alfarma da gayu sai baza k'amshi yake kallo d'aya Zarah tayi masa tayi kasa da kanta saboda gabanta dake tsananin fad'uwa a tare suka fita Inda ya shiga driver sit ta zaga ta shiga gaba sun fara tafiya kenan ta Hango wata yarinyar mai tallar ta aya a faranti cikin Sauri ta d'ago tare da cewa "Dan Allah ka tsaya zan saya abunchan" Kallonta yayi tare da Kallon abunda take nuna masa ya ce "me zakiyi da abunchan ya gama shan kura a titi jifa " Tana Shagwabe fuska ta ce "Nidai ina so" parking yayi tare da mik'a mata 1k ya ce Amshi ki saya zage glass din motar tayi cikin Sauri ya sadda kansa Dan karma wani ya gansa a ganesa Zarah ko mamakinsa tayi kamar wani marar Gaskiya Juyawa tayi ta kira mai ta ayar Inda ta saya ta 500 ta bar mata chanjin a leda aka sanya mata har lokacin kan MD sadde saida ta Zage glass din kafin ya d'ago ya tada motar sukayi gaba kasayin shiru Zarah tayi ta ce "Wai Dan Allah me yasa baka San ana ganinka yanzuma ka sadda kanka " Is not your business "ya fad'a yana cigaba da driving" Turo baki gaba tayi tare da Fara cin ta ayarta har wani lumshe ido take Dan sosai tayi mata dadi ita kanta mamaki take da bata tabajin sha'awar wannan Abun ba Amma yau sosai taji dadinta Ta wutsiyar ido MD yake kallonta yanda ta dage take gintsar Abu da shi baimasan menene ba "bismillah" ya tsinkayi muryarta"Alhmdllh kici kayanki""Ka dandana kaji da dadi "Girgiza kai yayi a takaice ya ce "Banajin irin abubuwan nan" tab'e baki tayi tare da cigaba da cin abunta har cikin makaranta ya kaita Daidai gab da hostel d'insu yayi parking sauran ta ayar ta sa a jaka tana shirin fita Ya ruko hannunta Tare da damk'a mata 5k a hannu ya ce "Ki dawo da wuri yau please da yazo ki biyosa kidaina tsaidasa" Kasa tayi da kanta Tare da cewa"Toh ngd"har lokacin bai saki hannunta ba Ganin irin yanda yake kallon hannun tare da murzasa tanason tayi magana amma kwarjini yau da yayi mata ya hanata Chan Bayan few minutes ya ce "Kidingayin lalle zaiyiwa hannunki kyau inason ganin lalle a hannun mace"gaban Zarah na fad'uwa ta d'ago ta Kallesa saikuma tayi saurin kasa da kanta samun kanta tayi da cewa " To kace Matarka ta dinga yi maka mana"Murmushin da bai shirya saki ba ya saki ya ce "Kenan sai matata zatayi mun" Eh"ta fad a hankali"wani murmushin ya k'ara saki ya ce "To Matar wata Tara nace ta dingayi yimun ba ta gidan ba" ba tare da ta Kallesa ba ta d'an turo baki gaba ta ce"Matar wata d'aya dai ai wata Tara baya ne yanzu saura wata d'aya ko ka manta"ina sane harkin k'agara lokacin yayi mu rabu ko"D'ago da dara daran idanunta tayi ta sauke a kansa saitayi saurin kasa da kanta ta ce "Ina makara karya hanani shiga" Okay "ya fad'a yana sakin hannunta bud'e motar tayi tare da fita Daidai idonta ya sauka akan Hafiz dake gaban motar Kad'an sosai taga ya kara kyau da kiba yasha shaddarsa ash mai shegen kyau Ya harde kafa d'aya kan d'aya a jikin sabuwar motarsa sosai gabanta ya tsananta fad'uwa da karfi dafe saitin zuciyarta tayi daidai sukayi ido hud'u da shidinma ita yake kallo bako k'iftawa sannan yana bin motar da ta sauka da Kallo a matuk'ar rude ta juya ta kalli MD dake cikin mota har lokacin yaki tafiya Shima Inda take kallon yake Kalla Juyawa tayi ta k'ara kallon Hafiz da Shima motar MD yake kallo dukda baya ganin Wanda ke ciki lokaci guda Zarah taga fuskarsa ta sauya Wanda Bata tab'a ganin hakan a tattare dashi ba kamar wacce kwai ya fashewa haka ta k'arasa Inda yake ta kalli bayanta ta kalli gabanta haka ta dingayi ga MD yaki tafiya cikin jarumta ta k'arasa Inda Hafiz yake da har lokacin kallonta yake ya kalli motar da ta sauka dak'yal ta iya tattaro jarumtar da bata San tana da ita ba ta ce " Ya Hafiz Kaine da gaske kuwa"Juyowa yayi ya kafeta Da idanu tare murtuke fuska tamau nuna motar da ta fito daga ita yayi cikin muryar b'acin rai ya ce........... 07026166536 domin neman Karin bayani _Tofa ya kenan Ga MD ga kuma Hafiz_ *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ ...........*61 & 62* "Motar waye naga an sauke ki," A matuk'ar firgice ta d'ago ta Kallesa sai kuma.ta kalli motar da har lokacin yaki tafiya sosai Zarah ta shiga rud'u "nace motar waye kika fito.daga ina kike tun d'azu nazo school d'innan ina jiranki ina kikaje?Zarah rudewar da tayi batasan sanda taji hawaye na zubo mata ba hangosu da Asmy tayi ya sanya gabanta fad'uwa tasan Hafiz yazo tun d'azu yake jiran Zarah dalilin karyar da zatayi masa ma ta rasa hakan ya sanyata kin fitowa Dan tunda ta fito ta ganshi tamaza ta koma yanzunma fitowa tayi Dan ta kirkira k'aryar da zata masa saita iske abunda ya k'ara tayar mata da hankali tundaga saukar Zarah a motar MD har zuwa yanzu da Hafiz ke daga mata murya akan idonta komai ya faru dak'yal tayi jarumta tare da karasawa Inda suke ta ce " Ya Hafiz Kaine kuwa da gaske ko gizau ne kake mun?Dukda Hafiz hankalinshi tashe yake bai hana yiwa Asmy murmushin k'arfin hali ba ya ce "Nayi 30 minutes a nan nayi ta Kiran layin ta kashe shiyasa na tsaya najirayi b'ullowarta ashe mugun Abu zangani dubi motar da aka sauke Zarah a ciki Asmy na tambayeta waye shine Kinga ta durkushe ta sanyamun kuka"Kallon motar Asmy tayi saikuma ta kalli Hafiz ta ce " wayyo ya Hafiz Motar malamin muce kasan itace amirar makaranta to shine dazu da safe aka gayyacesu 'a wata makaranta da za ayi safka shiyasa ya tafi da ita saboda shine shugaban mss din na makaranta kaga kuma sundawo inaga to sabani ma kukayi Dan itama bata wuce 30 minutes ba da fita"y'ar Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke ya ce "Dukda haka bai kamata ta shiga ba motarsa ba sanadin yace yana sonta ne ko yayi sha'awar wani Abu daga gareta Gaskiya bazan lamunta da haka ba " Tsohone fa yaya Hafiz Ya haifeta sannanma matanshi hud'u kuma malami ne ustaz kuma ba ita kadai suka tafi ba yanzu haka da diyarsa a cikin motar "Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke ya ce " Wlh har Naji sanyi karkiji yanda hankali na ya tashi Ina son Zarah sosai Asmy kinsan da haka Ina tsananin kishinta da zanso ko kuda bazan bari ya tab'a ta ba sannan Ko k'aramun yaro bazai kallemun ita ba please Ki dinga lurarmun da ita na damk'a miki amarta a hannunki "murmushi asmy ta saki. Ta ce Uhm su ya Hafiz manyan kishi karka damu ai aski yazo gaban goshi insha Allah nan da wata biyu munbar sch d'innan kaga kuwa kana gab da mallakar kayanka " kasaitaccen murmushi Hafiz ya saki ya ce "Gaskiya kinci kyauta fa " Y'ar Dariya Asmy tayi nan ta gaishe shi kafin ta wuce Lectures durkusawa Hafiz yayi daidai saitin kunnanta ya ce "Sorry my bride banzata haka abun yake ba kiyi hakuri" Shiru Zarah tayi ta cigaba da shasheka"Oh My god "ya fad'a yana daga kanshi kafin ya k'ara cewa " Kiyi Hakuri my Zarah Bazan sake ba Kinga laifinkine da bakiyimun bayani ba "Sai lokacin ta d'ago turo baki tayi tare da cewa " shine saika rufe ni da fad'a "wara idanu yayi ya ce " ni na isa nayiwa gimbiyata fad'a kiyi hakuri baki ma murnar gani na ki Mike please "Goge hawayenta tayi tare da mik'ewa Shima ya Mike murmushi suka sakarwa juna Zarah ta ce " amma kayi surprised Dina sosai ya Hafiz "Fuskarsa sauke da murmushi ya ce " Daman surprised d'inki naso yi shysa banfad'a maki na dawo ba "Yaushe ka dawo" Jiya Tun jiyan naso nazo naga gimbiyata yanda ta koma sai dare
Chapter 50 · 0% Book details