Sashe 61
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bayan tayi picking daga bangaren Chuchu ta ce " yanzu zantaho sis ki turomun Address d'in gidan idan nazo Funtua wace unguwa zance"Sosai Zarah tayi kokari wajen daidaita Nutsuwarta ta ce "Jabiri Gidan Malam Yusuf Zakice " okay to gani nan insha Allah "Murmushin k'arfin hali Zarah tayi ta ce " Allah ya kawoku lafiya"Bayan sungama wayar angamawa Asmy gida suka wuce tare. <KD> K'aramar akwati chuchu ta zuba kayanta sai murna take yau zata hadu da su Zarah 50k Ammy Ta bata ta kai gudummawarta Dan tace bazata samu halarta ba Bayan ta fito Harabar parking space d'in gidan Driver ya saka mata akwatinta a boot MD ya fito fuska ba walwala "Karasawa Inda yataho tayi tana kamo hannunshi ta ce " yaya yanzu zan tafi daman kai nake nema "yana Kallon motar da zata tafi ya ce" Wani gari ne zaki?Funtua ne Yaya ka manta bikin momcy da na fad'a maka"yaushe ne d'aurin Auran Asabar ne " shine zaki tafi tun yau Dan azarbabi "kamar zatayi kuka ta ce " Dan Allah yaya karkace zaka hana wlh mune manyan kawaye idan banjeba tun yanzu sai yaushe"Dan tasan halinshi sarai sai yace zai hanata "Jim yayi kafin ya kalli driver ya ce " fito da kayanta Daga motar nan zankira Wanda zai kaita "Jaber ya dannawa kira Bayan ya d'auka ya ce " Bloody Dan Allah ba abunda kake yanzu"Daga bangaren jaber yace "bakomai ya akayi" Inba damuwa kazo gidanmu ina son ganinka"Okay gani nan zuwa kana gidan "Eh" Kallon Chuchu yayi ya ce "Koma ciki kafin yazo ya kaiki" To yaya "ta fad'a tare da Juyawa Dan ta lallab'ashi karyace bazata ba ba ayi 30 minutse ba Jaber ya Iso gidan a palourn sa na part dinsa dake gidan suka yada zango..shiru jaber yayi Bayan ya gama sauraren MD Dagowa yayi ya Kallesa ya ce " Allah ne ya kawo mana mafita cikin Sauk'i amma nayi mamakin yarinyar da iliminta da komai zata yarda a d'aura mata Aure kan Aure "Numfashi MD ya fesar ya ce " Ni kaina nayi mamakin ta dalilin sanin ilimin nata bazata yarda a d'aura auren ba Alhalin da igiyar Aure na akanta ya sanya harna rabu da ita kafin Allah ya kawo mana mafita amma kana gani komai na shirin jagulewa"Ai bazaiyu a daura Auren nan ba Tunda muka samu address d'inta ai mungama samun dama Dole ne za a fasa Auren nan "Cewar Jabir "nasan da hakan bazan tab'a yarda A tabka wannan Babban kuskuren ba Amma tayaya kake ganin zamu magance matsalar" Ka barmun komai a hannu na bloody yanzu ba zankai Chuchu garin ba Kuma zangano gidansu ai magana ta k'are"Numfashi mai zafi MD ya fesar ya ce "Allah fitar damu" Ameen bari naje na sauketa kawai kome kenan saina dawo "Gyada masa kai MD yayi yana lumshe ido kan Kujera Bayan tafiyar su Chuchu ya jima yana sake_sake a ransa gabak'i d'aya kanshi ma ya kulle akan Lamarin yarinyar nan lumshe ido yayi kafin ya bud'e ya ce " Allah yasa ta tabbata ciki ne da ita Ya rabbissamawati"ya fad'a yana daga hannu yana rokon Allah ji yayi duk duniya yanzu kuma ba abunda ayake da buk'ata irin yara sosai yaji soyayyar cikin dukda bai tabbarba shi kanshi da akwaishi ko babu Amma zuciyarsa tafi rinjaya masa Akan akwai cikin wayarsa ya lalubo daidai numberta da yayi save da "Mamy" ya dinga kallo kamar kullum sai yayi kamar zai Danna mata kira wata zuciyar ta hanesa Dan yasan har yanzu fushi take dashi lumshe ido yayi a hankali ya furta "Simple babe baki da hayaniya " Kara lumshe ido yayi tunowa da zazzak'ar qiri'arta Da har yanzu idan ya tuno yakanjita a tsakiyar kansa ya ce "Ashe kece mai zazzak'ar muryar nan" Juyar da kansa yayi gefe saikuma ya saki murmushi ya ce "Koya taji.lokacin da ta ga takardar nan" Samun kanshi yayi da tsananin Bukatarta a kusa dashi koba komai irin zaman da sukayi dukda na d'an lokaci ne yana yi masa dadi sosai dabi'un yarinyar da hallayarta yake burgeshi Kara juyi yayi kan kujerar ya bud'e idonsa ya ce "Ashe kece kika k'ara inganta rayuwar kanwata Tabbas baki chanchanci Rashin Kyautatawa daga gareni ba ,dole ne na gyara kuskuren da nayi a baya wata zuciyar tace masa " To idan fa Chuchu suka gane kayi mata haka ya zasuji"tsaki yaja ya ce "Ai ba Laifi na bane Laifin Jaber ne tun Farko daya kawo wannan muguwar shawarar " To me yasa ban Sake ta ba "Wata zuciyar ta basa amsa da " saboda kana tausayinta" "tausayi kamar ya " ya k'ara tambayar kansa "Tausayi irin na musulunci " idan kana tausayinta me yasa da yarjejeniyar auren ku ta kare kak'i sakinta ta auri wanda take sonsa yake sonta "Saboda ina son inganta rayuwarta" Shi wancen sani kayi da har bazai inganta rayuwarta ba "Suk shi daya yake maganganun nan da zuciyarsa "tsaki yaja tare da buga kansa da hannu da karfi ya ce "OH MY GOD" na zauna ina ta tunanin k'aramar yarinya zata chazamun kai ". Jaber yana sauke chuhu ya karema gidan kallo daga mata boot yayi ta fito da kayanta da kuma gudummawar jakunkunan da suke a wata k'atuwar leda zagayowa tayi Inda yake gaban mota bai fito ba ta ce " yaya Jaber Please ka fito ka taimakamun d'aukar akwatin nan wlh tayi nauyi "Harararta yayi ya ce " wannan Dan Abun ne bazaki iya d'auka ba Kice zasu kwana anan"Turo baki gaba tayi ta ce "Shiyasa banso Yaya yace kai zaka kaini ba wlh dan nasan kaima duk kusan halinku d'aya" Dariya yayi ya ce "Kome zakice kice " Tana shirin sake magana ta Hango Asmy ta fito daga gidansu ta nufo Inda take jaber na ganin asmy gabansa ya tsananta fad'uwa karta zo ta ganesa asirinsu ya tonu wajen Chuchu Dan yasan Sarai Asmy ba control gareta ba cikin Sauri bai saurari Chuchu ba yaja motar da karfi tare da saurin barin arear da Kallo Chuchu tabi motar Kafin ta tab'e baki Rungume juna sukayi da Asmy suna murnar ganin juna kafin Su wuce gidansu Inda Zarah take da gudu Suka Rungume juna suna Daukin ganin Juna Sosai Zarah ta d'an wartsake Dan tayi murnar ganin kawar tata sosai aka karrama Chuchu a gidansu Asmy fiye da tunanin mai karatu da dare yayi ma anan suka kwana Dan Zarah batason zuwa gidan su taro ya fara yawa washegari gidansu Zarah suka wuce sakamakon yawan nemanta da dangin babanta suke d'akin Zarah suka yada zango sosai Zarah ta nunawa Chuchu taji dad'in gudummawar jakunkunan da akayi gudummawar Ammy kuwa kin amsa tayi ba yanda Chuchu batayi da itaba amma taki amsa tace hidimar tayi yawa ganin jayayyar tasu tayi yawa ya sanya Chuchu Maida kudin jaka da niyyar ranar da za akaita ta had'a mata dasu ....Mama Rabi ce Gaban malamin ta (nikam nace boka dai)Cikin tashin hankali ta ce "Malam baki na da naka kace Auren nan Babu shi bazaiyu ba akwai Babban al'amarin dazai ruguza Auren Kace basainasa anyi komai ba Amma har yanzu banga Alamun lalacewar Auren nan ba har ana jibi d'aurin Aure hankalina fa a matuk'ar tashe yake Malam" buga kasa bokan yayi ya ce "Kina da gaggawa a kowani al'amari rabi na buga na buga amma amsar d'aya ce Auren nan babu shi Leko ki gani da idanunki " Lek'awa cikin kwaryar Rabi tayi ta ce "Malam ban fahimta ba " Da yatsa ya nuna mata ya ce "Kinga wancen na nesa da Hasken nan guda biyu Wanda ya fad'i d'innan" tace Eh "To shine mijin da ake shirin daura Auren ta Riga tayi masa nisa nesa ba kusa ba Babu Aure tsakaninsu" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "To Malam hasken nan fa guda biyu Dana gani hannayensu rik'e Dana juna" Itace tare da Abokin rayuwarta tun sanda kikaban aikin nan Dana buga haka nake ganinsu Saidai naga Haske amma fuskokinsu sunki bayyanuwa "Cikin tsananin tashin hankali ta ce" Malam abokin rayuwarta kuma to meyasa Sukaki bayyanuwa sai Haske"Saboda suna da tsananin ibada da addu'a ko tsafi mutum yake tofa ina tabbatar maki bazasu tab'a Tab'uwa ba biyun nan ba kinsan ba irin aikin da ban maki ba kinsan yanda aiki na yake kamar yankan wuk'a to wannan Biyun bani da k'arfin ikon da zan iya musu asiri saboda babu Aljanin dazai iya tunkarar su yin kokarin hakan ma zai iya jawo mana asara babba Saidai a iya binciken da nayi su biyun suna da tsananin Kusanci da junansu sannan dukansu Haskene a cikin rayuwar kowannensu musamman ita Yarinyar da haskenta yafi nashi "uwar zufa ce ta ketowa Mama Rabi Cikin tashin hankali ta ce " Malam kace Haske ne su Duka biyun"Wannan maganar haka take kuma duk Inda kikaje haka za a fad'a maki"To Malam bazaiyu a raba su ba dan tun yanzu hankalina ya fara tashi aiduk Inda Haske yake alkhairi ne Taya za ayi Ace Zarah Haske ce kuma Shidinma ya zama Haske"Dariya yayi ya ce "Kina da tsananin hassada Rabi yanzu ki fad'a abunda ya kawoki " Goge uwar zufar data keto mata tayi ta ce "Malam Auren nan bana son yayu so nake ayi aikin da zai ji baya kaunarta ya tsaneta bazai iya Aurenta ba Wanda da kanshi zaizo ya furta hakan" Yana buga kasa irin tasu ta y'an tsubbu ya ce "Wannan mai sauki ne saboda yaron bashi da wani karfin ibada sosai A yanzu ma za a iya Gamawa dashi amma ina Kara tunasar dake kinyi gaggawa zaki k'ara daukawa kanki zunubi ne a banza Bayan Abun daman bazaiyu ba Auren nan babushi na fad'a maki tun farkon zuwanki da maganar nan" eh Malam nidai ayi aikin hankalina zaifi kwanciya"Dubu Biyar din da saida ta sayar da fantekun ta na Aure ta bashi da niyyar idan Aiki yaci zata cika masa sauran "......yau ta kama Juma'a kuma yaune Ranar da za a fara Event din bikin Wanda yau walima kawai za ayi tunda Zarah ta tashi yau ta tashi da zazzabi mai zafin gaske da ciwon kai ga tashin zuciya Chuchu da Asmy kadai suka sani basu fad'awa kowa ba har Wajen 12:PM tayi Tana kwance jikin Chuchu jikinta yayi zafi rauu cike da damuwa Chuchu