← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 92

Sashe 75

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

safe tun tanajin Abu Kad'an har yazo yayi yawa Sosai take zufa a d'akin tana yarfe hannu tuni ta fara fita hayyacinta sunan Allah kawai take Ambata a haka Chuchu ta shigo ta sameta tana ganin haka a d'imauce ta ruga wajen Ammy ta ce "Ammy kizo kiga yanda momcy take zai zufa take kamar ta mutu" ba shiri Ammy ta mik'e ta sanya hijab d'inta ta ce"inaga haihuwarce tare suka koma d'akin Inda suka tarar da Zarah na murkashi Sannu Ammy tayi mata tare da kamata ta kalli Chuchu tace "yi Sauri D'auko hijab d'inta Da Sauri Chuchu tasa mata hijab tare da takalmi su biyu suka kamota har wajen motoci Inda Chuchu ta kwalawa driver kira ba shiri yatado mota Tare suka shiga su Ukku Chuchu dukta rude asibitin mafi kusa dasu suka nufa da ita Inda suna isa aka wuce labour room da ita zirga zirga kawai Ammy take da Chuchu Sosai zahra take karb'ar wuta tayi awa guda tana wahaltuwa sosai takejin wata irin azaba da tunda uwar da ta haifeta bata tabajin irinta ba D'aya Daga cikin likitan d'aya duba ta ya fito ya kalli Ammy ya ce " A Gaskiya Hajiya Kuyi hakuri Ayi mata cs bazata iya haihuwa da kanta ba sakamakon Rashin bud'ewa da batayi ba na Auna bata Inda zata iya haihuwa Inma akace dole saita haihu da kanta Gaskiya zata wahala over sannan abunda ke cikinta Shima zai wahala"Innalillahi Ammy ta fad'a ji take kamar ta fashe da kuka ta ce "Dr Kuyi mata Cs din kawai Kar wani abun ya sameta" Chuchu ko kuka ta fashe dashi Okay "Zamu shirya yi mata yanzu amma ana buk'atar ganin mijinta da mahaifinta da Susa hannu" Ba matsala dr ku shiryata yanzu mijin nata zaizo saiya wakilci nbaban nata tunda emergency ne cikin Sauri Ammy ta kira MD Cikin tashin hankali ta ce "Ka sameni a asibiti" Bayan ta fad'a masa sunan asibitin ta kashe ba ayi 20 minutes ba saiga MD yazo afutatan wajen Ammy ya nufa ya ce "Lafiya ammy" Da sauki Zahra ce Zata haihu muka kawota sunce bazata iya haihuwa ba sai anyi mata cs shine muke buk'atar sa hannunka"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ammy yanzu tana ina Ina ne za a sa hannun"Sosai MD ya rikice ya rude Shi ya sanya hannu kuma shi ya bada jininsa kasancewar group o garesa suna gani aka shiga Theater room da zahra sosai Chuchu ta fashe da kuka Ganin kamar zata rasa kawartata Ammy ma hawaye take tana addu'ar Allah sa ayi aikin lafiya MD ma addua kawai yake hankalinshi a matuk'ar tashe yake "Ba ayi 30 mminutes ba sukaga fitowar dr D'auke da jariri a hannu fuskarshi d'auke da Fara'a suna ganin haka suka Kallesa Ammy ta ce " An sauka"Alhmdllh Dr ya fad'a yana mik'a mata jaririn"Amsar jaririn Ammy tayi "Allahu akhbar Allahu akhbar" kawai Ammy ke fad'a ganin yau ita ce rik'e da jinin MD a hannunta shiko gogon har yanzu gaba d'aya hankalinshi yana kan ga wani hali zahra ke ciki Nurse biyu suka ga sun Kara fitowa rik'e da wasu jariran a hannu"sai sannan MD ya kusa daskarewa ganin sun nufo su da Yaran Daya daga cikin nurse ta mik'awa MD.jaririyar ta ce "Congratulation Sir Allah ya raya" d'ayar kuma ta mik'awa Chuchu da itama ta daskare a wajen Kallon y'ar MD Yayi ya kalli sauran yaran dake hannun Chuchu da Ammy kamar Wanda bakinshi yayi masa nauyi ya ce "Kuna nufin Duka yaran nan aka ciro kuma Duka nawa ne" Murmushi nurse din tayi ta ce "Triple ta haifa gasunan Allah raya "farincikin da MD ya shiga fadarsa bata baki ne ji yake tamkar a mafarki wai yau shine Allah yaba yara har Ukku baisan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zubo masa ba ya goge ya ce " Alhmdll....... *Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ ...........*83 & 84* Gaba d'aya MD yana rikice ya rasa wace irin Godiya zaiyiwa Allah s w a da yayi mashi wannan gagarumar kyautar yara Ukku lokaci guda yana Rungume da babyn yayi sujudu shukur sosai yake kwararo yabo da gdy ga Allah s w a Kafin ya bud'e fuskarsa d'auke da murmushi kamar gonar Auduga ya kalli Ammy ta ce "Ammy wai wannan din Duka yara na ne da gaske" murmushi kawai Ammy ke masa Dan farinciki harya mantar da ita wani b'acin rai Ta ce "yaranka ne babana " Daga hannu ya sakeyi ya ce "Allah Alhmdllh Alhmdllh bansan da wasu kalamai zanyi amfani ba wajen gode Maka " murmushi kawai suke Chuchu ma uwar kuka yanzu andawo murmushi cikin d'oki ta ce "Yaya wlh Duka kamarsu d'aya kuma dakai sukayo kama " daidai lokacin da na hannun Ammy ya fara kuka jijjigashi Ammy tayi ta ce "Yi Sauri Babana Kaje gida D'akin nan na kusa da na Chuchu zakaga kayan jarirai kodan ku tafi da chuchun Aje a d'auko duk abunda ya kamata sannan Ka taho da Dabino mai laushi tare da zamzam ka basu " to to Ammy Amma ya jikin nata ita mu bari a fito da ita"Jikinta Alhmdllh Dr ya ce "anwuce d'akin Hutu da ita bazamu samu ganinta yanzu ba allurar bata sake ta ba kuje ku kawo kayan yaran" Mik'a mata Namijin Chuchu tayi shiko MD Kallon yarinyar kawai yake dake tsala kuka yana murmushi wai yau shine rik'e da jininsa sosai yaji k'aunar yaran ta musamman Na ratsa sa wata nurse ta amshi yaran biyu Ammy ta rik'e d'aya Dan Aje a shirya su Kafin a kawo kayan "Cikin doki Ammy ta kira Zey tayi mata albishir Hajiya kaka takeson kira ta mata albishir to bata San taya zatayi musu bayanin zahra ba Hakanan dai Ammy ta lalubo number Hajiya Bayan suun gaisa ta ce " Hajiya Albishir na kira miki addu'ar ki dai ta amsu Matar MD ta sauka yanzu an haifi y'an Ukku"Ammy saida ta kauda wayar daga kunnanta saboda irin. Bud'ar da Hajiya ta rangada kira take "Alhmdllh Alhmdllh Ina kike rukayya maza taho ki kiramun iyayenki muyi musu Babban Albishir Matar Mustapha ta haihu"Ammy lura da Hajiya murna tama mantar da waya ya sanyata katse wayar tana murmushi ta window ta lek'a ta Hango zahra dake baccin wahala sanye da blue din rigar da aka gama mata aiki hannunta biyu Duka sanye da kalula d'aya Karin jinin da aka diba a na MD ne d'aya kuma Karin ruwa ne Goge hawayenta Ammy tayi ta ce "Allah ya baki lafiya zahra ya tashi kafadunki" ba ayi Minti goma ba saiga zey ganin yanda ta fito daga motar kasan ba karamun gudu ta sharara ba cikin farinciki ta ce "Ammy da gaske Ta haihu kuma y'an ukku yayanmu ahima ya zama uba" Murmushi ammy tayi mata ta ce "da gaske zainab kinga ikon Allah ko Yanzu haka Ana ciki ana shirya yaran ana jiran su maryam su kawo kayan da za a sanya musu kinsan a dimauce muka zo " Ajiyar zuciya zey ta sauke tare da goge hawayen farinciki ta ce "Alhmdllh ammy Adduar tsawon shekaru goma ta amsu Ta inda ba ayi tsammani ba ina mamyn take yanzu?tana ciki kinsan cs akayi " wayyo Allah ya bata lfy kaico "ba a dau lokaci ba su Chuchu sunkadawo tana rik'e da kayyayakin MD fara'a ta kasa barin fuskar sa sai nan nan yake Bayan an shirya yaran nanfa Chuchu ta shiga yi musu hoto Kamarsu d'aya har macen dukansu kuma da dimple d'insu irin na zahra dukda jariraine amma saida suka fito Fari da kammani da kyau duka MD suka biyo dimple din zahra kadai suka biyo nan fa aka shiga liliyar yaran d'aya Bayan daya MD ya d'aukesu ya tauna musu Dabino da zamzam rik'e Namijin dayan yayi yana ta kallonsa kamar zai cinyeta sai Murmushi yake yanajin wani irin farinciki na ratsa sa Ammy bata damu da irin rawar k'afar da MD yake ba ko Kara bayayi saboda tasan dole yayi abunda aka ta roka tsawon shekara goma yanzu Allah ya kawo ai dole yayi rawar kafa ganin yaran sun fara kuka ne ya sanya hankalin MD tashi duk ya rud'e Kallon Ammy yayi ya ce " please Ammy me za ayi musu suna kuka fa "Harararsa Ammy tayi ta ce " Waikai baka da ta ido"Sosai k'eya yayi ya ce "Ba haka bane Ammy kar wani abun ya samesu" girgiza kai kawai tayi koda Chuchu ta kira Asmy ta fad'a mata irin ihun murnar da tayi bana wasa bane farincikin data shiga bana wasa bane Koda ta fad'awa mamansu itama tayi farinciki matuka tana Jinjina ikon Allah tare suka shirya a motar babansu ya taho dasu Kaduna Dan suga jikin na zahra tunda ance musu cs ne "Kafin one hour sun Iso sosai Ammy ta karramasu da girmamasu dukda a Asibiti ne akayiwa juna barka Asmy ko tunda ta rik'e macen taki ba kowa saida tayi hawayen farinciki wai wannan din Duka yaran zahra ne nanfa hankali ya koma jiran farkawar Zahra Dan har yanzu saida su lek'a ta window MD ko tsaye yayi a jikin window din sosai yaji tausayinta ya k'ara kamashi ganin halin da take ciki saida yaga y'an gidan su Asmy tukwana yabar jikin Window din sai wajen 4pm zahra ta farka koda ta bud'e idonta Kallon d'akin ta dingayi kafin ta kalli jikinta da hannunta duk drip yunkurawa tasoyi Dan ta tashi amma ta kasa komawa tayi tana lumshe ido wasu hawaye na zubo mata tunowa da wahalar da tasha dazu bata manta da lokacin da za ayi mata cs ba kasancewar bata ido
Chapter 75 · 0% Book details