Sashe 60
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi kasa kasa cikin k'asa da murya ta ce "A tunaninki haka zan zuba ido ayi Auren nan ina nan ina ganinku wacce ta tsonemun ido ta rigaku Aure Aurenma kuma gidan Hutu ai abunda bazaiyu bane kusa ido Kuyi kallo wasa na gaba Dole zan saki jiki ayi komai dani saboda idan Abu ya lalace kar a zarge ni kina gani dangin Malam ba wani kaunata suke ba so suke ayi tashin hankali Wanda ni ban shiryawa haka ba ... Zarah ko tana shiga daki ta zunduma duniyar tunani gani take abun kamar mafarki Bikinta da Hafiz Wanda inbanda wannan K'addarar ta afka da ba Wanda zai kaita farinciki amma Kuma yanzu Shine take fargabar Auren to wai yanzu haka zata zuba ido A daura mata Aure kan Aure batasan sanda wasu hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata ba Cikin muryar kuka ta ce " Ya Allah ka kawomun mafita a cikin al'amarin nan kafi kowa sanin halin da nake ciki Kaine mai iko akan komai babu abunda ya gagari ikonka ya Allah Kakawo mafita ta yanda ban tsammaceta ba Allah na tuba Ka yafemun Ka cireni cikin kangin rayuwar nan nasan wannan din duk yana cikin jarabawa ta ne ya Allah ka sassautamun jarabowowin nan da suke bibiyata tun yarinta ka kuma bani ikon cinye su kuka ne yaci karfinta Sosai tashiga rera kuka Daren ranar Zarah raba dare tayi tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin rayuwarta..... a halin yanzu y'an uwa da dangi na nesa da na kusa duk sunzo domin ayi kome dasu Maman Asmy ma sosai take taka muhimmiyar rawa a bikin nan da za ayi dangin Baban Zarah sai Godiya suke mata na jajircewa da tayi tamkar bikin y'arta za ayi Dan wani irin tsumi takeyiwa Zarah dukda kwana biyun nan ba lafiya gareta ba yauma da Hafiz yazo da dare dak'yal ta samu ta fita cike da damuwa ya ce "Wai Dan Allah me yake damunki ne my Zarah bana gane maki kwannanfa" Kasa tayi da kanta tana maida hawayen da suka zubo mata Dan karya gani kasancewar duhu ne cikin rawar murya ta ce "Bakomai kawai banajin dadi ne" subhanalla ankaiki asibitine"eh Maleria ce" ta basa amsa Dan karya ce saitaje asibiti Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Allah ya baki lfy please kidinga shan magani sosai yanda zaki warke da wuri saida biki ya matso Maleria zatayi mana cikas " Shiru tayi batace komai ba "Kamo hannunta yayi abunda bai tab'ayi ba cikin firgici ta d'ago ta Kallesa Duka hannun nata biyu ya rik'e yana kallonsu tare da murzawa cikin Sauri tayi saurin kwace hannunta ta kauda kai tana hade rai" Sai sannan Hafiz ya dawo cikin hayyacinshi ganin yanda ta had'e rai dukda duhu ne ya ce "Sorry" a sanyaye ta ce "Dare nayi" Okay Good Night dinkunan nan dai sunyi kyau ko?Gyada masa kai tayi dukda ko kallon d'inkin batayi ba saboda yanzu bata wannan take ba "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Duk abunda kuke da buk'ata keda kawayenku kuyimun waya "Insha Allah " ta fada a sanyaye Bayan sunyi bankwana ta koma gida Nanma saida ta kafa sana'ar tata ta kuka tana jin bata kyautawa Hafiz ba a halin yanzu Zarah bata da wata mafita data wuce Ta Allah Shi kawai take jira yayi ikonsa akan Abun tasan ko giyar wake Tasha bata isa ta tunkari wani da wannan Maganar bare yanzu da biki ya rage saura kwana shida.... "Ammy ba haka bane kiyi hakuri Dan Allah"ya fad'a cikin ladabi"Bani ya kamata kaba hakuri ba Matarka da kayiwa laifi ita ya kamata kaba hakuri"laifi kuma Ammy to me nayi mata "Ohh tambaya ta ma kake me kayi mata Bayan banzatar da ita da kayi Tunda akace tana da ciki baka Kuma waiwayarta ba " Ba haka bane Ammy kumin uzuri please yanzu ina amerar take "Ta tafi Gidansu kasan halinta ba sake mana take ba washegari ta shirya ta ce " zata wuce gidansu Ta kwana biyu ta warke a chan'?"Niko ban hana ta ba nace Allah ya kiyaye nasan duk haushin abunda kayi mata ne yasa ta tafi"Zankirata Ammy ina Hajiya wai tunda na shigo ban ganta ba "Dazu ta fita Ta lek'a gidan Zainab ne " Okay Chuchu fa "bai rufe baki ba yaga shigowarta palourn hannunta rike da waya kai tsaye wajenshi ta nufa fuskar ta cike da fara'a ta ce " Lah yaya yaushe kazo ina yini"Alhmdllh Auta ya gidan"Lafiya qalau ta fad'a tana zaunawa gefenshi tare da cewa "Yaya kazo a Daidai tun safe na rasa shawarar Wanda zan nema bikin momcy ne ya taso za ayi Saturday d'innan ina son ne na tafi wednesday tun gobe ma naso na tafi wlh ammy ta hana wai sai wednesday to shine zanyi mata gudummawar jaka nakirata akan taturo mun hotonta na biki tace batayi ba gashi nafison nayi mata mai hoto to shine nake gani ko hoton waya zaiyi akwai hoton Dana tab'a mata a hostel kuma yayi clear sosai bari ka gani kaga idan zaiyi ayi dashi ko kuma Wanda muka tabayi tare Shima tayi kyau saikaga idan zaiyi a datse ni " ta fad'a tana nuna masa hotonta data tab'a mata da Abaya ta ce Kalli yaya Dan Allah kana ganin zaiyi "Amsar wayar yayi daidai idonshi yakai masa hotonta sanye cikin doguwar Riga Abaya ta yafa beil din rigar Dimple d'inta Duka sun lotsa sakamakon murmushin da tayi a hoton sosai hoton yayi masifar kyau Kallon mamaki ya dinga bin hoton dashi kafin ya d'ago ya kalli Chuchu da itama shidin take kallo ganin yanda ya rik'e wayar gam yana yiwa hoton wani irin kallon mai kama Dana mamaki maida Kallonshi yayi ga hoton Kara murza idonsa yayi Dan son tabbatarwa itadince kuwa koko gizau ne Tabbas ita ce " ya fad'a a ransa "Kafin ya sake Dagowa ya kalli Chuchu a karo na biyu ya ce......... 07026166536 domin magana da marubuciyar kai tsaye *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ .........*71 & 72* "Daman ita ce momcy din taki?Gyada masa kai tayi ta ce " Eh ita ce Yaya"ita ce mai muryar nan kenan?Nanma sake gyada masa kai tayi"Maida Kallonshi yayi ga hoton yana mamakin kenan k'awar Chuchu ce da takeji dinnan da ita yayiwa haka sosai Abun yazo mai a bazata yanda bai tab'a kawowa a ranshi ba "Kallon Chuchu ya kumayi ya ce " sunan ta na Gaskiya"Zarah Yusuf yaya ko ka Santa ne Wai"Zarah Yusuf ya maimaita a ransa Tabbas ita d'ince "Kafin ya kalli Chuchu ya ce " ta ina zan Santa Bayan ba tab'a ganinta nayi ba "Eh yaya Amma kagani ko ta had'u sosai ko?Ba Laifi ya fad'a yana Mikewa " binshi tayi ta ce "Yaya ina zaka kuma Bayan baka bani shawarar abunda zanyi mata ba bakace hoton yayi asashi ba "duk yanda yayi miki kiyi amma karkiyi mai hoto ?,binshi tayi ganin ya nufin hanyar stairs ta ce " Yaya Saboda me nafison nayi mata me hoto"Saboda bazaiyi kyau ba da hoto please ki barni na huta "ya fad'a yana hayewa sama Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma palour gefen Ammy ta zauna tana d'ora kanta kafadarta ta ce " Ammy wai kinji yaya kar ayi me hoto ko ayi me sunan kawai"Amsar hoton Ammy tayi ta ce "Masha Allah hoton yayi kyau amma kiyi mata mai sunan kawai zaifi watak'ila batason saka hotontane kinsan y'ar tawa ustaziya ce " Murmushi Chuchu tayi sosai takejin dad'in yanda Ammy ke son kawar tata ta ce "To shikenan Ammy wai Kinga da yaya yaga hotonta wlh saida yayi ta Kalla Kinga yanda lokaci guda ya sauya kamar daman ya santa" Murmushi Ammy tayi ta ce "Yanzu ba wannan ba kiyi Sauri ki kira mai jakar kar lokaci ya k'ure " Mikewa tayi ta ce "Barima kawai na tafi da kaina na masa bayani Dan gobe nakeson su iso guda D'ari biyar ai sunyi ko Ammy,?" Ta fad'a tana yafa beil"Eh sunyi please ki dawo da wuri banda gudu da mota a titi"......MD tunda ya shiga d'akin ya rumtiya duniyar tunanin Zarah Bai tab'a tunanin Zarah zata kasance itace kawar Chuchu kuma ita ce mai Qiri'ar wannan data ki barin kwalwarsa "sosai yaji zuciyarsa ta k'ara chunkushewa a halin yanzu baya da buri da yake dashi fiye da na ganin yarinyar tunda suka rabu Baccin kirki baya iyayi batare da tunaninta a ransa Wanda shi kanshi har mamakin hakan yake amma sai ya lakanta hakan da tausayinta ne da yake A ransa ya ce Tabbas wannan babbar dama ce ta sameni da zanyi amfani da ita wajen Gano Address d'inta Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " wannan Karin da Chuchu zanyi amfani"Wayarsa ce tayi ringing Ganin Amera ce Ke kiran ya sanyashi picking baiyi mamakin kin masa maganar kin kulata da yayi kwana biyu Dan yasan indai tana gidansu bata da matsala bataki ya barta tayi wata a gida ba Bayan sun gama waya baice yaushe zata dawo ba haka batace masa zata dawo ba dukda tana son ganinshi. Yau Tuesday Zarah ta tashi da zazzabi kin fad'awa kowa tayi ciki harda Asmy ranar mai lalle tazo dak'yal ta daure akayi mata danma a gidan su Asmy akayi mata ba Mutane sosai sai wasu cousin sisters d'inta na wajen Baba da sukazo Akayi musu tare sosai K'unshin Zarah yayi masifar kyau sai sannan ta fito a Amaryar Washegari Laraba tunda Safe sukaje saloon dukda tana Kokarin nuna ba komai a fuskarta ana cikin yiwa Asmy Bayan Angama yiwa Zarah tana gefe wayarta ce tayi ringing dubawa tayi taga Chuchu ce